KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

PC ya kama Zainura yace ta miko tafin hannu ya dinga tsula mata bulala ba Imani sai da yayi mata Goma masu Zafi hannu yayi jajir ko a jikinta sai ma tambaya tayi ka gama?yace iyeeeeee…..ya kara mata biyar tace ta mahaukaci ance a taimaka ya fada Rijiya yace ni wankana nake so sweet more ko na tafi? Pc ya gaji yace na yar Iska be ths girl,Zainura ta Mike tare da kakkabe hannu tare yiwa me Rake gwalo,yace na ganeki ai zan kamaki ne da kaina zan dau mataki,Zainura tana zuwa gate ba student duk an tafi gate man ya rufe gate,yana zaune a benci yana ciye ciye yana jin radio tana karasowa taga kanshi yasha aski Kwalkwal tace bude min gate da kai kamar bayan kwarya,Gate Man yace sai dai ta bude da kanta tunda ta masa ba’a, kallon tsab ta masa taga bashi da hanci sai dan mitsit daga karshe shima ya baje sai kafafen hanci ta fara dariya tace dan Sanmin Hancin ai kuwa har wanda suke kusa zasu fita suka dinga dariya sabo da kowa yasan hancinsa kamar na biri,Gate man yace Allah baki da me irinsa,Tayi waje tace dan Sanmin Hancin ya mun kyau.
Tana fita taga Irfan yana jiranta wani dadi da sanyi ya ratsata amma wai sai taki ma kallon motar ta tafi da kafa,yana Binta a hankali ya sauke glass yana cewa lets go sai ta makale kafada wai baza ta shiga ba,
Irfan yace zan tafi fa kuma Driver bazai zo ba,ta zaro 1k tare da yi musu Kiss muah harda yin yaren yorubanci legbebe ta wani mawaki kaji ko to kudi ba yaren da basaji,ina da kudina,Irfan yayi murmushi tare da cewa to zo mu tafi dan Allah,yanzu kayi magana ta zaga ta shige, Suna tafiya wani yazo ya buga musu mota,kuma ya fara zagin Irfan wai shine da laifi,suka fara Fada,Irfan ya fito daga mota wancan ma ya fito suna zage zage zasu fara fada,Zainura ta fito ta shiga tsakiya tare rungume Irfan dinta mene haka zaka zubar mana da kima,ai ka wuce cacar baki da wannan,muje dan mota ai ko kyauta sai a bashi,Irfan yace kina gani zai raina min hankali ya buga min abu idan baka iya tuki ba kaje ka koya,wancan dan Gulf yace kai Bature ni ba karamin matsiyaci bane dan tasha ne ni,kunzo garin mutane zaku nuna mana isa ana cin arzikinmu,shegu matsiyata masu Jan kunne,dan kana takama da kudi muma ai da kudinmu ko nazo wajen uwarka ta taimakeni da wata hausarka gwari gwari,Zainura tace kai ka daina zaginsa wlh sunzo din me kuka tsinana a kasar taku na ci gaba,basu suke kawo muku komai ba,da basu yar kuturwar motar nan taka baza ka hau ba,Yace Allahhhh afiruwa au ke harda ke kaza yar me son kudi Karuwai kuna bin turawa akan Kudi, Irfan harda zabura,Zainura ta rikeshi kam tace Wai mene haka ai kafi karfin wannan,kana hada jiki dashi na daina kulaka,dan Gulf ya kalli Irfan da gani anga namiji ga kyau ga sura wandonsa duk sarkoki turawa Zalla,dan Gulf yace na fasa motar bazan biya ba a batar dani,Zainura tace da haka kace tun farko jeka an yafe ma shike nan,ke ni ba talaka bane yayana Sarkin jigawa ne, Zainura tace naga Alama jikinka ya nuna ciki kamar kwado muje Irfan,mutumin yace shegu yan bariki,Zainura tace me hannu kamar na Obasanjo wullu,Irfan yayi dariya suka tafi,Dan Gulf ma ya shiga yace ni za a rainawa hankali da banyi musu kaca kaca ba da tuni sunce sai na biya bani da ko sisi taya zan biya wannan jibgegiyar motar komai nata daban ai gwara da masifa ta kwaceni, shegiyar yarinya yar afiruwa ta samu shiga tana ta cinyewa bature kudi kuma wlh dan banzan jin maganarta yake,amma anyi sakarai,ya saki dariya yace shifa bature mahaukacine idan yana son abu sai abinda mace tace yakeyi wlh ni Jummai bata isa ba tuni zan jibgi banza,amma jiba yarinya karama dan tana da kyau uhmm anyi asara.
Irfan ya dinga dariya yace ni ban ma San me yasa na kulashi ba wlh,inama Na'im yayiwa haka ko Hunaif ya bige kuma wai ya zagi mutum,da baiyi magana ba wlh bazan ko kalleshi ba amma wai zai zageni,da Hunaif ne sai ya kulleshi yau ya kwana a wurin police,Zainura tace yana zaro Ido kamar kwan lantarki ba,shegen wuya kamar lauje hhh Na'im ya mika mata hannu suka tafa,a mma sai ya rike hannun yaki saki,yayi shuru na dan muntuna yace Zeena kince bakya so na ko?wani kike so?yanzu bare yafi dan gida? Zainura tayi shuru a ranta dadi kamar ya kasheta a fili kuma ta kwace hannunta tare da bata fuska tace ni dai Allah sai nayi tunani a kai tunda ai Usman yana nan shima,ya zanyi daku ni,kai nafi daukan ka a best friend kuma yayana,Bana so ko a yaya ki daina daukana in dai baza ki aureni ba mene wani best Frnd,Zainura ta share ma zancen,ta kawo wani,yaji haushi amma ya danne.
