KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana tsaye yana mamakin karfin hali na Salma,ta gama rainashi,ransa ne ya baci sosai Sabo da Na'im akwai son a girmamashi,cikin wata murya me nuna zallan bacin rai yace get out,lv My room now, kin fita tayi sai ma cewa tayi ba inda zanje sabo da gani take Raheel ne,
Mikewa yayi nan take ya daureta da Mari me matukar zafi da gigita dan Adam,da Sauri ta dafe kumatu yace fitar min a room kar ki kira shiga harkata a gidan nan as from today ko magana karki kara yi min,tsawa ya buga mata Out i said,sum sum tayi waje harda rufe masa room sadaf,salin Alin ta koma room din da aka bata ta shiga kwara amai na laulayi a toilet,rarrafawa tayi ta fada saman Bed kowa yayi sallah banda Salma,haka tayi baccinta shar ba abinda ya dameta.

Washe gari kuwa bata farka bama sai 10am ba abinda ya dameta da sallah,hakan ma Mummy ce ta shigo ta tashe ta tare da cewa hope dai kinyi sallah?tace ai tun asuba bana makara.brush kawai tayi kanta ba dankwali rigar baccin da Aisha ta kawo mata iya gwiwa me siririn Hannu itace kadai a jikinta sai pant,rigar silk ce me santsi haka tana tahamma ta fito har main Palo tana tangadin bacci kamar yar maye,idonta kuma a rufe haka ta karasa wajen dining kowa yana zaune ba wanda ta kula kawai plate ta ja ta ebi duk abinda take so ta juya tayi hanyar Bedroom nata gashi duk ya barbaza ya rufe mata fuska har tsakiyar bayanta,
Na’im dake zaune Ido ya zuba mata ya dauke kai irin fushi yake yi da ita gaba suke da juna.

Irfan Ya Mike da niyyar Binta ya dawo da ita Mummy tace zauna ban son shishigi fa,Hunaif yace da kin bari yaji ko lafiya take,Na’im ya wulla masa Harara,Aisha bata ce musu komai ba abincinta take ci kawai.
Salma na shiga daki ta cinye abincinta tas ta fada wanka ta fito bata canja kaya ba perfume ta shafa kawai ta zura rigar bacccinta tare da dannawa kofarta key, kawai aljanunta suka tashi ta fara chines a dakinta ita daya ba ji ba gani,ana jinta tana ta yi tun suna tunanin zata daina suka ji abu yaci tura,Zumbur Na’im ya Mike shima nasa so suke su tashi muddin yaje wajenta amma da sauri ya kwashi alluran bacci ya haura dakin Salma,gaba daya suka biyo bayansa,zuwansa jikin kofar kenan ya fadi a wajen yayi sharaf dashi idonsa ya juye kamar me suma,Mummy da Irfan suka rude su basu taba Sanin Na’im yana da Aljanu ba sai yau,ashe har tashi suna yi,da Sauri suka rufar masa da karatun Qurani sai gashi ya farfado ya tashi fes yana zare Ido,tare da rike kansa dake Sara masa,Allah Sarki duniya Salma bata da gata ita tuntuni takeyi babu wanda yaje da niyyar yi mata addua ta samu sauki Amma ga Na’im me gata yan Uwa duk sun rude anyi masa yaji sauki,
Na’im ya dan jima yana hutawa sannan ya mike ya murda handle din Salma gam gam a rufe,ya buga bugun duniya taki budewa yanzu ba chines take ba wani gurnani takeyi wanda nan take da Mummy,Aisha,Hunaif suka zura da gudu dakunansu tare da danna key su boye ciki wai tsoro,Irfan da Na’im ne kadai ke kokarin budewa,Spear keys Irfan ya kwaso suka dinga gwadawa har suka samu na kofar Salma suka bude,Allah Sarki Duk taji rauni a hannaye da kafafunta wajen ya kwailaye waje waje duk suna fitar da jini,tana kasan tiles gefen goshinta ya fashe sosai jini na zuba,harshenta ma ya fashe bakinta jini sosai,

Tausayinta ya kama Irfan da Na'im sai lokacin su Mummy suka dawo suka ga yanda Salma ta koma sai da suka firgita ta basu tausayi matuka,nan ma haka Mummy tace to mu hadu muyi mata yanda mukayiwa Na'im haka suka rufar mata har Na'im sannan Allah yasa bacci ya dauketa ta samu lfy,Alluran Na'im yayi mata sannan Masu aiki suka gyara bedroom din fes da gidan gaba daya,Irfan Da Na'im kowannensu ya wuce wurin aiki,Mummy ma ta tafi wajen Dada ita da Aisha,Salma kadai ke bacci cikin gidan sai ma'aikata da matakan tsaro ko ina.

