KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Salma da Na'im soyayya sai abinda yaci uban da,kullum Karuwa take a zukatansu kamar su hadiye juna, Malam Magaji ya siyawa Na'im waya me kyau yar dubu ashirin Tecno sabuwa dal,suka siyi sabon layi yasa,nan Salma ta karbo wayar Rahina suka tura hotunansu na Sallar taushe,Kullum sai sun dauki hotuna kamar hauka a wayar nan duk wanka sai sunyi selfie,Umma da Malam tun suna shiga har sun daina ana yin hoton dasu,har video suke daukan kansu idan sun fita yawo a garin,Yauma Umma ta aikesu a siyo mata Kubewa danya da dankalin Hausa,sun fita sai hira sukeyi suna tafka muhawara akan kalmar Soyayya da kauna,Salma tace na fika iya yaren nan fa So shine Love fa,Kauna kuma fa? Yace kauna...kauna ya tafi tunani ya kasa tunawa,Salma tace ahaf shine dai so,sanda kayi min kiss din nan jiya kasan sunansa?to soyayya mukayi fa,Na'im yace hakane soyayya?ke baki santa ba dalla,ai so shine soyayya ake soyawa,Salma ta langabe kai tace ohhh...na gane a kasko ko?yace kwarai ke baki ganewa ne har yau,tace to ai gwara da ka ganar dani kaga yanzu na gane,Ko dai mu tambayi Rahina? Na'im yace nop komai sai mun tambaya tunda muna ganewa mu daina tambayar kowa tace to.
Tunda Na'im yake bai taba zagi ba na ashar amma a kauyen nan ya iyata,daga shi har Salma basu san zagine ko ba zagi bane su Kalmar ma dariya take basu,sai suyi ta narkawa junansu ita suna video a waya,Salma ta daga waya sama yace Dan bura Uba shege suka kyalkyale da dariya,Salma ma ta fada masa,idan Umma ta aikesu har gajiya take da jira Sabo da hira da sukeyi da jarabar daukan hoto da video.
Suna dawowa Umma ta rufesu da fada tace daga yau na daina aikenku tare ba inda Dayanku zaibi daya,ya Isa na gama abinci Amma kuna can kuna daukan hoton Banza da wofi.

Saida suka bawa Umma hakuri ta daina musu masifa.

Tunda Na’im yace Salma zata jirashi a zaure yau kimanin 3days kenan basuyi komai ba akan Malam ya musu aure,waya ta dauke musu hankali sun manta da zancen nasu,Na’im garin danne danne ya gano yanda ake searching abu a Google nan ma Google yaga ta kansa shi da Salma duk kudin Malam suke karbewa suna Sa kati suyi ta searching Words na banza da wofi.
Malam Magaji ne yace ko su daina ko Ya kwace wayar shike nan aka samu salama basa dannawa sai jefi jefi,Malam yaga Sabo da waya ko addininsu yaja baya kawai ya kwace wayar ya kashe tare da boyeta yace su zauna haka tunda ba a musu abin arziki,Yanzu ba waya sai radio FM da Am da suke jarabar ji kowanne shiri ji sukeyi kullum radio sai za ayi bacci ake kashewa nan ma sun damu Malam ko wanne shiri sun san da zamansa musamman shirin soyayya ko karatun Novel har na yaki,Da sunji abin mamaki Salma zatace kai kaji dan Allah Me gidana,shima da yaji zaice kinji yi shuru,yauma ana shirin rai dangin goro sunaji ana karantawa ance Farouq ya mike ya zabga mata mari Salma ta dauki radion ta manna ta a bakinta tace ki rama kema mana Sadiya,ta kara fada da karfi,Na’im ya kwace yace baki iya ba basa Jinki muryarki tayi low,nan ya jijjiga Radion tare da cewa Farouq ka kara mata 1slap me cuta ce,Radio shuru sai karatu akeyi Salma ta doka radio da kasa tare da cewa aikin banza dan wulakanci sunki mana magana,Na’im yace gwara da kikayi haka kin birgeni,Saida Umma ta fito sannan ta musu bayanin mene Radio sukayi Zuru suna ji suna mamaki,Salma tace wai a duniya duk ake da wannan abin haka? oh duniya ina zaki damu cewar Na’im.

