KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Kan Hamida na ƙasa zuciyar ta na mata zafi da raɗaɗi dan wata sabuwar ƙiyayya ce ke samin gurbi da mazauni a zuciyar ta game da auren nan da ita kan ta ƴar uwar nata,tsabar son kai wai har shekarar su goma da aure ita wancan matar nasa bata da lokacin sa tana business ɗin ta sai ita ce mai zaman gida marar aikin yin da zata na kula da tsoho kamar shi,ai ko da bata san shi ba a ido ta san in ba a yi wasa ba ya haife ta because a shekarun da Hajja ta kirawo mata akan shekarun sa da aure ita a lokacin ina take?sannan kwata kwata tana ten years as at then toh shi ɗin a shekaru nawa yayi auren?..
Muryar Hajja ta ji a kunnen ta tana ƙarasa mata labarin.
“Shi ɗin Brigade ne na sojoji,kuma dalilin da ya sa ya bar mahaifar sa zuwa ƙasar south africa shine,akwai wata shekarar da ta gabata kusan shekaru ashirin da suka wuce an sami wata tarzomar da ta tayar da ƙura a tsakankanin ƙasar nan Nigeria da Cotonou,duk sojojin da ake kaiwa wannan boarder ɗin sai dai su yi iya yin su ba tare da sun yi nasara ba,wasu su dawo da rai wasu a dawo da gawarwakin su wasu kuma ba ma za a gan su ba,toh a wannan shekarar ne aka umarci head division ɗin wannan yankin da ya saka hannu wun bada gudunmawar sa kuma a haɗa da na ƙasar chad dan ganin ko za a sami nasara dan in har aka bar tarzomar ta cigaba toh zata iso nan ƙasar gabaɗaya ta addabi ƙasar,a lokacin yayan ku Saheeb bai jima da fara aikin sa ba sai wannan buƙata ta taso,da zuciya ɗaya ya amshi umarnin da aka basa daga sama ya nemi addu’ar mu suka nufi wannan yankin Cotonou ɗin wanda suka shafe kusan watanni shida suna jeji sai a na bakwan ne suka fito da babbar nasara mafi yawan yabo ya sauka akan yayan ku Saheeb,wannan jarumta nasa ya sa ya ɗaukaka har ya sami cigaba sosai fiye da shekarun sa,toh ana haka ne wata tarzomar ta kuma tasowa a ƙasar south africa inda a nan ne kuma ya ƙara samin ɗaukakar fiye da na farin,toh kuma tun daga wannan sai suka buƙaci da ya cigaba da zama a can dan ƙasar na fuskantar barazana ta maƙiya kusan akai akai,zaman yayan ku a ƙasar ya sauƙaƙa yawa yawan faɗace faɗacen da ake samu akai akai dan sun haɗa kai da sojojin ƙasar ta yadda da zarar an sami ɓaraka ko ana gab da samu toh zasu baza battalions ɗin su nan kuma za a fito da nasara”!!kuma jan fasali Hajja tayi Hamida na sauraron ta kamar tana sauraron wa’azi..
“A shekarar da suka fito da wata nasara ce Allah ya nufa suka haɗu da matar sa Muhibbah wacce itama aiki ne ya kai ta can ɗin dan businesses ɗin mahaifin ta ya kasance mai faɗi ne ƙasashe daban daban take zuwa yin sa, a wannan karon sai suka haɗu suka saba,toh mu a nan gida dama a matse muke da yayi auren dan ya fara manyanta amma bai maida hankalin sa a nan sai da ya haɗu da ita ɗin ne sannan ya kawo maganar,ba a ɗau lokaci ba aka yi auren zaman su a nan wata guda suka tattara suka koma south africa da zama,bayan shekara ɗaya kuma sai ya kawo mana ziyara duk muka ga kamar ba shi ba,yin duniyar nan mun yi ya fayyace mana matsalar sa amma ya ƙi,ko da muka tuntuɓe sa da maganar inda matar take sai ya ce ai tana ƙasar Los Angeles wai tana kula da businesses ɗin mahaifin ta da ya rasu ya bar mata.a wannan lokacin hankali na ya gama tashi nayi tunanin samin mahaifiyar ta dan mu zauna a warware matsalar amma haka Saheeb ya hana ni ya ce min shi bai da matsala da wannan haka na ƙyale ba dan ina so ba”..
