KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Jim kaɗan da zaman ta Ammy ta shigo da wani babban tray cike da kulolin abinci da plates har huɗu da kofuna,fuskar ta cike da murmushi ta ƙaraso ciki da sauri fifi ta miƙe ta tarbe ta tana gaida ta da ƙoƙari.
  Zama suka yi kusan a tare fifi na ta yiwa Ammy sannu da ƙoƙari haɗe da tambayar me ya sa bata kira ta sun yi tare ba sai Ammy ta mata nuni da ai bacci take a lokacin shi yasa bata tada ta ba… 
  “Ammy what’s the surprise all about”?murmushi Ammy tayi mata tana shafo fuskar ta sannan ta amsa mata
“Family breakfast zamu yi yau kin sa yau juma’ah ne kuma haka al’adar gidan nan take”!!gyaɗa kai fifi ta mata tana tashi tsaye dan raka ta zuwa kwaso sauran abincin because a babbar falon ta za a ci abincin..

Jere kayayyakin abincin suka yi zuwa wani lokaci sai ga daddyn su da Hajja sun fito aka zazzauna a ƙasan carpet ɗin falon,ganin Ammy na serving ɗin su abincin ya tabbatar mata da su kaɗai zasu ci abincin ban da su Hamida..
  Cikin son juna suka ci abincin suka gama aka kwashi kayan abincin aka mayar kitchen sannan aka koma main parlor aka cigaba da hira inda a cikin hirar ne fifi ta roƙi alfarmar barin ta ta fita dan zaga gidan zaman wuri ɗayan ya ishe ta da fari dai Hajja fargaba ne ya shige ta kar su haɗu da Khalid ta tuno wasu abubuwan da zai ɗaga mata hankali amma ganin kamar ana danne mata hakkin ta da yawa sai ta ƙyale bata ce komai ba..
  Ammy ce ta ce mata ba damuwa sai dai kar ta kai kan ta sashen angon nata ta bari har ya dawo ya zo ayi siyan baki sannan a kai ta..
  Ita dariya ma maganar Ammyn nasu ya bata sai dai bata dara ba ta murmusa kawai tana mai tashi dan fita zuwa zagayen. 

A hankali a natse ta sauko zuwa farfajiyar gidan ta hau tafiyar ta ita kaɗai tana dube dube,duk idanun su Ammy da Hajja na kan ta daga windown sama suna monitoring ɗin ta dan kar wani abu ya faru da ita..
  A haka har ta ɓace masu dan ta zaga wani sashen da basu san hanyar da ta bi ba..
  A zagayen nata ne ta isa wani sashe da bata san ko na waye ba da kamar ta wuce sai ta dawo ta buɗe ta shiga ciki..
Da shigar ta idanun ta yayi mugun gani dan kuwa Hamida ce sanye da kananan kaya tana magiyar Khalid ya miƙo mata abin rufe jikin ta da ya ɗauke shi kuma yana daga nesa babu kaya a jikin sa yana mata wasa da abin rufan yana mata dariya…
  Silently ta koma da baya ta turo masu ƙofar sashen tana danne abin da ya fara ziyartar zuciyar ta tana ƙoƙarin nemar hanyar komawa inda ta fito.

Da ƙyar ta samo hanya ta nufi sashen Ammy,da shigar ta bata tsaya ko ina ba sai cikin bedroom ɗin Ammyn ta kwanta akan gado sai hawaye shar shar tana nadamar bin shawarar da zuciyar ta ya bata akan komawa ta shiga sashen da bata san zai ɓata mata rana ba..
  Kuka tayi sosai sannan ta nemo wayar ta ta kira layin Meena wacce tun ranar bikin ita da yayan ta Ameed suka koma gida basu sami damar ganawa ba..
  Ringing kaɗan Meena ta ɗaga suka gaisa ta ji kamar ta fallasa zuciyar ta ma Meena nan take ta bi shawarar ta hau zayyanewa Meena abin da Hamida ta biyo ta ta mata a kwanaki shida da suka wuce,nan dai Meena ta bata shawarwarin da ya kamata sannan suka yi sallama…

