KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Ɗage kafaɗa tayi alamar ba matsalar ta bane,gaida Hajjan kawai tayi irin gaisuwar barka da war haka,bata tsaya jiran amsa ba tayi gaba…
Muryar Hajja ta jiyo tana kiran sunan ta sai ta dakata haɗe da juyowa cikin mamaki ta kalle ta..
Da kan ta Hajjan ta ƙaraso ga Hamida ta riƙo hannun ta na hagu da babu komai ciki tana kallon ta daga bisani ta tambaye ta
“Wai nikam Kin ga min Mufida kuwa? ina ta jiran dawowar ta amma da gaske tafiyar tayi dan kunya ta wai ta ji”
ajiyar zucitayar Hamida tayi a zuciyar ta kuwa sai cewa tayi “Hajja da abin ban dariya take toh ni ina ruwa na da wata kunyar ta da fifi ta ji har take tambaya ta ko na gane mata ita,ai wannan tsakanin su ne,yanzu dama dalilin da ya sa ta dakatar da ni kenan ashe?ohhhh,,fifi,fifi,fifi ko nauyin ta basu ji kan su tsaye suke nuna mata wariyar soyayya,ko da yake ai komai ya kusa zuwa ƙarshe illar in na kasa cigaba da haƙurin ne amma da zarar na daure toh zan mori haƙurin da na daɗe ina yi”..
Jin tsyi shiru sai Hajja tayi saurib bijiro da tunan kafin ta dubi Hamida ta ce da ita cikin raha
“Hamida dama maganan aure ne?ko dai ke ma haɗa ku zamu yi ne dan na ga kin fiye son rayuwar kaɗaici nidai wannan salalan ba ajina ba?
Hamida taja tace haajja aure kuma?
Hajja tace eh
Daa wai nace mubawa mufida khalid ke kuma tun da ba wani shkuwa kukayi ba ai sai ahada ku da yayanku ko?kuma wannan haɗin shine zai yi daidai da tsarin rayuwar ki..
Wani kallon durus tayi ma hajja kanta na wani irin juyi,idan da za a ba Hamida dama da tace babu wanda yakai hajja iya nuna fifiko da sonkai dan babu cigaba a cikin lafuzan ta hala nata tsufar a haka ya zo mata da hauka,tana tambayar ta tun ma bata amsa ba ta kuma jefo wata tambayar da bata san ma’anar sa ba ikon Allah…Hajja..?wai waye na saheeb din nan tsoho shekaru aruru?Allah tir..Allah ya sawwaka itace za’ace ta auri wanda yazo duniya tunma kafin a aure mahaifiyar su?
Dariyar bazata Hamida tayi tana girgiza kai tana mai raba hannun ta daga na Hajja haɗe da furta
“Hajja kenan,zokije fifi na ɗakin ta ɗazu ta wuce ni zuwa ɗakin ta,sannan maganar ki ta biyu Hajja ni ban gane mata ba zai fi kyau in na raka ki ɗakin ki kika huta dan da alama kin gaji da yawa bayan tsawon lokacin da kika ɗauka baki ci abinci ba kina jiran dawowar….,fifi ko?”a kalmar Hamida ta ƙarshe sai da ta ja misali kafin ta ƙarasa sakamakon wani baƙin cikin da ya mamaye mata zuciyar ta tuno da cewa saura ƙiris ta yarda ɗan kada yayi girma a gaban ta ba dan tayi saurin yiwa tufkar hanci ba…
Ko jiran jin ta cewar Hajja Hamida bata yi ba ta janyo hannun ta ta kai ta ɗakin ta tana mai dangana ta da gadon ta haɗe da ƙare ma ɗakin kallo dan sai yanzu take shiga,duk da ba mai yawan magana ce ba ita,ta tsinci kan ta da complimenting ɗakin Hajjan..
A nan kuma Hajja ta kasa haƙura ta so ta kuma tado da maganar da ke ran ta amma Hamida bata bata damar yin maganar ba sai ta juya tayi ficewar ta..
Tuntuni Tana ɗakin ta tana shan banana smoothie tana tunano zantukar Hajja na ɗazu abin na mugun bata dariya dan ta fi danganta rashin natsuwar zuciyar Hajja da yanayin tsufa inba haka ba ina ita ina auren wani wai saheeb?