“Bayan ya koma da shekaru biyu ya kuma dawowa shi kaɗai nan ma da aka yi tambayar duk ɗaya ce,tana wata ƙasar tana kula da businesses ɗin mahaifin ta,a lokacin na san Saheeb bai yi dacen macen aure ba dan bata da niyar zama da shi bare ta haihu,daga ni har Ammyn ku duk mun matsu mu ga jinin sa a duniyar nan amma shi a wurin sa ba haka bane,a lokacin na ɗaga hankali na akan zancen ina ta nemar haɗa sa da jikokin aminai na amma haka zai ce duk basu mai ba shi hasalima bai da matsalar komai da matar sa akan me zai kuma yin wani auren,a ƙarshe dai komawa can south africa yayi kuma tun daga wannan komawar ne bai sake dawowa ba kusan shekaru shida da rabi kenan kullum sai dai a yi magana da shi ta waya in muka matsu da son ganin sa sai dai ta video call abin na damu na yana damu na a zuciya ta,yana jika na amma ya nesanta da ni ga mahaifiyar sa ya tsallake ta ya gwammaci zaman wata ƙasar duk dan baya so a ba matar sa laifi”..
“A ranar da mahaifin ku ya sanar da ni kun cika shekaru goma sha tara a duniya a ranar ne na saka sa gaba akan ya turo ku ku dawo tunda shi ɗin bai da niyar dawowa dan tun bayan rasuwar mahaifiyar ku shima ya ƙi yarda a mai maganar aure ya zaɓi zaman can germany akan nan,tun lokacin nake damin sa akai akai dan na san ba za a rasa wacce za a haɗa ta da Saheeb ba amma ya min nuni da cewa ai karatu kuke yi sai dai kuna gab da kammalawa kuma da zarar kun kammala zaku taho”..
“Kasancewar takwara ta ta fi yawan magana da ni ya sa na rinƙa damin ta da ta dawo gida,ku dawo gida kar ku gama yin girman ku a ƙasar da ba taku ba,toh alhamdulillah kun kammala karatun naku kun dawo gida Allah ya tsara maku mabambantan rayuwa ita Mufida ta dace da Khalid ke kuma muka maki sha’awar Saheeb sbd ɗabi’un ku kusan ɗaya,ke tamu ce muna da iko akan ki ba kamar matar sa ba da ikon da muke da shi a kan ta ƙalilan ne”!!..
“Dan haka muka ga dacewar ku kuma mun san kema a yanzu da kika ji labarin sa kika san ko shi ɗin waye zaki ga hangen da muka yi kuma ba zaki taɓa yin nadamar zaɓin mu ba”..
Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Hamida ta sauke bayan ta gama sauraton Hajja,ajiyar zuciyar na ɗauke ne da abubuwa masu wuyar fassaruwa amma dai ta barwa kan ta duk da zuciyar ta na mata zafi ganin irin mizanin da aka ɗora nata martabar akai,ƙasƙancin sa ya ɗare abin misali..
Wani baƙin cikin ta haɗiya sannan ta saka murmushin da ya fi kuka zafi da ciwo tana faɗin.
“InshaAllah zaku same ni mai bin umarnin nan naku da amana da gaskiya Hajja”!!.wani sanyi Ammy ta ji a zuciyar ta har ta fidda ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya haɗe da tashi cikin sauri ta rungumo Hamida jikin ta..
Abin mamaki yanzu dan na yarda da auren nan ne ya sa Ammy ta rungume ni haka?abin da tun da muka iso ƙasar nan bata taɓa yunƙurin yi min ba akasin fifi da ba zata iya ƙirga yawan hugs ɗin da ta samu daga wurin Ammy ba,oh ita Aysha yanzu wai ba dan ta cancanci hug ɗin ba aka bata shi ba sai dan ta yarda da zaɓin su..
Hawaye ne ya sauko mata daga idanun ta tayi saurin gogewa tana jan hancin ta sai muryar Ammy ta ji tana ta yi mata addu’a haɗe da bata tabbacin ba zata taɓa nadamar wannan haɗin da zasu mata ba.
Jin Ammyn kawai take ta yi har ta gama ta kuma jaddada mata ta tabbatar ta tafi inda ake ma fifi gyaran jiki dan itama a mata..
Gyaɗa kai kawai tayi ta sallame su suka rinƙa saka mata albarka tana jin su ita dai tayi gaba..
Tana hanya tana ta nazarin kalamomin su har ta zo ta wuce apartment ɗin da ake wa fifi gyara sai kuma ta dawo tayi peeping ta hango ta tana ta danna waya tana murmushi..
Komawa da baya tayi ta nufi nata ɗakin ta kwanta dan zuciyar ta bai mata daɗi,kasa baccin tayi sai ta tashi ta ɗau maganin ta ta zazzago guda biyu ta nemo bottle water ta haɗiye maganin..
Bata jima ba bacci ya sace ta bata farka ba sai 7pm kasancewar bata sallah sai ta sauko zuwa ƙasa dan a yi dinner da ita inda a nan fifi ta rinƙa mitar Hamida ta manta da ita yanzu sai dai su haɗu a wurin cin abinci in ta zo kenan bayan haka basu haɗuwa kuma ita a hana ta fita a apartment ɗin sai dai in ya zama dole..
Nan ma duk jin ta Hamida ke yi kowa ya kwaso blame ɗin sa kan ta ake sauke sa ba komai in yanzu sun mata wataran ba zasu yi ba..