KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Jin muryar ta tayi tana faɗin
“Ban sani ba amma zafin da nake ji yanzu ya fi na da doctor,ka taimake ni pls,i don’t wanna die soon”..
Gaban fifi ne ya buga jin kalmar mutuwa daga bakin Muhibba wic means ciwon da take yi yana iya yin sanadin rasa ran ta kenan…

Kamar ta tashi amma ta fasa ta bari akan zata ma Hamida mgn in ya so sai a sanar da su Ammy abinda Muhibba ke fuskanta dan kar ayi rashi biyu..
Ta tausayawa Marshall ba kaɗan ba tayi zaton ita kaɗai ce ke cikin matsala da damuwa ashe damuwar Muhibba ke ciki itama kawai dai nata tana ɓoye sa ne dan ita babba ce kuma babu wanda ya sani cikin iyayen su…

A daren ranar suka yi waya da Saheeb ta ji kamar ta sanar da shi amma ta fasa,sai da suka gama sannan ta kira Hamida ta mata bayani sai dai to her greatest surprise sai ta ji Hamida ta ce mata
“Sweetheart pls ki kula da kan ki before anyone else,it’s all about u and no one but u,ok so good nit je ki kwanta”daga haka ta kashe wayar..
Haka fifi ta kwanta cikin jimami da zullumin me zai zamo sakamakon rashin lafiyar su su duka kuma ya Saheeb zai ji in ya san duk ciwon da suke yi na ajali ne..

Mamuh[8/24, 8:12 AM] +234 808 540 5215: 38

Tun daren jiya fifi ke jin ta aani iri wanda ba komai bane sama da labour pains dan kuwa ranar ta gabato but sai tayi ta sharewa dan da ya mata sai ya tsaya,ganin haka ya sa ta kyale abin kawai ta sha pain relief ta kwanta tayi baccin ta..

Da gari ya waye sai ta ji sayau babu ciwon babu alamar sa sai ta ɗan yi ayyukan da zata iya yi kafin daga bisani ta tafi tayi wanka..

As always yau ma maternity gown ɗin ta ta saka na atamfa ta saka hijab ta fito tana tafiya a hnkl har ta iso sashen su Ammy…
Da Hajja ta fara cin karo wacce take zaune bisa three seaters tana danna counter dake hannun ta,tana sanye da hijabi..

Saurin taro ta tayi tana mata faɗar karambanin da tayi na zuwa nan sashen alhalin ta san ba wani lafiya ne da ita ba..
Murmushi kawai tayi ta zauna da ƙyar suka gaisa da kakar nata inda ta tmby ta me take buƙatar ci sai ta ce mata duk abinda ta ci itama shi zata ci..

Kiran mai girkin su tayi ta umarce ta da ta kawo ma fifi kunun accan da ta mata da alale kuma ta saka man shanun da ta saka mata..
Murmushi fifi tayi ta shiga zolayar kakan nata tana ce mata ta fiye kwaɗayi duk ita kaɗai ta ci wannan abin..

Dariya kawai Hajjan ta mata tana ce mata lallai tayi ƙwari tunda ta iya tsokanar faɗa.
Suna zaune a wurin aka kawo mata abincin ta zauna ta ci sosai har ta kammala sannan ta dubi Hajja ta ce mata

“Hajja ƙila fah abinci na na ƙarshe kenan a duniyar nan,kamar ta ƙaro min”!!wani faɗi gaban Hajja yayi dan straight foward person ce fifi bata ɓoye ɓoye shi ya sa ta faɗi abinda ke ran ta…

Matsowa kusa da ita Hajja tayi sai ta rungumo ta ta gefe tana mata kul da kuma nanata wannan kalmar but fifi insisted ta cigaba da furta mata kalmar rabuwa..
Sosai ta karya zuciyar Hajja har hawaye ya cicciko mata a ido but bata bari sun zubo ba sai ta aika a kirawo mata Ammy…

Ammy na zuwa da ƴar fara’ar ta sai ta ga mahaifiyar ta na ɓoye fuskar ta kamar kuka take yi..
Da sauri ta ƙaraso ta hau tmbyr ba’asi inda Hajja ta nuna mata fifi,ita kuma ta maida idon ta ga fifi…

Ko kafin ta ce zata ce wani abin har fifi ta fara yi mata mgnr mutuwa kamar dai yadda ta ma Hajja..
Zuciya a karye Ammy ta matso ta rungume ta tana kuka tana faɗa mata InshaAllah she will pass through da yardar ubangiji,kuma zata raini ƴar ta ko ɗan ta da kan ta..

