KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Irfan sai da yayi Sallar Isha ya dawo gida a gurguje yayi wanka yaci abinci,8pm da dare sai ga budurwarsa Rayhanat taci uban wanka dama yar gayu ce ta gaske tayi kyau sosai,ta samu Mummy suka gaisa,Hunaif ne kadai zaune a palo yana kallon Ball,abin na Rayhanat zuwa gidan Saurayi har da dare dan lalacewa,ta zauna tare da mikawa Hunaif hannu suka gaisa wai ita baturiya,Zainura fitowarta kenan daga kitchen ta dauka ma budurwar Hunaif ce yanda ta manne kusa dashi harda gaisawa kamar Maza,Hunaif ya yace Zeena ga budurwar Irfan je ki kira mata shi,Zainura tayi murmushi tace dama itace Rahane take ko Rayhanat,Budurwar tayiwa Zainura kallon Banza tace yan kauye ku dama masu shara da wanke wanke idan kuka samu waje sai ku nemi raina masu gida mene wani Rahane?

Zainura tayi shuru ta tafi dakin Irfan tayi Sallama daga kofa tace budurwarka tazo tana palo kazo,Irfan yaja tsaki yace kash akan wai 2days ban daga wayarta ba,Zainura tace kace mata an maka mata balarabiya a kasarku tayi hakuri ba laifinka bane Kanin Babanka ne Sarki yace ya baka yarsa,Irfan yace kin kawo shawara,suka fito tare da Zainura a jere,Rayhanat taji haushi gashi taga Zainura ta fita kyau da komai baza ma a hada su ba ko kusa,Cup ne a hannun Zainura tana shan Holandia ta mikawa Irfan tana dariya tace shanyeta,Irfan ya kalleta yayi dariya sai da kika gama shanyewa zaki ce wani na sha suna saman Steps sunki karasa saukowa ga Rayhanat tana kallonsu Zainura tace Allah sai ka shanyeta tare da kafawa Irfan Cup din a baki ta toshe masa hanci da daya hannun wai dure take masa,Hunaif yana ta dariya yace wlh anyi girman banza wannan yarinyar ce zata dinga ma dure kai kuma ka tsaya wai ko kai Irfan Namiji ne? Cup din Zainura yana bakinsa ya ware hannu ya zagi Hunaif wai zagin hausawa da ake cewa dakuwa.

Rayhanat ta cika fam,Zainura tace au Rayhanat yan gayu tana jiranka fa masoyan Asali je ku sha Soyayyarku,Rayhanat tana jin Abinda Zainura take fada,Irfan ya karaso Zainura tana saman Steps tana kallo yayi murmushi tare da zama yace ya akayi Baby barka da zuwa,Hunaif ya mike ya bi ta wajen Zainura tare da ce mata kai baki da kirki wlh kiji tsoron Allah,Murmushi tayi tace me nayi daga hada alkhairi sai ya zamo tsiya,nuna min taka Babyn?Hunaif yana dariya yace Allah kiyaye ki rabamu a banza ai ni ko gidana Bazan bari kije ba kashe min aure zakiyi.

Salma da Na’im ne suka shigo da ledoji a hannunsu da Alama daga Shopping suke,Na’im ya dauketa kamar Jaririya suna hira a haka,Zainura tace wlh tunda nazo garin nan Banga na gari ba,duk yan Iskane a nan,kowa da tsiyarsa,Salma ta dagawa Zainura hannu,Zainura tace sai shahararrun yan bariki munga na kauye ga na birni kuna bugawa,Hunaif yace ki bari na hadaki da Ilu me wanki kema ki fara naki kalar barikin,Hararar Hunaif tayi tace Sabo da baka kaunata ko? Dan ara min wayarka dan Allah,ina taki?ba Mummy ta siyo miki ba rannan? Zainura tace ai nasani tana jakata aro zaka dan bani kawai gani zanyi,Hunaif ya mika mata tace to jeka idan na gama zan kawo ma
Ya tafi room dinsa ta samu ta duba balance taga kudi wajen dubu ashirin a wayar,tayi transfer dubu daya ta goge komai ta kai masa tace ga wayarka ko kyau babu duk wayar duniya ka rasa wacce zaka zabo sai wannan me kirar doyar? Hunaif yace zaki dawo ne gobe ma ranace.

