KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Mahaifiyar su dr fatima yonas itama ba baya bace wajen nuna fifiko musamman wajen kulawa da lpyar mufida,sau dayawa in wani abu ya faru zakaga da ita da yaranta ameed da meena sun daga hankalin su matuka tamkar babu wani banbanci wajen kasancewar su jini daya.

Dr F.yonas ta kasance uwa kuma garkuwa agare su duka duk dama a hakan yanayin yake tafiya tsakanin rayuwar mufida da tawainiyarta hameeda.

Shiri ake yi sosai na komawar su nigeria

a kullum kakar su hajja da yayar ddyn su ammy sukan so su bugo waya ko dan adada jadadda musu ranar gamawar su karatu

Ana washe gari zasu gama angama shirya musu komin su an kikkimtsa

To kowa ya kasance cikin farinciki amma banda hamida dake kokari wajen kawar da idanun ta akan abubuwan dake faruwa da ma wayan da suka gudana acikin yan kwanakin nan

Sosai aka bada fifi dama tayi shagalin ta,satin daya gabata ma ta hada wani kawataccen house party ita da abokan ta batare da an mata hani akan komai ba.

Dama duk mutumin da Allah ya axurta sa da abunda fifi take da shi na kyau ilimi da farinjini tabbas bazai taba rasa masu jin haushin sa ba,ciki kuwa har da ni yar uwan ta hamida

Duk da halayyar sakewa da maida komai ba komai ba irin na fifi ahakan takan samu sabani da yan matan ajin su

sau tari xasuyi ta daddaga kai ma juna wani bib har yakaiga ta jawo musu asara ankawo kararta gida wajen ddy

Saidai tunda nake ban taba jin mahaifin mu ya dau wani mataki ko ma yace xai mata fada ba.

Ranar da zasuyi exams na karshe daddy ya kasance cikin tsananin farinciki da nuna jn dadin sa a fili

dukan mu ranar ya hada ya mana addua amma muna iddawa suka fara nuna min yar hali

Kyaututtukar da aka yisu domina da wanda akayi domin mufida akwai kyaun bambanci.

Tabbas fifi ta fi hameda ilimi da samun jinjina da lambar yabo amma wajen sanya albarka akan kokarin su sanda dukanin dangi da yan uwa aka taru aka nuna ma hamida cewa nata nasaran kamar bakomai bane.

Abunda ya fiye ci mata baifi yadda ake nunawa a fili ba

Shiru shiru me nuni da alaman rasa gatan kuruciya shiya dulmuye hamida

Ta kasance a tsakanin su batacciya marar amfani sai dai in abun ya mata ciwo seta tsame kanta tayi nesa da su..

Ana washe gari tafiyar su mahaifin su ya biyo dakunan su cikin dare kowacce acikin su yana mata furucin nasiha da bankwana

Fannin hamida Kwata kwata befi tattaunar mintina talatin sukayi tsakanin ta da daddy a dakin ta ba
amma se ta ga tunda ya je dakin yar uwarta mufida ya dade yama kusa cin awa uku ahakn ma baisa ranan fitowa

Komawa room din ta tayi da sauri dake dama ta sauko ne ko zata samu smoothie me sanyi ta jika makwagoron ta
“Wayasan ko in anje nigeria wani abu zai sauya amma anya kuwa?ammy da hajja ma ba baya ba wajen nuna tsananin gata kulawa da kauna wa mufida,kikkimtsa kayayyakin ta ta cigaba da yi aranta tana me hoping komai ya zo da sauki acan.

Anan dkin fifi kuwa Bankwana me cike da kauna da tausayi shiya wakana tsakanin daddy inda tsabar nuna damuwar sa da son ta harji yake kamar da ransa zaiyi bankwana yama kasa fita a dakin daren ranan gaba daya ya kasa samun sukuni kanta ya dora akan kafar sa kwance akan cinyar sa tayi bacci

Sai Washe gari da safe ta shirya tsaf suka taho dinning yin kari a Tare suna saukowa hannun su sarkafe da juna

Sun samu hamida ma harta shirya kanta cikin wata turkish gown lavender purple tayi roling da golden veil tayi kyau sosai mufida kuwa dama ta fiye saka classic collection musamman white shirt da wandon falazon ta me fadi da tsayi yau kalar ja ta kwama tayi rolling da jan veil me tsantsi tayi kyau itama sosai

Confidently take takowa ata hannun daman dady akan takalmin ta na kamfanin gucci me da tudu dayan hannun ta rike da gucci side bag shima kalar takalmin ta.