Haka Kullum Irfan sai ya tambayi Zainura ta aureshi amma sai aji take ja masa yayi yayi har Salma ya tura amma ba amsa.
Gashi yanzu an kusa bikin Aisha ma Saura 1mnth yana ta bin Zainura,Salma ta samu Zainura tace nasan dai kina son Irfan wai ke Jan aji,to ajin yayi yawa Zainura ki sauke ajin ki yarda kar ya hakura ya nemi wata,kamar Irfan fa Zainura ai kinyi sa’a,Zainura tace to shike nan tunda kin sa baki Zan so shi,Salma tayi dariya tace ke sarkin karya dama kina son Abinki kinga Sai da safe Honey yana jirana da kyar ma ya bari nazo.
Alhmdllh masu aikin Hajji sunje sun dawo lfy,aikin da Na’im yasa ayi a kauyen su Zainura har an kusa kammalawa,yanzu Malam da Umma suke jira kawai su sauka a Abuja,Salma ta gama waec da Neco nata lfy,yanzu Zainura ce take zuwa schl ita kadai.
Yan Uwan su Na’im suna nan suna shirin zuwa bikin Aisha Nigeria daga kasarsu,Zainura ma taje gida can kauyensu ita kadai tayi sati daya tayiwa iyayenta Sannu da zuwa na Makkah da sukaje,tare da kawayensu haka suka dinga yiwa Zainura tsiya wai ta rigasu zuwa birni sun rigata zuwa aikin Hajji wlh sun fita ci gaba.
Salma kullum Zuba Ido take ko zata ga Su Affa ko dangin Babanta sun nemeta amma shuru kakeji.
Gidan da Na’im ya Gina a kusa da gidansu na yanzu yake,makeken gaske part Uku ne ciki,bangaren Na’im daban,Irfan nasa sai Na Hunaif,kowa abinda yake so aka tsara masa a part dinsa babu abinda babu a gidan,komai na Alfarma,Mummy ce tace ita so take su zauna tare gaba daya zasu fi zumunci,Dada kuma sai ta dawo gidan Mummy da zama,gasu Malam da Umma sai su Zauna Shar abinsu,sai bayan bikin Aisha su Na’im zasu tare a sabon gidansu,Hunaif shi da wata Balarabiya yar kanin babansa Afrah da ita yake soyayya wai ita yake so shi bazai auri yar Nigeria ba sai yar uwarsa Balarabiya,Afra kyakyawa ce itama amma dan tana da haske da yawane Salma ta linkata a kyau nesa ba kusa ba,haka Zainura ma tafita kawai farar fata zata nuna musu amma sun fita komai,itama ba laifi ko a Larabawa me kyauce Afra,gata da kirki,bata jin ko wanne yare daga turanci sai larabci,Mummy tace shima Hunaif mene amfaninsa kawai a hada dashi a daura tare dana Aisha,kanin Abban su Na’im ya tsara komai ya yarda ba matsala idan zasu taho Nigeria da Afrah Za a zo ayi biki da komai a kai ta gidan Hunaif.
Irfan haushin Zainura yake ji taki yarda dashi ya aureta kawai shine ya daina kulata,ga wata budurwa a office da ta like masa,har gida take biyoshi yana korarta,Sakeena tunda take zuwa Zainura tana schl bata sani ba,sai yau tazo da yamma Zainura ganin Sakeena tare da Irfan a zaune suna ta hira kishi ya taso mata ta fito sai zirga zirga take a Palo,ta dawo harda buya a bayan labile wai taji wacce hira sukeyi,sai taji yanda Sakeena take jero kalaman kauna,Ihun Zainura sukaji ta fadi a kasa tana ta birgima ta rike ciki tana Zan mutu..zan mutu,Sakeena tace kanwarka wai bata da lfy wlh,Zainura kamar ana yankata haka ta hana kowa sakewa saida kowa ya fito wajenta a gidan,Mummy tace me ya sameki ta nuna Sakeena tace ta kama min kurwata,gata nan ta Zama Mage,wayyo ta koma Damusa,zata yankani,daga taga Ina Shan alawa ban bata ba shine ta rike min makogwaro wayyo hanjina,zata cinyeshi mayya tazo gidan.
Sakeena ta fashe da Kuka Jin sharrin da Zainura ta kala mata wai mayya,tace wlh ni ba mayya bace sharri tayi min,Zainura ta kara fashewa da kuka tana rike wuya wai Sakeena ta shaketa,daga nan kowa ya harbo jirgin Zainura bata son Sakeena da Irfan dama tuni ake Zargin Sonshi take.
Kowa yayi tafiyarsa,Salma tace munafuka kya fadi gaskiya ma,Zainura sai zaro harshe waje take wai ana shaketa,Sakeena bakin ciki yasa tace da Irfan An mata sharri a gidansu kanwarsa har sharrin maita zatayi mata akan tace tana sonsa za a wulakantata to wlh in anyi duniya dan Manzon Allah na hakura har ni zaka sa kanwarka tayi min sharri,akan na zubar da ajina nazo gidanku,ai ko mutunci da muke bai ci ace an min haka ba,aiki a company naka ma na barshi ka nemi wata,Irfan yace ba kanwata bace,Sakeena tace haske ka fita gata nan kuna kama itama me kyau,yace to tayi din ke ni nace ki zo ko nace ina Sonki zaki dameni,nan sukayi kaca kaca da Irfan Sakeena tayi waje kamar zata tashi sama.