KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Kusan rabin ƴan biki sun fara tafiya saboda yadda bikin ya kasance akasin burin da aka dora a bikin amma yau da yake bikin ne sai abubuwa suka sauya.
An bar gidan biki da abubuwan al’ajabi wanda ake ganin ba a taba samin irin hakan a wuraren hausawa ba kamar yadda yake faruwa a wuraren kudu..

A sashen su Ammy kuwa haka Ammy ta rinƙa ji kamar ta saka kuka ba dan komai ba sai dan irin wannan abin maganar da Khalid ya bar mata because ba ta kan Hamida take ba duk laifin a yau ta alaƙanta sa ne da Khalid kuma abin na ran ta..

Hajja kan ta kasa taɓuka komai tayi murna ya koma ciki duk burin bikin takwarar tata kuma jikar ta abin ya wargaje,bambancin fushin ta da Ammy shine ita laifin Hamida take gani while Ammy ta ɗau zafi sosai akan Khalid kuma ta shirya mai..

Daddyn su fifi kuwa rasa abin faɗi yayi dan da a ce yau wata ce hakan ya faru da ita toh ba zai ji ciwo a ran sa kamar yadda yake tsananin jin ɓacin rai ba a yanzu da abin ya shafi rayuwar sa(Mufida kenan)..

Tun ana neman na haƙuri har aka zafafa abin tun safe har dare amma babu wani kyakyawar outcome.
  Ƴan sanda da jami’an tsaro duk sun shigo lamarin amma babu wani sakamako mai daɗi da aka samo..

Hankula duk sun tashi tsoron Ammy bai wuce kar wani abu ya faru da Hamida ba dan ita ce mace da ko da wani abin zai faru ita ce abin a tausayawa..

Matuƙa Ammy ta ɗau zafi hakan ne ma ya sa daddyn su fifi bai nuna nashi ɓacin ran ba gudun kar abin ya fi haka amma ba dan baya jin zafin abin a ran shi ba..

Da ɗai ɗai dama aka bar gidan bikin gidan ya dawo shiru babu hayaniyar kowa kamar ba gidan biki ba abin dai abin ban mamaki da tausayi. 
  Misalin 10pm daddyn su fifi ya sa aka tafi dubo masa ita dan tun faruwar abin ƙulle kan sa yayi a ɗaki yana ba kan sa laifin gazawar sa a uba,yana ganin kamar ya kasa samarwa ɗiyar sa rabin ran sa farincikin ta wanda tunda ta taso tun yarintar ta har kawo yanzu komai take nema sai ya tafi ya samo mata shi..
  Sai dai abin mamaki yadda ya gaza wurin samo mata farinciki mai daweamuwa har ƙarshen rayuwar ta…

Yana zaune a ɗakin sa yana ta tunanin yadda duniyar ta sauya masu su duka a cikin ƙanƙanin lokaci sai aka yi sallama wanda muryar Ammy ne.
Shigowa ɗakin tayi rungume da Mufida a jikin ta da duk ta fita hayyacin ta ta sauya kamanni kamar ba amaryar da few hours ta baza murmushi da annashuwa ba..
 
Kasa hada ido da ita daddyn su yayi sai kawar da kan sa gefe da yayi yana danne zuciyar sa dan kamar hawaye ne ke son ciko mai a idanun sa kuma ya san yana barin hawayen ya zubo toh fah zai kuma karyawa ɗiyar tasa gwiwa..

Suna ƙarasowa cikin ɗakin Ammy ta zaunar da ita sai ta bi Ammy da kallo idanun ta duk ya koɗr dan tun bayan faɗuwar da tayi aka yayyafa mata ruwa ta farka babu abin da ya mata daɗi sama da yin kuka kuma shi ta rinƙa yi har sai da ta ji kamar zuciyar ta na mata nauyi fiye da misali sannan ta ɗan sarara..

Girgiza mata kai Ammy tayi alamar ba tafiya zata yi ba tana nan tare da ita sannan ta saukar da kan ta ƙasa ta zauna shiru. 
  Zama kusa da ita Ammy tayi bata dai taɓa ta ba amma tana tsammanin faɗowar ta jikin ta da zarar hawayen ta sun fara zubowa..

Kusan mintuna goma suna zaune shiru,babu wanda ya tanka ko motsawa,sai chan daga bisani daddyn ya kira sunan ta a hankali.
“Mufida”!!kan ta na ƙasa amma sai da ta ji sunan har cikin zuciyar ta,take taji zuciyar ta ta karaya sabuwar kuka na son kufce mata amma dai ta danne ta amsa mai.
“Na’am daddy”!.shiru ya biyo baya sannan daddyn nasu ya daure ya hau yi mata nasiha akan yanayin rayuwa da yadda Allah ke tsarawa bawan sa rayuwar sa,duk tana sauraron sa tana tanƙwara zuciyar ta dan kar hawayen ta ya fito,amma maganar sa ta ƙarshe sai da ta karya mata zuciya har ta kasa haƙuri ta saki marayan kuka..
  “Kuma ki sani matar mutum ƙabarin sa,dan kin rasa Khalid ba kin rasa miji bane hakan na maki nuni ne da ba alkhairi bane a gare ki kuma wani wanda shine mafi alkhairi a gare ki na nan Allah zai haɗa ku”..
  Kuka sosai take yi bayan sauraron wannan kalamai nasa,bata san ta faɗo mai ba har tana maganganu cikin kukan nata ba sai da Ammy ta zo ta ɗaga ta ta rungume ta ai kuwa ta damƙe Ammy gam gam tana ta kuka yanzu ne ma take asalin kukan daga zuciyar ta sanin ta rasa Khalid kenan har abada dan ko bata san dalilin sa na gudun ta ba ta san tunda tare suka ɓace da Hamida a rana ɗaya toh ba ƙaramin abu bane kuma a ran ta bata jin son da yake mata na da ƙarfi because da yana da shi toh da ba zai ɓace a neme sa a rasa ba a rana mai albarka irin wannan ranar da ita da shi suka ɗau lokaci suna tsara sa ba…

