KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

tun da ta ji kamar zuciyar ta ya ɗan sassauta sai ta cigaba da kukan,yi take yi tana tuno lokutan datayi sadaukarwa da yawa a rayuwar su ita da fifi har kawo yanzu…

Ƙirjin ta ne ta ji yana mata nauyi da zafi nan ma ta rasa ina zata saka kan ta ta sami sassauci,danne ƙirjin tayi da hannayen ta biyu tana jan numfashi hawaye na fitowa wani na korar wani…

A nan ɗakin Mufida kuwa ba ƙaramin kaɗuwa tayi da mamkin hamida ba,taga ta shigo tana yar fara’a batayi tsammanin zata ga shauƙi da zumuɗin ya yanke bayan ta bayyanawa Hamida sirrin dake zuciyar ta amma sai ta sha mamaki ta ga akasin haka.. Seta ke gani kamar mufida bata ji dadin zabin ba?

Dama wazai so tsoho?wani damuwar tuno da cewa ko itace na bayarda zatayi ba to amma me zatayi?wannan ai duk shirin su ammy da hajja ne.

Miƙewa tayi ta tsaya a tsaye tana kallon inda Hamidar ta tsaya daxun a yayin da ta juya mata baya tana mata wani irin amsar da bai yi kama da kalaman da kawai ya dace su fito daga bakin ta ba..

Mamaki kan mamaki ne ya saka fifi a gaba,duk iya inda hankalin ta da tunanin ta zai kai akan wannan abin da ya faru yanzu yanzun nan tayi ƙokarin kai hankalin ta nan amma bata sami abin da take so ba..

Juyawa tayi ta ɗauko gyalen ta ta yafa a kan ta ta saka takalmin ta ta fito da sauri dan zuwa jin matsalar Hamida gani take wannan reaction ɗin nata bai yi kama da abunda da mutum zai gani ya kawar da kai ya ƙyale ba dole ne dai akwai matsala dan Hamida ba haka take ba…

Cikin saurin ta ta fito tana tafiya sai ta ji a jawo ta ko da ta duba sai ta ga Ammy ce,cikin inda inda ta fara yunƙurin yin magana amma Ammy ta riga ta da fara’ar ta tana gyaɗa mata kai..

“Na sani,na sani,Hajja ta faɗa min komai,kuma na kasa haƙuri har sai kin bayyana mana da bakinki wanene wannan ɗin dan ni duk hankali na ga mutum ɗaya ya koma and i know it’s that person,yanzu kin ga ba batun kunyar Hajja ko ni zaki ji ba,ki zo mu tafi sashe na dan ki bayyana min abin dake zuciyar ki a matsayi na na uwa a gare ki ai na cancanci jin ra’ayin ki,so come let’s go my dear”Ammy na gama faɗin haka ta riƙo fifi da karfib tsiya suka hau tafiya ita kuma ba zancen kunyar ce ke damin ta ba a yanzu abin da ya fi damin ta shine ta san wani hali yar uwarta Hamida ke ciki..

Ɗan ja da baya Mufida tayi tana rau da ido cikin rashin jin dadi tace ma Ammy akan itafah ga inda ta fito da niyar zuwa amma amsar da Ammy ta bata shine
“Kibar wannan Hamida zata zo anjima itama aiko?itama akwai maganar da muka yi akan ta duk zan mata bayani amma bayanzu ba.let’s concentrate on yours..”daga haka ta kuma riƙo hannun fifi suka cigaba da tafiya..

Duk da zuciyar ta na faɗa mata a’a ta fara zuwa ta ji damuwar ƴar uwar ta amma maganar Ammy na daɗa buga mata ƙararrawa akan ai ta ce zasu yi wata magana akan Hamidar tare,sai kawai tayi shiru ta cigaba da bin Ammy har suka isa ɗakin ta…

Mamuh_Mamuhgee_

11

Zaunar da Fifi Ammy tayi tana kallon fuskar ta nadan wani lokaci sannan ta fara magana cikin kwantar da murya dan ta sami cikakkiyar hankalin fifin..

Ita kam fifi na ta bin Ammyn da kallon mamaki dan a zuciyar ta tambayoyi ne kala kala sai dai Ammyn bata bar ta ta sami ikon yin sa..

“Mufida kina ji na?,ɗazu Hajja ta kirawo ni ta sanar da ni matakin da ta ɗauka akan ki na haɗa auren ku sai dai ko kafin ta furta maki wanda ta zaɓar maki ke har kin nuna ta hanyar yin na’am da shawarar ta a ƙarshe har kika fita cikin kunya hakan ya tabnatar mata da cewa kina son abin da take maki sha’awar samu,toh ni yanzu ina so in kuma tabbatarwa ne,da gaske kin yarda da alakar dake tsakanin ku da yayan ku Khalid ya shiga wata matakin rayuwa wato matakin aure”?
karasa maganar tayi tana janyo hannayen fifi dan samin hankalin ta da yaddan ta dan basa so su yi mata ba dai dai ba..

