KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Dubawa tayi sai ta ga ƙanin nata ne wato mahaifin su fifi dan haka ta ɗaga kiran ta miƙowa Hajja..
Hajja na sakawa a kunnen ta ta fara magana kamar ran ta a ɗan ɓace sai dai bata yi faɗa mai yawa ba..
Haƙuri ya bata dan shi dama kira yayi dan ya ji ya lafiyar yaran nashi sabida yayi ta kiran layin Mufida amma bata ɗaga ba sai ya kira na Hamida amma itama bata ɗaga ba shi ya sa kawai ya kira na Ammyn..
“Hajja ai duk jikokin ki ne hala bata jin magana ne kin san Hamida ta bambanta da ƴar uwar ta,
Hajja tace ah a Mufida ce ke da matsala itace wacce ya kamata tayi ta zaman shiru amma sai ƴar uwar ta ce ke yin waɗannan ɗabi’un?
Dady yace haka hamida take amma in kuka saba ba zaki ga shiru shirun ta a matsayin matsala ba dan haka halittar ta yake”ajiyar zuciya Hajja ta sauke dan tayi tunanin wani matsalar ne da Hamida ashe kawai tsabar kama kai ne..
**
Fifi ta daɗe tana ta sallama a ƙofar ɗakin Hamida sai dai babu amsa,deciding shiga ɗakin kawai tayi,tura ƙofar ɗakin tayi sai ta ga Hamida kwance kan gadon ta alamar bacci ya jima da ɗaukar ta,gefe guda a ƙasa plate da spoon ne wanda ta ci abinci da shi,tsugunawa tayi ta kwashe plate da cup ɗin sannan ta kalli Hamidar tana murmushi a same time ta ce
“Please Hamee ki yi ki farka i have a lot to tell you,yau…is one of my best days a rayuwa ta kuma na san Allah na jin addu’a ta and zai amsa min because is a positive wish”kallon Hamidar tayi na dan wani lokaci sannan ta juya ta fice…
Haka ta sauko ƙasan ta same su duk suna zaune har da Khalid,nan take ta ji damuwar ta akan ƴar uwar ta Hamida ya ragu dan ta ga fitilar dake haske mata duhun ta wato Khalid ɗin ta..
Zama tayi da annashuwa a fuskar ta ta fara ba ammy haƙurin tashi da tayi ta bar ta da spoon a hannu ɗazu,ƴar lele ce bata laifi bare ɗazu daddyn su fifi ya tuno masu da matsalar fifin sai duk suka ji jikin su yayi sanyi amma ganin ta ta fito cikin fara’a sai suka ga kar su saka ta cikin zargin wani abin..
A walwala aka ci abincin Khalid na ta labarta masu yadda fifi tayi da shi cikin mota ɗazu,duk sai su rinƙa goyon bayan ta suna mai dariya,da haka dai aka yi lunch lafiya aka kammala Hajja ta ja hannun fifi zuwa sashen ta wai tana so su yi hira ta jika da kaka,wannam hikimar duk dan kar su bar fifin cikin kaɗaici da damuwa ne ya sa Hajja bijiro da wannan tsarin dan kam ta…
Mamuh_Mamuhgee_
10
Da isar su ɗakin Hajja Fifi ta hau koɗa ɗakin game da zuzuta kyaun d ɗakin yayi dan har wani qamshi yake fitarwa kamar ba na tsohuwa ba komai tsaf tsaf da shi..
Jawo hannun ta Hajja tayi ta zaunar da ita bisa kan silver colour royal bed ɗin ta da ya sha kayan ado na zamani kama daga kab throw pillows da aka zagaye gadon da shi kamar dai yadda ake gyara gado irin ta mutanin da sai dai wannan a zamanance aka gyare sa zanin gadon kan sa abin kallo ne.
Hajja ta gyra zama ta na ta famab murmushi dan ganin halin farin cikin da fifi ke ciki sai ta bar ta tayi ta kalle kallen ta tana yabe yaben ta har ta gama dan kan ta ta dawo ta zauna tana cigaba da yaba ɗakin Hajjan har ta so ba Hajjan dariya..
Riƙo hannuwar ta Hajja tayi tana kallon fuskar ta dake da ragowar murmushin da ya bayyana two sided dimples ɗin ta,hakan ya tuno ma hajja da mahaifiyar su fifin sai tausayin fifin taji ya kama ta sosai duba da irin rayuwar da yarinyar ta taso babu kula ta musamman daga uwa sakamakon bata raye sannan ga jarabtar da ubangiji ya mata na rashin cikakken lafiya,duk waɗannan dalilai ya sake jefa tausayin ta a zuciyar Hajja..