Nan take kuma tunanin zagayen su na ɗazu ya bijiro mata a lokacin da suka kai sashen sa,wani dariya ne ya taso mata nan ta tuno da yadda mama hasiya ke mata tayin shiga sashen tana ko, dariyar ce ta taso mata a fili ta furta
“Wai in shiga in gani?kaji munafurci suce kawai dama ni an zabamin shine ita kuma an zaba mata kyakkawa,toh me nake da buƙatar gani a sashen tsoho sama da karikitai?gaskiya mama hasiya da abin ban dariya take sosai, ni dai na san wannan babban ɗan Ammyn in har yanzu bai yi aure bama toh lallai akwai matsala dan bana jin akwai macen da zata wani aure sa wa ke son tsoho,lallai..sanda ya gama zamawo asalin tsohon za’a kuma bada hamida?..”dariyar hasashen kamannin sa tayi haka ta rinƙa ƙyaƙyatawa har ta ji dariyar ta ishe ta sai ta miƙe tana faɗin
“Ya zama dole in sanar da fifi wannan abin dariyar na san ta sarai ko son binciken ta kaɗai zai saka ta shiga sashen in ya so bayan ta dawo sai ta faɗa min ya sashen yake..
Ko tsayawa batayi ba ta fita ta nufi ɗakin fifi,babu doguwar sallama ta shigo kawai..
Fifi dake duƙunƙune cikin bargo ta ɗago kai dan ganin wa ya shigo mata,sai ta ga Hamida ce nan take ta kuma rufe fuskar ta..
By now attitude ɗin fifin shikansa na son shiga sahun abubuwan ban dariyar da Hamida take cin karo da su a yau..
“Tace hjiya fifi taso ki faɗa min menene ke faruwa na ga kamar ke da Hajja wasan ɓuya kuke yi”!!da sauri fifi ta taso ta zauna yayin da Hamida ke gyara zamanta bisa kan gadon..
Saurin tambayar Hamida tayi halan me Hajja ta ce mata,ita kam Hamida da dariya a fuskar ta ta hau yi mata bayanin yadda suka yi da Hajja ita kan ta fifi sai da tayi dariyar Hajjan amma ta ba maganar Hajjan ma’ana akan ko dai Hamida itama yi mata za a yi irin nata.. ?
“Faɗa min ƴar uwa ta,ina jin ki shin me Hajja ta faɗa maki ne da kike ta jin kunyar ta?Hamida tayi tambayar tana mugun danne dariyar takaicin ta..
Sai da fifi ta ɗau lokaci sannan ta riƙo hannun Hamida ta hau bayyana mata komai da ya faru ɗazu tsakanin ta da Hajja ta kuma ɗora da bayyana mata ko wanene wannan mai sa’ar da ta kasa bayyanawa Hajja shi ta gudo,still da yadda zancen ɗin da suka yi a tsarin su na cewa ita za’abawa khaleed ita kuma saheeb
Dan Fizge hannu Hamida tayi daga riƙon da fifi ta mata ta tashi tsaye dan take take ganin kamar duhu ya fara ziyartar idanun ta,bugun zuciyar ta ya ɗan dakata sannan ya cigaba a bugu fiye da ƙima,take ta ji kamar zata faɗi,ba shiri ta juya ma fifi baya tana tare hawayen dake shirin zubo mata da hannun ta,ɗaya hannun ta na bakin ta tana kare bakin ta daga sakin kukar da ke shirin fin ƙarfin ta..
Cikin dauriya Tace”Na taya ki murna fa Allah ya tabbatar da alkhairi”
iya abin da Hamida ta iya faɗi kenan daga haka ta tura ƙofar ɗakin Mufida ta fita da sauri tana haɗa hanya burin ta ta tsinci kan ta a ɗakin ta..
Har ta wuce sai ta dawo da baya jin wani irin baƙin tattaunawa dake tashi daga ɗakin Hajja tsakanin ta da Ammy..
Natsuwa tayi ta kasa kunnen ta tana sauraron su ba tare da sun san tana wurin ba,har suka gama zantukar su mai ɗauke da nazarorin su da fasahohin su suka yi jawo bakin zaren aka tsaya a matsaya ɗaya…
Juyawa tayi ta ga gidan na mata juyin fanka,kan ta ta dafe da hannuwar ta biyu ta hau dube dube a balcony ɗin ko zata hango ruwa dan ta sha ko zata sami damar kashe wutar da ya banku a ciki cikin zuciyar,amma bata gani ba kuma babu alamar zata samu…
Kusan da dafe dafen bango ta ƙarasa ɗakin ta,tana shiga ta saka lock ta zame a ƙasa tana ta juye juye tana fifita da hannuwar ta biyu sai shakar numfashi take kamar mai matsalar asthma ganin hakan bai gamsar da ita ba sai ta hau zubda hawaye tana numfashi cikin sauri sauri,tari ne ya sarƙe mata nan take ta hau yin sa babu ƙaƙƙautawa idanun ta sun canza launi daga farare zuwa jajazir.
Kwanciya tayi a ƙasa ta hau birgima dan har yanzu bata ji numfashin ta ya mata yadda take so ba..
Kimanin mintuna ashirin Hamida bata samu daidaituwar numfashin ta da ƙyar dai ta sami ikon sakin wani kuka