Abuwa me aiki ce ke yawan leka Salma tana duba lafiyarta yayin da Nurse tazo tayi mata dressing ciwon da tajiwa kanta Doctor Me Imani ne ya turota.

Na'im sam kasa aikin yayi yau kuma yana Embassy sharp sharp yayi abinda zai iya 2pm ya dawo gida,bedroom nasa ya shiga wanka yayi ya fito cikin Jallabiya fara me shegen kyau kamar balarabe haka ya fito kamshinsa na watsuwa, masu aiki ya tambaya ko Salma taci abinci?,suka ce ai bata tashi ba ma,
A hankali ya murda kofarta ya shiga ciki da Sallama, karar ruwa yaji a toilet kuma bata saman Bed din alamar wanka takeyi ta tashi,Kwanciya yayi sosai saman Bed din,minti kadan sai gata ta fito sanye da Hijab kato har kasa bata daura komai ba sai hijab ne a jikinta,ko kallonsa bata yi ba ta dauki Bodycream dinta a Cikin hijab ta shafa abinta yana kallonta yana dauke kai kamar munafuki.

kayan jiya data cire ta dakko zata sa ya Mike tare da fisge su ya hada har Night wear data cire ya fice dasu,part dinsa ya shiga ya kwaso mata wasu kayan ya kawo mata ba magana ta karba ta shirya ciki lace riga da skert tasha kyau kamar sarauniya,abinci yace me zaki ci? Hawaye ne ya zubo mata sharr tace na koshi,tausayinta yaji yace am so sorry for yestersay ok? Sai lokacin ta kalleshi tare da sakin murmushi me tsada wanda ke gigita mazaje,dimple dinta ya loba tace na hakura ai dama ba fushi nayi ba,kawai kace ne kar na kara kulaka jiya shi yasa naji haushi,yanzu na kulaka?ta kara tambaya,yeah kiyi ta kulani kullum kullum dariyar Jin dadi tayi tace to,ashe kina iya fushi haka? Ae aini duk nafi iya fushi idan baka kulani sai na koma kububuwa ma,ko na koma tolo tolo,dariya Na’im yayi tare da cewa kefa kana da shirme mene wannan Tolo Tolo oya muje dining to ki Zaba abinda zakana ci,a dining taci abinda take so sannan yace tazo suyi game,Ya kunna musu kowa ya rike Handle suna PS abin ya bashi mamaki yanda ta iya sosai bugawa,yace wannan ma Raheel ne yana
Dinga koya miki?tace yes tana danna handle nata suna ta dariya da Surutu sun cika palon da hayaniya,haka Irfan Ya iskesu shima da sauri yazo suka buga da Salma ta cinyeshi tas,Har tafawa sukeyi da Na’im idan ta cinye Irfan,Hunaif ma yace sai ya cinyeta rainasu tayi ana farawa ta cinyeshi da kansa ya gudu,Irfan ta kalla ta kalli Na’im tace kuna kama,sannan taci gaba da cewa baza ka daina abinda kake ba ko sai Allah ya konaka?Irfan yace me nayi kuma munafuka?yau Bilkusu me kukayi a Hotel dazu?kunya ta kama Irfan,yace pls ke aljana ce wai? Baki ta cuno ni ba ita bace amma ai naga Bilkisu yar gidan Gomnan Kwara state ko ba haka ba? To ki rufa min asiri karki fadawa Mummy kinji,to kayi kokari ka daina idan ba haka ba wlh a gabanta zan fada mata,Na’im yana jinsu yace Irfan kayi asararren na banza Banza ne
halinka,(Irfan kayi asarar Halinka na banza ne).

Irfan yace uhm amma ai Bana Shan alcohol ni,Na'im ya hade rai ya Mike ya bar palon,Irfan yace sai ki dage ki dinga Sallah sannan sai kiyiwa wani Wa'azi ya Mike fuuu ya wuce Bedroom.

