KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

“Well,Khalid…,ina ga ba sai na tsaya faɗa maki tsarin rayuwar sa ba dan ke kan ki shaida ce akan hakan kin gani kuma kina iya faɗawa wasu,sannan akan abokan sa…,Khalid na da abokai but mostly sai lokaci zuwa lokaci suke haɗuwa kinsan yanayin aikin nasu kowa na concentrating ne akan aikin sa,game da abincin da Khalid ya fi so kuwa,ina iya faɗa maki Khalid is a simple person komai yana ci muddin abin nan na ci ne,ba kamar yayan sa Saheeb da ba komai yake ci ba”…

Kallon Ammy fifi tayi tana gyaɗa kai alamar ta gamsu da duk bayanan Ammy tace Hamida fa,itama ai tare zaayi mana auren ko?sai tayi shiru aranta tana tunanin
“ya ita kuma zata kasance in aka ce ita zata yi aure ba tare da Hamida ba?bata taɓa mafarkin hakan ba ta fi planning ranar auren su ya zo daidai komai su yi tare amma ba a rabe ba..

Yin wannan tunani sai ta ɗago ta kalli Ammy directly ta jefo mata tambayar dake zuciyar ta…

“Ammy ya labarin na Hamida”?shiru Ammy tayi tana ɗan kasaƙe for a while sannan ta amsa tambayar..
“Dear ban manta da Hamida ba ai dama na faɗa maki za mu yi maganar nata bayan naki so yanzu bari in fayyace maki nata dan surprise ɗin da Hajja ta mata ne

“..nan take fifi ta zaƙu a faɗa mata dan sanin ko wa ita kuma aka zaɓar mata dan dan tasan bazata taba yin aure ba tare da ƴar uwar ta ba..

“Kin ga kasancewar Hamida mai ɗauke kai ne ga duk wani al’amurar rayuwa,ba ni kaɗai na hango hakan ba har kakar ku Hajja ta hango hakan,tana da shiru shiru bata cika magana ba babu ruwan ta,so haɗa ku da za a yi da yayan ku Khalid sai Hajja ta ga me zai hana itama a mata hakan dan ɗabi’un ta ya zo sak irin na wanda take hasashen haɗa sun,sedai shi ba anan yake ba

kuma….”!!!sai tayi shiru sai fifi ta girgiza mata hannu cikin zaƙuwa tana son Ammy ta ƙarasa mata bayanin…

Kawar da kai Ammy tayi tana takaicin furucin da zata furtawa fifi dan bata san yadda zata ɗau maganar ba amma dai dole ta sanar da ita dan ba zai yiwu ta ɓoye wani sirri ba alhalin haɗin da suke son yi haɗi ne na har abada..

“Mufida wanda muke son haɗa sa aure da ƴar uwar ki Hamida yana da mata,kuma sun share shekaru da yawa suna tare sai dai…”!!nan ma Ammy tayi shiru sai fifi ta ƙyale ta bata ce mata komai ba…
Sai da suka ɗau lokaci a hakan sannan fifi ta sake tambayar su haɗe menene matsalar da ajiyar zuciya Ammy ta furta bakomai sunan sa..
“Muhammad Saheeb,yayan Khalid ne, shine mutumin da muke son haɗa Hamida aure da”!!fata na hadin y zame mana alheri

wuf Mufida ta miƙe tsaye tana kallon Ammy baki buɗe…

Ammy duk ta gama azawa ki wani abu ne

Dariya ne ya cunkushe a zuciyar fifi sai dai bata son yin sa a gaban Ammy kar Ammy ta ji wani iri,haka ta rinƙa tarar dariyar dan kar ya fito,a ƙarshe dai ɗagawa Ammy hannu tayi alamar zata je ta dawo…

Bin ta da kallo Ammy tayi tana mamakin reaction ɗin fifi dan ta ɗauka zata ga tayi negative reaction ne sai ta ga akasin haka…

Mufida na fita daga ɗakin Ammy bata tsaya ko ina ba sai ɗakin Hamida wacce ke kwance ƙasa tana baccin wahala..

Da zuwar ta bata tsaya tunanin bacci ƴar uwar nata ke yi ba kawai ta hau tapping nata a baya tana kiran sunan ta..
“Hamee…,Hamee na ki tashi…common wake up i have a gist for u,dan Allah ki tashi”.jijjiga ta fifi ta rinƙa yi tana assasa mata akan lallai lallai sai ta farka daga baccin dan kawai ta labarta mata abin da Ammy ta sanar da ita..

Daga cikin baccin da bai jima da ɗaukar ta ba Hamida ta ji muryar fifi sai ta buɗe idanun ta a hankali ta zuba su a kan fuskar fifi dake ta dariya kamar wacce ta ga abin dariyar..

Fifi na ganin ta farka sai ta riƙo hannun ta tana mai cigaba da yin dariya tana magana..

