KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sati biyu Afrah ta gyaru ta gane komai,ita kanta yanzu tafi jin dadin jikinta bata kwanciya kullum ba exercise aikin gidanta shine exercise nata ana motsa jiki ana kara samu lafiya da karfin jiki,kullum cikin kazar kazar,Girki kuwa ta fara iyawa da yawa Salma ma tana koya mata wasu,Zainura tayi namijin kokari sabo da kullum sai taje a Keke,yauma ta dawo suuuuu a keken ta hango Irfan,Na’im,da Hunaif suna tsaye suna tattaunawa sai nishadi da zumunci sukeyi,su Kansu sunyi dariya ganin Zainura a keke tana ta tsere da keke a gidan nan,Shi kanshi Irfan Bai taba Sanin ta iya kekenta ba sai yau,sabo da bai San tana hawa ba,tunaninsa ma a kafa take zuwa har gidan Hunaif tunda tace masa itama exercise zata fara,ashe a kekensa take zuwa,dariya suka dingayi,Na’im yace matar nan taka bata Ji akwai kiriniya,Irfan ya daga mata hannu ta daga masa itama ta figi kekenta tayi part dinta ta koma ciki,ta huta sannan ta tayi sabon wanka ta dau wankan kananan kaya na daukan magana tare da fadawa kitchen tana shirya abinci.
Ta baya Zainura taji Irfan ya rungumeta yana sinsinar wuyanta tare da shakar kamshinta,ba tare da ta juyo ba tace sannu da Zuwa habibty muje ka huta,nooo… Muyi girkin a haka,hannunsa suna rungume da hips dinta ya kwanta a jikinta gaba daya a haka suke aikin,Zeena ta mika hannu zata dauki plate hannunsa a haka ya dauko mata yana jikinta,sai ya karbi spoon din yana juya abincin kuma still yana rungume da ita kwance a bayanta hannun kawai yake dagowa daga hips dinta yayi abinda zaiyi ya maida abinsa, tana soya naman kaza yana dauka a haka ya ci itama yana bata a baki.

Afrah kuwa yau tuwon danyar shinkafa tayi miyar egusi tayi dadi sosai,Hunaif yana son sa sosai ya dinga murna yana godewa Afrah,ita kuma sai dadi take ji tare da godewa Zeena,Afrah ko Dattijuwa me taimaka mata bata bari ta zauna a Palo idan Hunaif yana gida tsoro wai takeji Kar ta kwace mata mijinta abin alfaharinta.

Kwance take cikin  Jin dadi amma abu daya ya hanata sukuni wato rashin su Affa a kusa,i dan ta tuna yanda suka riketa da Amana tun tana karama amma yanzu gashi lokacin da zasu ji dadin abin basa tare,tana tunani bata San Sanda hawaye ya fara sintiri a fuskar ta ba, tana wannan Na'im ya shigo yana Sallama amma bata San yanayi ba,ganin tana kuka ya karaso da sauri tare da mikar da ita zaune ya daurata a jikinsa yasan bazai wuce su Affa take tunani ba,tunda ita Salma dasu ta shaku sunfi kowa a wajenta,Na'im yace su Affane? Ta daga kai cike da shagwaba,its ok ko kidnapping dinsu wlh zanyi na kawo miki su,ko suna so ko basa so Salma na sai na kawo miki su very soon surprise zan miki ina sane dasu,sai lokacin Salma tayi murmushin jin dadi,yana lallashinta yana lashe mata hawaye da harshensa har ya samu tayi shuru sannan ya dauki abarsa suka shiga wanka.

Ayi Sharhi fans,kar a gaji.

AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????

221-225 256-230

Official

By
AsmaBaffa

   ASMABAFFA FANS CLUB INA MATUKAR GODIYA.