Sati daya tsakani Malam ya siyo sabuwar mota Gulf 2 zai dinga kai kayan nomansa kasuwa,dama ya iya mota Sabo da ya taba driving Taxi a Abuja.
Nan ya fara koyawa Na'im,Na'im sai yaji kamar ma ya iya tukin Amma ya kasa tunawa,sabo da tun da ya iya kawai sai gani akayi ya iya mota Amma ya kasa tunawa,kwana Uku ya koyi driving na kwararu,Tofa mutanen an samu abin yi,duk ranar da Malam baza su kai kaya kasuwa ba shi da Na'im to sai Na'im su shirya tare da Salma yasata a gaban mota su zaga kauyen da wasu kauyukan.
Yau kuwa Saturday Malam yana gona suka dauki Motar har cikin garin katsina city Salma ta hangame baki wai nan a ina muke haduwa wayyo,ta dinga nune nune kalii laaaa kalli kaga,Shima Na'im abinda yasa ya sani suna dan zuwa watarana da Malam,sukayi parking wani waje falau falau ya rike hannunta suka dinga zaga gari a kafa,suyi can suyi nan kamar yan tasha,Salma da yar doguwar rigarta da mayafi iska na kadata,Na'im kuwa Jallabiyace milk a jikinsa yayi kyau duk inda suka wuce kallon turawa akeyi,musamman Na'im da yake me farin Bature.
Tun Safe suke zaga garin unguwa unguwa wani a mota wani a kafa har wajen magrib,sannan suka fito zasu tafi gida Salma ta hango Bra a rataye suna Lilo tace laaaa kaga siya min wannan a Cikin kayana babu ita,ai kuwa kudin man mota da kudin Masara na Malam da ya bashi gobe za a sha mai dashi,S sauran kuma za ayi harkar Noma wajen Dubu dari,Na'im ya ebo bazai iya kasa siyawa budurwarsa abinda take so ba sai daĆ­ a fasa shan man da noma,Nan yace nawa wannan? Dari bakwai ya siya mata har kala Uku,me saida kaya yace ga panties ma suma ya siya mata har goma,aka kara cewa ga short Wando na mata da Maza ya siya musu kala Uku Uku,Salma taje layin masu glass tace kai a ina ake Sa wannan yace a ido harda gwada mata dan su siya,Na'im yace a siya miki?tace ae ta zabi wani baki wuluk kafcece na manyan Yara ya siya mata tun a wajen ta sa abinta yan kasuwa suka dinga zuki kai kai,Na'im ya hade rai harda masifa yace zasu fasa siya ma,Salma ta hango Atamfa yar 3k da wasu Yadi na Maza tace a siya,Na'im yace ke saura kudin Malam na masara da ya siyar,amma tunda kina so ba matsala nan ya dauko kudin a mota ya siya mata Atamfa har kala Uku tace a siyawa Umma daya,aka siya,tace kaima ga Yadi ka siya sai mu Bada dinki a Cikin birni tunda ance nan birni ne komai me kyau akeyi,Ana taba Yadi kala biyu dubu goma haka ya Cake kudin suka siya,harda siyawa Malam shadda light blue yar dubu tara,layin takalma suka je Na'im ya zabi kala biyu zalla zalla nasa dubu Bakwai bakwai,Salma kala biyu flat masu kyau 2k ko wanne harda na rubber na yawo a Cikin gida da kuma kofar gida,Sarka da dan kunne Silver ya siya mata masu kyau,harda Bangles,a wajen suka ce a ina ake dinki me kyau?Ai ko aka nuna musu shagon dinki dan gaske kusa da wajen,Suka shiga atampopin Salma guda uku harda zabar style aka gwadata tare da daukan size nata,nan take Na'im ya Cake kudin dinki. Umma sukace a kai mata tayi kalar na kauyen,Jikin wajen kuma wajen Maza ne na dinki,Na'im ya shiga ya kai nasa aka gwadashi yace wanda yake tashe ake yayi yanzu banda kato dai dai shi za ayi nan ma ya biya kudi cas aka ce Next wk su dawo su karba.

