KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Kallon ta Hamida tayi tana jin maganganun yar uwar nata tsanake har yana son yin tasiri a zuciyar ta dan ta san bayan matsalar ciwon nan dake damin ta,inba don aan ware ta ba to da rayuwar su ba a haka zai ginu ba

dan sarai ta san Mufida bata da son kai bata da kyashi,amma wasu lokutan abubuwan dake faruwan be sai take ganin kamar fifin na da son kan ta da yawa wajen janye komai da kowa..

Matsowa fifi tayi ta riko hannuwar ta biyu cikin nata tana kallon cikin idanun ta hade da kuma yi mata tambayar

“Ko dai nan dakin bai maki bane mu yi musayar daki ke ki koma wancan nawa ni in dawo nan”?

kallon ta Hamida ta cigaba da yi kafin ta cire hannun ta cikin na Mufida ta mike tsaye tana fadin

“A’a fifi na,ko daya cikin tambayoyin ki babu wanda ke dami na,yanzu ki zo mu je mu ci abinci dan kin ga sai da daddy ya kuma min gargadin kar in rinka barin ki da yunwa in kular masa da ke,so mis Khadijah Mufida Mande can we go for our dinner now”?

sunan da ta kira ta da shi ne ya saka ta murmusawa dan da sigar tsokana ta fadi sunan..

Fifi Tana son sanar da mufida sirrin zuciyar ta game da Khalid amma sai ta ga kamar lokaci baiyi ba,gani take zai fi in ta bari abin ya kara karfi sai ta fadawa yar uwar nata…

Tare suka fito suna dan hira kadan kadan har suka karaso main parlor suka nufi dinning table..

Hajja ce ta fara ankara da Hamida sai ta dafe kai cikin jimami tana fadin
“Hamida kina gidan nan amma aka yi ta sha’ani amma baki fito an yi da ke ba kuma baki aiko kowa ya kawo maki abincin rana ba?ni dai bani son irin wannan dabi’ar taki da kika dauko ta turawa a ce mutum na cikin ahalin sa amma yana jan jiki da su kamar ba shine nasu ba”?kasa karasa zaman Hamida tayi ta tsaya a tsaye tana kallon Hajja har ta gama maganar ta sannan Ammy ta dora nata..

“Hajja ni wallahi mantawa nayi da ita da na aika mata da nata dazu, kin san sam yaran nan na zamani ba cika son takurawa rayuwar su suke son ana yi ba kin ga bai dace ana yawan shiga harkar su ba”!

kamewa Hamida tayi a tsaye tana nazarin zantukar nasu,da kamar ta juya ta koma amma sai ta ji hannun fifi a kan hannun ta da ta saka ta janyo kujera da niyar zama amma ta kasa…

Kallon ta tayi sai ta ga ita murmushi ma take yi dan haka sai ta fasa komawar kawai ta zauna ba tare da ta ce kala ma maganganun su ba..

Serving din su abincin Ammy tayi suka zazzauna har sun fara ci sannan Khalid ya zo shima yayi joining din su saidai duk hankalin sa akan fifi ita kdai yake,bayan ita kuma Hamida hankalin ta akan shi yake tana mai ambaton kaunar sa a ran ta..

Abubuwa kala kala sun faru a gun cin abincin sai dai duk ba a sako Hamida ciki ba sai ita fifi,dannewa Hamida ta rinka yi har aka kammala cin abincin ta mike tana masu sai da safe,bata jira amsar su ba tayi gaba dan ta san kara mata damuwa zasu yi..

Ammy ce ta bi ta da kallo kamar ta so dago wani abu game da hamida karar da fifi ta saki ne ya sa tayi saurin maida hankalin ta ga tana tambayar ta lafiya..

Ashe spoon Khalid ya saka cikin abincin ta ya dauke mata last sliced of cucumber din dake cikin abincin shine ta sake kara dan har ya kai baki zai saka..

Fada Ammy ta mai akan yana babba amma madadin ya faranta mata a matsayin ta na kanwar sa shine yake kuma tsokanarta…

Hajja kuwa ta kasa hakura da dabi’ar Hamida dan tayi ma abun bahaguwar fahimta gani take hamida miskila ce marar saurin sabo..

Tace “Wannan yarinya dai dabi’ar ta daban take,ana zaune ana hira amma ta tashi ta wuce ciki anya bata da wata damuwa kuwa?karasa tambayar tayi tana kallon Ammy..

Dage kafada Ammyn tayi alamar oho bata sani ba,daga haka suka maida hankalin su ga shirmen Mufida da Khalid har suna tambayar ta ina take son zuwa gobe dan bude ido..