Bayan sunyi wanka zaune suke yana dan janta da surutu ko zata daina tunani amma bata wani magana sosai,kallonta yake a nutse kana yace wato sweetheart ban isa nace ki daina abu ko daina ba ko,su Affa nace Insha'allah zan kawo miki su mene abun damuwa,haba Babyna,why r u doing ths to me? Salma Hawaye taci gaba da yi abinta,yana kallon ikon Allah dazu fa ya lallasheta,tana shesheka tace na...dai...dai....na, baki yarda dani ba My love?nace miki zan kawo miki su kuma insha'allah zasu dawo dake kamar da,Salma a hankali tace Na yarda mana,amma kike kuka again? Cike da shagwaba tace ai na daina,kwantar da ita yayi saman Bed din rabinsa yana samanta,fuskarta yake shafawa a hankali ya hade fuskarsu tare da furta Smile Baby,murmushi tayi masa me shiga zuciya, nan take wani shauki ya kwashe shi ba bata lokaci ya mika lips dinsa tare da niyyar kissing dinta itama ta miko tare da lumshe ido sai ya fasa,sai ya kara haka,haka har ya hade lips dinsu yana kissing kadan yana janyewa har ya yi me gaba daya wato ya fara mata hot and deep kiss har hakoransu suna haduwa,tuni Salma ta karbi sakon hannu bibiyu.

 Yau kimanin wata 3 kenan da auren su Zainura Soyayya suke zubawa kawai,sun kusa tafiya Saudiya,Zainura taje gidan Aisha tare da Afrah,Salma ce bata je ba tukun,Mummy kuwa suna sosai suna gaisheta,zaman lafiya suke ba a magana.
Aisha ma sunzo da Doctor Aliyunta sunyi zumunci,Kwana nan kuma Zainura ta fara Dan Zazzabi da tashin zuciya sama sama,Yau Saturday Irfan yana gida zaune saman Sofa dake palon,tun safe Zainura bata iya cin komai tashin zuciya take,Tana gefensa yana lallabata taci ko kadan ne,tace Sam idan ba yashin Madina ba babu abinda zata iya Sha,Da sauri ya fita har wajen Tsohuwar nan dake Islamiyyar yara ya siyowa Zainura Yashin Madina da yawa,ta zauna tana ta sha kamar ta samu Nama,tana gamawa tace yaje gidan Salma ya karbo mata Wainar flour da danwake,haka yaje duk ya damu,Na'im yana gida yana shagalinsa a jikin Salma,Irfan yaje ya dameta yayi sauri ta yiwa Zainura abinda tace,Na'im yace idan zaka kaita hospital ma ka kaita ba kazo ka damu mutane ba,Irfan bai ce komai ba ta lafiyar Zainura yake,ana gamawa ta bashi a flask ya tafi da sauri ya kai mata,tana ci tana murna,abin Zainura bai tsaya nan ba sai da yaga ta fita neman inda ake siyar da agwalima,yaje ya siyo mata yace ta shirya su tafi asibiti,asibitin Na'im suka je ya samu Doctor mace ta aunata tare da tabbatar musu cewar ciki ne da ita har na wata biyu da sati biyu,Zainura harda Rawa sabo da murna,Irfan kuwa kamar ya tsage da ihun murna haka yake ji,Suna parking a compound Zainura ta fito kamar wasa ta dage ta kwalla da karfi jama'aaaaaa.......I naaaaa...da.....cikiiii,kuuuuu.....fito....ciki...ne dani....Irfan yana dariya yazo shima ya tsaya kusa da ita ya dage da karfi nayiii....mataaa....ciki....sai....niiiii.....kyakyawan result har ya fito,Zainura tace sai....mijinaa...me....lafiya.....Wlh...good...job..suna ta dariya tare da Haki, duk yan gidan da ma'aikata sai da suka fito da sauri sun dauka wani abu ne tunda basa iya jin me akewa magana kawai suke ji da karfi,Sai da suka saurari abinda su Irfan suke cewa sannan suka gane, ai Salma da Afrah kamar sune da cikin,ikon Allah Salma ta riga aure da wajen shekara ma amma ga Zainura ita wata Uku kacal har ta samu ciki,
Na'im da Hunaif sai murna suke tayasu haka matan ma da ma'aikata,ba bata lokaci suka kira Mummy suka fada musu da abokan arziki,har na kauyen su Zainura frnds,iyaye da yan Uwa sunji labari ta waya.

Zo kuga kula da Zainura wajen Irfan Kamar wata kwai.

