KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Zan nuna baqin cikin danai shekaru Ina boyewa tareda dannewa Ina qunsa kodan Su girba abinda suka shuka
I’m sorry my Fifi.
Kuma murmusawa Hamida tayi tana sauke ajiyar zuciya haɗe da furzar da iska daga bakin ta..
Tapping bayan fifi tayi ba tare da ta ce mata komai ba har sai da fifi ta buɗe heavy eyes ɗin ta ta ɗora su kan fuskar Hamida dake ta baza murmushi..
Tashi zaune Mufida tayi tana gyara hijabin jikin ta sannan ta zauna bayan ta matsa nesa kaɗan da Hamida..
Kallon behaviours ɗin ta Hamida tayi sai ta taɓe baki tana ɗan yin fari da ido unexpectedly sai kalmar zuciyar ta ya fito sarari..
“Na ji an ɗaura auren ki da…yaya Saheeb wai ko”!?ɗago kai Mufida tayi ta kalli Hamida sai ta ga sai murmushi take ta yi babu alamar damuwa a fuskar ta..
“Toh nothing big,kawai zuwa nayi na musamman dan in maki fatar alkhairi da samin miji irin naki wanda ban taɓa gani ba tunda nake a rayuwa ta ina maku fatar samun zaman lafiya mai ɗorewa har ƙarshen rayuwar ku”!!tana kaiwa nan sai ta miƙe tsaye ta juya leaving fifi to be staring at her kamar stranger..
Ɗan dakatawa tayi bata fitan ba sai ta juyo irin surprisingly ɗin nan ta kalli fuskar fifi,cikin son ƙure haƙurin ta ta ce
“Oh na manta,kina cikin jimami ne shi ya sa kika kasa yi min ni fatar alkhairi da nawa auren amma ba komai na fahimta ai na san ba zaki min baƙin ciki ba da nawa mijin dan bai zamo namijin da ya kwana biyu kuma second hand ba,jini ne ke yawo a jikin shi sabo fil yana ji da ƙarfi dan akan gaɓar sa yake lafiyayye ne ya haɗa duk abinda nake burin miji na na aure ya haɗa and guess what?i have been appreciate him for everything,though na tausaya maki ƴar uwa ta da kika yi rashi rashin da har abada kin yi sa dan ke da sanin dadin aure ina ga sai ko a aljanna in ana yi but a nan duniyar kam,
I’m sorry Fifi karkiga laifina laifin wainda suka zaba Mana wannan halinda muke cikine,,have a nice day ahead”!!tana ƙarasawa ta fita tana ɗan dariya haɗe da rufowa Mufida ƙofar ɗakin..
Tunda ta fara yaɗa mata wannan maganganun sai ta sanƙare zaune tana tunanin anya Hamida ƴar uwar ta na jini ce wannan ko dai an musanya mata da wata ne dan bata yi kama da Hamida ba ko daga yanayin maganaganun ta ya bambanta da na Hamida because ba ƙaramin abu ne ke saka Hamida tankawa mutum ba in yayi mata magana,sai ga wannan Hamidar ba tankawa kaɗai tayi ba hasalima ita ce ta janyo maganar kuma tayi sa ta tafi ba tare da ta jira amsa ba,anya wannan ƴar uwar ta ce kuwa?..
Wani sashe na zuciyar ta ne ya amsa mata “Eh ita ce mana ko baki ji tana ta yaba mijin ta bane?mijin da kika daɗe kina tunanin zai zama naki amma a yau ya zama nata,kuma baki ji ta ce she has been appreciating him for everything bane?kenan ita ce dai ƴar uwar taki Hamida ƴar ywar tawainiyar ki”..
Kuka ne mai ƙarfi ya ci ƙarfin fifi wanda ta bar zuciyar ta ya rinƙa tunzira idanun ta suka rinƙa fitar da hawayen,kuka tayi sosai har sai da ta fara shiɗewa sannan ta kwanta ruf da ciki numfashin ta na sama sama da ƙyar ta iya nemo wayar ta ta kira Ammy,jim kaɗan sai ga Ammy ta shigo a rikice hankali tashe..
Samin ta a halin da take ciki sai da ya tsorata ta because ɗazu bata ga kukan da tayi ba bayan ɗaurin auren sai yanzu..
Natsuwar Ammy ɗaukewa yayi ya hau nemo layin family doctor ɗin su akan ya zo ya duba masu Mufida dan al’amarin yana bata tsoro yanzu..
Kafin zuwan doctor ɗin har ɗakin ya cika da Hajja da daddyn su fifi hankalin kowa tashe,duk tunanin su ko auren da aka haɗa ne ya ɗaga mata hankali har ta shiga damuwa irin haka..
Bayan gwaje gwajen da Dr yayi ya san yadda yayi calming Mufida har ta fara bacci sai ya jawo attention ɗin su inda ya fayyace masu cewa ran ta na yawan ɓacin akai akai daga shekaranjiya zuwa yau kuma duk wani mummunar outcome da zai faru toh sune sanadi dan sun san condition ɗin ta amma suke ƙyale ta tana experiencing irin wannan pains ɗin a lokaci kusan ɗaya..
