KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Mamuh23

Fifi da tun bayan fitar ta daga sashen Marshall ta ɗan tsaya a gefe ta rinƙa dariya kamar wata sabuwar kamu,haka har ta ƙarasa sashen Ammy bata daina dariyar ba sai da Ammy ta tasa ta gaba da tmby sannan cikin dariyar da ta jima rabon ta da yi ta hau labartawa Ammy abinda ya faru tsakanin ta da Marshall nan itama Ammyn ta ɗan dara tana kuma kallon fifi da mamaki ta tmby ta dalilin ta na dariyar amsar ta shine
“Ammy he is old kamar yadda ya faɗi but he doesn’t look lyk an old man wai fah 45years Ammy ki ji fah,ta yaya zan yarda?ni na san da gangar ya faɗa min shi gani yake kamar shekaru na da na faɗa mai ba gaske bane shi ya sa da na tmby shi ya amsa min haka nan amma ni na san bai kai 45 ba right Ammy”?ta tmby Ammy tana murmushi sai Ammyn ta murmusa itama tana dariyar yarintar fifi a zuciyar ta..
“Ke kuwa baby me ya sa kike tunanin zai maki ƙarya?ai duk abinda Saheeb ya faɗa haka yake baya ƙarya iya gaskiyar sa ne dan haka ki daina ɗaukar zantukar sa da wasa iya gaskiyar sa kenan”!shiru fifi tayi tana nazarin zantukan Ammy,toh in dai da gaske shekarun sa 45 ne saura 5years ya cike 50years kenan..
Lallai Allah mai halitta wani bai kai 45 ɗin ba ma amma sai ka gan sa kamar ɗan 50 yayin da wani ɗan 50 ɗin sai yayi kamar bai ko taka layin 50 ba..
Tana iya cewa Marshall yana cikin layin waɗannan mutanin da ke da shekaru amma shekarun nasu bai nunawa ko kaɗan,but me ya sa hakan ta kasance a nasa case ɗin?shiru tayi tana tunanin rashin dacewar dariyar da ta rinƙa mai ɗazu..
Kalkon ta Ammy tayi tayi shiru tana jiran jin ko zata kuma yin wata mgn amma sai ta ga tayi shiru dan haka ta kuma jaddada mata cewar duk abinda Marshall ya faɗa mata ta ɗauka gaskiya ce dan baya ƙarya ko wasa in har akan muhimmin mgn ce,daga nan fifi ta rinƙa wasu tunane tunane kala kala har dai lkc ya rinƙa tafiya tana abubuwa ne amma hankalin ta na ga tunanin Marshall tana ganin kamar bata mai daidai ba kamar ta mai rashin kunya ne a matsayin sa na babba dake gaba da ita..
Haka dai ta ƙarar da ranar cikin tunanin rashin kyautawar ta ga Marshall har yamma tayi wankar yamma ta dawo ta natsu wuri ɗaya tana saƙa abinda zai haɗa su ta ba shi haƙurin abinda ta mai ko da zai ɗaure fuska ne…

Ammy dai ido take ta bin ta da shi tana observing ɗin ta amma bata nuna mata ta san halin da take ciki ba bare ta saka ran zata sami encouraging words daga gare ta..

Yamma lis suka iso gida duk a gajiye amma hakan bai hana Marshall saka Ammy ta aiko mai da abincin sa na dare ba a cewar sa ya gaji baya jin yana iya zuwa nan part ɗin ta sai dai ko gobe…
Tayar da fifi Ammy tayi daga ɗan taƙaitacciyar baccin da ta fara yi yanzu tana kiran ta a hankali,sai ta ɗan buɗe idon ta ta dubi Ammy..
“Tashi ki kaiwa mijin ki abinci yanzu ya dawo kuma a gajiye yake ba zai iya ƙarasowa nan ba ki je ki haɗa mai abincin sa pls yi sauri bai da jimirin yunwa”!!tashi fifi tayi zaune tana duba bed side clock ta ga 8:45pm sai ta sauko daga gadon ta ɗau hijabin ta ta saka sannan ta nufi hanyar kitchen dan haɗa mai abincin..