Yin ƙasa da kai Mufida tayi cikin jin nauyin Ammy da tambayar da ta aiko mata..

  “Mufida amsa min bana son kina jin nauyi na ko kin manta ni ɗin Ammyn ki ce”?girgiza kai fifi tayi tana mai buɗe bakin ta cikin jin nauyin Ammyn ta ce
  “Ammy ai shi bai ce komai ba”!!shiru Ammy tayi tana sauraron ta a zaton ta akwai cigaban maganar amma ta ji shiru sai ta ɗago ta kalli Mufidar cikin jin daɗi dan ta san in har ita tayi na’am da zancen toh shima Khalid ɗin ya zama dole ya amince dan bai da matsala dama sun jima da jiran ganin ya kawo masu mace da sunan matar da zai aura anma babu labari shi yasa da Hajja ta tunkare ta da maganar kawai ta ji hankalin ta itama ya kwanta da shi dan ta matsu ta ga jikokin ta ko zata mori albarkar ƴaƴa itama tunda auren na danta na farin bai yi working out ba toh yanzu addu’ar ta bai wuce ta sami jikokin daga tsatson Mufida ba…

Hajja Tace…”In dai Khalid ne wannan ba abin da zaki ɗaga hankalin ki bane saboda ya jima da bari mana zaɓin matar sa a hannun mu,yanzu dai menene kike son sani game da shi da baki sani ba wanda bai faɗa maki ba”!?

murmushi fifi tayi tana daɗa sunkuyar da kan ta ƙasa kafin ta amsa kamar da Ammy takeyi..
“Ammy kaɗan na sani daga rayuwar sa kin ga kamar ban san komai bane so kusan komai akan sa nake son sani”cikin jin nauyin su duka ta ƙarasa maganar nata.

Ajiyar zuciya Ammy tayi sannan ta kuma faɗaɗa murmushin ta tana gyara zaman ta..
“Kamar dai yadda kika ji ana kiran sa da Khalid,toh asalin sunan nasa kenan Khalid,kwata kwata shekarun sa bazasu wuce 27 years ba bai ma gama kaiwa ba sannan shi ne ɗa na biyu a cikin gidan nan babban yayan sa shine Saheeb wanda ba a nan yake ba,Khalid yayi karatun su both primary and secondary schools ɗin sa a nan ƙasar ne so bayan ya kammala ya nuna interest ɗin sa a fanin karatun gynaecology wato ya zaɓi ya zurfafa karatun sa a fannin sanin matsalolin mata.

duk da ban raine su tare da Abban su ba sakamakon barin mu da yayi a daidai lokacin da muke buƙatar sa dan kuwa Allahn da ya bamu shi ya karɓe sa,hakan bai sa nayi ƙasa a gwiwa ba kakar ku Hajja ita ta ƙara ƙarfafa karatun Khalid ɗin sai ya zaɓi ƙasar Cyprus a inda yake son zuwa yin karatun,bamu hana sa ba iya fatar alkhairi da muka mai,wani abu shine Khalid ya kammala karatun sa ne a dan kankanin lokaci dan ya karasa yana da shekaru ashirin da biyar abin da ba kasafai ya fiye faruwa ba,so ya dawo kuma alhamdulillah ya sami aikin sa yana aiki a nan cikin gari sai dai ba ko da yaushe yake zuwa ba sai har in shine on call kuma a halin yanzu yana kan cigaba da karatun sa dan zama cikakken consultant so zuwan ku ne ya sa yake zaune a gida kuma ya haɗu da hutun sa da ya shigo..

Kuma he really wants you to feel at home that was why ya zaɓi kai ki wurare daban daban tun dawowar ki kuma daga dukkan alamu shima ya gamsu da ke dan naga kamar jinin ku ya zo ɗaya daga yanayin da yake sake maki”..ɗan dakatawa Ammy tayi tana sauraron jin ta bakin fifi..

Fifi sai ji tayi kamar an kara rura mata wutar ƙaunar Khalid a zuciyar ta ina ma a ce karantar fannin zuciya yayi da sai ya magance mata damuwar ta amma duk da hakan bata ji ƙaunar sa da ya mata shigar farat ɗaya ya ragu ba..

Can Tace “Ammy, baki sanar da ni komai akan social life ɗin sa ba irin meyafi so,abokan sa da dai wasu abubuwa da suka shafi personal life ɗin sa”..
murmushi Ammy tayi tana shafo fuskar fifi sannan ta cigaba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button