KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Salma kafin Irfan ya dawo ta dami Na’im da shagwaba ita yunwa,shi kuma sai lallabata yake,Irfan har wasu tsofaffi ya tambaya a wani Super market mene yashin Madina,da kyar wata tsohuwa bahaushiya tace dan nan matarka ce me ciki take nema?Ai a kauye ake samunsa,ban san inda za a ganshi anan ba,wata yarinya tace ana siyarwa a Islamiyarmu wata tsohuwa muna siya,Irfan yace Dan Allah bani Address yarinya ta gwada masa yaci sa’a ba a tashi student ba,yamma lis ya shiga ana ta kallonsa ya tambaya aka nuna masa tsohuwar gaba daya kayan Yara take siyarwa iri iri kawai ya siye kwando gudan komai da Komai Amma yace a nuna Masa yashin Madina?Ya gani garin Kuka da sugar fari kal,ya dinga dariya ashe kayan Yara ne bai san su ba shi.

Na’im ya Kira a waya fito Malam ka karbi abinka,Na’im murya na rawa da gaji dai Iskancinsu suke da Salma????
Irfan yace wai mene haka jiranka fa nake,ka kawo min palona mana ka tafi,Irfan yace ni ban iyan kallon wannan harkar taka ba wlh gwara kayi Sauri ka karasa gidanka ku tafi,Haka Irfan ya kai palo ya ajiye masa ya tafi zai kira Zainura ta karbi nata.

Tunda Zainura taga sakonta ta dinga Murna tana zuba godiya tana lasa tana lashe lips sai ta zazzagoshi a tafin hannu ta lashe,ko kula Irfan batayi,tace sai na sanwa Salma nasan itama tana sha,Allah ya biyaka ya kara arziki da budi har na tuno su Jamila,Sadisu ya dinga siya mana muna jin dadinmu,na sanmaka?Ya miko tafin hannunsa ta dan zazzaga masa kadan ya lashe yanda yaga tayi,suna ta zazzaga suna lashewa haka Hunaif ya samesu ga abu a leda a gabansu da yawa,yace shima a san masa,Zainura ta dan zuba masa shima ya lashe sai yasha tsami Gaye da carbin Malam kawai sai ya zauna shima suna ta lashe lashe har dare Salma ta fito da Na’im tana gani itama ta fara murna ta ebo wasu tana sha ta sanwa Na’im yaji tsami da zaki yace wannan sai yara,Salma ta kwasa da yawa Na’im yace muje ke wannan sunfi iya shirme, suka koma Bedroom yana manne da ita suna maganganu kasa kasa tare da gabatar da Sallah suka sake sabon lale

Zainura kwana biyu ta gaji da birni fa ko magana ta daina sosai duk surutunta wai sai an kaita gida ita ta gaji,ba irin wayon da ba a mata ba amma taki yarda,duk wasan da take musu da tsokana ta daina sai taki fitowa ma,yau ma da kyar Salma ta fito da ita amma cewa tayi baza ta sake fitowa ba sai dai ranar tafiya kauye tazo,ba komai ne ya damu Zainura ba face Aisha da take hanata sakewa a bedroom dinta yanzu idan dare yayi,Aisha da ta daina Lesbian amma ganin Zainura na kwana a dakinta sai abin ya fara dawo mata,Sai tace yanzu ta yarda Zainura ta dawo su dinga bacci gado daya,tana janta a jiki da mutunci,Saida ta saki jiki sai tana bacci taga Aisha tana shafata tare da kokarin cire mata kayan jikinta,idan tayi niyyar fada sai taji tsoro kar ace sharri ta mata ko yan Uwanta suga laifinta,shi yasa Zainura Sam bata da sukuni ita bata gane nufin Aisha ba,ita kuwa Aisha yanzu sha’awar Zainura take tana birgeta,shi yasa sai tayi ta mata kyauta abubuwa masu kyau da tsada.
Zainura duk sunfi mutunci da hira da Irfan sai su zauna suyi ta hira tana bashi shawara suna dariya abinsu,sabo da su ba ruwansu da wani wulakanta mutum ko dan kauye kowa yayi harkarsa ayi wasa da dariya,Aisha ce ma halinta ya dan banbanta kadan.
Yau Zainura ta sawa Ranta sai ta fadawa Irfan abinda Aisha take mata,samunsa tayi a Palo yana kallo tare da danna waya yana chat,batayi magana ba ta tsaya can nesa tayi shuru,Irfan ya ganta Sam bai son ganinta haka sun saba da abin dariyarta tana sasu nishadi amma yanzu ta canja lokaci guda ko mene dalili oho,yafitota yayi da hannu kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tazo tare da Zama kusa dashi,ya kalleta yana mata murmushi tare da tsokanarta kinga ma kinji dadin birni har kyau kike,murmushi tayi kawai bata ce komai ba wanda da dane sai yasha surutu ya gaji a kan maganar nan,can ta bude baki tace magana zan fada ma amma baza ka fadawa kowa ba? Yace ae ai bazan fada ba kin sani muna sirrinmu,tace ka sa a canja min dakin kwana dan Allah ko kayiwa kanwarku fada kullum da dare sai ta dinga shafa min jiki tana kokarin ciremin kaya rannan ma a Palo na kwana,i dan ba haka ba a maidani gida,sai ta dinga lasheni kamar kare,tana min abinda su Salma keyi da Na’im.