Dama akwai abincin a food warmers sai ta jere a saman tray sannan ta haɗa mai coffee mai ɗumi ta fito,ta hanyar baya ta fita dan ya fi sauƙi..
Da sallama ta shiga sashen nasa tayi sa’ar ganin sa a parlor yana ƙoƙarin zama..
Da ganin sa ka san yayi wanka ne dan kayan bacci ne a jikin sa sai dai akwai Cardigan a saman rigar baccin nasa sai abin ya ɗan ɗaurewa fifi kai tana tunanin yanayin garin ba wani sanyi ake yi sosai ba bare ya ce sanyin ne ya saka sa saka Cardigan ba,wata sashe na zuciyar ta ya ce mata kin sani ko shi sanyin yake ji tunda tun safe a waje suke ke kuma kina cikin gida?..
Yin wannan tunanin sai kawai ta kawar da abinda ya bijiro mata ta ƙaraso cikin parlorn tana kuma yin sallama..
Amsa mata yayi ba yabo ba fallasa kamar ba shi ba sai ta kalle sa a karkace sai kuma tayi ƙasa da kan ta tana gaida sa..
Amsa mata yayi yana kallon ta yana tuno abinda ta mai da safe sai ta riga sa fara mgn..
“Ammy ce ta ce in kawo maka abinci”!kallon ta yayi na wasu daƙiƙi sai ya buɗi baki ya tambaye ta
“Ke kullum aiko ki ake yi baki zuwa dan kan ki”?sai tayi shiru bata ce komai ba har dai ya ce da ita ta zauna,ba musu ta zauna tana ɗan kame jikin ta..

Janyo abincin yayi gaban sa ya bubbuɗe ya mayar ya rufe sannan ya dube ta ya ce
“Wa yayi girkin nan”?mamakin tmbyr nasa tayi sai dai ta amsa mai da
“Ammy ce”!ga mamakin ta sai ta ji ya kuma tmbyr ta
“Ke fah me kika yi”?a wannan karon kasa cigaba da kallon ƙasa tayi sai da ta ɗago ta kalli fuskar sa tana mamakin sa sai ta ce
“Na taya ta hira a lkcn da take girkin”!!abin dariya but ba damar yi sai ya gimtse ya buɗe food warmer ɗin ya tsaya yana kallon abincin yana kallon ta..
Tun kallon nata baya affecting ɗin ta har ya fara,ta rasa ya zata yi kuma ta rasa me yake nufi da irin wannan kallon sai da ya mata wata tmby sannan ta fahimce sa
” Je ki kirawo min masu girkin nan”!wato su su zo su yi serving ɗin sa kenan lallai al’amarim soldier sai shi..

Tsam ta tashi ta ƙarasa gare sa ta tsuguna ta fara serving ɗin sa tana yi tana tmbyr sa ko yayi,da ƙyar ma take tmbyr dan jin wani iri da ta rinƙa yi bata saba ba..
Shi dai bai amsa mata ba amma yana kallon yawan abincin da take zuba mai yana jiran ta ya ga ko zata tsaya ko cigaba da zubawan zata yi.

Dan kan ta ta tsaya dan ta san duk cin abincin sa wannan zai ishe sa sai ya maida kan sa gare ta daidai tana yunƙurin zama dan ta gaji da tsugunen..
“Na gama”!!ya kuma kafe ta da ido yana ɗage mata gira ɗaya sama wai bai fahimce ta ba sai ta dage ta kuma ce mai
“Na gama zuba abincin yayi”?sai a sannan ya dubi abincin ya dube ta ya ɗau spoon ya fara ci ba tare da ya tanka ta ba..
Ajiyar zuciya ta sauke tana jiran ya ɗan ƙara yin nisa da cin abincin sai ta sako mai mgnr dake ran ta,amma tana shakkar sa tana ganin ya wani yi mata ƙwarjinin da ba zata iya tunkarar sa kai tsaye ba amma da zama da abin a ran ta gwara ta ba shi haƙuri.
Kawai sai ta daure ta fiddo mgnr kai tsaye bayan doguwar wasi wasin da zuciyar ta ya gama yi..
“Ka yi haƙuri da childishness ɗi na da na maka da safe”!!kasa cigaba da cin abincin yayi ya tsaya yana kallon ta sai ya ce
“Ban gane ba”!oh ya salam yanzu waye zai ce bai fahimci wannan hausar nata ba?tmbyr da fifi ta yiwa kan ta kenan sai ta kuma yi mai fashin baƙi..
“Na tmby ka kuma bayan ka amsa min sai na saka dariya ka yi haƙuri Ammy ta ce min gaskiya ka faɗa min”!a wannan karon sai da ta ba Marshall dariya amma yayi murmushi mai sauti ita kan ta sai da ta ji mamakin murmushin sa dan bata taɓa gani ba tunda ta ssn shi fa ya dawo..
“Dama kin yi zaton wasa nake maki?na maki kama da mai wasa a mgn?me ya sa ke komai Ammy ce ke maki?wato ni na faɗa maki amsar tmbyr ki amma Ammy ce ta tabbatar maki da gaskiyar amsa ta unbelievable”!ya ƙarasa mgnr yana cigaba da cin abincin sa..

Shiru ta mai tana sauraron sa ganin bai wani ɗaga mata murya ba sannan in ta natsu tayi tunani kamar akwai alamar rashin lfy tattare da shi dan muryar sa ya nuna..
Bata kuma faɗin komai ba kamar yadda shima bai ce komai ɗin ba,zaman kurame suka yi a wurin har ya ƙoshi ya matsar da abincin ta zo ta hau tattarawa dan a takure take so take ta koma inda ta fi sabawa da shi wato sashen Ammy..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button