KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zainura tace ni fa ba yanga nake ba kawai kwana biyu ne Bana Jin magana amma ai kasan dai inayi jiya ma ai ka dakko ni a schl kuma ai munyi hirarmu ko,ae na sani nafi so kullum na dinga ganinki haka,Zainura tayi dariya tace to insha'allah zanyi,yanzu me kike so za kiyi?na baki kudi? Zainura tace ni bana son kudi fa ka daina yi min zancen kudi idan ina so zan fada ma,lefen kin gani sunyi?ko akwai abinda za a canja? Kayan sunyi yawa ma fa akwati set sunfi 12 har yanzu ban gama kallonsu ba,da baka da kudi sai nace ka rage ka siya mana kayan abinci amma tunda me kudi ne ba ruwana.
Mata da yawa suna shawarar kayan lefe da saurayi amma basa shawara ta kayan abinci,sai kaga mace tasan mijin da zata aura bashi da wani karfi wai sai ta bashi common body cream din da zai zuba a lefen sai ta bada me tsadar wasu Dubu Hamsim guda daya,wani ashirin,sha biyar,wanda za ace ma sanata ko dan majalisa ne zai iya yi miki wannan,ba ruwanta da me zasu ci nan gaba,maimakon suyi shawara ayi komai na hankali sai kawai ta barshi a gama biki ba abincin shekara daya ko biyu,sai ya dogara da gara da iyayenta suka kawo,gara tana karewa zuciyarsa ta mutu an kashe masa zuciya sai ki ga ko yana da halin yana kasa siyen abinda take son taci,ko kuma iyayen nata basuyi mata gara me yawa ba,ko ma basuyi fa wuri ba,shi kuma kudinsa ya kare kat,sai kika sai katon gida da sutura store ba komai a ciki sai dan mitsitsin buhun shinkafa irin dan karami,sai dan gishiri komai sai dai a dinga dan cefano kadan,Yar taliya guda uku a gefe,doya uku a jingine,sai ta fito tana taku dai dai cikin sutura gidan ba abinci,me kenan to ya kamata a dinga Zama ana fahimtar juna,wasu kuma mazan idan ba a lefen ba ba ta inda za a moresu,sai a fahimci halin mutum ayi shawara mai bullewa sai a zauna lfy ba tare da an takura mutum ba an shiga hakkinsa ba.

Bayan Sati biyu biki ya rage Saura sati daya kenan,mummy tace baza ayi party ba,Daurin aure kawai za ayi da Walima,da yamma suyi Dj a gida shike nan da dare a kai Amare ba wani party da za ayi ta faman yi.
Su dai Angwaye sunfi so ayi party amma Mummy tace a’a baza a wahalar da kowa ba.saura kwana Uku biki su Barira frnds din Zainura na kauye kaf Malam yasa aka kwasosu za a Sha biki dasu a birni,ko wacce da hakorin makkanta da taje aikin Hajji ta gallako guda,Zainab harda saka guda biyu irin shegiyar nan daya sama daya kasa kuma sun mata kyau abunta ta Zama Hajiya wai,baki yan biki duk Wanda ya gansu sai yayi dariya gaba daya ko wacce da hakorin Makkah kamar masu anko.
Mamakin kyan gidan su Irfan suke kamar ba a duniya ba,Zaunura ta karbesu hannu biyu ita da Salma,dakin Zainura suka sauka wai su nan zasu zauna har a gama biki,Hunaif da Irfan tare da Salma yanzu dakin Zainura ya Zama majalisa nan suke haduwa dasu Jamila aci dariya har a gaji suna nishadi,su Hunaif susha labarin dariya kamar me,idan kaga Na’im a ciki to Salma yazo nema kawai baya bata lokacinsa.