A ƙarshe wasu special bulk laxatives ne ya rubuta masu da wasu magungunar akan su samo mata dan su zasu rinƙa taimaka mata in ran ta ya ɓaci tunda su iyayen sun kasa samo mata kwanciyar hankali…
Bayan tafiyar sa Ammy ta zauna a gadon ta dake bacci ta rungumo ta jikin ta ta rinƙa kuka tana maganganu wai ta kasa samarwa ɗiyar ta farincikin da take so she feels like she failed as a mother..
Daddyn su da niyar sa ya koma tun jiya in da komai ya tafi yadda ya kamata,amma faruwar wannan abin ya sa dole ya zauna a nan ɗin duk da ya so ya koma gidan sa a nan Nigeria ɗin amma condition ɗin fifi bai yi warranting nasa matsawa ko nan da can ba…
Hajja ce ta rinƙa rarrashin Ammy itama tana share ƙwallar ta cikin tsananin tausayin jikar nata dan duk yadda ta ƙiyasta azabar da fifi ke ji a zuciyar ta abin ya fi haka basu taɓa shiga tashin hankali ba irin ta wannan kwanaki duk a sanadin Khalid..
Fifi bata farka ba sai wuraren magrib,buɗe idon ta na farko a fuskar Ammy ne da yanzu ta gama share hawayen ta..
Dama ita take ta kallo tun ɗazu kafin ta farka toh yanzu da ta buɗe idanun ta sai Ammy tayi saurin matsowa kusa da ita ta ɗago ta ta haɗa ta da jikin ta tana bata haƙurin laifin su ita da Hajja haɗe da yi mata alƙawarin in har ta ce bata son auren nan yau sai a warware sa dan da zaman rayuwar takura gwara zaman ingantaccen rayuwa.
To Ammy’s greatest surprise sai fifi ta ce a’a kar a ma auren komai a bar shi Allah ne ya sauko mata da wannan jarabtar a daidai wannan lokaci dan ya gwada imanin ta kuma ba zata kaucewa wannan jarabta ba har sai ranar da ya ƙare…
Zantukar ta ba ƙaramin daɗaɗawa Ammy zuciya yayi ba sai ta ji wani sabon so da ƙaunar ta ya shiga zuciyar ta bata taɓa ganin yarinya mai tawakkali kamar Mufida ba wannan ya sa ita kuma tayi alƙawarin kare ta har iya inda ƙarfin ta ya ƙare…
Ita Mufida a zuciyar ta tana jin raɗaɗin abin da ƴar uwar ta ta mata ɗazu amma ta danganta hakan da ƙaddarar ta ne kuma bata isa ta sauya nata ƙaddarar ba ko da kuwa hakan na nufin saɓawa Ƙaunar da take yiwa Khalid ne da ƴar uwar ta…
Tun daga ranar Ammy ta maida kular fifi ɗakin ta komai nata ya dawo sashen Ammy cin abincin ta shan maganin ta ruwan shan ta hatta da murmushin ta Ammy na kula da shi dan kar su rasa ta ba tare da sun shirya ba…
Kimanin kwanaki bakwai kenan komai nata baya tsallake sashen Ammy tana iya cewa tun ranar da Hamida ta zo ɗakin ta ta mata wannan maganganun bata sake ganin ko shadow ɗin ta ba har yau kuma hakan ya fiye mata dan tana tsoron haɗa ido da ita bata san me zata kuma jefar ta da shi ba..
Khalid kam bata gan sa ba kuma bata son ganin sa dan ganin sa daidai yake da karayar zuciyar ta ita kuma ba so take ta cigaba da saka iyayen nata da kakan ta cikin damuwa ba akan ta sake jiki tayi kamar ba abin dake damin ta duk da ba kamar old self ɗin ta ba magana jefi jefi take yin sa ba sosai ba amma a cikin maganar sai ta saka abin da zai ba mutum dariya ko kaɗan ne but ita ba zata yi dariyar ba sai dai ta ɗan murmusa a hakan ma family ɗin nata na jin daɗin sauyin da suka gani tattare da ita….
Mamuh16
Yau da farinciki fifi ta tashi so tun safen ta yi wanka
ta saka doguwar rigar ta cikin waɗanda Ammy ta fitar mata a matsayin irin suturar da zata rinƙa sakawa duba da yanayin ya canza da da yanzu ba ɗaya bane,auren wani ne akan ta presently..
Zaman jiran shigowar Ammy ta zauna yi dan ta roƙe ta alfarmar fita zuwa zaga gidan zaman wuri ɗaya ya ishe ta ga ba abokan hira wayar nata ma Ammy ba kasafai ta cika barin ta tana taɓawa ba gudun kar a yi wani kiran da zai ɗaga mata hankali.