KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Ameed na matuqar son Fifi itakuma amatsayin aboki Kuma Dan uwa ta daukesa sbd Dr Fatima data zamar musu tamkar uwa Dan kuwa ita kanta irin gata da qauna da Dr Fatima ke nuna mata yasa ma take kallonta tamkar mahaifiyarta haka take zuba mata shagwaba musamman idan ciwon na Fifi din yataso to tabbas kowa hankalinsa tashi yakeyi har mutanen Nigeria haka Dr Fatima zata tsaya tsayin daka a asibiti tamkar uwarta.

Meena ma Batada qawar datafi mata Fifi shiyasa kusan koyaushe suna tare musamman gurin yawon guraren shaqatawa sbd hameeda Bata shiga cikinsu.

Fifi a duniya bayan mahaifinta Babu Wanda takeso arayuwarta sama da ‘yar uwarta hameeda wadda takewa kallon uwa Kuma ‘yar uwa,

Qaunar datakewa hameeda qaunace irin wadda Allah ne kawai ya isa ya cire mata ita cikin ranta musamman sbd sanin ba lallai tayi doguwar rayuwa sbd ciwonta,

Tana Jim dadin rayuwarta da shaqatawartane sbd tunanin tabbas ita bamai jimawa bace a duniyar shiyasa Batada abokin fada Bata saka komai na damuwa aranta kowa natane sbd wata Rana Babu ita.

Ita mutumce mai tsananin son life musamman idan ta zauna takance idan har Allah yasa zata jima a duniya hartayi aure to Sam Babu abinda zai hanata auren miji irin ameed sbd itadai duk namijinda bai wayewaba ya iya rayuwar turawa Yana geaming ya handa muscles da abs to tabbas bazata iya aurensaba ita dai mijinta dole zai kasance kamarta Kuma wanda baifi yabata shekara uku zuwa huduba idan yabata shekaru to kardai su wuce biyar sbd me qarancin shekaru kamarta shine zai fahimci rayuwar Jin dadi yabarta suyi rayuwa yanda suke so kafin ta mutu tabarsa.

Ahankali ta bude idanuwanta dasuka Sha bacci ta miqe da sauri tareda cewa”

Oh shitt nayi latti sosai inada practical 10:00 and it’s 9:40 yanxu.

Da sauri ta sauko daga kan gadon tana mayarda hular baccinta data zame gurin bacci ta nufi toilet da sauri tana adduar shiga toilet din ta fada tana cewa”

Maheeda zata kasheni da masifa wannan lattin danayi.

Sharp sharp tafito ta shirya cikin Marron Turkish gown me hadeda hula me gyale dazakayi rolling tayi rolling dinsa ta fesa turarenta na possess ta dauki Maroon channels handbag da loafers na Clark ta fito da sauri tana Kiran nurat me aikinsu akan takawo mata robar guava shake

Tana kawo mata ta karba da sauri ta bude zata saka a bakinta aka riqe robar tayi saurin juyowa taga hameeda ce tayi saurin Bata fuska tace”

Hameeda please kibarni Mana wlh nayi latti sosai fa….

Dadynsu ne yafito Yana waya idanuwansa suka sauka kan robar guava shake din sai hayaqin sanyi takeyi
Ya datse wayar Yana qarasowa gurinsu ya kalli robar yaga harda qanqara yakai hannu ya karba Yana kallon hameeda yace”

Hameeda kina kallo Zaki Bari Tasha wannan sanyin?
Kinmanta wayece itane?

Kallonsa tayi Takoma kallon Fifi din tana cewa”

Dady zan hanatane ka taho.

Kallon Fifi yayi Yasake kallon hameedar yace”

Ki ringa kiyayewa hameeda dukanmu bamason komai qanqantar ciwo yasamu mufeeda ok?

Miqa mata robar yayi Yana kallon Fifi datayi fuskar tausayi tace”

Dady nayi latti bazan iya tsayawa breakfast bafa.

Table ya nuna mata Yana cewa”

Ko exams ne mamana bazan taba barinki ki fita bakici komaiba indai I’m around.

Suna zama table din su duka hameeda datakai drink din fridge itama tazo ta zauna sai alokacin suke gaidasa ya amsa cikin kulawa Yana cewa”

Ummy takirani hajja ta sake ‘dago rigimar wai sai andawo dake agabanta so takeyi taga aurenki kafin ta mutu.

Dariya tayi tareda kallon hameeda tace”

Hamee kinji nice hajja keson ganin aurena kifada mata raayina idan kunyi waya sbd dady yanzu ina kiranta ko ummy zata fara min kukan tanason ganina dady ba’a Nigeria zanyi aurebafa anan bana tunanin zan samu choice dina acan.

Murmushi yayi yace”

Mamana kifara zuwa Nigeria din tukuna zakisan choices naki duka suna can bama choice kadaiba,
And idan kina maganar life ne kije idan kinje Zaki bani labari sbd KHALID is also gonna be around.

