KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Basu bar garin ba saida akayiwa masu tafiya aikin Hajji passport a garin Katsina,aka bada kwangilarsu an biya kudaden da komai,sannan aikin da Na’im yace Zai gina musu a garin duk an kawo kayan da komai shima an fitar da kudi an bada kwangila me gari ne jagorana aikin har a gama,tafiya Saudiya harda me gari,Su Barira dasu Jamila kamar zasu haukace zasu je Makkah,Salma tace duk iya frnds dinta da sukayi Kamu tare kayan daki idan aure ya tashi ita zata musu kyauta gudun muwa, suka dinga ihu shewa da tafi,Na’im sai da yaje sukayi magana da chairman na local government din su Malam ana kammala aikin makaranta da Hospital a turo ma’aikata su dinga aiki gomnati na biya su albashi.
Chairman yazo garin anyi komai dashi anyi godiya tare da jinjinawa su Mummy masu taimakon aluma Basai lallai ace Gomnati ba.

Kwana biyar sukayi zasu tafi Malam yace zasu biyo bayansu amma tunda zasu je Saudiya da mutanen kauye zai zauna sai sunje sun dawo sai su taho Abuja shi da Umma,Salma tace suna dawowa ma zata musu booking Flight su dawo Abuja.

Salma takaicinta su Affa sunki gane gaskiya taso ace sune aka fara yiwa haka,suma suji dadi Sanadiyyar riketa da sukayi amma ina,sai tayi tunanin kara komawa sai ta fasa kawai sabo da tasan zai wahala ma su yarda da ita,h aka yan uwan mahaifinta ta rasa me ta musu da basa kaunarta ita,amma tana addua Allah ganar dasu.
Kwanan su Na’im biyar a kauyen nan sai da suka gama saita komai sannan suka nemo Zainura da kyar suka ce tazo su tafi Abuja,k afin su Mummy su fito saida ta tambayi Irfan a sirri ko yana son Zainura?yace Sam shi ba soyayya suke ba kawai frnds ne tasu ce tazo daya ba so bane,Mummy tace shike nan amma taso ace sonta yake da sai ayiwa iyayenta magana tun kafin su bar kauyen a tsayar da magana amma yace ba soyayya bace shi.

Jamila suna jikin motocinsu suna ban kwana,Zainura tace Sababbin kawayena na Abuja sunce na gaisheku,Zainab tace Allah?kice Wallahi?Zainura tace am serious,Jamila tace ai kece Amasiros din Dalla mu me muka sani,Zainura tace da gaske sunce na gaisheku,Zahrau tace dan Manzon Allah? Zainura tace kullum nayi ta basu labarinku,Barira tace kice Yasin,Zainura tace to karku yarda din aikin banza, ai baku ga tafiyarsu ba tab,Kamar baza su taka kasa ba,Jamila tayi dariya tare da cewa ko dai tausayin kasar suke ji ne? Zainura tace na sanma yan Iska,Zainab tace cab ai taketa nake duf duf har girgiza nake a kan kasa wlh to haka kawai ranar da aka binneni fa  sai ta matseni ai gwara na moreta nima,Hunaif ya dinga dariya wai har girgiza take a kai,

Zainura ta shanye hannu ta sagaleshi kunga yanda sukeyi yan bantan uba ta fara yanga tana Shan kamshi tana taku dai dai,yan matan suka dinga shewa Zahra’u tace amma yan Birni anyi yan kwalabar uba wlh dan Iskanci kawai a kama yanga to ta uban mene,Zainura tace ke ai ita take tashe yanzu a can idan bakyayi babu namijin da zai kalleki,kici uban kwalliya Malam nima yanzu na fara koya so nake na Zama star,
Rahmatu tace ke Zainura ki rufawa kanki asiri karki koyi iskanci,Zainura tace na nawa kuma,ni ai komai ba a barina a baya in dai Harkar gayu ce,tsaya kuji Salma tazo a tambayeta.

