KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

har fifi ta gama maganar ta sai ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana girgiza kan ta cikin halin ni ban da wani damuwa..

Hakan bai gamsar da fifi ba sai da ta kuma nanata mata tambayar a wannan karon sai Hamida ta yi magana da bakin ta bayan riƙo hannuwan fifi da tayi cikin nata.

Tace”Fifi na kar ki damu kan ki akan matsalar da bata nan,ni ban da matsalar komai dan dai kawai a ƴan kwanakin nan nakan yi tunanin irin kewar ki da zan yi bayan bikin nan dole dama wataran duk shaƙuwar mu dole mu rabu in ba mutuwa akwai aure kuma auren babu inda baya kai mutum hala mu rabu wata rana,alaƙar dake tsakanin mu ba ta fuska bace kaɗai,Mufida alaƙar mu ta jini ce wacce ko bayan rabuwar mu in an yi bikin nan wannan alaƙar tamu ta jini ita zata cigaba da ƙarfafa Ƙaunarmu dan haka ƴar uwa ta kar ki damu advantage ɗin auren mazajen namu kenan,gida ɗaya zamu zauna kuma in muka so a rana sai mu haɗu fiye da ɗaya,so calm down my dear auren nan ba zai raba mu ba ok”?ta ida maganar tana ɗage girar ta..

Gyaɗa kai fifi tayi dan duk abin da Hamida ta faɗa mata a yanzu gaskiya ne babu ƙarya cikin ta..

Rungume junan su suka yi Mufida ƴar shagwaɓa sai kuka take ta yi ita kuma Hamida na rarrashin ta dan ita danne nata hawayen tayi…

Sai da suka natsa suka ɗan yi hira Hamida na kuma jaddada mata kar fa ta ɗaga hankalin ta akan behaviours ɗin ta ba komai bane kawai kewar ta da zata yi ne da na su daddyn su,da hakan fifi ta sami relief ta saka a ran ta in ma an gama bikin ba zata yarda su gudu zuwa honeymoon ɗin ba har sai sun jima sbd ƴar uwar ta kar ta yi zaman kaɗaici…


Yau ce ranar da za a yi family get together inda a cikin gidan farfajiyar gidan aka taru aka gabatar da shi bayan an ƙawata farfajiyar gidan da decorations wanda ya kasance adon royal blue aka yi amfani da shi dan su kan su amaren kalar kayan da suka saka kenan sai sauran ƴan uwa da abokan arziƙi da suka halarci event ɗin,su ma royal blue ɗin suka saka bambancin nasu da na amare shine na amaren an haɗe sa ne da off white head turban da aka masu ɗaurin sa sannan doguwar transparent designed net ɗin da aka ɗora masu saman asalin rigar jikin su ma ya kasance off white,takalman su da purse ɗin su duk off white,makeover aka masu sosai da ya fito da su..

Duk babu wanda zai gan su ya ce bai yaba da su ba,basu da kamanni dai amma da an gan su annga jini,ita Hamida in tayi murmushi gefe ɗaya dimple ɗin ta ya fito ita kuma Mufida in tayi murmushi duk two sides ɗin su bayyana..

A haka cikin kwanciyar hankali suka yi event ɗin su aka yi coverage da hotuna,masu selfie na ta yi ƴaƴan abokan mahaifin su Khalid duk sun taho sannan friends ɗin sa maza da mata sun zo wurin ciki har da close colleagues ɗin sa..

A fannin ammy Da zarar an yi tambayar ina amaryar Khalid sai a hau nuna ta su kuma su yi ta zuzuta kyawun ta dan dama ita ɗin mai kyau ce ko ba ado…

Lafiya ƙalau suka gama event ɗin aka koma cikin gida washegari ma aka yi bridal shower duk da ba su da friends amma close ones sun halarci event ɗin dan a jiya suka sami friends yawanci ƴaƴan abokan daddyn su da na mahaifin su khalid ne suka dawo bridal shower ɗin..

Dama in ka taho da kayan ka toh zaka cire a baka dress of the day da ya kasance mini peach chiffon inner da outer top ɗin sa kasancewar cikin ɗakin Ammy aka yi event ɗin kuma duk mata ne sai abin ya bada armashi nan ma haka aka yi aka gama..

Next day aka yi walimah da ya afku a cikin gidan kuma ya sami albarkar jama’a da dama dan marigayi mahaifin su Khalid ya tara jama’a sbd irin zaman kirkin da yayi da su,haka matayen abokan nasa ma suna mutunci da Ammy sosai Haka shima walimar aka yi aka gama sa lafiya

misalin 6pm daidai ana gama sa daidai Ameed da Meena suna shigowa cikin gidan,wani irin annashuwa fifi ta tsinci kan ta ciki wanda baya misaltuwa dan bata san har da Meena zata zo ba..
Welcoming nasu alka yi zuwa cikin gidan aka gabatar da su.