Lura da daddyn su fifi da Ammy tayi kamar kuka zai yi sai ta janye ta suka bar ɗakin dan ita kan ta jarumtar ta ya ƙare ƙiris ya rage ta saki nata kukan dan wannan irin babbar embracement da Khalid ya saka ta ciki bata taɓa fuskantar sa ba..

A ɗakin Ammy haka fifi ta buɗe sabon babin kuka gwanin tausayi dan duk wanda ya kalle ta sai ya tausaya mata..
A haka tana kukan Ammy na rarrashi Hajja na zaune gefe rungume da ita bata sani ba bacci ya sace ta..

The next morning wuraren ƙarfen goma na safe sai ga mai gadin gidan ya shigo a guje kamar ya ga abin ƙi yana haki yana kallon Ammy dake zaune a kujerar dinning ita ɗaya tana tunanin fifi da kusan sau uku tana zabura cikin baccin ta jiya ƙarshe sai da aka kirawo family doctor ya zo ya duba ta cikin daren ya mata abin da ya dace sannan aka sami sukuni..

Kallon sa Ammy tayi ta tambayi lafiya,sai a sannan ya iya buɗe baki ya faɗa mata ai Khalid ne ya dawo yanzu tare da Hamida..
  Rass gaban Ammy ya bayar dan haka ta tashi ta wuce mai gadin ta nufi hanyar ƙofa ta leƙa ta ga su ɗin ne abin su..
  Dawowa ciki tayi da sauri ta nufi sashen Hajja ta faɗa mata abinda ke faruwa itama Hajja cikin tsinkewar zuciya ta tashi ta fito zuwa parlor..
  Daga ɗakin Hajja Ammy ta nufi ɗakin ƙanin ta daddyn su fifi ta ce da shi ya sauko zuwa parlorn ƙasa ga su Khalid nan sun dawo..
  Tashi yayi ya fito tana gaba yana bayan ta suka sauko ƙasan,step ɗin daddy na ƙarshe yayi daidai da shigowar su parlorn..
  Sai bai ƙarasa saukowa ba ya tsaya a nan last step ɗin ya ƙurawa Hamida ido yana nazarin ta yadda ta zamo so selfish..

Ammy kuwa bin su da ido kawai tayi tana jinjina kai dan ko ɗazu sai da aka kawo masu feedback akan fah ba a gan su ba ashe suna hanya…
  Tsayawa suma suka yi a tsakar parlorn ganin all eyes on them sai ya ja hannun Hamida ya maida ta bayan sa shi kuma ya fuskanci iyayen nasu..
  Riƙe hannun ta da yayi a idon Ammy da daddy sai gaban Ammy ya faɗi tsoro ya shige ta firgici ya rinƙa ziyartar ta akai akai..
  Suna tsaye kamar an dasa su Hamida na a bayan sa kan ta ƙasa shi kuma ya buɗi baki direct babu ɓuya ya ce
  “Ku yafe mana”!!wani dum gaban Ammy ya bayar dan bata yi tunanin abu mai kyau bane ya faru a tsakanin su ba..
  Babu wanda ya tanka masu sai Hajja dake zaune ce ta dube su ta ce
“Na me”!?sai ya kuma haɗo jarumta da tattaro qarfin hali da zare tsoro da kunyarsa sbd shine namiji Kuma shugaba sunyi alqawarin shine zaiyi bayani ba wani kwana kwana tunda dai sungama komadai menene. amsa kakar ta su yayi
  “Na gudun da muka yi,ku yafe mana”!!sai Hajja ta ji ran ta na kuma ɓaci a ce a shashancin namiji mace ta saka kan ta ciki..
“Gudun da kuka yi?me ya sa kuka dawo bayan kun zaɓi gudun”?tambayar da Hajja ta masu kenan wanda ya dirar masu ba tare da sun shirya ba sai Khalid ya ce
  “Mun dawo ne dan dalilin gudun namu ya riga ya gabata”!!turus Ammy tayi tana sauraron su yet Hajja ce ta kalle sa ta ce
  “Wani dalili kenan da ya gabata har ya sa kuka waiwayo daga gudun naku”?dama tambayar da yake so ya ji kenan sai ya ce
  “Auren mu,ni da Hamida”!!Ammy was like what??aure?shi da Hamida?wani irin madness ne wannan..
Kasa haɗa ido yayi da Ammyn nasa dan ya san tambayoyi da dama na yawo a zuciyar ta sai kawai ya hau bayani because ya san ko yayi shiru he owe them an explanation..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button