KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Jamila tace yo ai ke da sauki akan Abdullahi na idan ya bude bakinsa kamar mushen tsuntsu ya rube hhhhhhhh suka sheke da dariya,Barira tace yanzu a haka da kike yarda yana rike miki hannu?Zahrau tace duk baku san me rubabben baki ba ai doyin baki yana wajen Shamsiyya Mahamudi wacce akayiwa aure rannan kun tuna? Suka ce yeeeee kwarai kuwa Shamsiyyan gidan na Ilalo,Barira tace Shamsiyya me doyin baki dai dana sani?Suka ce ita domin har yau tana da aure Amma bakin nan sukub a rube ba a zuwa kusa da ita ai Uwarta me dambu ta gado itama haka take,gaskiya Na Ilalo Baban Shamsiyya yana hakuri da Uwarta,

Rannan a masallaci yace a tayashi da addua ko zai samu kudin kara aure.

Zainura ta kalli Salma tace ku tsotsi bakinku da kyau ku gaba dayanku yan kamshine Amma mu kam a wannan fanni billahillazi babu mu a ciki Alquran Bazan yi Couse ba Bazan ma yi amfani da wannan darasi ba, domin ina ji ina gani bazan yarda Idan Allah yasa na auri Isyaku ya baje bakinsa cikin nawa ba,Barira tace ke yo ni aka aura min Ashiru ai kafin ya kawo bakin na Suma,

Zahra’u tace ya kuka gano min bakin Audu me kifi cikin na Aishalle hhhhhh suka sheke da dariya,Ubale me Rake fa?wai wai Zainab ta toshe hanci tare da cewa ai gwara na leka Masai na Shaka ya fiye min,nan Su Zainura suka dinga iya shege a gidan nan Salma tana ta dariya, Zainab tace yo yaushe zan Yarda kwakwarar Runguma ta hadani da Gali,Gali kunga Gali matashi yaro amma ya kashe bakinsa ya rube,idan Gali ya miki magana tun daga jikin kofar can to wlh warin bakinsa har nan wajenmu.
Zahra’u tace Indo fa duk kyan Indo fara ga kyau amma ya tashi a banza tana magana zakice Billahillazi anyi Asarar sabulun wanka,luf a jikinta tasha wanka amma baki ba kanta.
Zainura tace to ai wasu masu auren mazansu kuka suke wai ana Saduwa wajen na bashi hhhhhh Jamila tace sai kace Bomb Zainura aji tsoron Allah,Yasin idan karya nake Allah tsine min,Alquranin Allah Ku tambaya, basu tafi ba sai da sukayi Sallar Isha suka kwashi tuwonsu harda Salma sannan suka mata Sallama sukace sai watarana kuma.
Salma tasha hira yau su Zainura sun kusa illata mata ciki da dariya.

Wata biyu kenan da bikin Na'im da Salma,suna ta zuba soyayya amma har yau ba ayi babban iskancin ba,Rahina watan haihuwarta ya kama,Salma suna yawan zuwa gidan,kuma duk taje har gidan Su Zainura daya bayan daya tare da Na'im sunji dadi sosai,suma suna yawan zuwa suyi hira,haka Na'im ya dauketa har Katsina gidan Rukayya suka yini suka dawo,wajen dangin Malam dana Umma duk suna zuwa su gaishesu watarana.

Yau tun Safe Rahina tana asibiti cikin Katsina zata haihu,tasha wahala sai wurin magrib ta haihu lfy danta kato Namiji,washe gari da Safe da wuri aka sallamosu,yan Uwa da abokan arziki ana ta zuwa barka,Salma da Na’im ma da dare suka je suka ga yaro kyakyawa kato.