Wata daya tsakani suka bar kasar zuwa Saudiya,Na'im da Salma,Irfan,Zainura,Hunaif,Afrah,Aisha tare da mijinta Doctor Aliyu,suna gama aikin Hajji suka suka tafi Lebanon ansha riti,sai USA,daga nan suka dawo Nigeria,Zainura da Irfan sunje kauyen iyayenta kwanansu uku  sunsha hira dasu Jamila suka dawo gida,Jamila ta samu miji a birni itama,Haka Zainab cikin Katsina,sai Zahrau Kd,Barira kano kusa da Rahina a nan ta samu miji,duk an sa ranar bikinsu,Rahmatu ma wani dan Uwansu aka bata dake Zaune a cikin dutse Jigawa state counselor ne a can dutse alhmdllh sun samu nutsatsu samari duk da cewa Zahrau ce kawai zata auri wani me mata me kudi dan 40yrs duk sauran masu rufin asiri ne amma samari kuma wayayyu yan Birni.

 Bayan wata biyu da dawowar su Salma daga Saudiyya Afrah ma ta samu ciki wata daya,lokacin na Zainura har ya girma ana ganinsa,Itama sai murna kowa ta fara iya hausa yanzu,Salma har tausayin kanta taji,sai tunani take ko bata haihuwa ita Na'im zai iya karo aure wata ta haihu,hankalinta ne ya tashi duk da tana kokarin dannewa tana addua tare da turawa Allah Lamarinta,bata gama tsurewa ba sai da taji cewar Aisha ma ciki ne da ita na wata biyu,Allah sarki Salma ranar sai da tayi kuka a boye na tausayawa kanta.

Gashi sai taga Na’im normal harkar gabansa yake ko a jikinsa,tana so ta masa zancen ko zasu je asibiti amma tana tsoro.

  Tana zaune a Palo ita kadai tana tunanin halin da take ciki ita har yau ko bari bata yi ba,katsam sai ga Na'im ya shugo bayansa Ummitu da Malam ne Shar dasu gaba daya babu alamar cewar Affa yayi wata cuta,haka Ummitu babu maganar wahala a jikinsu kamar ma sun Zama yan Birni haka suke,a rude Salma ta Mike harda kukan Dadi,Affa da Ummitu suka zube a kasa tare da fara bada hakuri,Salma da sauri ta katsesu haba Ummitu ashe ma zan bar iyayena na jini su bani hakuri,ai ni ya kamata na baku hakuri,ku zauna dan Allah Affa in ma nice na yafe muku kuma ku yafe min,Ummitu tana kuka tace baki mana komai ba yar nan mu ne da laifi sabo da son zuciya,yanzu mun gane gaskiya,Allah yayiwa mijinki Albarka,kinyi dace Salma,Salma tayi murmushi sannan Ummitu ta bata labarin halin da suka shiga da cutar Affa,Salma harda kukan tausayi,sannan Affa yace mijinki shine silar warkewa ta,muna zaune cikin kunci katsam sai gashi yazo da motoci,yana ganin halin da ya samemu yasa aka kwashe mu har birnin Abuja cikin asibinta sa shine yayi min magani ya kashe makudan kudi na warke,haka bayan na warke ya mai damu gidan kakarsu Dada a nan aka bamu bangare guda,da masu aiki bama komai sutura da komai sai dai mugani ya kawo ko ya aiko dasu,yanzu in kinga jin dadin da muke,kuma Mummy mahaifiyarsu da kowa nasa ya sanni ke kadai ce baki sani ba,har su Zainura da Afrah sun San damu,yace kar a fada miki sai mun murmure munyi kyan gani sabo da idan kin ganmu cikin wahala hankalinki zai tashi.

Ummitu ta kara da ki godewa Allah Salma kinyi miji managarci,ki dage kiyi masa biyayya haka suka dinga Kwara addua suna yiwa Salma nasiha,Salma kam ita bata San ma wacce godiya zata yiwa Na’im ba abin yafi karfinta,suna ta hira dasu Ummitu har dare sannan Driver ya maidasu gidan Dada,Salma tace itama gobe Zara zo musu yini,a bedroom ta iske Na’im yana aiki a system jikinsa ta fada tana ta murna da jin dadi tana masa addua da godiya har sai da yace ta daina ya isa haka,tace ni ban san me ma zan maka dan na faranta maka ba ka gama min komai a duniya,Na’im yace akwai mana kema kin San me nafi so sai ki min,Salma ta rufe ido a kunyace tace Allah yasa kayi min ciki,Na’im ya kalleta tare da cewa yanzu kuma matsalarki kenan?wannan bani nake badawa ba sai ki roka wajen me azurtawa,Salma tace uhm Insha’allah ai amma ka dage,Dariya yake yace taya zan dage?duk wannan abun Baby bai isa ba?Allah ne bai kawo ba zai baki kema naki Bana son kina damun kanki,Salma tayi shuru da ita yanzu kuma ta gama matsalar su Affa ma kawai Haihuwa ce take damunta,Maganar Na’im taji yana mata nasiha da karbar kaddara me kyau ko marar kyau.

