KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Washegari a cikin gida misalin ƙarfe goma na safe aka ɗaura auren MARSHALL MUHAMMAD SAHEEB Maƙarfi da KHADIJA NUHU MANDE ɗaurin auren da aka yi sa cikin shiru ba tare da hayaniya ba ko gayyata dan basu buƙatar kowa sai su…

A ranar bayan an ɗaura auren Mufida ta ƙulle kan ta a ɗaki ta sami damar fitar da damuwar zuciyar ta dan kuka tayi sosai har sai da numfashin ta ya rinƙa sama sama sannan ta sararawa kan ta ta watsa ruwa ta fito da alwala tayi nafila raka’a biyu tayi addu’ar da zata yi sannan ta kwanata bisa sallayar.

Tunani takeyi aranta gameda yanda rayuwar ta juya cikin sauri,
Itace da auren tsohon datakeyiwa ‘yaruwarta maganar aurensa,
Shin ita wane farin ciki ko Jin dadin rayuwar aure zata samu a auren Wanda ya tsofeta?

QADDARA TA RABATA DA WANDA TAKE TUNANIN SHINE ABOKI MAHADAR RAYUWARTA,

MIJINDA ‘YAR UWARTA DASUKA FITO CIKI DAYA,
RANA DAYA,
AWA DAYA MINTINA BIYARNE A TSAKANINSU ZATA AURA AURENSA YADAWO KANTA BAYAN TANA TUNANIN BATADA WANI ABOKIN RAYUWA KAMAR KHALID,
WACE QADDARACE WANNAN?
SHIN MENENE MAKOMAR RAYUWAR AURENTA DA WANDA HARYAU BATAGA KALARSABA.

Ahankali ta rintse idanuwanta dasuka fara bushewa da kuka tana Kiran sunayen ubangiji sbd yanda zuciyarta ke zafi da nauyi.
a nan bacci ya ɗauke ta dan ta sami sassaucin cunkushewar zuciyar ta..

MamuhMamuhgee

15

Da safe aka kawo abinci sashen su Hamida daga Hajja kuma saboda Khalid ba dan Hamida ba dan halin da Hamida ta nuna a shekaranjiya ya saka Hajja jin wani iri tana mace amma tunanin ta irin na da namiji har yau abin bai bar kan ta ba..
Bayan an kawo abincin a ajiye masu aka fita dan basu tashi daga bacci ba sai wuraren 11am tun sallar subhi da suka yi suka koma sai yanzu suka farka kenan an yi ɗaurin auren Mufida da Saheeb ba tare da an gayyace su ba musamman shi Khalid ɗin..

Cikin shigar atamfa riga da zani haɗe da babban mayafi Hamida ta fito ta tarar da angon nata yana jiran ta sun je su gaida su Ammy su kuma yiwa Hajja godiyar abincin da ta aiko masu da shi dan sun san dama Ammy na fushi da su ƙila sai anjima zata saurare su..
Shima Khalid din a yau yayi shigar alfarma ya fito a angon shi half kaftan da hula shirin da bai taba yi ba kenan tunda ta san shi dan ko a ranar bikin nasu wani irin kaftan ya saka da bai fiddo sa ba..
Murmushi shimfiɗe saman fuskar su suka nufi sashen Ammy inda ta amsa gaisuwa kawai ba tare da ta kuma tanka masu ba har suka ƙaraci zaman su suka wuce zuwa sashen Hajja da tunanin ita zata tarbe su da sanyin fuska tunda ta aiko masu da abinci sai dai ba yadda suka yi tsammani bane dan yadda ta ɗaure fuska ta kawar da kan ta gefe kaɗai ya tabbatar masu har yanzu fushin take yi da su kuma fuskar su kan sa bata jin ganin sa..
Tashi suka yi suka nufi sashen daddyn su,inda aka sami bambanci kenan dan shi ya amsa gaisuwar tasu ba yabo ba fallasa kuma ya masu fatar alkhairi haɗe da sanar da Khalid batun ɗaurin auren da aka yi na ɗan uwan sa da ƙanwar sa yana mai ce da shi ya kira ɗan uwan nasa ya masa fatar alkhairi..

Ko da Khalid ya ji wannan zance babu inda bai yi sanyi ba a jikin sa dan bai yi tsammanin farat ɗaya za a ɗau hukunci mai zafi haka ba,yayi tunanin za a ba Mufidar damar zaɓar abokin rayuwar ta ne dan har ya fara tunanin haɗa ta da wani abokin sa na kusa mai ɗabi’u kusan irin nasa amma an riga an gama tunda aka aura mata yayan sa sai dai matsalar shin tana son yayan nasa kuwa ko dai haɗin iyaye ne?

