KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Na'im yace sai dai a baki Room ke kadai dai amma Salma tana da aure taya zaku kwana tare bazai yuwu ba wlh ni kuma fa?
Mummy ta harari Aisha tare da cewa nasan zaki aikata dama kuma wlh sai ta zauna dake,ke Zainura idan tayi miki ki rama ko zaginki Aisha tayi ki rama ko dukanki tayi ki tabbatar kin rama,Zainura tace an gama Mummy wlh zubarwa yarinya hakora zanyi,Aisha tayi mukus da ita,Malam ya kira Baban Zainura yayi masa bayani cikakke yace ba matsala Malam ai mun yarda da kai.
Zainura ta dan bigi Salma ta kalleta tare da yi mata signa da Ido tana kallon kayan abincin wai su kwashe mana su wanke,Salma a hankali tace akwai masu yi,Zainura kowa naji tace mun shigesu haka zamuyi ta yini muna kwana ba motsa jini ba aiki daga wanka sai ci? Ni wlh bazan iya ba na saba da aiki na zauna haka ai sai jikina ya fara ciwo ni dai zan dinga taya yan aiki muna yi tare dasu bazan iya zaman kashe wando ba,Mummy tace ba matsala ai Salma ma tana aiki a gidan nan ta nuna Aisha kinga dai wacce ko cokali bata dauka,Zainura ta kalli Aisha tare da rike baki tace keeeeeeee kiyiwa kanki fada kiyiwa kanki Kiyamullaini ki koyi abin duniya haka za a miki aure Me gida yaji baki iya girki ba wlh koroki zaiyi,Mu yanzu Mummy a kauye baki iya tuwo ba ai kin shiga uku da gori,bakiga wata kawarmu ba Marsiyya abin mamaki bata iya miyar taushe ba ranar Juma'a batayin tuwon shinkafa miyar taushe Juma'a guda aiko mijinta Lawwali ya kai kararta gida aka zaneta aka ce muje mu koya mata,to kema Aisha idan baki iya ba Allah Mummy kisa na koya mata kuma wlh sai na dinga dukanta idan ina koya mata,Dada tayi dariya tace ni dama ke aka barmin muka tafi gidana mukayi zamanmu tare a saki a makaranta,Zainura tace keeeeeeee iya rufa ni ki sayani a nan ma na dan rabe kafin na tafi garinmu,Dada tace da gaske nake fa,Mummy tace Hajiya ki Bari ta gama aikinta da nace idan iyayenta sun baki shike nan ai,Dada tace Allah kaimu.
Malam tuni sun koma wajen da aka saukesu suna hira Dada tana wajensu da Mummy,Zainura tana zaune a Palo ita da Salma sai ga Irfan Ya shigo ya Sha wanka ya kalli Salma yace fatan dai yanzu ana Sallah matar Yaya Na'im, Salma tace kai ka sani an fada ma yanzu da ne? Irfan yace ina Raheel wai?Salma tace ni ban san wani Raheel ba wlh waye? Ganin fa Aljanine kuma idan mutum yana Aljanu idan ya warke baya Sanin me yayi ma sai ya share zancen,Zainura tana zaune sai ga Hunaif ma sun fito da Aisha suna ta faman dariya suna kallon wata katuwar waya,Hunaif Yace Bro muyi game mana mun dade ba muyi ba,Aisha tace zanyi nima,Zainura ta watsa mata harara tare da dauke kai can kasa tace uwar iyayi ba a iya girki ba,Aisha taji ta,Salma ma harda dariya,Irfan suka fara game sosai Zainura tana kallon abin mamaki kuma tana ganewa kafin kace me ta gane yanda ake game din to akwai basira,Aisha bata wani Iya ba cinyeta suke tayi,Sai muryar Zainura suka ji tace zan iya nima a bani abun muyi da wani,Suka sheke mata da dariya,Irfan yace ke ko Aisha bata iya ba sabo da ke ba brain zaki ce ayi dake,Hunaif yace to ko Handle zata iya rikewa ne? Muryar Na'im suka ji yace hey guys ba a haka fa wannan shirme ne idan zakuyi da ita kuyi idan baza ku bata tayi ba mene na mata dariya.
