KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
‘KAUNARMU
Mamuhgee…
1
Labarin qaunarmu labarine akan soyayyar data shigi mutane biyu batareda sun ankareba duk da kasancewar banbancin dake tsakaninsu na kasancewar kowannensu nada abokin rayuwarsa Wanda suke ganin sune rayuwarsu saidai so yayi musu shigar sauri Dan kuwa tuni suka daina kallon waincan amatsayin abokan rayuwarsu…..SO NE WANDA BAIDA KATANGA YAYI MUSU SHIGAR SAURI…YAYA ZASUYI DA ABOKAN RAYUWARSU NA FARKO…
Zata sadaukar da farin cikinta dominsa,
Zai sadaukar da rayuwarsa dominta,
Zasu sadaukar da komai domin juna,
‘yar uwarta wadda suka fito ciki daya,
Rana daya, awa daya saidai bambamcin mintuna biyarne a tsakanin fitowarsu duniya
‘yar uwar tata zai aura Amma qaddara ta juyo da auren akanta bayan tanada nata abokin rayuwar dataiwa kanta tanada Kuma a uba suke kallonsa shikuma atasa duniyar baimasan dasuba
saidai qaddarar so ta sauya musu akalar rayuwarsu zuwa ga zazzafar qauna da bazasu iya juyowa su kalli bayansu ba bare abinda yayi sanadin auren nasu……sun shirya yaqar maqiyan soyayyarsu batareda sun tabbatarda qauna da zazzafar soyayyar dasukewa junansuba…
BRG MUHD SAHEEB MARSHALL MAKARFI
And
KHADIJA MUFIDA NUHU MANDE FIFI
‘KAUNARMU
Mamuhgee
1
BismillahirRahmanir Raheem.
????????????????????????????
https://youtu.be/MJxY0y_SrOc
HAMBURG garmany.
10:30am
Gyara zamanta tayi akan kujerar dake fuskantar ta Dr Fatima Omar yonas tareda gyara zaman glasses na idonta ta bude bakinta dake mata nauyi aduk lokacinda zatayi maganar ‘yar uwarta sbd jin kunyar kanta da takaicin kanta akan yanda konyaushe ‘yar uwartace ciwon ranta da damuwarta,
Duk yanda taso dauke Kai da danne alamarin ako yaushe sabo abin ke dawo mata sbd tsoron meyene zata samu agaba ‘yar uwarta ta rabata dashi sbd wannan shine asalin dumuwarta da tsoronta sbd batasan mezata iya zama agaba ba itama akan hakan.
Kamar yanda tasaba kullum idan tazo gurin Dr Fatima yonas yauma farawa tayi da cewa”
Sunana AYSHAT HAMEEDA NUHU MANDE sunan Tawainiyar haihuwata KHADIJA MUFEEDA NUHU MANDE,
yan biyu mahaifiyarmu ta haifemu shekara ashirin dasuka wuce,
Mintuna biyarne kacal atsakanin haihuwar tamu,
Nice nafara fitowa duniyar kafin ita,
Nice na cancanci mafi yawan soyayya da qauna daga iyayenmu da danginmu kafin ita sbd nice nafara haskaka idanuwansu dasuka jima da jiran ganin wannan Rana dazasu rungumi nasu ‘yayan suma kasancewar sun jima harsun fara manyanta babu haihuwa,
Bayan fitowata duniya iyayena sunyi farin ciki mara misali na samuwata Saidai SO da QAUNA Dana samu daga garesu na mintuna biyarne kacal sbd fitowar ‘yar uwata duniya ya sauyamin komai har zuwa yanzu,
Itace sanyin idanuwansu,
Itace farin cikin gidansu da wajensu,
Saidai Allah dayafisu iko da ita bai sakota a duniyarba sai daukeda cuta ta RAUNIN ZUCIYA ma’ana WEAK HEART (CARDIOMYOPATHY)
Wannan cuta datake daukeda ita ta qara rage kaifin qauna dake tsakanina da iyayenmu,yan uwanmu,likitocin da duniyama gabaki daya.,
Ciwon raunin zuciyarta yasa ba’a qaunar bacin ranta,baa mata fada,baa ganin laifinta,kowa qaunarta yakeyi,kowa sonta yakeyi Wanda tuni gata yayi mata yawa tako wane bangare musamman Kai tsaye mahaifiyar dadynmu ta yanke cewa asakawa ‘yar uwata sunanta tanason ta gajeta
Ba 6ata lokaci taci sunan kakarmu da mahaifiyarmu wato KHADIJA MUFEEDA inda ni naci sunan Mahaifiyar mamanmu wato AYSHAT HAMEEDA.