Irfan ransa ya mugun baci wato Aisha bata daina halinta ba harda bakuwa zata lalata,nan take ya mike a fusace,Zainura ta rikeshi tace idan kaje zata ce sharri na mata fa,Mummy zata ji haushina,idan kana so kayi fadan da hujja ka bari na jawo ka kamata da hannunka,ka bari da dare kazo ka gani da idonka,ni wlh duk ta hanani sakewa haka kawai ni na taba ganin haka abu iri daya dan lalacewa ai wlh gwara hannun Audu me kifi ya taba ni da nata,haka rannan ina bacci na ta danneni da kyar na tureta na Arce Billahillazi in dai ba a dau mataki ba kaji na rantse Yasin sai na fasa mata kai,nan Zainura ta dinga mita yi take yi take kamar Irfan ne ya mata,saida ta Amayar da abinda ya dameta tas sannan tayi shuru ta zauna tare da zumburo baki tace kuma ka kaini yawon shakatawa kafin ka dawo kaci ubanta ko na dauki mataki da kaina haka kawai a dinga lashe min jiki,ana taba ni banyi da Namiiji ba sai mace,Irfan yayi dariya yace yanzu nasan Zeena ta farfado Amma da gidan nan ba dadi ashe Aisha ce,
Yo ai wannan wlh a daina kiranta da suna me daraja Aisha Albasa batayi halin ruwa ba,ku koma kiranta da Indo ko A’ilo Amma ba wata Aisha.

Irfan dai ya kwantarwa da Zainura hankali yace haka ma Maza ana samun masu mummunar dabi’a haka,Zainura tace ikon Allah katako da katako Allah ya masa mace shi gwara ya nemi gardi me jiki duk tauri kamar katako da wari,Irfan ya kunshe dariyarsa yace to mazane masu wari? Zainura tace ai ba irinku ba gasu nan da yawa a gari basa wanka ba Tsabta Amma har kaji suna zagin mata wai ba tsafta.

Irfan yau yasha hira har su Mummy sunji dadin ganin Zainura yau ta saki ranta,Irfan dare nayi ya je har Bedroom din Aisha ita kadai ya sameta ya dinga cin ubanta yace wlh ko hannu ta rikewa Zainura sai ya farfasa mata jiki,Aisha dama su basa karya tace to ai ba wani abu na mata ba kawai dan jin haushinta nayi,Irfan yace ubanki ya mata jikin?da zaki taba ta kije kiyi da yan uwanki yan Iska ba Zeena ba,yarinya ta gari zaki lalata ta kin hanata sakewa Nan Irfan ya kwashe kayan Zainura tas ya canja mata Bedroom,Amma duk da haka saida Zainura taje dakin Aisha daga jikin kofa tace sai dai ki lashe kanki in Allah ya yarda sai anyi girgizar kasa a dakinki a kaiki can kasar da aka kifar da wanda suka ki bin Annabi lut,kuma farko ana saki a kabari walakiri zai janyeki can kasa ta Bakwai ya miki guduma daya a goshi sannan ayi can dake wajen yan uwanki.

Aisha tayi murmushi tace koma me zakice kice Amma kina da kyan sura Zainura,Zainura tayi tafi tace da ace Irfan ne ya fada sai ya birgeni naji dadi Amma ke da karya daya kuke a wajena,kiji tsoron Allah A’ilo,A’ilo ina jiye miki fushin Allah tam,ta rufe kofar tayi waje tana jin dadi yau zata yi bacci domin ta dade bata bacci sai da asuba Sabo da tsoron Aisha,tana kwanciya ta baje saman Bed tace haba Amma kullum bacci sai da ido daya,Aisha kuwa tace wlh baza ta kyale Zainura ba sai ta cimma burinta,da ace ma Salma zata amince da har ita zata hada su dinga shanawa yan mata kyawawa a kusa.
Aisha da tayi niyyar Aure Amma yanzu ta fasa Maza basa birgeta sai su Zainura da Salma,A mma tana tsoron Na’im bashi da Imani akan Salma indai ya kamata wlh wajen Sarki Kanin Babansu zai kaita kasar larabawa a mata hukunci mai tsanani,Na’im baya daukan hauka, musamman da ya tsani masu wannan rayuwar,shi yasa baya shiri da Aisha.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????

141-145  146-150

Official

By
AsmaBaffa

Wannan page nawa ne ni kadai ASMABAFFA????????????saura naji yan bakin ciki.

   Aisha ce kamar munafuka kullum tunani take ya zata samu Zainura ta mata wayo ko kuma Salma zata Yiwa wayo Sabo da Salma tafi saukin kai kuma yanzu bata da Aljanu shuru shuru ce.

Salma tana Bedroom dinta tana shirin Tafiya wajen oganta Na’im tasa kayan daukan magana domin duk wanda ya ganta cikin wannan kayan sai yaji kunya da kansa ya tafi,Aisha ta dade a tsaye tana kallon Salma wacce bata san tana yi ba,jikinta ya mutu sai lokacin ta shigo tare da Sallama,Salma ganin mace ce kuma kanwar mijinta da fara’a tace Aysha ina zuwa haka,Aisha tace Wow Anty Salma kinyi kyau nan ta rike hannun Salma,Salma ta dauka kawai yabo ne,ta shafa gashinta gaskiya kina da gashi,Salma tace tnx ai kin fini,nan Aisha ta wani rungume Salma tana fakewa wai murna take,Salma taga abin yana wuce hankali sai wani shafa mata wuya Aisha takeyi,Salma tace ke Aisha mene haka ?Ban gane ba anyi yamma da kare,kwartancin naki kaina ya dawo?ko kin manta nasan halinki da sanda na fara zama a gidan nan,a gabana ake miki fada fa ni wlh na dauka kin tuba ashe karya ne na muzuru ne,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button