 Kwanciya tayi a sofa tana kallon American film na turawa kuma na love,tana kallo suka fara Romancing juna har Sex Salma ta rumtse Ido tace da gani za a ji dadi a  wannan Harka bari muyi aure da Raheel,hade rai Na'im yayi domin yana jinta ya sakko daga samansa sharewa yayi kamar bai ji komai ba,key din mota ya dauka zai fita tace nazo muje? Hospital fa zanje cewar sa,ae naji zan bika pls,ok dakko mayafi muje,kalar kayan ta dauko ta bishi suka fita tare,yana Driving tana ta faman Surutu,ko da suka je Office tana saman Table a zaune sai jagwalgwala masa takardu takeyi,dukkan masu ganin Doctor me Imani tunaninsu kanwarsa ce tazo yau, shagwaba take ta yi ta hana ayi aikin ma,ita wai sai an tafi yawo.

  Hashim da Matarsa Maimuna kullum a fada suke a tsakaninsu kai kara har Hashim ya gaji ko me yayi mata sai ta fito tsakar gida wajen matan gidan Maimuna ta kwashe ta fadawa matan gida ayi ta shewa,suma sauran mata duk sanda mijinta ya kwanta dasu haka suke kwashewa su fada a  junansu,
Maimuna ce zaune cikin dabar matan gidan tace Sakina kin San jiya Gogan nawa kwana yayi yana kuka da ihu ai maganin nan yayi,ke kuka fa wiwi wai shi mutuwa zaiyi ma idan bani, sai ya tafi Bahar Maliya a kasa sannan ya tsunduma ciki,matan gidan suka rafka shewa heeeee ayyiriri,matar Shehu tace shege yaji harkoki,kin San ranar dana Sha nawa Shehu ko masallaci kasa zuwa yayi,yara suna bacci zasu je makaranta ina so  naje wajensu na gyara su amma Shehu yace Bai San zance ba,ke fada karce ni da Malam Musa cewar matar Malam Musa itama tace ai ranar ban taba Sanin haka Malam yake ba sai ranar,nace Malam Almajirai sun fito karatu fa yace dan Ubansu su shekara da jira bazan je ba,ke ni daga yau in kika ce  na daina koya musu ma zan bari,in banda takurani da akeyi me akeyi,nan ma Suka sheke da dariya Maimuna yanda suke zubar da mutuncinsu kamar ba suraka da suraka ba ko wacce bata kunyar ko wacce girma da mutunci babu,Maimuna ta San me uban Hashim keyi haka itama uwar Hashim tasan me danta keyi,Allah shirya haka ake samun wasu da dama suruka tana batsa gaban matar danta sosai,dukkan matan gidan sinkai su goma haka suke wannan iya shege.

Mummy da taje gidan Dada wani malami me yaki da Aljanu suka je wajensa can wani kauyen Kebbi takanas suka daukoshi yayiwa Na'im maganin Aljanu,
Na'im ba masifar da baiyi ba amma haka aka dinga masa magani kala kala har aka samu Aljanin yayi magana shine dai Raheel wanda ke jikin Salma cikin nasara Raheel yaji azabar ayar Allah ya bar jikin Na'im gaba daya dama ba wani shigarsa yayi ba zuwa jikinsa yakeyi.

Suffarsa yayi amfani da ita yake zuwa wajen Salma zance,sai yanzu su Mummy dukkansu suka gane zancen Salma Ashe yarinya da gaskiyarta Raheel ke zuwa mata a suffar Na’im.
Maimakon Su Dada su hada da Salma suyi mata magani itama tsabar son kai da Salma kuma ita bata da gata basuyi ma zancenta ba iya Na’im kawai suka yiwa ya warke tsab,Salma tana nan da cikinta sai girma yakeyi tana Shan wahala.

 Irfan ne ma yayiwa Momma dinsu maganar ayiwa Salma ma amma ta share zancen ma Sam.