Irfan yafi Saukin kai yace to ke taso muyi na dura miki kaya,kuma baki isa kin daina ba sai an gama komai cin da za ayi miki,Zainura tana dariya tace to,Hunaif ya bata Handle dinsa ita da Irfan,Zainura Uwar basira sai ga Irfan Ya kasa cinta,sai wahala yake Sha,tana ta dariya bata ci ba shima Bai ci ba,suna ta yi,Hunaif ya dinga mamaki da sauran mutanen,Da kyar Irfan yaci daya da zero suna tayi ta farke dayar daya da daya,har game time ya kare 1-1 suka tashi,kuma a haka Irfan yafi kowa iya game,Hunaif yace sai ya cinyeta suka farayi da Zainura ta masa 2-1,Aisha ta karba ta mata 5-3, suna gamawa ta jefar da Handle irin shegiyar nan tare da cewa Ku kiyaye hada kwanyata da taku haka Allah ya yini ni,dukkanku yanzu zan iya yin kalolin muryoyinku tafiyarku da komai naku,ni ba a ja dani ko a kauye,Na'im ya zauna gefen Salma da tayi shuru tana mamakin Zainura da basira ko ita duk zamanta gidan bata iya ko gwada game din ba.
Na'im taji ya kwanta mata a jiki tare da cewa muje Bedroom Ki tayani hira yanzu naga Alama gudu na kikeyi,Salma tace uhm ni bazanje dakinka ba,Zainura tace ke yar Iska wannan karya kike a gabanmu wlh kuke tsotsar juna bakwa kunyar uban kowa har kinfi me kyau maita,wanne iskanci ne bakuyi ba sai yanzu zaki dinga karya,to wlh ba abinda me kyau baiyi dake ba domin mu shaida ne,Irfan ya dinga dariya kamar me yace yawwa Zainura kike ko?gwara ki dinga tona musu asiri wlh,Hunaif ya kalli Zainura yace ke mene tsotse juna Zainura tace kaji yaro kato da kai baka sani ba duk iskancin da samari keyi yanzu,yo kai daga ganinka Alla ai ka dan yiwa mata wani abu,yanzu Ko a kauyenmu su Ubale,Ashiru,Habu,Audu me kifi,Dan Isya me Rake sun San Iskanci bare kai me Jan kunne,Irfan yana dariya ya Kalli Hunaif yace kaga ka jawowa kanka hhhh kuma gaskiya ta fada mene baka yi ba dan Iskanci zaka tambayeta.
Zainura tace wlh duk yaran gidan nan daga Me kyau sai kai Irfan kunfi kowa kirki amma wannan mai fuska kamar tana Mura bata da kirki,shi kuma Hunaif ya fiye iyayi yanyanyanyan ta gwada maganarsa nan ma suna ta dariya,Na’im sai gani akayi bashi ba Salma a palon,Irfan yace Ina Salma da Bro?Zainura ta tabe baki tace wannan ka daina zancensu da kunga abinda suke a kauye Wlh Allah baza kuyi magana ba yan Iska ne na gaske.Irfan yace ke kinga Illarki baki waye ba da na kaiki yawo tunda kina da hira da abin dariya,Zainura ta rike kugu tace koya min ka gani idan ban iya ba yau din nan zan rikide na koma yar birni,Hunaif yace Aisha ce zata koya miki,Salma baza ta koya miki ba wannan mijin nata bazai barta ta samu time naki ba,Aisha tace kuna dai ji Mummy tace ko zaginta nayi ta rama har duka,Zainura tace kuma kin San ni tantiriyar yar duniyace wlh kina min sai na miki ko Mummy batace ba,ke Allah na tuba da dasu Zainab aka taho ai da tuni kina asibiti Alquran ki godewa Allah ni aka kawo nan, Ke fa Aisha na fuskanci gani kike kinfi sarauniyar Ingila wayewa ko? Ke gani kike ba wacce ta kaiki haduwa ko? Aisha tayi fari tace sosai ma,Zainura ta fara dariya tare da cewa Yasin kinji na rantse tun a Tafa da muka tsaya cin abinci naga wacce ta dameki ta shanye,ke tun a Mararrabar Jos tasha naga wacce ta fiki ki daina bata lokacinki haka Salma nan ta mitsitsikeki a komai,tausayi kike bani yasin,ni kaina duk sanda na Zama yar gayu sai na wuceki.
Irfan da Mummy data shugo suka dinga yiwa Aisha dariya tana Jin haushin Zainura.
Da dare ma da Zainura ta shiga zata kwanta Aisha sai bargo ta jefo mata wai ta kwana a kasa tunda bata da mutunci,Zainura ta shareta ta shimfida abinta ta kwanta ta shaki baccinta.