 Kudin da suka kashewa Malam yau sun kusa dubu dari ko basu kai ba kadan ne,kuma amfanin nomansa ne na masara jiya ya siyar da ita tsautsayi yasa ya bawa Na'im wai ya ajiye a wajensa jibi zai karba to sun kashe kudin tas domin har abinci suka ci a resturant me tsadar gaske da 5k kadai suka dauko hanyar kauyensu.

suna Tafiya dare ya fara Motar ta samu matsala ya gangare gefen hanya kuma har sun kusa karasawa kauyen nasu ma abin haushin,Su basu san me zasu taba jiki ba,Salma tace dan bude murfin motar ka kare min Sabo da mutane zanyi fitsari, hakan ya mata ta tsula fitsarinta ya mika mata ruwa pure water tayi tsarki tace to yanzu ya za muyi ga sanyi wlh kuma dare yayi gashi da dan nisa tsakaninmu da kauyen.Na’im ya dan tura motar da kyar suka shiga can cikin wata hanya da ta nufi daji.
Su dai basu san wani tsoron dare ba,Na’im yace a nan zamu kwana kawai da Safe muje gida,Salma ta fara rawar Sanyi ta tsuguna tare da jingina jikin motar,kusa da ita ya dawo shima yayi yanda tayi,nan kowa ya fara jin shaukin dan uwansa sai tunane tunane sukeyi,kowa nason yaji jikin dan uwansa a jikinsa,Na’im ya matso kadan,itama ta kara matsowa,ya kara matsowa sadaf,itama haka har saida kafadarsu tana gugan juna,Salma ana dan rawar Sanyi shi kuwa karkarin sha’awa yake,hannu ya dan sadado itama ta miko masa da Sauri suka rike kam dama jiran kadan sukeyi.
Sai wasa da hannun juna suke kowa yayi shuru yana sake sake,can Salma ta jiyo zatayi magana shima tunaninsu yazo daya ya juyo,lips nasu saitin juna,a hankali suka dinga matsawa da fuskarsu lips dinsu yana gogan na juna suka hadeshi wuri daya suka fara tsotsar lips din juna da Zafi zafi, tuni Salma ta Fara Mutsu mutsu tare da zame hannunta ta daura su saman wuyan Na’im tare da sakalosu ta shige jikinsa tsam ta rungumeshi kam,shima hannayensa yasa tare da kara manneta a jikinsa,suna tayi ba ji ba gani,da kyar Salma ta tuna da fadan Malam Magaji ta zame jikinta,Na’im ya kasa magana domin ya kai kololuwa da kyar ya lashi lips nasa na kasa yana cije shi, yace Need more pls,Salma ta make kafada ka bari dai ayi mana aure kaji,Na’im ya mike muje gida a kafa mu fada masa wlh,sai yanzu aka tuno da auren? Salma ta furta,tsaki yaja kizo muje mana Ayi mana auren,Salma tayi dariya tace kalli nisa fa kafin muje Dodo ya kamamu,jin tace Dodo ya Tsorata domin Na’im mugun tsoron Dodo yake yace ni kin bani tsoro Allah,mu gudu cikin mota mu kulle sai muyi bacci ciki.
Bayan motar suka fada da gudu a tsorace nan suka danna lock ai sun tsira mota na cikin duhu kamar daki suke,Salma ta kwanta,yace to ni fa a ina zan kwanta kuma? Tace ga Dodo nan ta Window da Sauri ya fado kanta da kyar tana nishi tasa ya dagata tace to kai kwanta tun kafin Dodo yazo ba ruwana,ta dan mike a motar ya kwanta ya mike sosai kafafunsa ma sai kasa ya sauke tsayinsa motar tayi masa kadan,Salma tana tsugune kasan motar sai nishin wahala take,Na’im yace baza ki zauna ba sai wani abu ya cijeki a kasan motar ko kunama,da Sauri ta mike har tana bigewa tunda baki da nauyi to kwanta a samana,Salma tace tab naki,taki kwanciya har yayi baccin karya tunaninta bacci yayi tsoro ya kamata tace kai tashi mana banyi bacci ba zakayi tsoro nakeji fa,ya bude ido ta fara gyangyadi gefen kafarsa,ya bigeta da kafar tashi só kike Dodo yazo,ta bude ido da kyar bacci takeji sosai bata kulashi ba idonta rufe cikin mayenta na bacci tace muyi baccinmu tayi kwanciyarta a samansa tayi balance harda gyara kwanciya ma abinta,abinda Na’im ke jira dama kenan,sai ya rungumeta bacci ya tafi dasu me dadin gaske, jefi jefi mutane suna wucewa amma ganin mota suke tunanin ko mugayen mutanene kowa da gudu yake karasawa cikin kauyen ba wanda yayi tunanin zuwa jikin motar ko a tambaya lfy?