Irfan yana tare da Rayhanat dinsa tana cewa ya bata kudin Mai zata zuba a motarta,har ya zaro 20k zai mika Zainura tace haba baiwar Allah har dubu ashirin ina laifin dubu biyu,Irfan yace kyale a bata,Zainura tace tab to wlh daga garinmu zuwa birnin katsina katuwar motar Boss ma gingimari Man dubu daya sati yake musu suna jigilar Passenger,amma ke a wannan yar kurkurar motar taki me kirar kwado kice har dubu ashirin,Yo gingimari da tafi taki na nawa take sha Amma sai kace Tanker ce dake,dubu daya za a baki na sati daya,

Zainura ta kwace kudin ta mika mata dubu daya ciki karbi,Rayhanat ta mike a fusace ta fisgi dubu dayan ta yagata ta watsawa Zainura a fuska,an baki dubu Amma kamar Naira ashirin aka baki Sabo da son kudi,shi ya sai miki motar? Wa yace a siya miki motar an san baza a iya zuba miki mai ba,ki koma wajen wanda ya baki motar mana ya zuba miki man,ba alhakin Saurayi bane zuba miki mai a mota,ba hakkin nan gidan bane,Rayhanat bakin ciki yasa ta fusata zata daki Zainura,Irfan yace ke mene haka yarinya ce fa zaki ji haushinta ai Yara lallashinsu akeyi,karki soma dukanta wlh idan baza ki lallasheta ta baki kudin ba ki tafi,gidan nan ba a duka da zagi a ciki,Mummy ma kika sake a kanta zaku bata,Rayhanat tace aikin banza ni zaka wulakanta akan yar kauye?wlh ba haifeka ba,kace kawai sonta kake yi,nan Rayhanat ta dinga zage zage da ashar har Mummy ta fito tace lfy? Irfan ya bata labari,Mummy tace Zainura tayi gaskiya kai Irfan ba kudin banza gare mu ba,nema ake ana samu ba injin bugasu bane a gidan nan,gwara a tallafawa talakawa ko marayu akan a dinga barnarsu anyhow,Rayhanat ba kunya ta harari Mummy ta fice fuuuuu,

Irfan ya samu makaranta me kyau da Tsada ya kai Salma da Zainura,Zainura Ss1 Salma Ss3 zata zana waec da Neco,Tunda Driver ya fara kaisu Zainura ita bata iya turanci ba sai karatun Hausa Amma basira ce da ita duk abinda aka koya tana gane me ake nufi Amma bata iya karanta turanci ba,Salma kuma indai turanci ne to ko Bature sai haka Amma bata kai Zainura fahimta ba,Salma idan anyi break zasu zauna ta koyawa Zainura karatu da rubutu na turanci,tunda suka fara zuwa makaranta Zainura take bawa yan aji dariya ba fada ba masifa Amma yanzu za kuci dariya kuma idan kayi mata rashin mutunci to fa kasan ba daga kafa,shi yasa ko turancinta idan tayi ba dai dai ba babu me tsokanarta.
Har fada Zainura ke tarewa Salma a ajinsu domin kullum sai taje ajin su Salma ba ruwanta da wasu seniors.

Koda Salma suka fara Exam ba kullum take zuwa ba kuma ba lokacinsu daya da Zainura ba,Na’im sau tari shi yake kaita ya daukota,Zainura suna tsaye da Salma ta fito daga Exam Driver Na’im ya Parker Na’im yana baya a zaune wai daukan Matarsa yazo,Zainura tace masu gata da galibu anzo daukanki,Dariya Salma tayi tace ke fa?Sai dai Driver mu ai,Zainura suka jera ta raka Salma tare da lekawa cikin motar tace yaya Na’im kullum Irfan da Hunaif sai sun bani kudin break Amma kai Salma kadai ka sani bayan ni nake tare mata fada,Na’im yayi murmushi Ya mika mata 2k tace kai wasa nake fa ni ina zan kai wannan kudi ,kawai tuna maka zanyi ka kira Malam da Umma ku gaishesu wlh bai dace ku watsar dasu haka ba ko da Memory dinku babu tunda Kunji labarin komai ya dace ace kuna kiransu ko a waya a gaisa,Salma tace jiya na fada masa ai mantawa yayi,Zainura tace to uwar Iya ba cewa nayi ki tare masa ba tunatarwa nayi Sabo da kar kuji kunya nan gaba,Na’im yace tnx Sis zan kira su Insha’allah,Driver yaja suka wuce Zainura ma basu dade ba aka tashesu,Irfan yana ta kiran wayarta ashe tana gida ta boyeta a jaka,