Ta karbe soyayyar iyayenmu,
Ta karbe soyayyar kakanni da danginmu haka ta karbe sunan Mahaifiyar da rayuwarta Dan kuwa tun bayan fitowarta duniya mahaifiyarmu Bata qara lafiyaba munada shekara daya ta rasu tabarmu da dibbin kewa da maraicinta,
Anyiwa mufeeda aikin zuciya Wanda akayi cikin nasara da saa Saidai likitocin sun tabbatarda akwai yiyuwar asake mata wani aikin agaba wanda sukeda tabbacim ba lallai ta rayuba idan anyi.,
Wannan shine yaqara assasa wata sabuwar qaunarta mai tsananin qarfi a zuciyar kowa.
Muntaso cikin gata da kulawar mahaifinmu da kakarmu wadda tsufa yasa tuni Takoma gidan babbar yarta yayar dadynmu dake zaune a Lagos mukuma mahaifinmu ya daukemu muka dawo wannan qasar da zama,
Soyayya da qauna wadda mahaifinmu kewa mufeeda ta dabance wadda baa hadata da komai,
Ummy yayar mahaifinmu da hajja baza hada qaunarta da komai Dan kuwa ummy ko ‘yayanta biyu maza kacal da Allah yabata Bata musu qaunar datakewa mufeeda,
Mufeeda Allah yayi mata gatanda bazance nasamu irinsaba Dan kuwa tako wane fanni Allah ya Bata duk wani Abu dakowa ke buqata,
Dukiya,
Arziki,
Gata,
Kyawu,
Kyawun jiki,
Farin jini,
Haiba,
Ilimi da wayewar rayuwa Amma Abu dayane bai horeta dashiba shine lafiya.,
Takasance lafiyarta qarantattace duk yanda takaiga holewa arayuwarta to lafiyace ke kawo mata tsaiko Dan kuwa ita mutumce mai tsananin son more rayuwa tareda abokai na wayewa dajin dadi,
Tun muna primary kowa da mufeeda yakeson qawance,
Kowa mufeeda yakeso haryanxu da muke a matsayin ‘yan mata haka rayuwar take,
Nazama tamkar tsohuwa ko uwa sbd duwa da kishin ‘yar uwata dake cin Raina tun ina qanqanuwata,
Ayanzu zuciyata cike takeda kishi tareda qaunar yar uwata Saidai abinda bansaniba shine tsakanin qaunarta da kishinta wanne yafi yawa cikin Raina??????
Wanne ne zai rinjayi waninsa acikin Raina Dan kuwa ayanzu nafara jin tsoron yanda tarabani da kamai na rayuwa mezata rabani dashi anan gaba????
Zan iya jurewa qaunarta ta rinjayi kishinta da jin zafinta kuwa kokuwa kishintane zai rinjayi qaunarta.????
Cikin sakin dogon numfashi Dr Fatima ta dakatar da ita ta hanyar miqa mata magani tareda glass cup na ruwa tana cewa”
It’s time for break hameeda.
Jeki ki huta zamu Dora next time
Karki manta duk lokacinda kikaji zuciyarki na zafi gameda hakan Zaki iya zuwa ki sameni
I’m always here for you and always ready to listen to you okk?????
Gyada Kai tayi tareda sakin ajiyar zuciya Yana sake kurba ruwan ahankali kafin ta aje glass din tana kallon Dr Fatima ahankali ta furta”
Thank you mss yonas.
Murmushi Dr Fatima tayi tareda dafa hannunta tace”
Idan nadawo gida zanshigo
Karki Bari shedan tashiga tsakaninki da qaunar da kikewa ‘yar uwarki,
Kece yakamata ace kinfi kowa qaunarta da tausayinta a duniya sbd kece twin dinta.
Gyada Kai tayi tareda miqewa tana sake cewa”
Thank you..ta dauki handbag dinta da wayarta dake kan table ta miqe ta nufi qofa ta fice.
Numfashi Dr Fatima tasauke sbd tausayin hameeda din da kishin yat uwarta yayiwa zuciyarta mugun kamu hartakai tanajin tsananin tsanaar ‘yar uwarta wani lokacin wanda lura da hakan yasa tafara kulawa da mufeeda din ta hanyar sakata amayar da damuwarta kullum wanda Kuma hakan ba qaramin taimakawa mufeedan yakeba Dan tanajin sassauci idan tayi hakan Tasha mgani tana zuwa gida bacci yake sata maganin tana tashi zataji zuciyarta sakayau.
Dr Fatima Omar yonas maqwafciyarsu ce Kuma consultant ce ta bangaren tunani da karantar Dan Adam sune irin likitocin da idan Dan Adam baisan meke damunsaba idan ankaika gurinsu daga yanayin yanda kake amsa musu tambayoyinsu suke gano matsalarka.
Asalin ‘yar qasar Ethiopia ce Batada miji ya dade da rasuwa yabarta da ‘yaya biyu rak namiji da mace
Ameed da meena,
Ameed saurayine wanda shima Dr ne be wani jima da zama Dr dinba and ko shekara beyiba
Dan gayu me ji da kyau da gata da dukiya shima gashi dason rayuwar hutu da wayewa shiyasa aduniya Babu wadda yakeso kamar mufeeda wadda qawayenta da duk yawanci ma da FIFI MANDE,