KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Wani fushi me hade da Faduwar gaba ne ya riske ta toh me yake nufi da yar uwar ita is attractive kuma?mswww fifi fifi fifi and ffi again,ji tayi kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ga bata nan cikin gidan…

Janyo mata trolley din ta yayi zuwa ciki yana mai dan jan ta da hira,gabadaya zuciyar ta na ayyana mata cewa kar ta sake Khalid ya kufce mata sabida fifi wannan kuma nata ne ba zata barwa Mufida shi ba,dan duk cikin su shi kadai ya dan nuna ma ya san da ita…

Wani babbar bacin rai dataci karo da shi kuma shine ganin hanyar dakin da aka kai ta nan kusa da wani new abandoned room da yake shiru shiru kamar babu kowa sai ita kadai…

Dannewa haushin ta tayi Bayan ta mai godiya garin boye damuwar tane yasa tayi saurin rufe kofar dakin da key ta jingina bayan ta da kofar tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya akai akai wasu zafafab hawayen kunci na diga,jin kamar zuciyar ta zai fashe at any moment ya sa ta dauko karamar jakar ta ta hau lalubar maganin da Dr Fatima Yonas ta bata wanda dama kullum in ta tafi ta fadi mata damuwar ta shi take bata ta sha,bude robar maganin tayi ta zuba guda biyu ta hau nemar bottle water din da ta sha a jirgi ta rage,tana ganin sa ta bude bakin murfin ta jefo maganin ta bi da ruwa…

Gadon dake gyare a dakin ta hau ta kwanta a kai idanun ta na kallon gefe daya hawaye na silalo mata har bacci ya dauke ta bata sani ba.

MamuhMamuhgee

Zafafa biyar na kudine ka nemi wannan numbern ka biya kudinka ko katinka

07067124863
09032345899

6

A nan fannin su Fifi tunda ta shigo cikin dakin nata da ya sha kayan alatu taji sam takasa zama dan tamkar wata sarauniya haka aka tsantsara mata dakin sai da ta karewa dakin kallo ta yaba kyaun sa hade da maimaita kalmar “wow cancadi”.

Cire kayan jikin nata tayi ta nufi hanyar bandaki dan watsa ruwa,nan ma duk abubuwan bukata an tanadar mata wanda diya mace da ta amsa sunan ta mace yar gata ke alfahari da shi,haka tayi wankan a karkashin shower ta gama ta fito daure da fari kal din towel..

Sallah ta fara gabatarwa sannan ta hau kan kujerar gaban madubin ta,dama tayi tunanin jere cosmetics din ta gaban madubin ne amma zuwan ta dakin sai ta ga wadanda aka jere mata ma sun dame nata sun sha dan kuwa kaf babu cosmetics din da suka fito daga wani kamfanin kwalliya dake african

hatta jam baki da hoda duk products din La pariso ne daga kasar Persia hka komai suka fito ras dan a jeren su suke suffar su daban da na kasar nan..

Nan ma sai da ta yaba da kyaun koma ta kuma kara yarda da kaunar da ake mata a cikin zuri’ar nasu,lallai duk soyayyar da tayi tsammanin samun shi daga gare su ya wuce yadda ta tarar dan tun a wurin dauko su ta gasgata hakan..

Kwaliyyar ta ta cancanɗa mai daukar hankali dama akwai kyaun sai ga adon zamanin da ta dora a fuskar nata me sanyin haske..

Duk dakin nata ya gama amsawa da kamshin designers perfs din ta na matron daga haka ta saka suturar ta irin ta kullum bata canza ba wato shigar kananan kaya riga da wando ta kamfanin Dior sai ta dau kimono deep red ta dora a sama hade da saka head hoodies kalar rigar cikin da ta saka,flat foot wear ta saka ta dauko wayar ta cikin kazar kazar da karfin jiki ta fito da nufin tambayar inda yar uwar ta take..

Kicibis tayi da Khalid da shima fitowar sa kenan da zumar zuwa duba ta,anan suka shiga zagowa dan su hade a hanya wanda yake half way a balcony din gaban dakin hamida…

Dakatawa yayi ya tsaya kusan inch biyar da inda fifi take yana mata kallon da bai san yana yin sa ba

kwata kwata bai san yadda aka yi yake kasancewa a zauce ba musamman a duk lokacin da ya hada ido da ita…

Kasa karasowa kusa yayi yana tsaye ita kuma ganin sa sai da ya saukar mata da kasala domin kuwa white shaped long sleeves shirt ne a jikin sa mai two  black straight line mai dauke da botara masu matukar tsada

wannan rigar ta shi ta bayyana asalin ginannen jijiyoyin muscles dinsa dan dama bai saka botins din duka ba ya bar na sama da mai bi mai a bude,kusan quarter daga sirrin faffadan kirjin sa a waje suke

ga wani irin glowing da haske da bared chest din nasa ke yi,kan sa ya sha gyara da mayuka har fiye dana dazu da ta gan sa..