Tana Table din me agwalima sai ligwigwitasu take kuma taki siya,ta latsa tace yanzu wannan har talatin dan kawai kuna Abuja,sai a dinga tsada wlh Bazan siya ba,wannan nawa? Ya naga bata da hanci ya cire Iska tana ta shiga,Me agwalima yace baiwar Allah idan baza ki siya ba ki daina lagwitse min shi ki tafi mana dole ne,Zainura ta kara daukan wata ta mulmulata tare da cewa sai kace kayi mata allura tayi girma haka kufa masu siyar da abu zalunci gareku baza a kyale abun Allah da annabi ya nuna ba sai an Sa masa kamikal (chemical) Me Agwaluma yace tunda ba siya zakiyi ba ina ruwanki hatsabibiya,Zainura tace rake zan siya ma ta koma wajen me rake tace kai yanka min na goma kuma kato,ya zabo wani dan siriri tace kai mene wannan sai kace raken Dan Isiya Alquran Bazan siya ba,yace to ai na fara yankawa,sai daĆ­ ka dau asara mu raba ka shanye na biyar ka bani na biyar,Me rake yace ke mu nan babu kayan biyar, me yasa to engine kudi ya buga da ita cikin kudi tunda bata da amfani,ka rike rakenka Bazan siya ba,yace zaki dawo ne ai na ganeki wlh gobe wajen Principal zan kaiki kara,Tuni Zainura tayi wajen me carrot ta tsaya wajen carrot sai dariya take tana kallon carrot,me carrot ba bahaushe bane yace a’a Ajiya(Hajiya) babu lfy?wannan kwakwalwa babu?Zainura tace yasin Bazan ci ba ni a kauye ma a boye nake cin karas saboda ai sai na ga kamar yar Iska ce ni,wannan da abun Maza yake kama Alquran Bazan ci a gaban mutane ba,a boye ta zaro Naira Hamsim ta dauki bakar leda tace Sauri kar a ganni,ana zuba mata ta boye tare da jefawa a jaka kar a ganta.

Me rake yace na ganeki wlh gobe sai kinci ubanki wajen Principal,Me Agwaluma ma yace ai tunda aka kawo yarinyar Makarantar nan wlh ta buwayi masu kawo kayan siyarwa,rannan haka ta sha yogourt da bones tace baza ta biya ba yayi mata tsada,kuma haka taci banza,abin mamaki wanda suke kawota masu kudin gaske ne a kasar nan,wannan yarinyar ba yar arziki bace,Zainura tace yo dan ban siyi kayanku ba sai ku dinga tsine min Bazan siya ba Alquranin Allah dole ne ku dinga alkinta sana'arku baku san darajarta ba.

Suna haka sai ga Irfan ya shararo motarsa labebiyar gaske ya sha wanka,Zainura ta hangoshi tayi kamar bata ganshi ba sai da wata tace ga yayanki nan fa yana ta horn,sai lokacin ta juya tayi wajen motar,tana zuwa ta shige gaba da Sallama tace barka da zuwa ni Alquran nafi son Driver yazo daukana kai idan ka dauki mutum baza ka dinga nuna min duniya ba,amma Driver kuwa har kallon doki ya kaini rannan,kai kuwa fa ko gida me kyau idan na nuna ma sai kayi ta min fada ku komai sai anyi gayu da yanga,haka rannan ma kace muje yawo da ka tashi kaini sai ka kaini wajen masu iyayi ko wacce ta fito tana iyayi tana tabe baki,yan iyayi daga mazan har matan,Irfan yace Driver ne ya kaiki kallon doki?tace ae wucewa za muyi nace zan kalla ya tsaya na kalla,ai wlh ya fiku wayewa da sanin duniya ku aikinku kawai wajen gayu ayi ta yanga,kuma ana siyar da alawar gajimare nayi ta sha a wajen,wani pampo yana ta shararo ruwa sai da naje na zuki ruwan,ai wlh ko yanzu ni Driver ya gama min komai,Irfan da kyar ya iya danne dariyarsa domin kauyancinsu sukayi da Driver,lallai Driver fa zai sace Zuciyar Zainura Sabo da biye mata yake da Alama suna shashanci,shi yasa idan Mummy tace Hunaif ko Irfan ya kaita sai tace Gwara  Sabitu Driver.lallai Sabitu zai rasa aikinsa cewar Irfan a ransa.

Irfan a ransa yace lallai gwara da Na’im yace ayi Sauri a Sa Zainura a schl,kallon Irfan tayi taga yayi shuru sai tayi tunanin haushi yaji tace Driver ya fisu sanin ta kan duniya,tace kuma fa kun san duniyar nan nufina Ku na yan gayu kuka sani kar kaji Haushi ai kuma kun waye,Irfan yace yau Friday wanne kitso aka baku? Tace wai ko 2step suka ce ni dai 3step za amin ko Bene idan yayi tsayi ai yafi kyau a ganshi reras a jere,yace to Saloon za a kaiki gobe,Zainura tace Salma ta iya kitso ita zata min,Irfan yace wannan mayen ne zai barta ta miki kitso? Bazai bari ta taba gashin wata ba bare ta miki kitso to ina ma suke fitowa kullum suna daki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button