Salma dan Adam dole baya Zama babu wata jarabta,wani damuwar mutum ko kashe kansa zaiyi sai sanda Allah ya yaye masa ita,addua kadai ke sawa ana iya canjawa mutum ko rage wahalar ta,ki barwa Allah komai,mutane nawa basa haihuwa da wuri amma mu har yau bamuyi 2yrs bama kin damu kanki,ki godewa Allah da muke da lafiya,Nasiha ya dinga yiwa Salma sannan ta dawo normal ta daina damuwa,amma duk da haka idan ta tuna takan shiga damuwa.

Zainura kwance take a jikin Irfan yana mata tausa tare da lallashinta,Zainura tana shagwaba cike da salo tace Habibty Allah ka bani wahala,cikin nan ya girma amma baza ka dan hakura ba sai na haihu,Irfan yana murmushi me dauke da nishadi ya furta taya ina da kamar ki zan iya hakura Mine?ina ganinki kema kin san bazan iya ba,yanzu idan ma kin haihu tausayin kaina nakeji wanne Hali zan shiga,Zainura tayi wani fari da Ido tare da lumshesu ta kara wani kyau,Irfan ya shagala da kallonta iska ta hura masa a Ido kadan,ya dawo daga tunanin shaukin Zeena dinsa daya fada,gira daya ya dage mata tare da kashe mata Ido daya kyawunsa ya kara bayyana,Zainura taja ajiyar zuciya,Habibty kai me kyau ne,kin fini kyau Zeena,yawwa Habibty na tuna kaga fa ka hanani komawa schl,ina ss2 kace sai dai na zana Waec da Neco bayan na haihu amma zaka nemo min University ko? Irfan nan take ya bata rai tare da cewa a'a me kike nema My love?nifa ko kinyi karatu bazan barki kiyi aiki ba,yanzu so kike ma ki koma schl yanda kike din nan maza suna kalle min ke,nasan lokacin kin kara girma kin kara Zama yan mata kinga maza zasuyi ta damun matata,Zainura tayi dariya tare da cewa Habibty ka fiye kishi ni dai dan Allah ka barni nayi ba sai nayi aikin ba to,zan barki amma Bana so sai dai na hakura haka.

Afrah cikin nan nata wahala yake bata,tana laulayi sosai,Hunaif wani kara sangarta ta yakeyi sai abinda tace kamar a jikinsa cikin yake,ko Office bai fiye fita ba kullum yana wajenta,Haka Aisha matar Doctor ana zuba Love da dan cikinta a gaba, yana kula da abarsa kamar me.Na'im ya biyawa Affa da Ummitu Saudiyya suma zasu tafi tare da Mummy,Harira Da Masa'udu sunga yanda dare daya Allah ya Azurta Affa ta dalilin Salma,haka mutan kauyen sunsha mamaki domin Affa har jama'a ya tara a kauyen ya sanar musu irin abinda suka yiwa Salma,da kansa ya wanke Salma tas a kauyen a daina zarginta,Gashi kuma Salma ta daukesu ma gaba daya sun koma Abuja makeken gida sai abinda suke so,har kauyen suke zuwa a dalleliyar mota driver ke kawo su suyi musu kyauta tare da dangi albarkacin Salma yar riko,Harira sai wani noke noke takeyi anji kunya,sai dana sani take marar amfani,Masa'udu ma da sauran dangi sai kunyar abinda sukayi sukeji suna dana sani,dama duk abinda akayi hakuri zai wuce komai dadewarsa.

