KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Su da suka ce zasu dawo kafin magrib sai gashi sai 7:24pm dai dai Khalid ya ja birkin motar da suka fita da shi.

Hannun sa cike da shopping bags da packaged eatery leathers duk na fifi Khalid dinne ya siyo mata dan kawai ya faranta mata..

Dawowar su yayi daidai da lekowar Hamida ta windown ta dan tun dazu ta damu tana ta duba lokaci tana leko window sabida bata ji muryar kowa cikin yan gidan ba,.

alama ne na cewa yar lelen tasu bata nan dan haka annurin gidan ma dole ya dauke na dan wucin gadi..

Tana kawo kan ta kuwa ta hango Khalid na bude ma fifi mota har fito tana mai dariya hannun sa ya saka a motar yana kwaso tsarabar outing din da suka futo..

Sosai hamida take ganin cikakken view din na duk abunda dake faruwa a nan farfajiyar gidan sakamakon hasken kwayayen lantarkin da ya dallare gidan ya haska ko ina..

Tsaye take tana kallon su wayar dake hannun ta ta dada damkewa dan saura kiris ya fado daga sama zuwa kasa kasa rike hawayen ta tayi kawai ta bar su suka rinka fitowa,babu murya bare wani reaction da tayi,wannan tsantsar hawayen bakin ciki da takaici ne ke bin fuskar ta wanda ya samo asali ne daga ciki cikin zuciyar ta..

Kasa cigaba tayi da kallon nasu kawai ta koma ciki hade da buga kofar window din wanda su kuma daga kasan suka ji karar bugun dan da karfi tayi kuma dama windown asalin metal ne mai kyaun gani da tsada..

A hanzarce duka suka dago kai suka dubi windown wanda babu alaman kowa,Kallon junan su suka yi suna mamakin wa zai aikata hakan?amma da yake abin dake gaban su ya fi karfin wannan yar hayaniyar sai suka cigaba da hirar su kamar ba gida daya zasu kwana su tashi ba..

“…Sai da aka fara kiran sallar isha’i sannan suka karasa ciki inda suka tarar da abinci shake saman dinning table alamar ba a ma ci abincin ba dan komai a shirye yake neat babu kowa,aranta tace kenan sun shiga yin sallar isha’i .

Murmushi tayi tana mai karbar wasu daga cikin kayayyakin nata shi kuma yana rike da wasu,haka ya raka ta har dakin ta ya ajiye mata kayan yana mai nuna mata kar tayi lattin fitowa dinner ta amsa ta hanyar gyada mai kai…

Bayan fitar sa ne ta sakawa kofar lock tawani daka tsalle da dariya dan yau is one of the best day da zata iya kirgawa na sakawa har cikin tarihin rayuwar ta

“kusan duk abubuwan da take bukatar sani a rayuwar Khalid din nata yau ta san kaso tamanin kuma ta san da sannu zata gama sanin sauran halayyar sa..

A tunanin ta da nazarin ta gaba kadan ita da Khalid din zasu yi sabon da ba a yi zato ba dan hallayar su kusan iri daya ne yadda take son morewa ta ji dadin rayuwa haka shima yake,ire iren suturun da take sha’awar sakawa shima haka ne..

Bata san ina zata saka kan ta dan tsananin farinciki da annashuwar da Khalid din ya saka ta ciki yau ba,mannewa tayi da jikin wardrobe din ta tana ta yiwa kan ta murmushi tana kara tuno awannin da suka gabata kafin yanzu..

Jin ana sallame salla ya sa tayi wuf ta shige toilet dan yin alwala dan dama ko magrib bata yi ba ga isha’i tayi har an idar…

Sai da tayi wanka ta kimtsa kan ta tayi sallolin nan ta fito ta nufi hanyar sashen yar uwar ta hamida dan ganin ya lafiyar ta yake dan a dazu da suka fita rabin hankalin ta na ga tunanin yar uwar tawainiyar ta

ganin yadda duk ta bi ta kasa sake jikin ta kamar ba cikin family din ta take ba abun na matukar damun fifi..

“….Tsayuwar ta da sallamar ta a bakin kofar dakin Hamida ya kai kusan mintuna biyar tana ta sallama da dan bubbuga kofar dakin amma ba a bude ba kuma ba wai dan ba a ji bane a’a kawai jin budewar ne kawai mai dakin bata jin yi..

Har fifi tagaji ta dubo number din Hamidar da zumar kiran ta aganin ta ko bacci take yi amma in ta ji karar wayar kila ta farka,sai kuma ta ga wani kiran ya shigo wayar ta,duba numbern tayi ta ga daddyn su ne dan haka cikin sauri ta daga kiran kuma a dai dai wannan lokacin ne aka bude kofar..