Nan da nan hawaye suka cicciko daga idanun ta amma bata bari fifi ta gama fahimtar dalilin cikowar hawayen ba bare ta tambaye ta,sabida ta gama sawa a abu mafi sauƙi a gare ta shine ta aiwatar da abin dake ran ta ayanzu game da rayuwar fifin dan a ganin ta hakan ne kawai zai fiye mata kwanciyar hankali..
“Hajja ɗakin ki kamar na amarya sabuwa fil,ji kamar ɗaki na ne”!!
kallon mamaki Hajja ta mata sannan ta ce da ita
“Da gaske ɗakin ya maki kina so a ce kina da irin shi ko fiye da shi ko!?da sauri fifi ta gyaɗa mata kai tana dariya..
Hamdala Hajja tayi jin da bakin ta ta ma furta sha’awar ta ga son samin ɗakin kan ta ba tare da ta cigaba da zama a ƙarƙashin su ba amma a ƙarƙashin mijin ta…
“Dama na jima ina son yin wannan magana takwara ta sai dai rashin wanda zan tunkara da maganar ya sa na barwa kai na amma sosai na damu da samun cigaban rayuwar ki a mataki mai inganci da ba zamu sami ɗar ko fargaba ba, amma tunda yanzu kin yi maganar da kan ki ina so ki faɗa min ra’ayin ki kar in maki shigar bazata,kina da wanda ya kwanta maki a rai ne da kike jin ba zai maki riƙon ƙasƙanci da son zuciya ba in an aura maki shi?
Fifi tace haajja aure?laahhh,abin dariya abin mamaki wai fifi da jin kunya sai ta faɗa jikin Hajjan tana ta ɓoye fuskar ta dan ba zata taɓa mantawa ba akwai ranar da suka zauna lokacin a germany suna lissafa irin mazajen da suke son aura ita da Hamida,sai bayan sun gama hirar har Hamidar ta wuce sai ta zauna da zuciyar ta akan in har Allah ya bata aron rai tayi aure ta sami ƙaruwa toh in mace ce sunan Hamida zata saka mata in kuma namiji ne sunan daddyn su zata saka mai har ta samo other name da za a rinƙa kiran baby girl ɗin da shi haka ta samo wanda za a na kiran mai sunan daddyn da shi…
Dariyar manya Hajja tayi dan ta ga amsar tambayar ta ƙarara a fuskar fifi tunma kafin ta amsa,sai ta rungume ta tana taɓa bayan ta game da ce mata
“Amma ni kam takwara ta wanene wannan saurayin ne da yake mana shigar bayan gida ba tare da mun sani ba,fata na dai ba baturen ƙasar can kika samo mana ko?dariyar itama fifin tayi tana cewa Hajjan toh in baturen can ɗin ne ma ba zata so shi ba..
Sai da fifi ta gama juye juyen ta sannan ta rufe idanun ta da tafin hannun ta tana faɗin
“Hajja ai kin san shi dama kike wani kwane kwane “…tana gama faɗin haka ta tashi ta fita daga ɗakin a guje wannan tabbaci ne na alkunya dake jinin matan arewa koda ba anan ta taso ba…
Ganin yadda ta fita da gudu sai Hajja ta fashe da dariya tana girgiza kai dan ko ba a faɗa mata ba ta san hasashen ta ne ya zamo gadkiya kuma da yardar mai duka zata ga tayi iya ƙoƙarin ta dan cika wannan hasashe nata..
Mezai fiye mata dadi ace an Hade mufiida da khalid,ita kuma hamida in Allah ya so ba sai akara ma yayan shi saheeb ba?
Da gudu fifi ta nufi hanyar balcony dan shigewa ɗakin ta dan bata san tana da kunya mai tsanani ba sai yau da Hajja wacce take a matsayin kakace ma a gare ta toh ina ga Ammy ce ta mata wannan maganar,lallai da ta daɗe bata bari Ammyn ta ƙara saka ta a ido ba..
Tana cikin wannan yanayin ta ji kamar ta bangaje mutum sai tayi saurin buɗe idanun ta ai kuwa tayi tozali da Hamida,take ta kuma jin wani kunyar sai ta matsa ta cigaba da tafiyarta..
Hamida da dama ita ta fito nema sai ta tsaya a tsaye tana mamakin dalilin farincikin fifi amma sai ta basar ta ɗage kafaɗun ta ta ƙarasa saukowa ƙasar ta ɗau abin da zata ɗauka ta juya ta hauro saman…
Zata wuce kenan ta ga fitowar Hajja cikin fara’a da ragowar dariyar mamakin fifi,ko bata tambaya ba ta san labarin gizo bai wuce koƙi,fifi ta fito ɗazu da fara’a a fuskar ta tana rufe fuska yanzu kuma Hajja ta fito da nata fara’ar..