Salma yanzu tafi kowa gata iyaye hudu gare ta,ga danginta su Shehu yanda suke ji da ita kamar kwai,Malam da Umma,Affa da Ummitu,ga kuma Mummy uwar mijinta,tun kafin Na’im yace yana son Salma Mummy ta dauki Salma a matsayin yarta.

 Cikin Zainura ya cika wata tara cif Haihuwa kawai ake jira,Irfan baya fita aiki sabo da Zainura,yau Monday yace bari ya leka Office ya dawo da wuri zai ga wasu mutane,Zainura tace Habibty kullum baka fita sabo da jiran haihuwa gashi har yau Bana jin wata Haihuwa,yaune ma kawai nake jin ciwon Mara kadan,Irfan yace ai yanzu zan dawo ciwon Mara ma ai kwana nan kullum dai kin ce kina yin kadan,Salma sukayi ya fita da niyyar ya dawo da wuri,Bayan ya fita da 1hr Ciwon Zainura yayi karfi sosai da sosai,tun tana iya daurewa ta kasa,Waya ta dauka ta kira Irfan bata shiga ba,Sai ta Kira Hunaif bugu daya ya daga,tace Kanina kayi sauri kazo dan Allah ka kaini asibiti maybe Haihuwa zanyi,Habibty ya fita wayarsa bata shiga,kafin ta karasa magana tuni Hunaif ya kashe wayar yasa Afrah ta shirya su tafi dama shi yanzu baya fita,da sauri yazo da mota suka dauki komai na haihuwa suka tafi asibiti,Zainura tana bayan Mota tana daurewa bata cewa komai,Har sukaje Hospital din Na'im,Allah ya taimakesu ana bawa Zeena Room ta Haihu,kamar dama jira ake,Ta haifi danta Namiji kato kyakyawa na gasken gaske.bayan an gama komai sannan Aka sanarwa su Hunaif,Afrah dama tana ciki wajen Zeena,Zainura ta hana su fadawa kowa tace dan Allah karsu fada,Wanka tayi ta shirya tsab kamar ba ita ta haihu ba,Afrah ta dauki dan cikin kaya masu kyau farare,suka shiga mota sai gida.

Lokacin Irfan ya dawo yana tunanin Zainura ta shiga wajen Afrah ko Salma yana jira ta dawo sai tsaki yake ja,Doorbell ce tayi kara ya bude kofar Hunaif ya fara gani,Sai Afrah dauke da Jariri,Zainura ta fito itama charas da ita kamar ba ita ce me jegon ba,binsu yayi da kallo yana mamaki ganin Zainura ba cikin kenan haihuwa tayi,Hunaif yayi dariya sannan ya sanar masa da komai,Naushin Wasa ya kaiwa Hunaif wai basu fada masa ba,nan ya dinga murna tare da karbe dansa yasha addua,sannan yace su Afrah suje gida su huta zai fadawa Mummy yanzu sai a turo dattijuwa me aiki ta zauna tare da Zainura,Haka kuwa akayi,yan Uwa da abin arziki kauye da birni kowa da suka San Irfan da Zainura sunzo,amma baza ayi suna ba,kawai a masallaci za a rada suna ayi yanka shike nan ba wani taro,shi yasa ko dangi da frnds na Zainura daga na birni har na kauye barka suka zo suka koma,jariri yaci suna Arif.
Bayan suna da kwana hudu Zainura tana kashe wanka na tashin hankali,Irfan kuma yace Bai San zance ba,sai dai su rabu da kyar ko ta gudu,h aka sukeyi har Allah yasa tayi arba’in,tasha gyara wanda yaci Uban na Amarya,Zainura Abar kallo ta koma sabo da kyau da tayi,Irfan ya kara rudewa kamar wanda za a kawo masa sabuwar Amarya haka yake zumudi, yafi me Sabuwar Amaryarma murna.
Jariri Arif kuwa yana can shi da dattijuwa me rainonsa tare da taimakawa Zainura da wasu ayyukan,Zainura yau Angon nata ko kuda baya so ya giftasu,sun gurji Amarci son Ransu,sun nunawa juna so,sunyi missing juna,wannan rana ta shiga cikin ranaku mafi girma a zuciyarsu,Zainura wannan game din ita ce jagoran bugata,har kyautar mota Irfan ya bata sabo da dadin da yaji tare da farin ciki,Allah sarki Salma sai yanzu ta samu Hutu,tunda Zainura ta haihu take sintiri a gidan Zainura tana taimaka mata,hakan har fushi Na’im keyi da ita,Na’im yana matukar son Arif ji yake kamar ya daukeshi.