Ta karasa shiga dakin ne wayar na sagale a kunnen ta tana gaida daddyn nasu cikin shagwaba.

Ita dai Hamida tun da ta bude mata kofar ta koma ta zauna bisa sofa dake dakin bata kuma dago kan ta ta kalli Mufidar ba dan ta san wanda take wayar da shi ba kowa bane face daddyn su wanda ita ko digon missed call din sa bata sami arzikin samu ba..

Dadin mamakin Hamida shine lokacin da ta ji fifi tana cewa”Daddy ai gashi yanzu na daga kiran,dazu ma da ka kira muna tare ne da Khalid ya kai ni zagayan gari kuma ma ai daddy tun bayan saukowar mu in ban manta ba maganar mu da juna sau takwas fa ka kirani kenan and i have been ok tun dazu har yanz kadena damuwa kaji daddyna am fine wallhy…,ko ka manta tare da Ammy da Hajja da Khalid nake?duk fah cikin family nake sannan ga yar uwa ta abin alfahari na Hamida”

..dan shiru ne ya biyo bayan maganar da fifi tayi..

Hamida kan ta a kasa tana auna irin tsabar kiyayyar da ake mata a cikin ahalin ta kamar ba zama tare suka yi da Mufidar cikin cikin mahaifiyar su sannan aka haifo tare har suke rayuwa yau atare ba,ita ce ta zamo bare da ba a san tana raye ba?ko dai ta mace ne da har ba’a lura ba,8 calls daddyn su ya ma fifi ita tana nan tana ta jiran ganin kiran sa sau daya bai kira ba

even after seeing her 3 missed calls bai bi kiran ba sai fifi da ya kira ta har sau takwas..abun yanacin mata rai matuka

Waya ta ji a kunnen ta kuma shine ya ankarar da ita cewa a take muryar daddyn su ta ji yana ce mata
“Hamida ta yaya kuke?kina lura da yar uwanki kuwa? na ga kiran ki har uku amma bana kusa kuma da na dawo na gani sai nayi tunanin tare kuke da yar uwar ki dan haka na kira ta in ya so ita sai ta baki mu gaisa kawai,hamida tace hmmm.yace da fatar kema kina jin dadin gidan su Ammyn naku?murmushi mai ciwo tayi jin wai ashe ya ga missed calls din nata ma, amma bai biyo ta ba sai ya kira wacce ta fiye mai soyuwa a zuciyar sa sannan sai yanzu ne zaina tambayar ta akan jin dadin zaman gidan wanda in da zata sami dama da mutumin da ya cancanta toh da zata samar da shi irin rayuwar da ta fara ginawa a yan awannin da ta tsinci kan ta a ciki a cikin gidan da take ganin tana iya bugun kirji tayi alfahari da shi..

“Daddy komai alhamdulillah”iya kalmar da ya iya fitowa daga bakin ta kenan sai tayi shiru,ko me ya kuma ce mata sai ta mikowa fifi wayar tana tashi daga wurin dan bata muradin jin cigaban hirar tasu..

Sai da ta tabbatar sun gama sannan ta fito da fake face ta fuskanci fifin tana fadin
“So,ya outing din naku ya kasance”?ita kadai ta san karfin halin da tayi kafin tayi tambayar nan,tunanin ta kamar kullum fifi zata hau zayyano mata komai da ya faru ne dalla dalla sai dai yau ta ga akasin hakan

Dan fifi yi tayi kamar bata ji tambayar ba ita ta aiko mata da nata tambayar..
“Hameda meye ne wai ni kam, me ke faruwa da ke ne tun zuwar mu kasar nan?duk yanayin ki ya sauya kamar baki ji dadin tahowar mu ko dan nan kasar batamu bane ko?duk fah fara’ar ki ta dauke baki walwala hamida, baki sakin jikin ki dani na rasa gane maki Hamee

Please dan Allah ki sanar da ni damuwar ki kin ga duk duniyar nan baki da wata wacce zaki iya bayyanawa damuwar ki sama da ni,hamida ta a tare muka taho duniya, duk da ni din ba mai cikakkiyar lafiya ba ce kuma ina iya barin duniyar ma ako wani lokaci,
toh in baki fada min damuwar ki ba ta yaya kike so in taya ki saka farinciki a rayuwar ki, da fuskar ki wanda ba zaki taba mantawa da shi ba ko bayan na bar duniyar uhum?..fifi kamar zata yi kuka haka ta karasa maganar..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button