KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

A haka aka cigaba da shirin bikin su Hamida da fifi wanda tun a washegari Hamida tayi joining fifi aka cigaba da yi masu gyaran jikin sai dai bata tsira ba still akan nuna bambancin dan bayan an gama sai Ammy ta kira fifi separately ko me suke girkawa Allah ne masani ita dai ta san babu wani ƙaunar Mufida a zuciyar ta ko na ɗigo ne but su sun kasa ganewa,bambancin da suke nuna mata bai haddasa komai sai ƙiyayyar masoyiyar tasu wato Mufida…
MamuhMamuhgee
13
Ana saura kwanaki biyar da bikin su fifi sai shaƙuwar su da Hamida ya ninku ya fi da duk da ita Mufida ta fi alaƙanta shaƙuwar tasu da yanayin bambancin rayuwar auren da zasu fuskanta,duk dama ta san cewa gida ɗaya zasu zauna amma apartment ɗin kowa daban ba lallai bane su rinƙa haɗuwa kullum ba in an gama bikin..
Lokaci zuwa lokaci sukan zauna zama ta musamman tsakanin su su zanta mafi yawan hirar tasu takan karkata ne a ɓangaren kewar junan su da zasu yi bayan bikin,though sau da yawa hirar ta su takan ƙare ne da faɗa wanda fifi ce mai yawan janyo sa dan takan so ƙure Hamida akan zaɓen mijin ta ita kuma Hamida bata ba fifi hankalinta ɗin ta iyakar in an gama masu gyaran jikin sai ta tashi tayi gaba abin ta ƙarshe Mufidar ce ke zuwa ɗakin Hamida ta bata haƙuri sai su shirya hakan bai hana washegari in sun kuma haɗuwa ta ƙara tsokanar ta ba sai dai Hamidar da girgiza kai ta ce mata Allah ya shirye ki fifi..
A yau ne suke saka ran zuwan daddyn su dan kusan one week ago suke ta waya da shi ya sanar da su zai zo inshaAllah cikin kwanakin nan..
Tun safe suka kasa sukuni musamman fifi da ta fi zumuɗin ganin daddyn nasu dan dama tayi kewar sa fiye da tunani..
Har kasa natsuwa tayi saboda zumuɗi sai da Khalid ya ja hankalin ta da hira sannan ta sami natsuwa shima ya tafi ɗauko daddyn..
A cikin gida kuwa har girke girken da aka yi fifi na a ciki dan sosai ta ce tanaso daddyn ta yayi tasting abin da ta girka da kan ta..
A lokacin da daddyn su ya iso gida tare da Khalid haka fifi ta kanainaye sa ta ki barin sa ya sha iska tana ta yi mai surutai akan yadda tayi kewar sa,hakama su Ammy da Hajja da suka matsu da ganin sa sai dariya suke ta yiwa fifi akan yanzu kenan da take da ƴancin ganawa da daddyn nata take mai haka ina ga in ta yi aure kuma ita da mijin and da zarar sun tsokane ta da haka sai ta saka kukan shagwaɓa tana kallon Khalid da kwana biyun nan sam tadena gane masa
Sau dayawa ta rinƙa tambayar sa ai ba zai bari ta rabu da daddyn ta ba ko? shi kuma da dariyar sa zai amsa ta yana ce mata ai babu mai raba ta da daddy da su Ammy..
Azuciyarta tana dannewa ne kawai amma Halaye khalid gaba daya ya sauya mata in ya amsa ta se tanajin kamar ba shiba
Sai da aka ci abinci aka natsu sannan aka dawo parlor domin cigaba da hirar da aka faro tun akan dinning,sam Hamida takasa sakin jiki tayi da su sai ta nemo excuse ɗin da ta san zai bada babbar muhimmanci ta gudu zuwa ɗakin ta ta kwanta sabida duk yadda kwanakin bikin na ƙaratowa the more fargabar ta na ninkuwa..
Kusan raba dare suka yi suna hirar su duk kuma saboda fifi ne dan ta ce wannan shi ne best moment ɗin rayuwar ta da ba zata yarda ya tafi haka nan ba sabida ita dai tun tasowar ta daga ita sai daddyn su sai Hamida suke rayuwa a cikin gidan banda ma’aikata,a yau da suka haɗu duka with exception of saheeb wato mijin ƴar uwar ta da ita kan ta ƴar uwar nata sai ta ga wannan kamar dama ne babba da zata yi amfani da shi dan barin memories ɗin ta a zukatan ahalin nata…
Wasa da dariya anata hira Sai kusan 11pm fifi ta raka daddyn su masaukin sa inda nan ma ta rinƙa labarta mai abubuwan da Khalid ke mata tun zuwan su da irin kula ta musamman da yake bata tun zuwan su,shi kam daddy bai da abin cewa sama da yiwa Allah godiya dan ya kawo mai saka ɗiyar sa farinciki a rayuwar ta ba kuma zuwa kaɗai yayi ba tsayawa ma zai yi na har abada..
