KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Zagaye farfajiyar gidan suka yi har suka ɓullo ta asalin kofar babban falon suka shige tare ita mama hasiya ta wuce sashen ta ita kuma Hamida ta haura zuwa nata ɗakin dan ko da suka dawo babu wanda suka tarar a parlorn..
Hamida ta kai kusan mintuna talatin tana ta saƙa da warwara akan yadda game ɗin ta zai kasance dan a jiya ta rasa courage ɗin komai amma safiyar yau da tayi magana da fifi sai kawai ta ji kamar an yi tursasa mata wani karfin gwiwa ne tun safen har ya kawo iyanzu bata da shakku a zuciyar ta game da alaƙar da take shirin ƙullawa tsakanin ta da Khalid dan ta san Tarayyar su zata zamo abin alfahari..
Ko da rana yayi bata tsaya jiran ganin saƙon su na ta zo a ci abinci ko a aiko mata da shi ba ta sauko da kan ta ta kuwa same su zazzaune suna jiran dawowar su fifi..
Babu wata damuwa a fuskar ta ta sauko ta tunkare su tana fara’a ta jawo kujerar ta zauna sai duk suka bi ta da kallon mamaki dan yau gabaɗaya kamar an sauya ta daga Hamidar jiya da suka yi welcoming daga filin saukar jirgi ba..
Ganin irin kallon da suke bin ta da shi ya sa ta ɗan yi ƙaramar dariya ta kalli Ammy ta ce
“Ammy barka da rana da fatar kuna lafiya”!kallon ta Ammy tayi ta ce
“Lafiya ƙalau Hamida,ya zagayen naku ya kasance ne hope you enjoyed it”?faɗaɗa fara’ar dake saman fuskar ta tayi ta gyaɗa ma Ammyn kai daga haka ta hau buɗe food warmers ɗin dake jere bisa dinning table ɗin ta ɗauko serving spoon da zumar ɗibawa ta zuba a plate amma wani irin magana da Ammy ta mata mai kama da faɗa faɗa ya sa ta dakata ta dago ta sauke idanun ta a fuskar Ammyn wanda ya saka Ammyn jin ba daɗi dan itakanta ta ji ajikin ta kamar ta zafafa abun da yawa sai ta sauke muryar ta ƙasa tana faɗin
“Kiy hkuri Hamida ba fada nake miki ba,kin gane,wannan abincin da nayi na yi sa ne dan in yi surprising ƴar uwar ki dan jiya cikin hirar mu ta sanar da ni cewa tana marmarin cin abinci irin wannan wai jiya ta ci irin sa a outing ɗin su da yayan ku Khalid sai na ga bai dace a ce mutum na da abu a gida amma yana cin na waje ba shi ya sa na shiga da kaina kitchen ɗin na girka mata,yanzu da haka ita muke jira ta dawo sai mu ci abincin dan na kira Khalid kuma ya faɗa min suna hanyar dawowa shi ya sa na sa aka jere su a nan,amma akwai wani variety ɗin a other food warmer kina iya farawa da shi kafin ki dawo!!..
Kallon da Hamida ta bi Ammy da shi ne ya sa Hajja riƙo hannun Ammy ta ƙarƙashin dinning table tana girgiza mata kai alamar bata kyauta ba duk da ita kan ta ba haka ta so ba,ta so a ce wacce aka yiwa abincin ce ta fara gani amma na yadda zasu yi dan ita kan ta Hamidar tasu ce…
Rasa abin yi Ammy tayi sai ta tashi tsaye ta hau bubbuɗe food warmers ɗin da ta ce na fifi ne ta ɗau wani serving spoon ta fara zubawa Hamida a plate,har yanzu kallon ta Hamida ke yi da tsantsar mamaki da alhini..
Ammy na gama zuzzuba mata ta kalle ta tana faɗin
“Bismillah”!girgiza kai Hamida tayi alamar ba zata ci ba,serving spoon ɗin dake riƙe a hannun ta ta saka cikin food warmer ɗaya dake kusa da ita tayi serving kan ta cikin plate ta saka spoon ta janyo cup ta tsiyaya chilled coco smoothie a ciki ta kwashe ta bar dinning musu area ɗin zuwa sama zuwa ɗakin ta…
“Duk bin ta da ido suka yi suna jin wani iri a zuciyar su duk su biyun,har dai suka rinƙa ba kan su laifin abin da Hamida tayi a yanzu na barin su zuwa ɗakin ta…
Sede har yau gani suke kamar adaidai suke game da lamarin su da fifi
Ko sau daya sun kasa nitsuwa su fahimce cewa sune asalin silar jefa hamida a cikin dukan wani hali datake ciki arayuwanta
Su fifi kuwa zagaye sai inda ba a ƙirƙiro ta ba amma kusan kaf wuraren buɗe ido sai da Khalid ya kai Mufida suka ba idanun su abinci rough driving kuwa fifi sai da ta saka Khalid raina kan sa dan tun da ya miƙa mata maƙullin motar bayan fitowar su daga wata resort ta riƙe sitiyarin motar,toh bata sarara ba haka ta rinƙa tuƙi tana yi tana jijjiga motar,sai tsoro ne kuma ya shigi khalid dan duk rashin jin sa ta fannin tuƙin ganganci bai taɓa kuskurewa yayi irin wannan tuƙin ba sai gashi mace na yin irin sa…
So yayi ya kai ta wani wuri da ba kasafai ya cika zuwa ba sai dai kiran Ammy ya hana sa dan saka shi dawowa da fifi gida tayi akan ta gama yi mata surprise ɗin da ta daɗe tana mata tun bayan fitar su..