Tambayar da ya rinƙa kai kawo kenan a zuciyar sa amma ya san bai da wannan ƙimar na tambayar daddyn dan laifin sa na nan bai goge ba da saura ko da zai gogen amma sai ya ɗau lokaci shi ya sani,wannan dalili ya sa ya ja bakin sa yayi shiru har daddyn ya gama nasihar sa a gare su ya sallame su suka fita bai bar tunanin ya lafiyar fifi ba kuma a wani hali take…

Suna fita Hamida ta ja hannun sa zuwa old room ɗin ta tayi saurin saka lock ta cire mayafin ta da dama ya ishe ta sbd rashin sabo..
Dariyar ta da ta rinƙa dannewa ne ya fito fili sai da ta dara har tana riƙe cikin ta mijin nata na kallon ta sannan ta matso kusa da shi ta rungume sa tana mai cigaba da ƙarasa ƴar dariyar da ta rage mata..
Shi dai Khalid bai san me ya saka ta dariyar ba kuma hankalin sa da tunanin sa na ga fifi ko a wani hali take,wannan dalili ya sa bai ce mata komai ba har ta zo ta rungume sa sannan ya sami damar tambayar ta..
“Me ya faru ne love kike dariya haka tun ɗazu”?jujjuya kai ta shiga yi tana murmushi sannan ta ce
“Miji na dariya ta manufofi biyu gare ta,na farko aurar da fifi da aka yi ga wannan tsohon da aka so a haɗa ni da shi,na biyu kuma murnar samin ka da nayi a matsayin miji na da na rasa ka in har a ranar nan an aura maka fifi ni kuma aka aura min wannan tsohon amma Allah na amfani da zuciyar mutum ne ba kalaman sa ba shi ya sa ya bamu ikon mallakar junan mu a matsayin ma’aurata bai bar mu mun zalunci wani ko wata ko wasu ba ya bar mu tare dan Allah kaɗai ya san abinda ke zuciya ta da ban mallake ka ba miji na,na godewa Allah da ya bani kai kuma ya mallaka min kai please don’t ever leave me i will die if you forsake our love”!!da ɗan muryar kuka ta ƙarasa maganar dan wani irin azababben so ƙauna da shauƙin mijin nata dake shigar ta bata san ya zata iya rayuwa a doron ƙasar nan ba tare da shi ba..

Khalid dake sauraron ta cikin mamaki da jimami sai ya kasa faɗin abin da yayi niyar faɗi musamman da ya ji yanayin muryar ta ya sauya kamar kuka take yi sai shima ya ƙara tightening hug ɗin yana mata alƙawarin duk wuya duk runtse suna tare babu mai raba su sai hukuncin ubangiji..

Cikin zurfi a tunanin maganarta cikin ransa nazarin maganarta,
Shin sunkuwa San waye Marshall dasuke kiransa da tsoho?
Tabbas basuda masaniyar waye Marshall Amma bazai fadaba zai Bari su gani a idanuwansu.

Kusan mintuna sama da biyar suka kwashe suna a haka sannan ya raba jiki da ita ya ɗauko mata mayafin ta ya yafa mata dan su koma sashen su su ci abinci..

Har sun fito hannun sa cikin nata sun zo giftawa sai ta ji zuciyar ta na raya mata yin wani abu a ɗakin da suka wuce yanzun nan dan haka ta ɗan ja da baya tana ce ma Khalid
“Baby ka tafi ina so in gana da ƴar uwa ta zan zo in a jiffy”!!shi babu abinda ya zo mai rai jin ta ce zata gana da ƴar uwar ta sai ya gyaɗa mata kai ya ce zai raka ta amma ta ce ta yafe mai ya tafi ita zata zo daga baya.
Sai da ta tabbatar ya tafi gabaɗaya sannan ta koma da baya ta nufi ɗakin fifi bakin ta ɗauke da sallama sai dai bata ji an amsa ba so ta tura ƙofar ta shiga..
Hango fifi tayi kwance saman sallaya tana bacci fuskar ta ya ɓaci da hawaye sai tayi murmushi tana jin wani sanyi a ran ta..
Ƙarasawa gare ta tayi tana taku ɗai ɗai har ta zo ta tsuguna tana ƙare mata kallo,tunowa tayi da ranar da fifin ta kawo mata ziyara ta gama tsokanar ta sannan ta gaya mata wai tausayin ta take ji duk kyawun jikin ta wannan tsohon ne zai mora,sai tayi murmushi haɗe da lumshe idanun ta sannan ta cigaba da maganar zucin ta tana faɗin yanzu wa yayi asarar kyau da da surar jiki?ke Mufida dan ke kika ƙare da tsohon da kike murnar ni zan aura oh na tausaya maki dama haka rayuwa take yau kayi dariya gobe ko anjima ka yi kuka…
Ina tsananin sonki yar uwata fiyeda komai da kowa a duniya
Sai zuciya Batada qashi bansan ya zanyi na Hana zuciyata tsanarki ko kishinki ba sbd sune sukeda haqqin sakamin qiyayyarki yar uwata duk da nasan ba laifinmu bane Amma we’ll have to pay the price for abinda iyayenmu keyi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button