Bangaren Na'im da Salma kuwa tunda ya janyeta Bedroom dinsa Kuka takeyi wai ta tuna Affa da Ummitu sai ta tafi wajensu,ba yanda Na'im baiyi da ita ba taki yarda,shi dan Iskancinsa ma yake so yayi ko kadan ne amma Salma taki yarda sai wani kukan banza takeyi kan su Ummitu da Yan uwan Babanta,shi yasa ta kasa sakin jiki a gidan tunda suka zo,da kyar tayi bacci ya rungumeta shima yayi baccin,washe gari Zainura ta riga kowa tashi tayi brush da wanka ta shirya ta tayi sallah ta fito Palo da sanyin safiya ko haske gari baiyi ba ta zauna tare da sa wata cikin yan aiki kunna mata TV, taga yan aiki suna ta gyare gyare wasu suna kitchen ana shirya girki,ta shige ciki ta karbi mopper akayi aiki da ita aka gama,ta shige kitchen aka karasa girki da ita tana kallon abincin yan gayu,Irfan ya shigo daga Gym ya shiga kitchen dakko fresh milk da ruwa ya hango Zainura an tsege daurin ture kaga tsiya tana yanka Albasa a cikin kwai.
Shi tana birgeshi yanda take wayayyiya bata duhun kai na yan kauye bata tsoron kowa harkarta takeyi kamar yar gidan,Muryarsa taji yace ke da safe har kin fito? Zainura ta washe baki tare da rufe idonta wai kunya ta ganshi da dan wando short da yar riga,tace Laaaa kai ko kunya haka kuke yawo tumbir billahillazi Rahamanu ni bazan kalleka haka ba,Idonta a rufe tace ina kwana,yace lfy lau yana dariya su Kansu yan aikin dariya sukewa Zainura wai bata waye ba,tace mu dai ka fita sai kace Gambo dan Fulani a kauyenmu haka yake yawo aiko kowa dan iska ake ce masa Yasin,Tabe baki Irfan yayi tare da daukan abinda yazo dauka yayi waje yana ganin kauyancin Zainura yayi yawa.
Na'im da Salma sun tashi Na'im yana zuba murmushi yace wai dan Allah baza ki fada min ba nayi Iskanci ko bamuyi ba?Salma tana dariya tace nifa ban gane ba bazan iya ganewa ba,tana kwance ya hau samanta tare da rike hannayen Salma wai sai ya duba wlh ya gani,Salma tana dariya suna ta kokawa suna dariya,ina wayarka ta kauye da faifan CD ka sa mana mu gani mana cewar Salma,ki bari sai Next weekend sai mu saka a Palo gaba daya a kalla me akayi a bikin,Salma tace Allah ya kaimu.
AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????
121-125 126-130
Official
By
AsmaBaffa
ASMABAFFA FANS CLUB wannan page naku ne Ku kadai,love u all.
Na'im yana wa Salma magana amma ko daya da kyar take amsa masa sabo da kunyarsa da takeji,shi mamaki yake kamar ba Salma daya sani ta Raheel ba,wanka ma tayi a part dinsa guduwa tayi Bedroom nata wai kar Mummy ta ganta ta kwana wajen Na'im.
Bayan ya hade cikin suit fara Kal kamar a jikinsa aka dinka,wandon pencil yasha kyau,gaba daya turawan dake Embassy ne zasu zo yi masa murnar bayyana,haka Doctors na hospital nasa,da managers na companies nasu duk sunzo anyi musu masauki a palon Mummy suyi mata murna, Mummy ce ta fito cikin shiga ta Alfarma haka su Irfan ma gaba daya an gaisa sun musu murna,Na'im room din Salma ya shiga ya tadda ta hade cikin wani arnen material nata tana fesa turare, ta mudubi suka hada Ido kafin tayi wani tunani taji ya rungumo hips dinta tare da juyo ta suna facing juna,nan tayi kasa da kanta,Hannu yasa ya dago habarta yana kallonta da mayun idonsa cikin salo ya daura lips dinsa saman nata,tuni ta lumshe ido tare da zura hannayenta ta kankameshi suka fara hot kisses abin ba a magana sai da suka gaji ya saketa suna maida numfashi tare da sakarwa juna murmushi,kunya tasa tayi kasa da kanta tana murza yatsunta tana murmushi,mayen nata kuwa tuni idonsa yayi Jajir da kyar yake daurewa,hannunta ya rike tare da furta let's go mu suke jira sauri suke.