da asuba da wuri suka farka har gari ya danyi shaaaa,Salma taki tashi tunaninta a Bed take,ta gyara kwanciya tare da tura kanta can cikin wuyan Na’im,Na’im a ransa yace sanyi ma takeji ya zame gyalenta ya rufa mata,ta dan dade har gari yayi haske kadan ya fara tashinta,Salma ki tashi haka mana,mikewa zaune yayi da ita a jikinsa yasan baza ta tashi ta dadi ba,Da kyar ta bude ido tare da cewa wayyo Umma a ina muke,ke tashi min a jiki mana, jikina zafi yake min fa,Salma ta tuno tare fa da Na’im suke a mota,tace gari ya waye ne? Jikinka yafi katifa dadi Allah,Na’im harda murmushin jin dadi yace ke naki ai yafi auduga laushi da dadi, komawa tayi saman kujerar ta kwanta tare da ci gaba da baccinta,shi kuwa Da pure water yayi alwala ya dauki Sallayar motar yayi Sallah a wajen tare da addua Allah yasa Malam ya aura masa Salma kuma ya ganar dashi shi waye shi,Saida ya idar Sannan Salma ta tashi da kanta tayi Alwala da Sallah itama adduar iri daya data Na’im,sai tace Kaji dana kwanta a kujera kamar a dutse nake, harda kukan shagwaba wlh jikinka me dadin bacci,dariya ya kyalkyale mata yanda take shagwabar.

rashin wayo har rana ta fito suna wajen a tsaye suna azkhar dinsu suna jiran me zuwa ya taimakesu,Salma uwar cin abinci ta saka masa Kukan shagwaba ita yunwa take ji,ya rasa yanda zaiyi da ita,suna haka sai ga Wata Bus zata wuce ragargajajjiya ta kauyen,nan mutumin ya sansu ya tsaya ya tambaya sukayi masa bayani,nan take ya bude motar dan abu daya ya taba ya tasheta lfy lau yace to suzo su tafi gida,jiya Malam Magaji ya cika gari da addua a masallaci sun baca,godiya sukayi ya tuka su sai gida,Malam Magaji da Umma sai murna sukeyi basu bace ba,Na’im yace mun kashe kudinka duka munyi siyayya,Malam yace ba komai tunda kun dawo lfy ta dukiya me sauki ne,Allah yayi rabonku ne kudin ko mene ma mun godewa Allah da kuka dawo lfy hankalinmu ya tashi,ruwan Zafi Umma ta dafa daya bayan daya sukayi wanka tare da Brush,kafin su shirya an kawo musu Kunun gyada da kosai masu zafi,nan ta dafa musu Indomie da kwai ma suka ci suka koshi kowa ya koma bedroom dinsa sai bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button