 Bayan wata Uku da Haihuwar Zainura Afrah ma ta haifi danta Namiji kato balarabe sak,Itama ba shagalin suna a mosque aka rada tare da yanka mata raguna guda hudu manya kamar na Zainura,Yaro yaci sunan Babansu Alawwal suna ce masa King,wata daya tsakani Aisha ta Haifi yan biyu mace da Namiji,ansha murna da tsalle sabo da Doctor Aliyu danginsa suna da gadon haifar yan biyu,ga Aisha ma ta haifa amma Aisha ita sai da akayi shagalin suna a wani hadadden waje cikin Abuja suka kama anci an Sha an cashe,yara sun samu suna Suhail da Suhailat abinsu Shar Shar dasu.

 Ranar da dare da suka dawo daga shagalin sunan da dare wurin 2am Salma Kuka ta fara wiwi na tausayin kanta,Na'im ya rasa yanda zaiyi da ita tayi shuru,ba irin lallashin da bai mata amma taki ji,har haushi ta bashi ya shareta haka sukayi shirin bacci,shi ya shiryata  ta fes tana ta hawaye yace ta kwanta taki kwanciya ta zauna a kasa tare da jingina da jikin Bed taci gaba da Kukanta ba Sauti,Na'im ya kwanta ya kyaleta idan ya fara bacci sai ta fara me Sauti yanda bazaiyi baccinba,idan ya tashi yace tayi shuru baza tayi ba,Fushi yayi ya tashi tare da komawa Palo baya son jin kukan Salmansa,gashi bazai iya bata abinda take so ba Allah kadai ke bayarwa,
Yana PA saman Sofa ya kasa bacci,kawai ya hakura ya dawo cikin bedroom tare da daukan Salma kamar tsinke,yayi jifa da kayan jikinsu gaba daya,saman bed ya daura ta yana a samanta sannan yace yi min shuru malama kin San ni bazan iya baki da ba,amma kin San ba abinda Bana miki Allah bai kawo ba,dan me zaki sani gaba kina kuka,bafa ni na hanaki ba,Salma tana shesheka tace ai kaine kaki dagewa gashi nan su sai haihuwa sukeyi,karfa kiyi sabo Salma,ya kike so nayi miki,mene ne zaki hana kanki zaman lfy?why all ths? Salma cike da Shagwaba ta furta ni...ni...to...kawai kaje kayi min kishiya,dariya ma ta bashi dama duk akan kishi take wannan abun,to wa yace miki zanyi aure?ba wata wacce zan aura ko na hadaku bazan iya adalci ba,ke zan fifita Salmana yana maganar yana kissing din lips nata tare da cewa Yau till down zamu yi Allah yasa ki samu cikin to tunda kin fi damuwa da Baby a kaina.

Baki ta turo gaba tana kunkuni ae naji ni dai ayi min,me kike cewa,shuru tayi tare da cewa cewa nayi to Ameen fa,murmushi ya saki domin yaji me tace,fuskarsa take kallo kamar zata hadiyeshi a hankali ta rada masa kana da kyau Honey ban san ya akayi kafi mace kyau ba,dariya yayi ta jin dadi yana me kara kankameta tare da shakar kamshinta me matukar dadi da sanyi,kansa ya tura tsakanin boobs dinta yana wasa dasu,Salma ta kara matseshi a jikinta tana lashe masa wuya kamar wata Akuya ta haihu tana lashe danta????????,Ranar Sun kwashi shagali Salma taji maza ranar amma buri take Allah yasa ita ma ta samu cikin Na’im dinta.