Tunda surprise aka ce sai bai faɗa mata ba ya juya akalar motar zuwa hanyar gida sai ta tambaye sa lafiya sai ya nuna mata ba komai kawai wani emergency ne ya same sa kuma ba yadda ya iya..
Tun a hanya yayi ta bata haƙuri akan gobe zasu cigaba ita kam ƴar son jin daɗin rayuwa ta nunar mai ba komai su koma gidan…
Suna hanya suka tsaya ya siyo mata ice cream vanilla flavour suka dawo gidan tare,duk ta matsu su dawo ta sha ice cream ɗin dan tun jiya take sha’awar ice cream ɗin..
Da shigowar su Ammy ta taso ta riƙo hannun ta tana mata sannu da zuwa haɗe da tambayar ta ya fitar tasu ta kasance har da tambayar da fatar dai Khalid bai yi tuƙin ganganci da ita ba cikin mota..
Haɗa ido suka yi ita da Khalid sai ya hau girgiza kai yana faɗin
“Ba zaki so ki san ya drive ɗin nan ya kasance ba Ammy,ga ta nan tambayeta meya faru?
!kallon ta Ammy tayi da mamaki sai kawai taga ta fashe da dariya har da riƙe ciki tana faɗin
“Ammy Khalid matsoraci ne kawai dannna karɓi tuƙi sai ya ruɗe wai ina tuƙi da too much speed kuma fah baki gani ba Ammy ahankli nake tafiya
“ta ƙarasa tana kuma kallon sa sai ya kaɗa kan sa yana faɗin
“Haka kika ce ko?toh ba zan fita da ke ba gobe sai dai mu fita tare da Hamida
“saurin marairaice fuska tayi tana girgiza kan ta haɗe da langaɓar da shi alamar ban haƙuri sai ya saka mata dariya yana faɗin
“Ammy yakamata abata kyautar ta kar ta ƙulle min ciki da abin dariya”!!jin haka sai fifi ta dubi Ammy tana faɗin
“Ammy surprise”?gyaɗa mata kai Ammy tayi tana jawo hannun ta zuwa kan dinning table ta zaunar da ita sannan ta saka ta rufe idanun ta da sharaɗin kar ta buɗe sai ta ƙirga uku..
Da murna fifi ta jijjiga kai cikin zumuɗin son ganin surprise ɗin,haka aka yi bata buɗe idanun ta ba sai da Ammy ta ƙirga ɗaya zuwa uku sannan ta buɗe idanun ta ta sauke sa kan abinci exactly irin wanda ta ci jiya a yawon buɗe idon su…
Bata san lokacin da ta taso ta rungume Ammy ba tana ta yi mata godiya sai kuma tayi saurin sakin ta ta dawo ta zauna ta fara yunƙurin zuba abincin amma Ammy ta hana ta ta karɓe spoon ɗin ta zuba mata da kan ta har zama tayi akan zata ciyar da ita..
Tana buɗe baki sai tunanin Hamida ya bijiro mata ko ya suka yi da aminiyar nan nata bata sani ba kuma tana son jin karshen zancen dan haka ta maida bakin ta ta rufe tayi wuf ta miƙe Hajja da yanzu take leƙo su dan ganin ko Mufidar ta dawo sai ta gan ta tana sauri sauri zata haura sama..
Kiran sunan ta tayi amma bata juyo ba ta cigaba da tafiya tana ce mata
“Hajja ina zuwa Hamida nake son dubowa yanzu zan dawo”!..
Haɗa ido Hajja tayi da Ammy dake riƙe da spoonful of abincin da ta ɗibo da bawa fifi a baki..
Ajiyar zuciya Khalid yayi yana juyawa da nufin tafiya sashen sa dan kimtsawa kafin ya dawo a yi lunch ɗin dashi shima.
Zama Hajja tayi tana kallon Ammy da alamar tambaya sai dai ta furta..
“Anya Hamida ba damuwa gare ta ba kuwa?kin ga yadda jiya ta rinƙa janye jikin ta daga gare mu sannan yau ɗazu ta sake jikin ta amma ɗazu kuma ta rikice kamar ba ita ba?ina ga ki kirawo min Nuhu in ji asalin abin dake damin yarinyar nan dan ina jin tsoro”
..kallon ta Ammy tayi bata ce komai ba ta ɗauko wayar ta da nufin kira sai wani kiran ya shigo..