KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
“Ammy,Hajja,Daddy ku yafe mana ba fushin ku muke so ba a yanzu,albarkar ku zai fiye mana dan in har babu albarkar ku auren nan namu da muka yi ba zai yi tasiri ba”!!dum gaban daddy da Ammy ya bayar jin wai har sun yi aure ba wai zasu yi ba but how??..
“Ni da Hamida mun gudu ne dan samarwa zukatan mu abin da muka daɗe muna muradi kuma shine auren junan mu ba auren mabambantar ra’ayoyin mu ba da aka zaɓar mana”!cutting nasa Ammy tayi a tsawace ta ce
“Mabambantar ra’ayoyin ku da aka zaɓar maku,Mufidar ce ba ra’ayin ka ba”?shima a hanzarce ya maida mata da amsar
“Yes Ammy,Mufida was never my choice,Hamida ce zaɓi na kuma ita na so tun asali”!!kan su ne ya ɗaure sai kawai Khalid ya cigaba da maganar sa
“Eh Ammy,Hamida ce zaɓi na ba Mufida ba”wani tsawa Ammy ta daka mai but sai daddy ya dakatar da ita dan cin ribar zancen dan haka ta haƙura tayi shiru nan fah Khalid ya hau warware masu ai tun kafin su haɗu a ranar da su Hamida suka taho nan Nigeria shi ya riga da ya san ta kuma sun san juna haka suna soyayya toh da suka yi realising cewa su ɗin families ne sai abin ya ƙara ƙarfi dan haɗuwar su a wata experience ne da ita Hamidar ta tafi yi a ƙasar Cyprus sai suka haɗu toh shine suka ƙulla alaƙa wanda daga baya ya girma for almost a year,a ranar da suka haɗu kuma a airport sai basu sami damar bayyana kan su ba a matsayin waɗanda suka san juna ba,abu ɗaya da ya shiga tsakanin alaƙar su ta soyayya shine shigowar fifi rayuwar su,duk yadda fifi ta ɗau alaƙar tasu ba haka bane shi a wurin sa dan ya fi ɗaukaka relationship ɗin su a matsayin ƙanwar sa ta jini kuma twin sister ɗin macen da ya fi so a rayuwar sa..
Ana haka suna soyayyar su a ɓoye ba tare da sun bayyana ba akan suna jiran right time su kuma basu sani ba ashe iyayen nasu na hango masu wani abu ne daban..
A cewar Khalid,ranar da labarin ya riske su ne shi da Hamida suka hau nemar hanyar hana faruwar auren amma lokaci ya ƙure ba yadda suka iya sama da bariwa Allah komai dan in suka ɗaukaka maganar toh hankalin fifi zai tashi kuma ba lallai bane a yarda a bar su su mallaki junan su ba,shi yasa suka yi shiru kawai but ganin lokaci na ta gabatowa kuma ba lallai bane su mallaki junan su ba sai kawai suka yanke shawarar guduwa a rana bikin ba tare da sun bari an gano su ba dan kar a yi yunkurin nemo su ba tare da sun mallaki junan su ba..
A jiyan bayan gudun su ne suka tafi wani wuri aka ɗaura masu aure kuma yanzu da haka suna a matsayin mata da miji ne..
Yana rufe bakin sa hawayen dake maƙale idanun Ammy ya zubo Hajja kuwa kasa ko da motsi tayi sai Ammyn ce ta kalli Khalid ta ce da shi ya matsa mata ta ga fuskar Hamida,cikin sanyin jiki ya matsa mata sai ta ɗan tako kusa da ita ta tsaya ta ƙare mata kallo sannan ta buɗi baki cikin sanyi ta ce
“Ta ya aka yi ke kika fita kika bar gidan nan ba tare da mun sani ba”?shiru Hamida tayi daddy na kallon ta da sauraron ta,sai da Ammy ta kuma maimaita tambayar ta sannan Hamida ta ce mata
“Ammy a lokacin da ake ƙara yiwa fifi kwaliyya ne bayan an gama yi min nawa,toh na ga hankulan mutani na kan ta ana ta ɗaukar hotuna sai na ɗau hijabin ta na saka na janyo shi ya rufe min fuska,shine na sauko na bi hanyar ƙofar baya na fita a nan na ga yaya Khalid cikin wani taxi sai ya ɗaga min hannu na tafi na same shi muka tafi inda aka ɗaura mana auren toh a gidan limamin muka kwana ni na kwanta a ɗakin matar sa shi kuma ya kwana a ɗakin baƙi,sai yau da safe muka ɗau hanyar dawowa gida dan mu nemi yafiyar ku”!!kai ayar bayanin ta yayi daidai da isowar daddy gaban ta a harzuƙe abin da bai taɓa yin sa ba,ɗaga hannun sa yayi da nufin marin Hamida cikin ɓacin rai da raɗaɗin zuciya yayin da ita kuma ta runtse idanun ta tana jiran saukar marin dan ta shirya masa tuntuni..