Zainura an girma fa danta Arif har ya fara rarrafa da zama,wani zukeken gaske dashi,amma Zainura abin dariyarta baya karewa kuma Arif bai isa yayi mata ta'adi ba sai ta kaiwa Irfan kararsa wai yayi masa fada,yau Sunday Irfan yana gida yana aiki a laptop nasa,Zainura tana kitchen ta fito zata shirya dining,sai ta hango Arif Ashe ya tashi daga bacci ya fito ya bar dattijuwa me Kula dashi bata sani ba,ya dauka remote na TV ya farfasashi,Zainura ta kalleshi ta rasa ma me zata ce masa, shi kuwa wasan sa yake yana mata dariya,da sauri ta wuce palon Irfan,yana ganinta haka yasan Arif ne yayi mata ta'adi,kallonta yayi yana murmushi tare da cewa Babyna ya akayi?Zainura tana shagwaba tare da direren kafafu Allah...ka masa fada yanzu sabo da Allah kalli yanda ya lalata remote ni banji haushin lalata remote din bama tunda kai zaka siyo wani amma yanda ya bata min Palo da tarkace For God sake,to yanzu ya zan masa Babyna dukansa kike so nayi ko me? Ke da danki sai ki gyara wajen,Zainura tace ni Allah sai ka bimin hakki na haka kawai,Dauko min shi to na masa fada,da sauri ta fita ta daukoshi,yace yawwa kawo min shi na zageshi yau zaneshi zanyi yana sa min Matata aiki,Zainura tace a'a Dan Allah karka zaneshi,ni baza ka dukar min yaro ba fada zaka masa,oh to kin San hakane zaki ce ya miki laifi,dariya tayi tana shafa kan Arif tace bari na masa wanka na shiryashi sai na kawo ma shi.

Afrah ma Alawwal dinta ya girma haka ma Aisha duk sunyi dagwai dagwai dasu abin sha'awa,suna zamansu lfy da kowa ana zumunci.

 Salma dai har yau shuru ba ciki ba alamarsa,sai wani kyau da haske tare da yar kiba da takeyi,Yau part din Zainura ta yini,Zeena ta kalleta tare da cewa ya akayi ne Hajiyar Na'im?naga sai wani kyau kike karawa,ke fa kin fiye sa Ido mene abin wani kyau ke baki ga yanda kika koma ba kamar wata Queen sai ni cewar Salma,Zainura tayi wani fari kamar tana gaban Irfan Afrah da Aisha sunfi  ni Kiba ai sosai,Yeah ai suna hutawa Salma ta furta,Ke Zainura ki tashi ki cire wannan matsiyatan kananan kayan kafin Na'im yazo daukana,Hararar wasa Zainura ta aikawa Salma to an fada miki haka zan zauna ya kalleni,Yanzu ma zan sakewa Habibty na sabon wanka kafin ya shigo,ni dama yanzu ba fiye sa man yan kaya nayi ba a gida,ai naga alama a kanana nan ma kusan tsirara kike Zama ke,Haka yake son ganina me gidan abinda yake so shine nawa,Salma ta bude baki da niyyar yin magana sai ga Irfan ya shigo dauke da Arif,direct wajen Zainura yazo tare da manna mata kiss,S alma tace ko kunyata Babu,Dariya Irfan yayi tare da cewa Sorry Aunty na manta,Zeena Bedroom ta bishi tare sukayi wanka sunyi shiri,Ta hade cikin wata doguwar riga na Lace dark blue ta sha kyau kamar a sace ta,Arif ma an shiryashi cikin kana nan kaya na Yara farare tas,Irfan yasha Shadda light blue fitted links dinkin kamar ka sacesu sai kamshi sukeyi,bayan sun fito sai ga Hunaif tare da Afrah da dansu King,King da Arif suna ta wasansu,su kuma gaba daya suna dining zasu fara cin abinci sai ga Na'im kayansa iri daya dana Salma shadda light Silver color,Salma kamar wani Sarki ne ya shigo haka ta mike tsaye tana murmushin jan hankali,yana zuwa rungumeta yayi sosai tare da dagata Sama suna dariya,sit yaja ya zauna ko kula su Irfan baiyi ba Salma ta dauke masa hankali,Sai Hunaif ne ya mika masa hannu Bro How far? Sorry na manta cewar Na'im sannan suka gaisa da kowa,Arif da King suka taho wajen Na'im suna dariya sai murna suke Sabo da kusan kullum sai Na'im ya fita dasu yawo shi yasa suka saba dashi,daya bayan daya ya daukesu suna jikinsa Salma tana bashi abinci a baki,suna gamawa ko minti daya bai kara ba ya dauki Salma kamar Jaririya suka bar gidan,Salma tana ya tsaya suyi Salma Amma yaki yarda yace sun yini suna hira Amma bata Isa ba.