Sunyi Sallar Isha sunci abinci Saura kwana biyu biki,Zainura duk ta karbo musu dinkinsu ko wacce kala Uku masu kyau,Atamfa,lace da shadda,sai murna suke zasu sa kaya me kyau dinkin yan Birni.
Yan Uwan su Hunaif ma da Amaryarsa Afrah duk sunzo Larabawa part dinsu daban suma gida ya cika da yan biki kowa da bangarensu,Zainab da su Barira duk suna kwance saman bed suna ta zuba surutu,Zainura ta shigo taci uban takalmi me tsini wai zasu fita da Irfan,Barira tace ke Zainura Wallahi kema kin Zama yar gayu har kinfi ma yan birni,Zainab tace ai wanka sai Salma mayyar kamar a jikinta aka kirkireshi,Jamila tayi shewa heeeee Zainura dadi miji tun ba a daura ba ya fara daukanki yawo ai dole ya dan eh…hhhh suka sheke da Dariya,Jamila tace to nima Alhmdllh sanda muka je kano Gidan Rahina nayi Saurayi dan Birni sunansa Mahmud kuma yace da gaske yake zai aureni,Zainura tace Na miko murna bari naje Baby yana jirana,Zainab ta bude baki tare da cewa kamar wani jariri dama ana fadawa babban mutum Baby haka sangangan dashi kice wani Baby gaskiya ki canja masa Suna ina laifin ma kice Me gidana ko Yaya,Zainura ta rike baki see ur face Me gida or what so ever u called it an daina yayin wannan sai kauye,ku bari na dawo na baje muku labari,to muna jira,suna haka sai ga Irfan yana Precious let’s go kin shanyani,Barira tace wannan Kalmar sai dai mu shiga dictionary Zahra’u kin iya duba kalma ki duba mana ma’anarta,Bari Salma tazo iyayen turanci ta fassara mana,Rahmatu tace nima ina yin Aure zan dinga cewa mijina Babyna yasin sai dai a yankani amma billahillazi sai na fadi hakan,Z Zainab tace yo tun yaushe ma Wanda yayi magana ya raina uwatas ni Darling ma zance masa naga shegen da zai yi magana,ai ina cewa Darling akace nayi Iskanci to Alqur’an ta Salma zanyi Na koma ce masa Honey yasin.

 Zainura suna mota yana driving yace Mummy ta bani aiki ni ban san me za ayi miki a gidan matar da tace sai na kaiki,Zainura tace zai wuce gyaran jiki ne,wannan gyaran jiki bazai kare ba kullum gyaran jiki wai me akewa fatar ne haka? Zainura tace ina zan sani nima wani daki ake cewa mu shiga yana fitar da tiririn Zafi sai kaga skin yayi smooth shike nan fa,Irfan yayi dariya Allah Zubaida ni zaki rainawa hankali bafa Audu me kifi bane,au dama ka sani kake tambayata Ashe? Na sani mana zanji dadi gaskiya,Zainura taji kunya harda rufe fuska Auzubillahi,bayan ya kaita saida ya jira ta gama sannan ta fito suka tafi a hanyarsu ta dawowa ya siya musu kaji, ice cream da snacks ta bawa su Jamila kawayenta,taji dadi sosai sai godiya take masa,tana shiga ta zube musu ledoji tace gashi nan Baby yace a baku,Rahina matar Abubakar itace ta bude ledar tare da lekawa tace Wai cakwala dadi sai ko suka taso suna ci suna Santi,Jamila tace kai Zainura kinyi dace,Zahrau ta yagi kaza tace Wai cikinsu wa yafi wani kirki ne,Rahmatu tace ai mijin Salma da ya kaimu Makkah shine na farko,Sai Hunaif kullum da muka zo shi yake kawo mana kayan dadi,kalli dunkuna ma duk shi ya siya mana ya biya kudin dinki emergency,Zainura ta bata rai tace ae wato Irfan din nawa ne tsinanne,Rahmatu tace shi Irfan shine yasa aka kaimu Saloon ya biya kudin ko wacce aka yi mata na yan gayu,yasa aka dauko mana me lalle tayi mana,ga kudin liki duk ya bamu,gashi yanzu ya mana siyayya,Zainab tace kin manta har takalma ya bada kudi Salma ta siyo mana masu kyau na birgewa sabo da mu fito Shar muma,cikinsu kowa yana da kirki ba baya,Zainura tace to dai Irfan dina yafi kirki,sannu sarkin Son kai ai wlh mijina yafi na kowa kirki da komai Salma ta furta da shigowarta kenan,suna Zaune sai ga Hunaif tare da balarabiyarsa Afrah sai fara'a take bata Jin Hausa sai dai suyi turanci,wai kawota yayi su saba da Salma da Zainura sannan ta shiga Hausawa yan mata itama,sai dai tayi ta dariya tana kallonsu bata San me suke cewa ba,Salma da Zainura kadai ke mata turanci duk da cewa Zainura bata gama gogewa ba a turancin amma tana kokari,sai dai idan wata Kalmar ta gagareta tace ke ni ban sani ba.