Da ta dawo ɗakin ta kuwa sabon babin hira taso ta buɗe ta musamman ita da angon nata Khalid dan kiran da ta mai ya kai sau uku bai dauka ba,can yazo yadauka bata gane masa ba in sun yi good night sai ta sake kiran sa a haka dai har aka yi final good night duk suka kwanta bacci..
A washegari suka haɗu a ɗakin Ammy ta saka su gwada ɗinkunan su na bikin har ma da na events ɗin da za a yi,duk babu wacce kayan nan bai yiwa kyau ba dan dirin jiki da kyan halitta Allah ya hore masu shi..
Ita fifi da ta gwada na ƙarshen ƙin cirewa tayi ta bar shi a jikin ta sai da aka shigo ɗakin da sallama ta ɗago kai ta ga Khalid ne nan take ta fara nemar abin da zata rufe jikin ta da shi da alamr bata so ya ga kayan dan in ya gani toh ba wani birge sa da take son yi da zata yi a ranar event ɗin kayan..
Dariya Ammy ta mata itama Hamida ta ɗan dara tana mata gwalon Allah ya kara wai angon ta ya ga kwalliyar ta tun kafin ranar bikin,abin sai ya ba fifi haushi amma da yake bayan ya shigo Ammy ta kora sa waje dan kar ya ga kayan fifin sai ta ji sauƙin abin bata saka tsokanar ƴar uwar nata a ka ba…
Da safe yau ma family breakfast aka yi dan an san daga yau ɗin ba lallai bane a kuma haɗuwa on special breakfast haka ba sai dai in bayan biki..
Ana cin abinci ana hirar yaushe rabo Hamida dai bata yi gigin saka masu baki a hirar tasu ba dan ta san ko ta saka toh ba wani ƙwarjinin da zata yi duk hankali na ga fifi..
Suna gama breakfast ɗin tayi gaba abin ta sai dai a yau Hajja ta yi magana akan ƙyaliyar Hamida na damin ta,toh ana ta fifi sai kawai aka ce hala yanayin fargabar ta kenan ita tunda ko wacce amarya na da nata sigar fargabar in bikin ta ya zo toh maybe nata a haka ya zo na son kaɗaicewa ita kaɗai..
Bayan an gama hirar fifi ta tafi ɗakin Hamida wacce ke kishingiɗe tana danna wayar ta da hannu ɗaya babu wani sutura a jikin ta sai ƙaramar armless top marar kauri ƙafar ta tayi crossing ɗaya kan ɗaya,hakan ya bada damar viewing elegant well groomed skin ɗin ta da ya sha gyara yana ta ƙyalli da walwal..jin fifi abayan ta ya sa ta boye abunda takeyi a wayar tana me cusawa a kasan fillow
Ƙare mata kallo fifi tayi sannan ta ƙaraso ciki tana murmushi ta zauna kusa da Hamidar ta taɓa ta..
Kallon ta Hamida tayi sannan ta tashi ta zauna sai fifi ta kuma kallon ta har abin ya saka Hamida tsarguwa sai ta nemo outer top ɗin rigar ta saka tana kallon Mufidar haɗe da tambayar ta ko lafiya da irin wannan kallon..
Murmushi kawai fifi ta mata sannan ta fara magana cikin gaskiya da gaskiya..
“Hamee ni kin san me ke dami na ne,wallahi ba komai ke dami na ba sai ganin irin wannan gyarar da aka maki kika fito tas da ke amma wai a ce wannan tsohon ne zai ga gyaran abin na taɓa min zuciya ƴar uwa ta,ban da yadda zan yi ne da na taimaka maki,ba ƙaramin tausaya maki nake yi ba,duk yanayin ki ina ankare da su kawai ƙyalewa nake yi dan na ga kamar kin fi buƙatar ki zauna ke kaɗai ne dan ki jajanta rayuwar da zaki shiga ciki,wannan dalili ya sa nake barin ki ki bar mu ko da hira ake yi sai dai a yau na ga damuwar taki har ta ɗare na kullum shi ya sa na biyo ki,shin Hamida akwai wata matsalar dake damin ki ne a zuciyar ki da baki son sanar da kowa”?.
Kallon ta Hamida ke yi cikin wani yanayi me wuyar fassara da sa tsoro wanda babu alaman shi akan fuskan ta sai a ziciyarta