Salma suna Tafiya Aisha Da Doctor tare da Danta suka zo suma suka Iske su Afrah nan suka dasa sabuwar hira,da zasu tafi suka biya ta wajen Salma sannan suka wuce gida cikin farin ciki.

Hashim ma Alhmdllh duk halayarsa ta banza ya daina suna zaune Lfy,Iklima da Maimuna saida suka dage suka dinga fadakar da matan gidan masu zaman majalisa ana munafunci,batsa,tare da tona asirin mazaje na kwanciya,yanzu sun daina sun gane gaskiya domin har wata Malama aka dauko guda ta tara su tare da yi musu wa'azi yanzu sai daí suyi hira ta Karuwa da juna wajen siyen maganin mata da Sauran kayan kamshi da gyara etc.

Affa da Ummitu suna Zamansu tare da Dada abinsu lfy sai daí suje kauye ziyara wajen yan Uwa su dawo,haka Malam da Umma tare da su Mummy.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????

231-240 241-250

Official

By
AsmaBaffa

       FINAL

ASMABAFFA FANS CLUB wannan last page naku ne.

   Shekarar yaran su Irfan 1 da rabi da haihuwa suna Tafiya dagwai dagwai Salma ita Allah bai bata ba kullum addua sukeyi Allah suma ya basu.

Salma gani take yawan saduwa shi zai kawo ta samu ciki,Na’im kuwa dadi yaji har zugata yake suyi ta shan dadi ba ruwansa sai yanda yaga dama,yauma Sunyi shirin bacci Salma ta gama lalata Na’im da kwarsar dadi,baya jira itama haka suke gurzar Amarci yanda suke so, light ta kashe ya kunna yau Bazan kashe light ba sai anjima so nake na kalleki sosai sweetheart,Fuska ta rufe tare da cewa nifa kunya nake ji,Murmushinsa me matukar kyau wanda ke gigita Salma ya sakar mata yana lumshe ido Sabo da jaraba.

Kwanaki kadan Salma ta fara wata Mura me zafi zafi,ta dan sha wahala ta warke,bayan ta warke ta kara kyau da haske kowa cewa yake ciki ne da Salma amma bata yadda tunda ita bata wani laulayi,haka su Mummy ma suka ce Na'im yace baiga Alama ba,tun Na'im baya yarda har shima ya fara zargin ko dai da gaske Salma tana da ciki ne,tana kwance saman Sofa tana cin green Apple,Na'im yana zaune a gefenta yana kallon news kafafunta na saman cinyarsa Babyna juyo naji wani abu,bata kawo komai ba ta juyo ya fara latsa cikinta yana murmushi yace ke tashi muje Hospital kamarfa ciki ne dake,Salma bata gama ji ba ta fada Bedroom tare da figo gyale ba wani shiri ta bishi suka tafi tana Allah Ameen a ranta,suna Isa Hospital da kansa yayi mata duk wasu gwaje gwaje ya tabbatar kuwa ciki ne da Salma har na wata Uku,Na'im kamar ya suma sabo da murna,yana fadawa Salma taga result ai rawa ta fara Office din bata sani ba,Na'im yana riketa yana dariya Amma Salma tace ina ai sai ta cashe,da kyar ya lallabata ta hakura da rawar,tun a can ta kira duk su Zainura da sauran frnds ta fada musu,Na'im ma haka yana ta faman bige bigen waya yana fadawa mutane.

Yanda ake ji Salma kamar wata yar gwal ko kuda ba a so ya hau kanta,su Mummy,Umma tare dasu Ummitu,Dada,har su Zainura bare kuma Uwa Uba Na’im yanda yake ji da Salma yana lallabata abin ya zarta tunani,baya wani fita sosai,idan ma zai fita to bazai bar Salma ita kadai a gida ba sai tare da Afrah,Zainura ko wata,yan Aiki kuwa tuni an kawo mace Dattijuwa daya da Namaji suna part din masu aiki a Cikin gidan tare suke da yan aikin su Zainura aiki kawai ke kawo su part din iyayen gidan nasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button