Yanzu ma Zainura tayi turancin tayi ya kare mata ta manta kuma me zatace ta kalli Afrah tace ke dan Ubanki nima bafa wani kwarewa nayi ba,Afrah ta mata zancen kurame tana dariya me tace? Zainura tace ai wlh bazan kara yin turanci ba yau na gama baza ki wahalar dani ba,Tace what? Tana tambaya Still Zainura tace Wai cewa nayi Ubanki ko bakyaji? Tace I don't understand what do u mean? Zainura ta fara shure shure wayyo ni wlh an takura min sai nayi turanci nima fa ba gama iyawa nayi ni wlh bazan yi ba,

Afrah ta dinga dariya abinda taga Zainura tanayi na yara,Salma tayi dariya taci gaba da hira da Afrah,zainura ta fara masifa ke Salma dalla mene zaku hade min kai ni salon a wareni ko faccalanci zaku nuna min tun ba ayi auren ba,Allah shiryeki Zainura cewar Barira,Jamila ta kalli Balarabiya ta tuno da Islamiya yanda suke cewa malami,tace Sabahul khair ya Afran Hunaif,suka sheke da dariya,Zainab ma tace bisalam sai tace mu’assalam ya mu’allim ko ba haka ba Afrah? Afrah dai ta gane Larabci wai suke mata kadan,Kawai ta daga kai tana dariya,Zahrau ma tace nima sai na fadi nawa tace Afrah Ijilis,Jalasna ya sayyadina,Afrah ta dinga sheka dariya ta kara daga kai sannan ta fadawa Salma da turanci cewar Larabcin ai kala kala ne,wannan Bana kasarsu bane Saudiya suna yin irin wannan da suka fada duk da cewa harshensu bai iya fadi dai dai amma Na saudiyya ne,Zainura tace Ashe kunji bayin Allah a larabcinma akwai broken kamar turanci akwai Broken pidgin English,Dariya Sukayi sukace Ashe nasu ma Broken sukeyi ba irin na Saudi bane,cab Ashe ba larabawan kirki bane cewar Zainab gashi tun ba a je ko ina ba har mun kureta,Zainura tace ke Afrah mene Habbibty? Habibi ta fada musu ai kuwa Zainura tace yanzu Irfan zata dinga fadawa Habibty kar taji a bakin Afrah tana fadawa Hunaif shi ta rigata,Afrah ta dinga dariya harda kwalla tunda da turanci Zainura ta fada mata.
Zainab tace yawwa Zainura yama tallan da muke gani a TV din gidan Sale?wannan na madarar?cewar Rahmatu,Zainura tace Labanil mara’i Almara’i bari muji ko suna shanta,Zainab tace Afrah what is a Labanil mara’i Almara’i hhh Zainab anji turanci,Afrah tace ai wata madarace ta wani Company,Sai Jamila ace Al filun,ishajartu,jamalun,kalam,dar,Hazihi,Hazihi dar,Zainura tace kin manta Alburtuqal,Baqaratun cewar Zahrau itama,Sirasil,ankabut haka sukai ta faman jerowa Afrah tana ta fada musu amsa da turanci tana dariya,saida suka gaji sukace to taci jarabawa amma da bata amsa wannan ba koma mece ba Balarabiya bace kawai yar gudun hijirace daga wani yankin cewar Zainura,Salma tasha dariya kamar me,basu da aikin yi sun gama komai har lalle Mummy da safe da wuri tasa akayi musu komai,tace bata son ana biki Amare basa nan ayi ta batawa mutane lokaci wajen gyara,shi yasa komai akayi akan lokaci aka gama ba bata lokaci,Da kyar Na’im yace Mummy ta bari ayi wedding dinner guda daya tal ,haka ta hakura suka shirya komai,Friday gobe kenan za a daura aure da walima,da yamma za ayi Dj a gida kowa ya cashe, Saturday wedding dinner da dare,Sunday sai a kai Amare,Irfan yace shi a kaisu Saturday sai suje Dinner daga gidan mijinsu,Na’im ma yace haka,Mummy tace sai Sunday sabo da su sukace zasuyi Dinner baza su ruda su ba,ga shirin Dinner ga kai Amare kuma har Uku bazai yuwu ba,komai a nutse zasu yi.

 Barira taje wajen Mummy tace su dai wlh sai sunyiwa Amare kamunsu na kauye,a bawa Salma turare itace matar yaya tazo ta kama Amare ko a bawa Umma tazo ta fesa,Zainura tace Salma kawarta ce wlh bata isa ta mata Kamu ba sai dai a bawa Umma ko cikin danginta na kauye da suka zo,Iyayen Zainura ma suna nan sunce ba sai anje kauye daurin aure ba su zasuzo Abuja sun hutar dasu Mummy ai suma iyayen Zainura ne,shike nan kuwa har dangi masu zuwa suka zo bikin suna gidan part din Umma da Malam suka sauka,Baba zainura da danginsa Maza duk Malam ya saukesu bangaren maza baki.