Malami ya koma gida cike da makudan kudade yana murna,
Na’im ya warke yanzu mace ko wacce ba sai Salma ba zata iya tabashi a zauna lfy kome zaiyi bashi da matsala,Mummy bata San wannan magani ba gata tayiwa Na’im ba domin Raheel kariya yake bashi sabo da zai iya Zama fasiki,sha’awarsa dole sai da mace kusa dashi, taimaka masa yakeyi shi yasa duk masifar son iskancin Na’im da kuma son ya hole Raheel ne yayi Kane Kane ya hana hakan sabo da Salman sa,idan da Mummy sunyi hakuri akwai lokacin da Raheel ya ibama kansa dole zai bar jikin Salma da Raheel,sai gashi rashin sani yafi dare duhu har Mummy suna nuna son kai nasu kadai suka sani shi zasuyi wa magani.
Tunda sukayiwa Na’im magani kullum yake jajibo yan mata Allah ma yasa yana da tsoron Allah da kyankyami iya Romancing kawai yakeyi amma baya yi a gaban Salma bama yaso ta sani,kawai dai tana ganinsa cikin yan mata iri iri abinda ke damun Salma yanzu kenan kishin Na’im takeyi kamar ta kashe wata haka take ji dannewa take dan yi.
A gaban Mummy yake kawo mata su yini a gidan amma sai tace just normal frnds ne bata San me sukeyi ba har ga Allah,shi kuwa Irfan sabo da tona masa asiri da Salma keyi ya rage halayensa sai jefi jefi,Aisha kuwa tana nan yanzu ma take ganiyar shaye shaye da lesbian,Hunaif sai Club kullum,sabo da Dada ta hana su komawa turai sai dai da yawo,yanzu Private university sukeyi a Abuja ta masu kudi.

 Kamar kullum yau Weekend Na'im yana gida a part dinsa,Sha'awa ta motsa masa ya kwankwadi giya da yawa amma baiyi bacci ba,Ya rasa inda zaisa kansa,wata frnd dinsa Balarabiya da suke aiki a Embassy tana mugun sonsa ta hadu,kiranta yayi a waya tazo ta dan taimaka masa ya samu sauki,Dama Balarabiya Nadiyya abinda take jira kenan ko a kirjin Na'im ta kwanta,20mnt sai gata kuwa ta Parker da arniyar motarta,Lokacin Salma na Palo ta cakare cikin doguwar Riga fitted,ko wacce sura ta bayyana,Mummy da dukkan yan gidan suna Palo suna hira cikin harshen Turanci,Mummy tana musu fada hausa zasuyi dole.

Kwas kwas Nadiyya ta shigo tasha kyau kamar a saceta,takalminta cokalelen gaske,da Ladabi suka gaisa da yan gidan,turai ta ratsa su kawai tace Na'im yana ciki?Suka ce yana part nasa taje,Mummy tace Salma rakata Part dinsa abokiyar aikinsa,Salma ta hade rai kamar an Aiko mata da mutuwa ta wuce gaba,Nadiyya na binta a baya har hadadden part din Na'im,can kuma su Mummy ko a jikinsu hirarsu kawai suke ma.

 Na'im yana jin Knocking ya mike daga shi sai singlet da nicker,bude kofa yayi fuska dai ba rahma,kawai Salma ta bangajeshi ta wuce dakin kamar nata,tace bakuwa na kawo ma ta fada saman Bed din tayi kwanciyarta tace yi Sauri kuyi hirarku zan fita da ita,
Cikin Hausarsa da ba wani kwarewa yayi ba yace Mari kina son karba ne ko? Bana sho na iskanci,u knw me Better sheni iya mareki ko na Maki duka duka da yawa( kina son na mareki ko?kin sanni sosai zan iya dukanki sosai bana son Iskanci fa)

Baki Salma ta tabe tace ba inda zanje sai kun gama,Nadiyya kuma bata jin Hausa daga turanci sai larabci,harara ta zabgawa Salma tana tambayar Na’im me take nufi? Na’im yace ai kanwarsa ce bata so ayi having Sex shi yasa,Nadiyya ta gallawa Salma harara tace hey u better lv ths room before i give u a dirty slap.

Kawai sai Nadiyya ta shige jikin Na'im tare da rungumeshi jikinta na rawa har tafi Na'im jaraba,Salma bakin ciki ya kamata kishi ya taso mata bata san sanda taje ta fincike Nadiyya daga jikin Na'im ba tare da jefar da ita kasa ta fadi tim gefe,wuyansa ta Shaka nan take Ashe aljanunta tuni sun tashi ta koma ta cafki Nadiyya ta fara dukanta,Na'im yayi Korari ya raba fadan Amma karfin Aljanu ne da Salma ya kasa haka tayiwa Nadiyya lilis,Su Mummy suka shigo,Mummy tace yau naga yar iskar yarinya jimin yarinya kamar gidan ubanta,daga cin arziki,mutum bakuwa ma Baza ki bari suyi harkar aikinsu ba,N Nadiyya da kyar ta lallaba ta fece daga gidan tana tsinewa Salma tace kuma daga yau ba ita ba Na'im ya jawota gidansu anyi mata duka.
Salma na aljanunta Mummy na masifa,sai da Na'im yace why Momma? Kina kallo nata yana abu ba lafiya kina fada fada aka? Why ku daina bana so ba kyau,sai lokacin Mommy tayi shuru tabbas bata kyauta ba, dan Adam ajizine ,  addua tayiwa Salma da kanta har taji sauki ta fara bacci,Na'im ya daura ta saman Bed nasa da Katon cikinta da kullum girma yake yi.