  Ana gobe Sunan Rahina da dare 8:30pm Salma da Na'im suna kwance Salma ta kira Rahina a waya tace Hajjaju gobe suna wanne suna za a sawa dan Namu? Rahina tace wlh yace ya bani zabi na Zaba duk sunan da nake so,ni kuma wani suna dana taba ji lokacin da naje bikin wata a Kano sunan ne ya birgeni shine nace Insha'allah shi zan sawa dana idan na Haifa,ina son Sunan sosai kalar na Larabawa,Salma tayi dariya tare da cewa ya sunan muji idan da dadi,Rahina tace RAHEEL Salma tayi dariya tace aiko da dadi Allah raya to ya masa Albarka sai gobe zan zo da wuri nan sukayi Sallama ta kashe wayar, saman kirjin Na'im ta kwantar da kanta tana shafa kirjinsa a hankali tace Wai kaji sunan yaron da za a sa gobe? Yace Me? Tace Wai RAHEEL ta rada masa a kunne,tana dariya tace da dadi? Nan take kan Na'im ya dau Zafi ya fara ciwo ya Dafe kan nasa,Salma ta firgita sosai,Na'im ya rike kansa sosai kam ya rufe ido,wurrrrrrr....inda kasan ana tariyo film ya dawo baya haka Na'im yake gani a kansa,ya dade a haka sai da Memory din Na'im ya dawo kaf na baya babu kuma na rayuwarsa wacce yayi a kauyen su Malam.
Zumbur ya Mike tare da saukowa kasa yana kallon kansa yana kallon dakin,Salati ya fara tare da cewa Mummy,Salma ta matso gabansa da mamaki ya tabbatar dai Salmansa ce da yake nema,da karfi yace Salma...yaushe na ganki,ina kika shige ya jawo Salma da take tsaye kamar photo ya rungumeta yana ta murna,a ina muke nan muje gida wurin Mummy,Irfan fa dasu Hunaif? Salma ta fara hawaye tace ni ban gane ba wlh ban sansu ba,baki sansu ba kamar ya? Wai me ya faru dani ne? Salma tace muje wajen Malam da Umma,da Mamaki yace waye kuma malam da Umma ni Mummy nake nema,Salma tace Malam fa baka San Malam ba? Na'im yace ni na sanshi ban sanshi ba,Salma tace Muhd ban son karya,da sauri yace waye kuma Muhd Salma ni nake miki karyar? kalau kike kuwa?Salma tace wlh sunanka Muhd,No..no...kamar baki sanni ba Na'im ne fa,Na'im dinki kin tuna har kike ce min Raheel ne Aljaninki.

Salma ma jin ance Na’im sai kai ya fara Zafi ta fadi kasa wani bacci ya kwasheta,a baccin Memory dinta ya dawo kaf na baya,itama babu na rayuwarsu da Malam da Umma,Na’im yayi shuru yana gefenta ta ja ajiyar zuciya ta farka,tana kar ayi min Allura dan Allah ni ba mahaukaciya bace,a nemo min Na’im dina,jin haka murna ta kama Na’im yace kin tuna ni Salma?Salma ta Mike a rude ta fada kan Na’im tana ta murna tana kankameshi,zo mu tafi gida ina muke nan kamar gidan kauye ne? Na’im ya tabe baki yace bamu San ina ne nan ba,sadaf Sadaf suka dauki kayansu suka fito kamar barayi sai gasu sun gansu a tsakar gida,kasancewar dare baiyi ba Umma tana zaune kusa da Malam suna Jin Radio,sai ga Na’im da Salma suna sanda da akwatunansu,Malam yace ke Salma lfy,Salma ta firgita tace kaji yasan sunana mun shiga uku,ta koma bayan Na’im ta buya,Malam yasha jinin jikinsa ko dai kwakwalwarsu ta dawo dai dai ne,sai Yace Muhd? Sai Na’im yace ni ba sunana Muhd ba Allah,sunana Na’im kuma a Abuja muke da zama ya akayi na ganni a nan?Sato mu kukayi? Murmushin Manya Malam yayi tare da cewa Alhmdllh kuzo Ku zauna muyi magana,Na’im tsoron su Malam yake ji da kyar ya yarda ya matsa can nesa ya tsuguna,nan Malam ya basu labari tun haduwarsu dashi har zamansu dasu,da aurensu,da komai har cewar sun fi shekara tare dasu basu da memory na rayuwarsu,Na’im harda kuka ganin yanda Malam suka rikesu harda aure suka dau nauyinsu,yana so ya tuna wannan Rayuwar tasu da sukayi a kauye,nan take Na’im ya matso kusa dasu Malam tare da basu labarinsa da haduwarsu da Salma,Salma ma ta basu tarihinta kaf,Malam da Umma harda hawaye tare da cewa Ikon Allah kenan kunga duk abinda Allah ya tsara to ko Aljani sai dai kallo,basirarsa kwacewa zatayi sai abinda Allah ya tsara,shi yasa har kullum ake so komai a barwa Allah domin ya Zartar da Ikonsa,yanzu Ku koma wajenku zuwa gobe muyi shiri mu tafi Abuja wajen Iyayenku can Abuja sabo da ayi musu bayani.

