KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Tace “Hamida kiyi hakuri ki sassauta min dan Allah am sorry,am deeply sorry ki yafe min,wlhy wlhy ban san ya zan hukunta kai na akan laifin da na maki ba,na kasa samin sukuni a zuciya ta am deeply blaming myself for this mistake and i swear i want to make it up to u am ready to make u happy just listen to me ko da sau ɗaya ne”!!

juyowa Hamida tayi ta kalle ta ranta na ɓaci ba kaɗan ba sai ta watsawa Khalid ɗin kallo shima sannan ta ja doguwar tsaki tayi wucewar ta..

Gwiwar fifi ne yayi sanyi nan da nan hawaye ya kawo mata sai ta dubi Khalid da idanun ta dake cike taf da hawaye ta ce mai
“Am sorry,,i truly am”…!!duk tausayin ta ya ishe sa ya san abin na damin ta sannan ba laifin ta bane laifin iyayen su ne but da alama Hamida ta gaji, wa ke da laifi waye baida shi bata dubawa for all she cares shine tana jin mummunar kishin Mufida kuma kishin nata ya fara rikiɗewa zuwa ƙiyayya…

Fita fifi tayi ta koma sashen Marshall inda a nan ta riƙe ƙirjin ta ta fara zubar da hawaye a hankali ko da Marshall ya fito a bazata dan haɗawa kan sa tea ganin bata dawo da wuri ba sai ya gan ta tana kuka..

Kallon ta yake yi daga bisani ta ji muryar sa a kan ta sai tayi saurin ɗagowa ta dube sa,da sauri ta goge hawayen ta tana tmbyr sa me yake so..

Da kamar ya kuma tmbyr ta me ke damin ta amma sai kawai ya faɗa mata abinda yake buƙata haka ta je ta haɗo mai ta dawo da shi ta bashi.

Yana ankare da ita through out yau bata da walwala duk da dai ba sanin halayyar ta yayi ba amma daga shekaranjiya zuwa yau ya ɗan karance ta..
Da damuwar Hamida Mufida tayi bacci yau kuka kam kamar yau ya fara bijiro mata dan sosai ta yi sa tana yi tana tunano lifetime ɗin su a baya,ta dai san ko dukan ta Hamida zata yi ba zata daina bibiyar ta da nemar yafiyar ta ba har sai ta yafe mata dan ita kaɗai ta san irin halin damuwar da zuciyar ta ke ciki haɗe da nauyin da zuciyar nata ke mata akan rashin kula ta da Hamida ke yi..

Mamuh25

Da safiyar washegari fifi ta kuma maimaita abinda ta yi a safiyar jiya na yau ma Marshall bai da masaniya a kai ta tafi sashen su Hamida,har Khalid ya buɗe mata ƙofa sai ya tuno abinda ya faru a jiya da irin rarrashin da ya rinƙa yi wa Hamida akan ta saurari fifi ko da sau daya ne amma ta rufe idon ta ta nuna mai bata jin zata iya yin hakan duk kuwa da shi kan sa ya san abin na taɓa ta kawai rinjayar ta da kishin yayi ne ya sa take ɗauke kan ta akan abubuwan..

“Ina kwana Khalid”ta gaida sa ya amsa sai ta tmby sa lfyr Hamida nan ya ɗan yi shiru wanda ya bata amsar ta akan ba lfy ba kuma har yanzu fushi Hamida ke yi da ita..

Hawaye ne ya cicciko mata a idanun ta na tausayin kan ta da fushin da ƴar uwar ta ke yi da ita..

Kallon Khalid tayi sai ta ji zuciyar ta na mata zafi tana buƙatar wani wanda zai fahimci halin da take ciki..

“Khalid ai ka san manufa ta ko?ina so in gyara tsakanin mu da Hamida am deeply sorry for all my mistakes i really want to clear her mind akan alaƙar mu,na roƙe ka ka haɗa ni da ita i hv to talk to her”!!kuka me sanyi ne ya kusa cin ƙarfin ta sai Khalid ya kasa cigaba da kallon ta a haka kawai ya juya wai dan ya je ya ma Hamida mgn ta fito..

Juyawar sa ke da wuya ya hango ta tsaye bayan su tana bin su da kallo sai Khalid ya ƙarasa gare ta da sigar rarrashi..

“Hamida…Pls ki bada ƴar uwar ki ta gyara abinda ya faru kar fah ki manta ba itace kawai ta maki wannan laifin ba gashi ta ɗau laifin kuma ta yarda zata gyara ita kaɗai toh me zai sa ke kuma ba zaki fahimce ta ba?uhm”?kallonsa Hamida ta yi ta kuma kalli fifi dake tsaye tana hawaye ji tayi kamar tazo ta rungumeta amma tana tsoro..