suna fita taga mutane da yawa bakake da farare,suka gaisa cikin harshen turanci suka musu murna,Na’im ya gabatar musu da Salma matarsa ce sunyi mamakin kyanta suna tayashi murna sannan suka tafi wajen aikinsu shima yace idan ya huta zai dawo
Breakfast tuni an shirya shi,Zainura tana can tayi wanka ta gama komai Aisha tana faman kwalliya,Zainura tace dole sai ta bata aron kaya in ba haka ba wlh ta kala mata sharri wajen Mummy,Aisha tace kayana zaki sa na baki na karba na sa again sai dai na bar miki du,Zainura tace ae naji bani din,Nan Aisha tace Mayya tare da bude akwatina ta zabo duk wanda suka mata kadan wasu sun dameta daf ta zubosu wajen kala goma ta watsawa Zainura,Zainura ta kwashe ta zabi wata Atamfa riga da skert ta cika su tab dinkin yan gayu tayi kyau kamar ba ita ba,tace to Alhmdllh ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,Aisha dai tana jinta sai habaici Zainura take mata har ta bar dakin ta fito Palo,kowa ya hallara ana cin abinci,Malam yana can da Umma an kai musu nasu sabo da su sake sosai,Mummy ma tana can wajensu,Zainura tana zuwa taga plate din Salma da Na’im daban tace kai Ku hade shi waje daya a kauye tare kuke ci a plate daya,har ruwa Kofi daya kuke daukowa,Koko ma haka,Na’im ya zaro Ido yace Koko?tace ae Kamu Kamu wai dan ya gane tace to Kofi daya ake zuba muku,Su Irfan suka dinga dariya,Hunaif yace ah kace Koko ne a cikinka, Salma tace dan Allah Zainura da gaske kike?
Zainura tace bari Ku tuna Memory dinku zaku fada,Irfan ta kalla yasha wanka kamar me shirin zuwa party kusa dashi ta zauna tare da kallonsa tace Yasin kamar Ku daya da me kyau kawai,Hunaif yace nifa Baby?Zainura tana dariya tace Alquran kai kam hancinka kamar birona da nake rubutu,bakinka kamar yar ficika,komai naka Siri Siri jikinka kamar raken dan Isiya a kauyenmu,Hunaif dariya ta kamashi wai sugar cane yarinyar take nufi wlh sai nayi maganinta,Irfan yana taunar chewgum dinsa Zainura ta dinga rokonsa sai ya San mata tayi musu Kas Kas,Yace sai dai na bakina,Allah kiyasheni sai kace me kyau da Salma sune yan Jam'iyar kuss (kiss) yake ko me?
Hunaif yace kinyi kyau yau Zainura Ashe dai kina da kyau kema?Zainura ta harde kafa tana yarfe hannu yanda Aisha keyi tare da makale murya ta koma ta yan gayu tace sabo ma kake Man na fi shakira mawakiya,Na'im yace wai ni kam bakya gajiya da surutu? Zainura tace Salmanka ta fini surutu sanda kuna kauye Wlh zanceka takeyi yanzu kalleta sai tayi shuru dan kuturin munafunci billahillazi kai kake wani daga mata kafa wai ita kinibibi gidan Suruka,in kaga rashin kunyar da take tafkawa a kanka sai kayi Salati,Itafa ta Zama namiji kaine macen a kauye,har rawa take maka Allah ya tsinewa me karya wlh sabo da rashin kunyar ta Malam ya muku aure idan karya nake na nutse a nan,ko ka bari Malam ya fito kaji.
Na’im dadi ya kamashi yace na tambayeta munyi iskanci tace bata sani ba,Zainura ta saki Salati tace to Alquran Iskancin da kukayi yaci ace an fada a taskar labarai,billahillazi a gabanmu ma kunsha yi kafin aure amma da kukayi aure shine kuka koma yin Sunnah,sunnah ake cewa masu aure amma iskanci ko a birni babu kamarku,Salma ta rufe ido kunya ta kamata tace Zainura banda sharri.
Zainura ta Mike tsaye tace bari Malam ya fito ya bani aron wayarsa na kira Rahina da Zainab dasu Barira kuji yanda abinda yake amma fa karku bari Su Mummy suji,Hunaif yace ai iya mu kawai za ayi,Irfan yace ga tawa wayar kira,aiko Zainura ta hadaddace Numbers da dama,nan ta kira wayar Rahina tare da cewa sa min ita a handsfree kowa yaji,Na'im sai murna yake dama ace ya tuno irin dadin da yaji wayyoooo da ya huta,bugu daya karaf Rahina ta daga da Sallama.