“Hamee wai kin san wani babban albishir da su Ammy zasu maki kuwa?tayi maganar tana kuma ƙara ƙarfin dariyar ta…

Bin ta da kallo Hamida tayi dan in dai wannan ne special package ɗin,toh ta san da zaman shi…

Tace “Hamee me?na yi tunanin zaki matsu dan son sanin wannan zancen?girgiza mata kai Hamida tayi tana kawar da fuskar ta gefe..

Kai tsaye fifi ta hau bata labarin komai sannan ta ɗora da sunan wanda za a haɗa su auren..

“Hamee wallahi na fi dacen miji kin san fah wai har mata gare sa kuma ta ƙi yarda ta haihu over years,though Ammy bata sanar da ni gabaɗaya labarin sa ba amma daga wannan ɗin ma na gane cewa Ammy ta matsu ta sami grandchildren you see in aka haɗa ni da yaya…..Khalid ke kuma aka haɗa ki da….”!!!wani dariyar ne ya tasowa fifi ta rinƙa yin sa har Hamida ta ji kamar ta ɗauke ta da marin da ubangijin ta kaɗai ya san halin da zuciyar ta ke ciki game da wannan lamarin,ba fah ita aka roƙa aka nemi yardar ta da izinin ta ba kai tsaye aka nuna mata iko,amma ita fifi da yake ƴar so ce ƴar gida ce bayan Hajja ta yanke hukunci har sake tuntuɓar ta Ammy tayi dan jin ra’ayin ta wai kar a mata dole..

these people are unbelievable ta furta aranta .ta ja tsaki,ba ma su suke sanar da ita ba? Mufida ce yar aikan su akan maganar dan kawai bata da daraja da ƙima…

Duk wannan dariyar d fifi take bai dame ta ba dan dana ta ji shirun sua ɗazu,so wannan ba abu ne da zai ɗaga mata hankali ba duba da irin rayuwar da ta taso a ciki na kaɗaici da rashin samun kulawar kowa a kan ta..

Murmushi mai ciwo Hamida ta yi tana kallon Mufida dake ta ƙunshe dariyar ta,sai ta girgiza kai kawai dan wani lokaci in ta gwada nauyin ƙiyayyar da take yiwa Mufidar sai ta ga ya rinjayi ƙaunar da take mata hakan ya sa take ta ƙoƙarin ganin shaiɗan bai kai ta ƙarshe ba ta yadda in ta tashi barakar ta abin ba zai yi muni ba

sai dai daga dukkan alamu yazama dole ne tayi introducing Mufida zuwa ga other side na halayen ta dan ta san ba komai mutum ke yi ya tafi haka nan kawai ba…

Tae wai za a aura min
“Yaya Muhammad Saheeb ko”?sai fifi ta gwalalo idanun ta waje tana tunanin a ina Hamida ta san wannan labarin..

“Kina mamaki ne dan na san da shi ɗin dama za a haɗa ni, kuma kin san me fifi?hakan bai dame ni ba a hakan ma,ina son shi”!!

baki buɗe fifi ta rinƙa kallon Hamida jin cewa wai tana son shi a hakan ita da baya cikin jerin tsarin mazajen da take burin aura sai kuma yanzu wai har ita ce mai cewa ya mata a hakan..
Lallai Hamida ta sauya amma meyasa Kika ce kina son shi a hakan Hameeda”?

Gyaɗa mata kai Hamida tayi tana kallon ƙwayar idanun ta dan duk inda jarumta yake Hamida ta nemo sa ta ara ta yafawa kan ta bata so fifi ta ga gazawar ta har tayi taking advantage ɗin gazawar nata ayau dan ji take kamar hakrin ta ya riga ya kare..

Tashi fifi tayi tana yar dariyar rashin fahimta tana girgizawa Hamida kai cikin tsokana tana faɗin.

“Ni Mufida,yanzu Hamida duk irin burin nan da kika ɗaura akan samin namiji ƙerarre mai muscle duk sun tafi abanza kenan?tsohon nan mai mata zaki aura kuma wai kina son sa a hakan?unbelievable”!!

sai dariya dama on normal basis ya aka iya da dariyar tsokanar fifi bare yanzu da ta sami dalili…

Tsanar ta ne kawai ke ruruwa a zuciyar Hamida,ji take kamar ta kawo ƙarshen wannan masifar yau yau ta hanyar shakure ta,Mufida kowa Mufida kowa Mufida,daurewa tayi ta danne ɓacin ran ta ta cigaba da ɗora murmushin yake har Mufida ta gama tsokanar ta da zata yi ta ɗora da yabon nata husband to be ɗin wato Khalid…

Ƙala Hamida bata ce da fifi ba har ta gama ta dawo ta rungume ta tana masu fatar alkhairi su duka sannan ta tafi dan ta matsu ta san ko ta sami ƙarbuwa a zuciyar Khalid ɗin..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button