Salma harda hawaye takeyi ganin dangin kowa ya hadu amma ita babu nata ciki,sai Umma da Malam sai dangin miji,bata da kowa nata,sai ta fashe da Kuka ta koma part din Na’im ta kwanta Saman bed dinsa tana ta kuka,ya shugo bayan ya dawo daga Masallaci Sallar Isha ya Iske Salma tana ta faman Hawaye da shesheka,da sauri ya karasa kusa da ita domin shi baya ganinta sosai ma tunda aka kusa biki,Ba dai kuka kike ba Sweet Baby?lfy? Salma ta kara Volume harda na shagwaba,duk tunaninsa wani abun akayi mata,subhanallahi me akayi miki? My love what’s the Matter? Wa ya taba min ke? Fada min wanda ya batawa Amaryata rai,fada min wanda yasa Preetyna kuka take asarar tears haka,Salma cike da shagwaba tace ni…ni….ni…bani da yan Uwa…kowa yana da Uwa da Uba..da…danginsa…ni…bani..da ..ko..daya,Hawaye sukaci gaba da sintiri.
Na’im yaji tausayinta har cikin bargonsa am so sorry Wifey da ina da yanda zanyi wlh da yau sai na kawo miki yan uwanki gidan nan,kiyi hakuri kinji watarana sai labari,zasu zo ne kuma Insha’allah ko ba su zo ba zan je na basu hakuri nan gaba mu lallashesu ko? Salma ta daga gai yes,yace yawwa yan matana yana share mata hawaye da hannunsa,kar na kara gani kinmin asarar hawaye akan wannan ya wuce za ayi maganin abin trust me ok,tace tam tana ajiyar zuciya,kin min abincin? Salma tace ae dazu na gama,Mummy tace akwai a kitchen kar na dafa wani nace mata baka cin abun gidan biki,Na’im yace yes hannu yayi yawa,duk mata sai ayi jagwalgwalo,Salma tace to ai ba a gidan nan akayi ba restaurant aka kai suka yi ake biyansu,i knew Sweet Baby Bana cin nasu ne kema kin sani abincin restaurant sai dole nake ci,sabo da ko nama ne sai suje wajen siya baza su siyo me kyau ba sai marar kyau,Salma tace wasu ma sai suce idan an yanka akuya,tinkiya,ko Saniya masu ciki sai suce dan cikin suke so shi zasu siya yafi laushi da dadi,idan suka kawo sai sharp sharp a zabga farfesu ko girki dashi,kana ci kaji laushi da zaki limis kana ai sun iya girki shi kanshi naman daban ne Ashe ba a sani ba dan jaririn dake cikin Akuyarne ko Saniya,hhhh Na’im ya dinga dariya yace to kingani anci kazanta,Salma tace ko sai sunga naman da aka tare waje guda baida kyau za a zubar sai su siya a araha su kawo restaurant,haka kayan miya irin su tomatoes ma idan kaje layin marasa kyau gwalagwaje shi suke siyowa a gyarashi a Markade kaji ance rice and stew hhhh nan ma Na’im yace wai gwalagwaje banda Sharri Sweet wife,Salma tace Allah ba sharri bane a Nigeria da yawa haka akeyi,kaje mayanka wajen da dabbobi kawai ake yankawa ka gani,sai kaga Hajiya tasha kaya tazo a mota da Leda katuwa suna ta siyan jariran saniya ko Akuya ko marar kyau,haka kayan miya ma kagansu ana ta sa musu a leda suna figar motarsu,hhhh Na’im ya kara dariya yace gwara da kika kara gaya min gaskiya amma suna cutar da alumma a Nigeria shi yasa ba a ci gaba kowa zalunci da cuta yasa a ransa,Salma tace ga son Banza.
Na’im yace yanzu da ke ana abin kirki dake da kin dan jiyar dani dadi,Salma ta turo baki ka bari ni dai Allah sai jibi an kawo Amare,na hakura ai Allah ya kaimu,kuma ki tabbatar ranar kisa nayi suman Dadi ko nayi kuka sosai idan ba haka ba to Kin San sauran kema.
Dariya tayi tare da yi masa rada a kunne ta fece da gudu ta bar dakin,yana zuba murmushinsa me kyau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button