Na'im yace yanzu muna da Aure da Salmata? Malam yana dariya yace sosai ma kuwa dan Allah bai baku bane amma da yanzu ma watakil tana da cikinka,Salma ta rufe Ido tana dariya,tare da cewa Umma kuma kun gani yana sona dan Allah?Umma tace ai duk gari ma idan kun fita Ku tambaya zaku Sha labari,har kawaye ne daku a kauyen nan dasu akayi bikin.
Umma ya sunansu? Cewar Na'im Umma tace sai gobe duk zaku gansu ai.

Na’im ya Mike zasu shiga wajensu da kayansu da suka fito dasu ya dade yana kallon kofar wajen ya kama dariya tare da cewa kalli yar kofa ai tayi min kadan sai na duka,Salma ma tana dariya tace kaine baka San kauye ba ni na sani,suna shiga ya leka kitchen ya dinga dariya yace kinga dan kitchen wannan Indomie fa ragowa? Salma tace oho ko dai ni na dafata? Toilet ya leka yace kinji da kamshi ko kece kike gyarawa ne? Salma tace gaskiya gobe zan tambaya naji ko nice ko bani ce ba.

Suna shiga Palo yaga dan palon ya kwanta a kujerar ya latsata yace ikon Allah,Salma ta shiga dakin ta fito da gudu tace kaga waya wlh shigo kaga gadon da girmansa,Na’im ya shiga ciki ya kalli bed din ya kalli Salma yana dariya yace dan Allah na miki Iskanci? Salma tace hhh yo kaji kaima ina zan sani kayi ko bakayi ba,Na’im yace Allah yasa banyi ba yanzu naji dadina idan mun koma gida,Salma tace ai kayi ma kana ji ance fa 2mnths da aurenmu ai kasan ma ka shanye dadinka,Salma ta furta tana rufe ido wai kunya ta manta rashin kunyar da takeyi.
Na’im yace ai ni Doctor ne zo na duba wajen,ta makale kafada tace naki,Na’im ya taso zai riko ta ta fara gudu wai bazai taba mata jiki ba,kwanciya ma tace sai dai ta kwana a Palo saman kujera haka ya kyaleta ta kwana a palo.

Washe gari da safe ya dauki yar wayar yana dubawa ba charge bare ya bincika ciki haka ya jefata a jakar kayansa,yaga faifan DVD na bikinsu bai sani ba duk ya tattara a cikin akwatinsa har  kayan sawar yana dariyar arahar kayan sai dai dinkin size nasa ne,
Album din bikinsu yaki budewa shima kawai duk ya tattara a jaka,Salma ma ta dinga daukan kayan tarihi kaf ta hada wai ko zasu tuna sai su dauko kayan.

Umma yau tea ta kawo musu da kwai Karin safe sunci kuma sabo da tasan maybe baza su tuna suna cin har kosai ba ko kunu.
Bayan sunyi wanka sun shirya tsab,Su Malam ma haka sai Umma tace suje gidan Rahina suyi mata Sallama ta haihu kawar Salma ce,Abubakar abokin Na’im ne basu San gidan ba Sai Umma ce ta Raka su,Mamaki ya kama Salma yanda su Zainura suke ta zuba mata surutu bata sansu ba sam,Rahina ma Salma bata Santa ba,Nan Umma ta tara kaf kawayen Salma a gidan Rahina ta basu labarin komai,suka dinga Mamaki,Umma tace nan gaba zasu dawo idan sun tuna memory nasu,Zainura tace cab kice ke yanzu baki sanni ba,to Allah dawo da Memory dai dai,yo na taba Jin Memory na gogewa kamar wata wayar Salula,Malam da Me gari aka tara mutane kaf wanda suka San Na’im da Salma suma akayi musu bayani kowa sai mamaki jin dama tun a Abuja suna soyayya da Salma,nan gari ya dauka da labari cike da tausayinsu,Me gari yace shi yasa ake so kayi alkhairi ga kowa ba a zabar wanda akewa Alkhairi sabo da baka San wanda zaka yiwa ba.sai gaba ka tsinci abinka.