Ita dai jin su kawai take but ta san abu ne mai wuya bcos likitan ta ya faɗa mata kuma ita kan ta ta san tana ji a jikin ta komai ba lfy bane sai dai ganin halin da suka shiga ciki sai bata cigaba da kira masu kalmar mutuwar ba ta dai yi shiru…

Ta jima a nan wurin su Ammy suna ta nan nan da ita dan dai kar ta kuma tado mgnr mutuwar nan,Ammy kam sai da ta ɓoye kan ta a ɗakin ta tayi kuka sosai dan ta san gaskiya fifi ke faɗa,bcos an sanar da su,Khalid ya faɗa masu a scanning ɗin ta an gano tana da matsalar zuciya kuma ba lallai bane ta iya haihuwa da kan ta ba but ita ta ce ta fi so a bar ta tayi labour da kan ta..

“Wannan masifa da me yayi kama,tun haihuwar yarinyar nan har yanzu rayuwar ta a stalk yake,rayuwa take yi a duniya amma lfyr ta bai da inganci,yanzu da ta ɗan fara jin daɗin rayuwar nata kuma,mutuwa zai yanke mata shi”..Ammy ce ke kuka tana mgnr ita kaɗai bayan fifi ta bar su ta nufi sashen Hamida..

Har dare dai bata wani sami sauyi ba dan jikin ta duk yayi sanyi,tsoro ya shige ta,fargabar rabuwa da fifi bai bar ta ba,sai a yanzu ma take jin sabon shaƙuwa na shigar ta akan fifi..

Sallar dare tayi ta musamman dama ta saba amma na yau daban ne,ta jima tana roƙon Allah akan ya rangwama ma fifi ya ji ƙan ta ya kawo mata komai cikin sauƙi ya shigo lamarin su..
Haka ma Hajja ta kwana tana ma fifi addu’a dan zuciyar ta ya karye akan wannan abin..

Bayan fifi ta fita daga sashen su Ammy sai ta nufi sashen Hamida inda nan ma duk kalmar mutuwar ce,sai dai ita Hamida bata yarda memory ɗin yayi lasting a kan ta ba dan bata yarda fifi zata mutu ta bar su ba,ta yarda cewa in har fifi zata iya riƙe babyn ta for good 9 months toh ta san da hukuncin ubangiji she will pass through her labour successfully..

Ƙarfafa mata gwiwa Hamida tayi ta yi har Khalid da ya dawo daga aiki yayi joining nata suna ta ba fifi mgn da ya sanyaya mata zuciya but a can ciki,ta san me zai faru a ƙarshe…

Har bedroom Hamida ta rako fifi ta taimaka mata ta sauya kayan ta zuwa comfortable night wears sannan ta mata duk abinda ya dace kafin ta tafi dan ta ce a nan zata kwana but fifi ta ƙi yarda ta ce ta tafi kawai in ba haka ba toh kuka zata saka mata,jin haka sai Hamida ta rarrashi fifi ta ce amma ba bacci zata yi ba zata je ne ta rinƙa leƙo ta..

A hakan ma da ƙyar fifi ta yarda sannan Hamida ta kashe mata wutar ɗakin ta tafi..
Bayan tafiyar Hamida ne fifi ta ciro wayar ta tayi dialing numbern daddyn su inda bayan ringing huɗu ya ɗaga suka gaisa ya tmby ta ya jiki ta ce mai lfy take..

Suka ɗan yi hira kafin daga bisani suka yi sallama,instead tayi bacci sai ta hau kiran layin mijin ta but duk ringing ɗin da yayi ta yi ba a ɗaga ba,haka hnkl ta ya tashi har ta tura mai saƙonni babu iyaka ko zai kira ta ko ya maido mata da reply but bai turo ba bai kuma kira ba sai ta daure ta ajiye wayar ta rufe idanun ta dan yin bacci…


Misalin ƙarfe uku na dare ta ji wani abu ya murɗa mata cikin baccin ta but bata buɗe idanun ta ba sai ta ɗan gyara kwanciyar..
Can kuma ta ji wani azababben ciwo a ƙasan marar ta nan take ta buɗe idanun ta ta fara salati a ran ta,tana nan a haka kafin ta tashi ciwon baya ya riƙe ta,tun tana iya resisting ciwon har ta kasa ta fara addu’ar a bayyane,da abin yayi tsanani ko ina ya amsa yana mata ciwo da raɗaɗi sai kawai ta tsala ihu..

Ihun nata ne ya doki kunnen Muhibba dake faman murƙususun ta a ɗakin ta dan dare ne kuma babu hayaniya so ko spoon ne aka yi dropping mutum na iya jin ƙarar sa bare wannan ƙara ce mai sauti…

Ɗan dakatawa tayi daga juye juyen ta ta tsaya shiru duk da zafin da take ji haka ta tako a duƙe ta fito zuwa hanyar ɗakin fifi..

Ihun ta kuma ji a karo na huɗu nan take ta ruɗe ta fara yunƙurin kai hannun ta ƙofar ɗakin amma ina,juyi cikin ta yayi wanda ya haddasa mata faɗi wurin ƙasa tana ta riƙe cikin tana numfashi sama sama…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button