Duk wannan bidirin babu wanda ya kawo maganan zuwan angon Hamida wato marshall Muhammad Saheeb Maƙarfi,sai sha’anin biki kawai ake ta yi..

Hira sosai suka sha da Meena dan Ameed kam ya bi ayarin ango Khalid suna hira though basu san juna ba amma dalilin fifi sun saba..


Next morning

Duk wata shiri irin ta musamman da ya dace a ma amare an zauna an ma su fifi da Hamida misalin ƙarfe goma ne dama ɗaurin auren sai Mufida ta rinƙa hirar ta da ɗaukar selfies tare da Meena da wasu dake ɗakin waɗanda ba zasu wuce sa’oin juna ba,in tayi wanda ya mata kyau sai ta turawa angon ta Khalid amma setaga kamar ma baiya bada hanklinsa sosai,
Hakura tayi daga baya tabarsa atunanin ta hidimar biki ne ya sha masa kai

Suna kan ɗaukar hotunan nasu aka fara shirye shiryen ɗaurin aure inda nan fifi ta bar duk wani abin da take yi ta riƙo hannun Meena ta natsu tana sauraron mallamin dake kan huɗubar sa da nasihohin sa har ya gama..

Sai a lokacin tasake duddubawa tana qoqarin Kiran wayar hameeda data bace Mata tun dazu Bata ganta ba Dama tanason ganinta Dan kebewa tayi Mata tambaya sbd ganin wani irin sauyib data tashi dashi a yau din na tsantsar yalwan farin ciki Dan zata iya cewa ta jima batagan hameeda cikin sakewa da annashuwaba kaman yau din.

Ɗan shiru ne ya biyo baya sai ta kalli Meena da tensed face sai Meena ta gyaɗa mata kai alamar it’s all gonna be ok.. Karta damu

Bata gama tunanin ba sai ta ji gyarar murya a microphone sai a sannan ta sami relief ta yiwa Meena murmushi..

Ba a ɗau 3 seconds ba sai ta ji an kira sunan ta nan gaban ta ya faɗi sbd zaƙuwar da tayi ta ji an ce ta mallaki Khalid sai murmushi Meena ta mata
The next name that follows shine Muhammad Saheeb Maƙarfi..
Shiru tayi tana jiran jin a kira nata ango amma kuma sai me!?sai jiyo mallamin tayi yana faɗin
“jama’a ayi hakuri Adakace mu”..

Wani irin ras gaban mufida ya fadi
takalli meena
Tanason mgn saikuma takasa take ta ji kan ta ya sara kawai ta fara ganin dishi dishi bata ƙarasa jin yadda aka karasa wajen ɗaura auren ba ta koma ta mannu da bangon ɗakin idanun ta widely out tsaban fargaban da bata san mafarin sa ba

nan take hankulan matan ɗakin ya tashi banda mace ɗaya da yanzu ta shigo tana ce da su an dakatar da daurin aure kowa ya nitsu Mufida haka ta zauna shiru kamar statue babu uhm babu uhmuhm

Meena ce ta hau tambayar ya haka?
Wasu tambaya suke yi ko an sami akasi ne daga gun maɗaurin auren ko ya manta sunayen angwayen ne..

Matar nan dai na tsaye sai da surutur tayi yawa sai ta ɗan tsawatar masu ta ce
“Duk ku natsu,ina Hamida take?sai a yanzu aka fara waige waige inda Hamida take,nan hankula ya kuma tashi dan babu ita babu alamar ta..

Wata ce cikin masu duba Hamidar ta ce
“Mama ɗazu fah tana nan ana mata kwaliyya muna selfie tare da ita ina ta shiga”?gyaɗa kai matar tayi tana jinjina lamarin sannan ta ce

“Hamida da Khalid sun gudu,ba su gidan nan,ba su cikin anguwar nan kuma babu trace ɗin su”..

Babu wanda ya lura sai jin ƙarar faɗuwar mutum suka yi nan take aka juyo dan ganin wa ya faɗi,ko da suka juyo Mufida ce kwance a ƙasa kamar marar rai ga kwalliyar ta da ya shimfiɗu a saman fuskar ta ya mata kyau amma daga nesa kamar bata numfashi…

MamuhMamuhgee

14

Rikicewa gidan biki yayi a nan waje maganganu aka rinka yi da masu tir da sigar da Hamida da Khalid suka ɗauka da masu tausayawa Mufida dan shagulgulan da aka yi a kwanakin bikin ya nuna irin ƙaunar da ke tsakanin Mufida da Khalid sai dai kuma yau da wannan abin ya faru,jama’a sun kasa bambance irin wannan lamari..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button