Ko gaisawar kirki basuyi tsakanin su ba aka danna door bell inda duka hankalin su ya koma wajen dan ganin waye me shigowa

MamuhKNM

https://www.youtube.com/channel/UCMylPCg0TCgTWAmy6HHvcEQ

Please SUBSCRIBE

4
cikin dauriya hamida ta taso ta taho har bakin kofar domin duba wanda yake wajen,tana budewa a tsaye taci karo da wani mutum Irin Mai bada sako gida gidan nan hannun sa dauke da manyan manyan akwatunan kyauta tare da mai gadi da security sun rakoshi

Kai tsaye Dagowa yay ya dubi hamida cikin harshen turanci yace mata good morning maam House no22 nuhu mande residence?

Ta gyada kai tace yes?

…nan ya mika mata biro ya umarce ta data sanya hannu a yar takardan su na register wanda yake nuni da isowar sako zuwaga maishi tana rantabawa ta mika masa tace thank you,security ne suka juya tare da shi

tsaye tayi tana me kare ma hadaddun akwatunan kyautar da aka killace su gwanin sha’awa agaban ta kallo

Saidai Tunanin abubuwan da suka wakana jiya da shekaran jiya dik su suka bijiro mata a zuciyarta inda take nazarin cewa kusan dukanin kyaututtukar data samu daga wajen su daddy da familyn dr fatima yonas bai wuce yan kayan sawa takalmi da katin gaisuwa irin na greeting card din nan ba

babu wani abu kwakkwara acikin kyaututtukan daya ya burge ta bare ma yaje mata har zuci

Amma Sanin yanayin yadda abubuwa suke a tsakanin ta da yar uwanta yasa a cikin yan kwanakin sai ta tsame kanta tayi gefe duk takurawar da fifi tayi mata akan su bude nata kyautattukar a tare haka taki fir

Aranta ba wani abu mai wuya bane iya cin karo da abubuwan da take so a cikin kyautattukar da fifi ta samu wanda ita ba’a bata ba kuma tasan hakan zai iya jefa ta cikin wani mummunan hali

Ayanzu Tana so ne hankalin ta ya dan dawo jikin ta kafin su isa nigeria tunda bawai sanin ya kasar dazasujen yake ba

A Labari kawai sukeji,bare ita da sau dayama daddyn sun ya taba gaya mata tarihin su waye ammy da yayan ta guda biyun da zasuje su tarar

Cikin wannan halin sake saken taji an dafo kafadun ta inda ta waigo cikin sauri da nitsuwa suna mai hade idanuwan su da yar uwarta tata cikin yanayin jefo tambaya a tsaye fifi take da alaman ta biyo bayan tane tace

Hamida Waye ne?
Tun kafin hamidar ta amsa idanun ta suka sauka akan tarin boxes dake gaban ta awajen

“cike da mamaki ta durkusa gabansu tace waw nawaye?waya kawo miki.. masha Allah..

Nan Hamida tai saurin cewa Bafa mani aka kawo ba

Mai bada sakone yazo shima bai gaya min komai ba sai dai in mun bude hala xamu gani

Nan fifi ta taimaka suka tarkato dukan su suka dauko box daya daya a hannun su suka shigo har gaban mahaifin su da shi saidai baice uffan ba har suka shiga budewa

Atare suka kai hannun kan wani dan madaidaicin katin da aka manno sakon tare da shi wanda sunsan dole anan ne zasu ga sunan wanda yayi sakon da wanda aka aiko ma

hamida ce tayi nasaran fara dora hannu ta akai dan haka ita ta dauki katin cikin warware makullin sa ta bude shi tsaf ta shiga karancewa

Sako ne me cike da nuna tsantsar so gata da kuma kauna wanda yayi mummunan fallasa girman irin kewar ta da za’ayi…

tsaban kalaman da aka rubuto sun tsaru cikin nitsatsiyar harshe mafi sanyayawa a cikin sassanyar yanayi hamida ta tsince kanta nan take ta shiga maimata kalaman ma zuciarta wanda yayi musabbin janyowa idanun ta cikowa da ruwan hawaye

Danne duk wani abun da takeji tayi ta karance har karshe,ina ma ace ko sau daya zata same irin wannan damar arayuwan ta

Waye zai so ta ya fifita itama ya turo mata wayannan kalmoni masu ma’ana wanda zai sa zuciyarta tayi saurin amincewa da cewa ita ma mutum ce wanda ta cancanci nuna kulawa da kauna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button