Salma na zuwa zata shiga mota Zainura tace Salma da Allah ya batun iyayi da yanga a birni ai ke kin iya dama,Barira tace ai Salma ita dama girman Birni ce,Zainura tace inji ubanwa?to billahillazi ba Tonon silili ba Salma karki ji haushina na fada? Salma tace wlh in kika fada sai na fadawa Na’im,Zainura tayi dariya tace ke yakewa Kwarjini har zai miki fada kiji, to Alquran sai na fada Salma kauyensu bai fi gida takwas ba yasin gwara mu sau Dubu a birni muke,Salma bukkar yan fulanine duk ko katanga babu sai ta kara,idan kunga garin ko bacci baza ku iya ba,Jamila ta buga uban tsalle taja gefe tare da rike gefe wai ta firgita da labarin Zainura ta sheke da dariya suna an kureta wlh to a ina kika waye haka? Salma tayi dariya tare da cewa Wlh Zainura sai na miki rashin mutunci gida takwas fa kika ce,Zainura tace Sorry to gida Dubu na manta,Mummy tace wannan anyi yar ja’irar yarinya ba sirri,Zainura tace ai ita take ta mana wani iyayi bata fada mana ba tun farko,amma ai iyayenta a birni suke Maiduguri,amma asalinsu yan Nijar ne shi yasa suke suma kamar Arab,amma Allah Barira Ku daina ganin wani kimar Salma Ashe ma duk mun girmeta da wajen wata biyar ai naga takardar haihuwarta Yasin yarinyace muke wani daraja ta.

Salma tace Dan Allah mu tafi a bar banza a nan tayi ta tone tonenta,Sai lokacin Zainura sukayi Sallama ta shiga motar suka tafi Airport.
Yau a kusa da Irfan take,Na’im kusa da Salma,Hunaif yana gaba,Mummy motarsu daban,Malam da Umma har Airport suka rakasu a motar Malam.
Irfan suna hira Da Zainura yace ai gwara ma da za a koma tunda kika zo ko ganinki ba ayi,Zainura tace kai Ya siyi kawuna wlh busy ba time ina ta Zumunci,shi dariya ma take bashi kamar wata Babba idan tana magana.

Na'im ne yace Salma Hijab zata sa sabo da a mota ko jirgi zai dan dinga zura hannunsa yana wasa da dukiyar Fulaninta ba tare da kowa ya gani ba,Suna mota tayi mukus a jikinsa yana ta tabe tabensa a jikinta,Salma in taji dadi sai dai ta kudundune cikin hijab kamar tana Jin sanyi,sai ta dinga fakewa da shigewa jikin Na'im wai sanyi take ji,Irfan har ac yasa aka kashe amma taki daina ji

Zainura ta gane me sukeyi kunya ta kamata harda baccin karya wai Salma tana sata kunya ko uban wa ya San me sukeyi oho amma wai haka kawai dan taga Salma na lumewa cikin jikin Na’im sai taji kunya wai.

Zainura taji itama inama ace da Irfan suke haka suma da taji dadi wlh nan Zainura ta fada tunanin Iskanci itama jikinta ya mutu,firgit ta dawo normal sai ji sukayi tace Bana so ma,me zanci dashi tir Allah kiyaye,sun San Zainura uwar shirme sai suka shareta,taci gaba da tunaninta,Irfan ya leka fuskarta tare da cewa lfy? Zainura ta girgiza kai tare da cewa wani abu na tuna,Wayarta ta dauka tare da turawa Salma text cewar dan Uwarki kina tayar da hankalin marasa aure ni na gane me kike sa mijinki yana miki ,Salma tana gani ta karanta sai ta nutsu ta zame jikinta an ganota,su kuwa su Irfan hankalinsu bai kai nan ba Sam basu San ma me suke ba.

Ta kara turawa Salma text dolene wai sai kin kwanta a jikinsa ki tashi mana mu baza ki dinga samu tunani ba.

AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????

171-175 176-180

Official

By
AsmaBaffa

JANNAT wannan page din Naki ne.

 Sun Sauka lfy a birnin Tarayya Abuja  yayinda drivers da Securities suka zo daukansu har zuwa gida,kowa ya kule bedroom domin hutawa.