Muryar fifi ne ya dakatar da daddy daga aiwatar da abin da yayi niya..
“Daddy dakata…,please”!!muryar ta a karye ta jawo hankalin sa abin da basu sani ba tun zuwar su Hamida gidan akan idon ta ne har kawo wannan warwararriyar bayani nasu duk tana ji kuma tana kallon su..
Ƙarasa saukowa tayi sai Khalid ya kawar da kan sa gefe Hamida kuma ta saci kallon fuskar fifi amma sai ta ga babu hawaye face tawakkali..
Riƙo hannun daddyn nasu tayi ta saukar tana girgiza mai kai alamar kar yayi komai ya bar shi kawai..
“Daddy babu abin da zaka yi da zai sauya destiny ɗin mu,ko ka manta jiya da kan ka ka min nasihar matar mutum bata wuce sa dan haka ƴar uwa ta Hamida ita ce matar yaya Khalid ba ni ba kuma Allah ya san da haka dan shi ya tsaro mana hakan a rayuwar mu dan haka daddy,Ammy da Hajja ku yi haƙuri abin da zai faru ya faru bamu isa mu sauya sa ba ok”?ta ƙarasa da murmushin dole wanda ya karya zuciyar Khalid sai ta kalle su ta ce da su
“Na taya ku murna ubangiji ya dawwamar da farinciki a rayuwar ku”!!tana kaiwa nan ta juya ta koma ciki,duk jikin su sai yayi sanyi fifi dake haba haba da mutani babu ruwan ta da damuwa dan ta san ko ta sakawa kan ta ba lafiya ce da ita ba,wai yau ita ce ta komo haka…
Kasa aiwatar da komai suka yi dan duk inda maganar kamun hankali yake Mufida tayi sa,hukuncin su ba komai zai gyara ba sai dai ya ɓata dan haka Ammy ta kalle su ta kuma tana girgiza kan ta kafin ta ce da su
“Sai ku tafi apartment ɗin shi Khalid ɗin Allah ya bada zaman lafiya”!!dama an gyare two apartments ɗin da na Khalid da na yayan sa Saheeb so amare kawai ake jira su tare…
Bayan Ammy ta gama magana ta juya abin ta daddyn su kam baya jin ganin fuskar Hamida bare ya mata fatar da Ammy ta masu dan haka wucewar sa yayi haka Hajja ta tashi itama ta bi su da kallon ta girgiza kai sannan ta wuce..
Ƙarshe komawa apartment ɗin Khalid ɗin suka yi inda suka tare a matsayin ma’aurata even though akwai matsalar family dake kan su hakan bai hana su raya daren ranar ba…
A fannin fifi kuwa wuni tayi cikin zugin zuciya da rarrashin kan ta wanda abin ya ishi su Hajja har Ammy ta ce mata
“Mufida ki ɗau shawara ta a ɗaura maki aure da yayan ku Saheeb dan kina buƙatar mai kula da ke fiye da wanda mu muke maki a yanzu duk da ya zo jiya amma ya koma immediately auren ku na iya faruwa in ya so daga baya in ya dawo sai kuyi assuming duties ɗin ku ko ke ki bi sa can inda yake kin ji”?Hajja tayi na’am da wannan shawarar dan haka ta gyaɗa kai ita kam fifi ba a hayyacin ta take ba sai ta saka murmushin dai mai galabaitar da zuciya ta ce
“Ammy duk yadda kika yi zaɓin ki daidai ne a gare ni kuma ni zan maki biyayya sbd nariga na rasa zabina har abada Don kuwa ko mutuwa hameeda tayi Khalid ya haramta ga rayuwata har abada,
Farin ciki da rayuwar auren danake fata da buri har abada na rasashi”!!?rungume ta Ammy tayi ba tare da ta bar hawayen idon ta ya fito ba tace”
Khadija da yardar Allah aurenki da SAHEEB sai kinyi kukan farin ciki domin saikin kasance cikin Mata masu Saar aure.
‘dan juyowa tayi takalli hajjn idanuwanta na cikowa da hawaye tana maidawa tayi murmushi mai tsananin ciwo ahankali can qasan maqoshi ta furta”
Mai matan???
Nida bantaba Sharing komai arayuwataba sai iyayenmu shine yanzu zance cikin tsofi muna gogayyar miji nida matarsa.
Har dare suna tare da ita suna bata magana da ƙyar dai bacci ya ɗauke ta,Ammy ta sanar da daddyn su tunanin da shawarar datayi da alhaji Abbas wani qaninta namiji daya rage Mata shima ya manyanta sosai
Akan mganar auren saheeb da fifin
ya ce in dai ta yarda shi bai da matsala Dan shima kam zaiso auren fifin da saheeb dama tun farko shi sukaso hadata dashi Amma ganin yanda take da Khalid yasa sukace shi din sbd ganinsu so ne atsanakin nasu Ashe ashe,
albarka Hajja ta saka mai dan yayi jarumta da tawakkali..