Nan kunji falalar Haihuwa Fans wani ana haifarsa yake Zama alkhairi ga wasu,gashi Jariri yayi silar warkewar Salma sanadin Sunan da za a sa masa ba sai ta wannan hanya ba akwai matsaloli da dama da Dalilin haihuwar wani ko wata sai matsalar ta warke,wasu iyayen ne zai zama sila etc.
Sai Alkhairi da taimako Fans ba sai anga mutum cikin yanayi me kyau ba ko shiga me kyau za a taimakesu ko ayi masa alkhairi yanzu abinda ke faruwa kenan a kasar nan ko biki kaje sai an ganka da sutura me kyau,shiga me kyau ko yar gidan wane ce ko dan wane ne sai kaga an rasa inda za a Sa mutum ana karramashi,wajen zamansa daban,abincinsa daban har take away na manya daban ne ko ba a sanki ba aka ga yanda ka kece raini sai a dinga baka daraja ta daban,
Sai wanda yayi shigarsa da Allah ya hore masa ba a ta tasa ma. ko mutanen kauye yan uwansu sunzo nan zaka sha kallon yanda ake wulakantasu wlh,ko a birni ne in dai ba masu kudi bane tayi shigarta ta talakawa ko kallonki baza ayi ba,ko kije neman taimako baza a saurareki ba,ko ana ganin kwafta cikin mawuyacin hali wasu ga kudi nan kamar ya kashesu amma kwandala babu me taimaka musu dashi,suna yawo cikin tsumma babu me basu ko kwancen kaya,sai daí ma a daukesu ba komai bane.

kowa yaji Na’im dan Sarki ne,kuma ga aikinsa, Dictor,consilor,Business nan companies birjik, nan fa aka dinga mamaki,Zainura tace Dan Sarkin Kasar waje bama na kasar nan ba cab dole yake me kyau Ashe bature ne,harda cewa Salma idan yana da Kani dan Allah kice ina sonsa wlh zan jirashi na fasa aure zan bijirewa Baffa Alquran in dai zaki mun wannan yakin billahillazi ina jiran dawowarku,Salma da Na’im suka dinga dariyar Zainura,
Zainura ta dage da gaske fa nake Wallahi Allah kunga dai nima ina da kyau gani yar fara,idan naje na goge a can nayi clean,dan Allah me kyau mijin me kyau ka fadawa kaninka yayi masoyiya idan yaki yarda dan Darajar Manzon Allah kayi masa auren dole dani,ka zare masa ido harda gwadawa Na’im yanda zaiyi maganar,Salma da Na’im sai dariya suke,Barira tace mun yafe mu ko Zainuran kadai a samu ta shiga ta dalilinta mazo birni.

Zainab tace wa cab billahillazi ka aura min ko me gadinka ne ina so yafi Samarinmu na sani, Jamila tace ke Zainab Dan Isiyanfa? Tace yo wa yake ta wannan Dan Isyan me kunne kamar kyankyaso hhhh aka sheke da dariya harda Umma tace oh wannan yara da abin dariya kuke.

Zainura ta zaga wajen Malam tace Malam dan Allah na ebo kayana mu tafi tare wlh ina da kudin mota,kaga ko ni zan wakilci kawayen Salma na kara bada sheda gaban iyayen Me kyau,shi Malam har yaran gari sonshi suke Sabo da biye musu yake suyi shirmensu,Malam yagafa maganar Zainura gaskiya ne sun San komai na bikin Na’im da Salma tunda Abubakar an masa haihuwa yana hada hada,Abubakar yana taya su Na’im Murna yanzu sun gano garinsu da komai haka Rahina ma,Malam kuwa yace Zainura taje tayo shiri da ita za a tafi,nan ya fadawa Baban Zainura yace ba matsala,Zainura sabo da zumudi dama tayi wanka yar doguwar rigarta tasa ta Atamfa tayi kyau sabo da ta Dame sama kasa ta bude harda jela a baya,da wasu kayan kala Uku a yar jakar Hanu me dan girma,takalminta na roba dan Dari biyar flat,Su Barira sai murna Zainura zata dawo susha labari domin sai ta gwada musu komai kamar tv,Na’im yace da Nisa Abuja fa yanzu ba Atm a hannuna bare mu hau jirgi ni bana yawo a mota in dai ba a Abj ba a jirgi muke tafiya ko?ya kalli Salma,Malam yace yanzu lalura ce ai,k kayansu gaba daya aka zuba a boot.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button