Aisha ita kadai a daki kamar mayya taji dadin dawowarsu koda Na’im ya shiga dubata zai mata Allura sai kuka takeyi dan Allah a bude ta haka,Na’im yace Sam sai an gama komai lokaci ya cika,taci kuka har ta gaji,Mummy har tausayin Aisha taji,
Bayan kwana biyu Zainura son Irfan ya shigeta sosai duk da cewa bata San so ba amma tace zata tambayi Salma taji ko cutar so ce ta kamata,kullum tasan lokacin da Irfan zai dawo ko zai fita sai ta san yanda tayi ta buya ta kalleshi a boye ba tare da ya sani ba,
Yauma da yamma ta cakare ansha wanka ta fito kamar kallo take amma Irfan take so ta gani taji sanyi a ranta,bata dade ba sai gashi ya shigo cikin shiga ta Alfarma,yasha light blue jean da farar riga,ba karamin kyau yayi ba dama suna kama da Na’im sosai kamar me,Zainura ta kalleshi a sace ba tare da ta bari ya gane ba ta dauke kai irin ko kallo Bai ishe taba,Ganin kwana biyu tunda suka dawo akan Mummy tace ko yana son Zainura shine ya rage kulata sai gaisuwa take hadasu,itama da taga haka shine take shareshi sai taga dama take gaisheshi ma,

Yanzu ma ko sannu da zuwa bata masa ba ta dauke kai,Irfan yayi mamaki yana jira ta kulashi yaga ko kallo Bai isheta ba to ko baiyi kyau bane yau?bedroom ya shiga ya kalli kansa ya kara fitowa ya wuce ta gaban Zainura sai ma ta kalli TV tana dariya irin bata San an halacci Irfan a wajenba,ya shiga kitchen ya fito dauke da Bowl karami me kyau da fruits ciki yana Sha da fork ya zauna kusa da Zainura.

Still Zainura saima ta koma danna waya tana dariya,kallonta yayi tare da cewa baki ganni bane? Zainura tace na ganka mana mene ne?ta fada tana kallon wayarta,to ki gaisheni,akan me zan gaisheka? Irfan yana kallon gefe can daban yace har tambaya kike,kofa Sannu da zuwa baki min ba,Hunaif ne ya shigo yace wow Zeena yau kinfi kullum kyau nan gaba za a ga zukekiya,rannan da mukaje gidan Dada frnd din nan nawa yace wlh yana Sonki zan hadaku idan ya miki baki gani ba komai da mace take so ya hada,

Zainura ita Irfan take so amma ta danne tace to Sai yazo na ganshi mun saba idan halinsa ya min shike nan,  Hunaif ya haura side nasa.

Irfan ya gama kulewa shi taki kulashi tana Kula Hunaif har wani Saurayi zai mata,kallonta ya karayi amma ko ta tasa batayi,yace baza ki min sannu da zuwa ba,kawai
Zainura tasa headphone ma a kunnenta yaji haushi ya Mike tare da fisge Headphone din ya tsinkashi gutsi gutsi ya watsar tsawa ya buga mata ni sa’anki ne? Zainura ta firgita bata taba Jinsa haka ba yafi sauran hakuri ba shiri tace Sannu da zuwa an dawo lfy to Alhmdllh,ya hanya ya aiki tana sunkuyar da kai kamar wacce tayi karya,ba kunya yace lfy yayi gaba abinsa ya barta nan.

Salma ce ta fito ta zauna tare da cewa Zainura Irfan yace kin rainashi yanzu wai kina kallonsa kin daina masa magana gaba kikeyi dashi,Zainura tace gaba kuma?da dan masu gida ni na isa,kawai naga yana wani shareni ne shi yasa nima Naja mutuncina,ni kin San ban son raini zanyi wasa da dariya amma da naga za a rainani zan canja wlh haka nake ni,da ace tun farko ma naga irin masu wulakancin ne harkarsu bazan shiga ba,ni ban masa laifi ba naga yana wani daure fuska ni dama gidan aka zo domin ko wanne part na iya bugawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button