Duk halin da fifi ke ciki abin na taɓa Hamida a zuciyar ta sai dai ta rasa ya zata yi controlling fushi da kishin ta akan fifi hakan ya rikiɗe ya zama kishin fifi ƴar uwar ta ya rinjaye ta har bata iya fasalta ƙarfin kishin nata..

Tsawon lokacin nan ace bata san da nemo min farinciki na ba sai yanzu?
In dagaske tana so na kuma ina da muhimmanci arayuwarta meyasa da chan bata iya bambamce bacin rai na da jin dadi na ba?meyasa bata karance zafi da kunan dake yawo acikin fushi na ba a duk sanda aka ware ni aka nuna min ni ba komai bane sai ita,….saida na furta?
Wannan ba kaunar mu bane,kowa kansa yafi so ya tafi kauna,dan haka nima kaunata ni kadaice bazan sake shi ba…

Kawar da tunanin da tayi yanzu ta yi ta dubi fifi dake kuka ta gasa mata kalmar nan da ke ma fifi zafi a zuciya.

“I hate liars and pretenders ki fitar min daga apartment”!

A hankli ta faɗa so calm and gentle ta yadda ta san zai taba fifin emotionally..

Ta kuwa yi nasara dan sosai fifi ta fashe da kuka mai ban tausayi haka ta juya ta fita ita kuma Hamida ta jingina bayanta da staircase har sai da Khalid ya matso ta ya rungume ta yana bata sassayanr runguma,shidai ba wai yana ƙoƙarin tursasa mata zuciya akan sai ta yafewa fifi bane a’a yana gudun kar kishin yayi yawa ya fi haka ne har ya zo ya taɓa martabar gidajen auren su gaba daya..

Gabaɗaya ranar Khalid aikin ban haƙuri da nuna ƙauna ya rinƙa yi wa Hamida tun tana ɗan kawar da kai har dai ta fara sauraron sa suka dawo daidai Yayin da fifi ta kasa samin kwanciyar hnkl tun bayan fitar ta daga sashen su Hamida daurewa tayi ta bincika kitchen ɗin ta ga abubuwan dafawa ta zaɓi wanda ya dace ta girkawa Marshall dan yanayin rashin lfyr sa..

Haka yau ma ya gan ta tana kuka amma ɗabi’ar nan ta bana shiga abinda babu ruwa na,jin kanshi yake kamar ai fifi yarinya ce ita shi kam ya haife ta ya juya ya dubeta baya jin wani tsaurara mata tambayoyi akan dalilin kukan ta zai ƙara mai mutuncin sa instead sai dai ta raina sa dan zata ga ya damu da ita..

Haka nan itama tayi ranar kaf cikin damuwa da kuka akai akai,abu kamar wasa zazzaɓi ya fara shigar ta a hankali amma ta yi ta dannewa tana kama jikin ta tana ma Marshall ayyukan da ya dace..

Sam bata cika damuwa da auren bata kamar yadda t sa lamarin hamida aranta,tasan sun ma hamida rashin adalci kuma bata ganin laifin kowa sai kanta ayanzu

Ba abu ne mai sauƙi ba a gare ta tun tana ganin zata iya gyara komai ita kaɗai har ta fara fiddo damuwar ta sarari in Marshall ya fita zai dawo ya same ta tana kuka,ba zata jira ya tmby ta ba zata fara tmbyr sa shin bata da hali mai kyau ne,abin na ɗaure masa kai dan shi bai san sanadin kuka da damuwar ta ba kuma baiyi lokacin tambayarta ba..

Kimanin sati biyu kenan masu kyau Mufida ta ɗauka tana ƙoƙarin ɗinke tsakanin ta da Hamida amma a duk lkcn da ta kusanci inda Hamida take sai Hamida ta bata wasu irin halayyar
Munana masu zafi

Hamida ce wacce bata rasa komai daga wurin mijin ta ba dan ba ƙaramin kula da ita yake yi ba

haka fifi take ziriyar sashen ta zuwa na Hamida a kullum a ƙalla sau uku ko huɗu a rana amma zuciyar Hamida ya mata dauri me wuyan kuncewa…
Abubuwa dayawa inta tuna takanji tsanan fifi da duk wani wanda ya lalata mata zuciyan ta ya dawo baki

Rayuwa ba ƙaramin sauyawa fifi ta yi ba ba dan komai ba sai dan damuwar ƴar uwar ta d ta sakawa zuciyar ta gashi tayi auren da bata san ma’anar sa ba,a haka ne rashin lafiyar ta ke ta tashi a hankali a hankali amma bata bari a gane ko shi Saheeb ɗin da take kwana tare da shi a apartment ɗaya bai sani ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button