Zainura ta tsaya a tsakiya tace Rahina ba gaisheki na bugo nayi ba domin ni yanzu Allah yayi min Baiwa da wayar dan Bature nake kiranki yanzu haka ina cikin daula,Rahina ta sheke da dariya tace Zainura shegiya ya kike,tace da Allah ki adana gaisuwarki sai na dawo kawai mayi irinta, tambaya zan miki tsakani da Allah,ranar da muke Kamun Salma karfe nawa takai wajen Saurayinta kafin ta zo? Rahina tace ai ta kai wajen shabiyu na dare suna daki tare wai yana bata abinci a baki tare da sauran Runguma ta yan Birni,Su Na’im suka fara dariya harda Salma,Zainura tace a saurara Alhmdllh,da ta kirashi a waya me yace mata idan an kai masa ita?
Rahina tana dariya ita da Abubakar tace yace idan an kaita wacce kwanciya zata masa,tace wacce yake so,yace to kar ta lankwashe masa ko wanne joint,Zainura tace Alhmdllh da sunayi wayar tace ya sata bacci me suka dinga yi? Rahina tace kiss iri iri wlh nima har Darasi na dauka,kit Zainura ta kashe wayar,Na’im harda tafawa kansa tare da kallon Salma da take ta dariya tana rufe fuska da gyalenta yace uhmmm Ashe soyayya muka Sha haka?
Zainura tace tafi soyayya ma,nan ta kira Zainab,Zainab cikin muryarta me karfi tace Hallo ya naji kamar Zainura wai? Ke dan uwarki kiyi magana mana Zainura kin San wayar nan kashe kanta takeyi fa,Sadisu yaki canja min wata matsiyaci, Zainura tace Zainab a gaida da kowa ni kam ina cikin Jin dadin duniya,tambaya ce nasan ke kadai zaki iya fadan komai ba kunya,Zainab tace hhhh yo kema kin San mu ina ruwanmu tsage gaskiya muke ko ta mutu ko tayi rai,
Hunaif jin Muryar Zainab ta shegun kauye ya dinga dariya ma,Zainura tace kin taba ganin Salma tayiwa Me kyau Rawa? Da karfi Zainab ta Dafe Kirji tace kutmar wannan yan Iskan da ba ruwa a idonsu wannan murgude murgudene batayi masa ba,ke ai na Rantse da Allah Salma ta kusa kashe baturen nan da salonta,Na’im yace wow hhh yana dariya su Irfan ma haka,Zainab tace Zainura dan Allah ya ranar daura auren nan muna kallo bayin Allah kiri kiri suka makure juna a lungu,sanda muna zuwa gidanta dan Allah wanne kalar ihu ne bama jinsu ta dakinsu,bare Runguma da kiss ai kamar tuwo haka suka daukeshi,kin tuna ranar da muka kai dare a gidansu mutumin nan kiri kiri ya dinga hararar mu mun rike masa Salma,da ya gaji ba zuwa yayi ya sureta kamar ya dauki buhun Omo wani cilll ya cillata sama yayi ciki da ita.
Zainura tace to anan sai wani munafunci take ta sabawa bawan Allah da soyayya amma zata fake da Memory ya goge,shi ya akayi yake so gashi nan gwara tsohon gwauro dashi wai ba memory tana ta gudunsa sai kiga tayi mukus a gefe kamar yar Iska yanzu haka ta koma.
Zainab ta saki Salati tare da cewa ke ki Bari dan Manzo kuji yar bantan uba tace ga Barira a kusa hadasu da Salma ta ladaftar da ita da kalamai.
Nan aka bawa Salma waya Zainab ma ta bawa Barira,Barira tace Salma? Salma tana murmushi da kyar tace Na’am bata iya sanin su waye wasu Barira ba,Barira tace ke dan Ubanki mu ba ruwanmu da Memory ya goge gwara ki saki jiki,aure ba wayar Salula bane zaki ce baya daukan wakoki ba memory, me yasa kike haka? Har zuwa muke kallon soyayyarku wlh wata zata kwace miki mijinki kina biyewa Memory ya goge,ai ance tun farko kuna son juna kuma kun tuna baya me yasa baza ki dawo da son baya ba da kika tuna Ku ci gaba kina ji kina gani wlh zai nemo wata dama ga kudi ga kyau yan matan birni ne zasuyi rubibinsa ya dauko daya ciki ko biyu ma kina haukar banza,wannan mijin naki to mu dai mun San son Iskanci ne dashi wlh idan baki nutsu ba wata zata janye shi,haka Barira ta dinga masifa kamar Salma yarta ce hhh wai akan ta girmesu da 4mnths shine komai su Zainura sai suce itace Babba ita zatayi fadan manya.