Kasancewar bata san ko ina ba sai Khalid ya rinka zayyano mata wuraren bude ido da daukar hankali,daga nan ta rinka zabar inda zata kai ziyarar a washegarin..

A haka dai suka karasa hirar ta sallame su akan zata koma ta kwanta dan kan ta ya fara ciwo,ai jin kalmar ciwon nan ya sa suka daga hankulan su har abin ya ba fifi tausayi dan ta san duk son da suke mata da kaunar da suke mata dole watan wata rana haka zata mutu ta bar masu duniyar..

Rungume su tayi tana furta masu kalaman so da kauna hade da godiyar kulawar su akan ta,sannan ta wuce su suma suka wuce zuwa makwamcin su..

Anan ma Bata tafi dakin direct ba sai da ta fara duba dkin Hamida ta zauna tare da ita ta rinka jan ta da hira mai ban dariya sannan ta bata sassanyar runguma dacewa kar ta manta in tana da damuwa ko tana jin tana bukatar shawara kar tayi kasa a gwiwa wurin sanar da ita ita kuma ta mata alkawarin bata dukkan lokacin ta da hankalin ta dan ganin ta taya ta magance damuwar ta..

Da haka suka rabu Hamida na ta nazarin kalaman yar uwar nata,taji dama dama sosai kamar dai ta dauka tayi amfani da shi,can sai kuma ta fasa dan karfin kiyayyar da take ma yar uwar nata kamar ya fara rinjayar karfin soyayyar da take mata..

kuma ko ba dan haka ba tasan ita ba zata taba zuba ido ta rasa Khalid ba,tace makanta enough is enough fifi,fifi,fifi,kowa fifi toh abin ya isa haka

Anan ko da ace mutum daya ne zai saurare ta tasaka aranta Khalid ne.

Da Hakan zai fiye mata kallon su da saurarar irin kalar son da suke ma Mufida..

A fannin fifi kuwa kasa runtsawa tayi har sai da ta karema hotunan da suka yi tare da Khalid kallo,ta kalli hotunan nan sun fi a kirga sannan daga bisani ta kashe bed side lamp din dakin ta runtse idanun ta tana me sa kan ta baccin dole dan ba baccin take ji ba ta fi jin kamar begen Khalid ne ya fi dacewa da ta yi a daren ba bacci ba shi ya sa ta runtse idanun dan dole koda bacci zai sace ta in ya so ko a mafarki ne ta lazumci begen sa..

MamuhMamuhgee

8

Da sassafe Hamida ta tashi ta bar sashen ta ta nufi
sashen Mufida dan aiwatar da wata kudiri da zuciyar ta tayi ta ayyana mata akan ta aiwatar da zarar ta farka daga bacci..

Kamar marar gaskiya haka tayi ta sanda tana bin hanya a hankali har ta zo kofar dakin nata ta ja ta tsaya ta hau bubbuga kofar a hankali tana kiran sunan ta a hankali kamar bata son a ji ta..

Sai da ta dan jima sannan ta ji an zo bude kofar dakin,ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala dan bata so a zo a riske ta a wurin a fara jero mata ka’idoji dan ta zo da sassafe tada diyar gwal..

Ganin Hamida ce sai ta kuma murtsike idanun ta tana mata kallon mamaki dan bata fiye ganin Hamidar ta farka da sassafe haka ba..

“Lafiya me ya faru Hamee”?tura ta ciki Hamida tayi itama ta karasa ciki tana maida kofar ta rufe sannan ta jawo hannun fifi ta rike cikin nata suka samu wuri a kan gadon fifin suka zauna…

Kallon kurilla Hamida ta mata tana ta nazarin yadda zata kasance a tsakanin su bayan ta gama fada mata abin da ta nufo ta da shi..

Ganin kallon yayi yawa sai fifi ta tambaye ta ko lafiya,sai Hamida ta sauya fuska zuwa kalar damuwa ta saka idanun ta cikin na fifi sannan ta fara magana kamar haka..

“Fifi na matsala ce ta dumfaro ni babba amma ban san ya zan magance wannan matsalar ba, tun jiya toh bayan tafiyar ki sai na kasa samo mafita amma hankali na ya kawo min ke,tuno da karfin gwiwar da kika bani nasanar da ke matsala ta sai kawai na yanke hukuncin tunkarar ki sai dai kash,ko da na duba agogo,sai na ga har daya da mintuna talatin da tara ya buga,sai na fasa zuwa sanin cewa kin dade da yin bacci kuma baccin mai dadi ne dan baccin gajiya ne”!!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button