Kallon Hameeda tayi tana dariya tace”

Hameeda ki shirya bazan iya zuwa badake ba I think it’s time muje mu zauna dasu ammy right.

Chips hameeda ta tura cikin baki badan tanajin taste dinsa ba ta daga Kai tana qaqalo murmushi sbd yanda dadyn ke fira da fifin cikin tsananin kulawa sai can can yake jefota.

Cikin qarfin hali tace”

Dady ‘yayan ammy shima wannan Khalid din Yana ciki???

Kallonta yayi cikin kulawa yace”

Hameeda yanzu duk bakusan ‘yayan ammynku ba I tot kuna tambayarsu idan kunyi waya da ammyn.,

To dady ai bamusansu bane.

Babban danta tun kafin na auri mamanku ta haifesa MUHD SAHEEB MAKARFI yanzu baya Nigeria Amma Yana south Africa acan yake zama sai KHALID MAKARFI sukadaine yayanta so gskia yakamata kusan yan uwanku shiyasama dole ku koma gurin ummyn sbd abubuwa ma da yawa kamar wannan din.

mamuh.

KU nunamin qaunarku ta hanyar dannamin subscribe @lafazitv????????????????

Littafin QAUNARMU na kudi ne akan naira 200 kacal.

Katura kudinka zuwa wannan account din…

2260792279
Maryam sani
Zenith Bank

Ka tura shedan biyanka ga wannan numbern

07067124863

Kokuma katura katin wayarka zuwa wannan numbern

.‭0903 234 5899ZAFAFA BIYAR NA KUDINE KA NEMI WAINNAN NUMBERS DIN KA BIYA KA KARANTA CIKIN AMINCI

07067124863
OR
09032345899

2

cigaba da cin abincin fifi tayi tana sauraran hirar su batace uffan ba da dan sauri take dan tuttura abincin tana lura da time,tana aje fork jakarta ta soma jawowa a gurguje ta mike tsaye tace dady pls can i go now?waaro idanun sa waje yay,a shagwabe tace pls,se ya rankwafo kai yana kallon ta kamar me tunanin wani abu can yace emmm not until u give ne a hug,da yar dariyar ta ta taho ta rungume sa sosai yana me sakar mata murmushi cikin tsananin nuna kulawar sa yace akula ok?tace ok bye..dad i love u..bai amsa ba wani irin kallon kauna me fallasa tsananin so yake biyota da shi.. taku dayan biyu tayi sai ta juyo kamar wanda aka tsakure ta tace,”hamee?dago kai hamida tayi ta bita da sassanyar murmushi me ciwon datake jin shi har can kasar zuciar ta..”tace natafi schl..bye..Gyada kai Hameeda tayi Bata ce uffan ba ta mayar mata da murmushi
Me dan fadi..

tun kan ta maida kallon ta kan dinninh table taga dady shima yana shirin mikewa da alaman zai bar wajen cike da mamaki tace”dady har ka koshi?yace yes dear dama na zauna ne sabida mufida ta samu ta ci abinci,u go ahead ni zanje daki..

murmushin karfin hali ta kwakwalo tace ok Nan ya wuce ya haura sama tayi jugum tana bin bayan sa da kallo

In akwai abunda yake mata ciwo bai
Wuce wannan yanayin datake shiga ciki,nobody have her time,rabon dady yay zama na musamman akan dining table domin ta ita kadai bazata iya tunawa…”oh Allah its always about fifi nikam ko oho..wani lumshe idanun tayi hade da sauke nannauyan ajiyan zuciya can ta mike tayi wicewar ta daki..

Classic bentley stance code shiya sauke ta a kofar makarantar su batare da ta maida hanklin ta kan kowa ba ta haura fifth floor inda ake gabatar da practical din sun

Ta riga da tayi lattin mintuna talatin amma dake ta saba da halin ta na creating drama so tana bude kofar ajin tayi lumui cikin sanda tace hey guys,”anan kusan duka ajin suka juyo suka kalle ta,ganib hakan ya sata ta boye fuskanta ta tana toshe bakin ta ridicoliusly.

Kawarta maheeda ce ta watsa mata harara tana mata alaman shushhhh da hannu..kwabe fuska tayi a shashance tana duban lecturer da sauran daliban da duk suka tsura mata ido tace sorry tazo ta wuce sadaf sadaf ta nemi waje ta tsaya,sauke ajiyan zucia lab co-odinator yayi yace “and that was mufida mande, now lets get back to business. ,jin haka wani dariya ne ya kufce mata inda hanklin kowa ya sake dawo kan ta tun kan malamin sun yy magana ta mike tsaye ta rike kunnen ta kamar marainiya tana cewa sorry sir..rasa abun cewa yyi yana girgiza kai ya rasa ta meyasa fifi taki sa seriousness arayuwan ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button