  Salma sai bacci take Sha abinta Na'im ya sata gaba sai kallonta yakeyi sai da ya gaji ya watsa ruwa ya fito ba ruwansa ya haura saman Bed dinsa bacci ya kwashe shi shima.
Salma tana farkawa ta hangoshi kusa da ita gefe daya,murmushi tayi yau kuma ta tashi fes cikin nishadi sakamakon cikin da ta duba taga babu shi a jikinta ko daya ya bace,sabo da murna ta fara tashin Na'im tare da daddagewa ta dana masa duka a gadon Bayansa,firgit ya bude Ido cike da bacci,tace ana ga yaki kana ga Kura duba cikina,kalli ya bace babu Raheel ya dauki abinsa.

Godiya Dubu masu Sharhi kuna birgeni,kuna kara min karfin gwiwa
Sosai.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????

       51-55

Official

By
AsmaBaffa

AsmaBaffa fans club
Hause of Hausa Novels
Taskar Fiddausi sodangi.
Yan wannan Gps ina matukar jinjina muku da Sharhi ba yankewa kuna kara min karfin gwiwa godiya nake.

Surayyahrms gp kuma ina godiya kuna gyara halayenku????

Sauran gps ma ina ganin masu Sharhi da tnx na gode sosai,sai gps wanda Bana cikinsa kuma suna Sharhi na gode sosai fans a ko ina kuke ina miko gaisuwa.






   Mamaki ya kama Na'im wannan wanne ciki ne gaba daya basu 1mnth da haduwa da Salma ba amma har ya girma ya bace abinsa babu alamarsa,yana tunani can tasa hannu biyu ta girgiza fuskarsa tare da jawo masa kumatu wai kayi magana mana ka tsaya kallona,hannunta ya cire a hankali,yaja tsaki cikin hausarsa yace sai ana bacci ne kuma sai kina duka na mutum,ciki is ur own Business zai kara baka wani wani soon.
 Da murna Salma ta Mike tsaye a saman Bed din,harara ya zuba mata,sauko mini from my Bed zakina zowa a taka min Bedsheet with ur dirty legs.
 Salma dadi yasa ko sauraren Na'im bata yi sai tsalle da tayi ta Sakko kamar abin arziki yana komawa tare da kwanciyarsa again yana kallon sama ya lumshe ido iya karfinta tasa hannaye ta riko kafarsa daya tana kokarin jawoshi kasa tana ta kici kici ta kasa,ta lankwasa ta can ta lankwasota nan,kallonta yake yanda take ta fama tare da Surutu tana dariya ai sai ka sakko kasa ba kai ba bacci dama yamma tayi,
Dariya ma take bashi,kawai sai ta maida kafarsa ta koma speaker kamar mawakiya ta kwalla da karfi ba ciki.........ya tafi....ehhhhhhhh......jama'ar Abuja birnin tarayya kowa ya sheda na haihuuuuu........ehhhhhhho........gaba daya su Irfan dasu Mummy tare da duk wanda ke aiki a gidan sai da ya jiyo siririyar muryar Salma me zaki,tunanin kowa aljanunta ne suka tashi,su Mummy suka taho da gudu part din Na'im,Salma najin tafiya ta saki kafar Na'im ta koma can saman Sofa da sauri ta kwanta tayi baccin karya,suna shigowa suka hango Na'im saman Bed idonsa bude sai murmushi yake zubawa,Salma tana can Sofa tana bacci abinta ba Susan baccin karya take ba,

Mummy tace kai ina na ji muryar Salma ko dai aljanunta a gidan suka watsu? Na’im ba karya ba boye boye shi dole sai ya fadi gaskiya da hausar tasa yace Bacci nata na karyane,anan tanayin bacci nata ya nuna kusa Dashi,ciki nata babu yanju,thts why tana murna tana iho now.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button