Tace..”Ya rabbi”abin da ta furta kenan a zuciyar ta ganin kawai ya amsa sunan namijin da ta dade tana mafarkin mallaka a matsayin saurayi kuma miji a gare ta dan sak yanayin jikin sa bai da doguwar bambamci da Ameed abokin ta kuma dan Dr Fatima Yonas a germany…

Kasa boye abin dake zuciyar ta tayi kawai ta sanar da shi ya mata cikin sakin fuska dan ita bata iya boye abin da ya birge ta ko ya bata mata rai..

“You are looking good mr Khalid”
..wani dadi ya ji a ran sa yayi ado ta yaba dan dama dan ita yayi adon kuma kwalliya ta biya kudin sabulu data yaba,jin kan sa yayi kamar yau din rana ce ta musamman a gare sa…

Karasowa yayi gare ta yana mata murmushin manyan maza masu ji da kan su akan gabar su..

“Na gode Khadijatul Mufida”!ya fada hakan yana mai karkata kan sa wanda ita kuma ta ji kamar babu wanda ya iya furta sunan nata sama da shi

dan babu mai kiran sunan nata a haka gabadaya sai dai ko Mufida ko Fifi ko Fifi Mande..

Tambayar sa tayi inda yar uwar ta Hamida take,shi kan sa sai yanzu ya tuno da Hamidar sai ya mata jagora zuwa chan dakin Hamidar inda yake da doguwar tazarar gaske tsakanin matakakan dakin ta da na yar uwar nata..

Shi ya rinka yin sallama amma ba’a amsa ba kuma ya san bai gan ta ba a nan kasa tun bayan barin sa dakin da ya kawo ta mata kaya..

Kallon fifi yayi yana fada mata cewa hamida bata amsa ba sai fifin ta matso adame kusa da kofar ta mannu da nufin yin sallamar da kan ta, nan ma kamshin turaren tane ya kusan sumar da khalid a tsaye wani sanyin yanayi yaji wanda har cikin zuciyar sa yake jin dirinsa,bai san menene yake ji game da ita ba amma yana mutunta wannan abin ko ma menene shi…

Haka fifi ta rinka doka sallama wani na bin wani kusan sau hudu but babu amsa daga ciki,nazari tayi ta kira ta da pet name da ta saba kiran ta da shi koda zata gane itace dan haka ta hau kiran sunan “Hamee”hamee,hamida
Sai shiru nan ma duk haka bata sami amsa ba..

Da rashin jin dadi a fuskar ta ta juyo ta kalli Khalid da shi ba sunan Hamidar ko amsa sallamar ta ke gaban sa ba illa ita mai yin sallamar da kiran sunan wato ita kanta fifi..

Cikin matukar yanayin damuwa Tace hamida
“Bata amsa ba ko bacci take yi ne”?kallon ta yayi yana fadin.
“Kila baccin take yi”!!gyada kai tayi tana dan juyi tana dada kallon kofar daga haka har suka juya zuwa kasa nan main parlor din gidan inda a nan Mufida ta ga tsantsar gata dan abinci kala kala aka baza a babbar dardumar cin abinci duk dan saboda ita..

Farinciki ne ya buwayi zuciyar ta ta rasa ina zata saka kan ta da irin wannan soyayyar da ake nuna mata duk ita daya…

Ammy ce ta taso cikin fara’a ta tarbe ta tana mai yaba kyaun da tayi hade da yaba kamshin ta ita kuma ta rungume Ammyn tana fadin
  “Ammy ai duk ke ce silar kyaun da nayi dan kaf kayayyakin dake gaban mirror din daki na ban taba ganin irin su ba ko da nayi amfani da su sai na ga ashe ni din bakuwa ce a fannin kayan ado,Ammy nagode da soyayyar ki gare ni na san ko da a yau na mutu na bar duniya na ga masoya na kuma na yarda da kaunar da suke min suke kuma nuna min”!!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button