  Kuma nemar layin wata aminiyar ta tayi cikin turawar ƙasar germany da suka yi karatu tare,sai dai bata sami damar yin kiran ba sakamakon shigowar da taji an yi cikin ɗakin nata.
  Ɗago kan ta tayi sai ta ga Khalid ne da Hamida a bayan sa cikin kwanciyar hankali kamar ita ɗin bata da wata damuwa a rayuwar ta abin mamaki twin sister ɗin ta blood ɗin ta..
  Hankalin Khalid tashe ya nemi wuri kusa da fifi ya ɗan tsuguna yana ƙare mata kallon tausayi.
  “Mufida ya jikin ki,ban sani ba sai yanzu Hajja ke sanar da ni da fatar kin sami lafiya”?kallon sa tayi sau ɗaya sai ta kawar da kan ta kawai alamar ba son ganin sa take ba bare amsa maganar sa..
  Ya san dama da hakan dan har yau yana jin wani iri a zuciyar sa akan abin da ya faru a kwanakin nan ya san ba nan kusa zata gafarce sa ba amma hakan ba yana nufin zai karaya bane da nemar yafiyar ta ba..
  Hamida dake kallon mijin nata yana nuna damuwar sa akan ƴar uwar nata sai ta ji wani baƙin ciki ya ziyarci zuciyar ta ga ƙasƙantar da kan sa da yayi yana tambayar ya lafiyar ta ga wulaƙanta sa da tayi abin sai yayi wa Hamida ciwo a rai..
Basu ankara ba ta ƙaraso gab da mijin nata ta saka hannu ta riƙo nasa daga baya ta sauke idanun ta tar akan fifi,cikin calm tune kamar ran ta bai ɓaci ba ta ce
“Ya jikin ki ƴar uwa ta da fatan kin sami lafiya,Allah ya ƙara inganta ki da lafiya sis i really felt bad a lokacin da Hajja ta sanar da miji na abin na damu na so sorry gaisuwar mu ya zo a ƙurarren lokaci”!!ɗago kai fifi tayi ta sauke a fuskar Hamida wacce itama ita take kallo..
Kallon kallo suka aikawa juna daga bisani kawar da kai Mufida tayi tana danne hawayen ta sai Hamida tayi murmushin da ita ta san manufar sa tana tashi riƙe da hannun mijin ta..
Kuma kallon fifi tayi fuskar ta ɗauke da murmushi ta san ko ba komai itama Mufidar na ɗanɗanar kwatankwacin raɗaɗi da zaman kaɗaicin da ta taso ciki tun yarintar su har kawo yanzu..
“Allah ya ƙara lafiya zan dawo in duba ki anjima for now ki ɗan sami hutu kin ji”?ta ida tana ɗage mata gira ɗaya sama..

Kamar ta ce da ita a’a bata buƙatar zuwan ta a karo na biyu amma sai tayi shiru dan maganar tata in ta fito toh kuka ne zai biyo baya..
Kan Khalid a ƙasa Hamida na riƙe da hannun sa suka fita daga ɗakin but kafin su ƙarasa fita sai da Hamida ta juyo ta kuma jefar fifi da wani irin kallon da Mufida ta kasa gane manufar sa..

Fitan su da mintuna biyu zuwa uku Ammy ta shigo tana tambayar yaushe ta shigo bata lura ba,kasa amsa Ammy tayi sai faɗawa jikin ta da tayi ta rungume ta tana ta sauke ajiyar zuciya dan hawayen da ta ƙi bari su sauko..
Kasa fahimtar ta Ammy tayi sai rungume ta itama suka kasance a haka har ta ji kamar fifin tayi bacci sai ta leƙo fuskar ta ta ga idanun ta a rufe,shafa fuskar ta tayi sannan ta kwantar da ita ta fito tana admiring kyawun ta..
Ɗakin Hajja Ammy ta nufa tana labarta mata sauyin yanayin da ta gani tattare da fifi nan Hajja ta fara tunanin ko dai su Khalid sun mata wani abin da ya ɗaga mata hankali ne a dalilin basu permission ɗin ziyartar ta..
Sanar da Ammy tayi abin da ya faru nan hankali tashe Ammy ta ce
“Hajjaa me ya sa kika yi hakan”?kallon ta Hajja tayi cikin halin ko in kula ta ce
“Sun matsa min suna son sanin halin da take ciki musamman shi Khalid ɗin sai kawai na sanar da su inda take ban san haka abin zai juya ba”zama Ammy tayi next to Hajja tana girgiza kai
“Hajja sun ɓata mata rai ajiyar zuciya ta rinƙa yi ta kasa yin kukan bare raɗaɗin zuciyar ta ya ragu bana son ran ta ya rinƙa ɓaci haka Hajja please a kiyaye gaba”gyaɗa kai Hajja tayi because ta gano kuskuren ta..

Tun daga wannan rana Ammy ta ƙara ɗaukar zafi da su Khalid iyakar ta da su amsa gaisuwar su amma abin da ya shafi sakin fuska sam basu samu daga gare ta ba ƙaramin damin khalid abin ke yi ba dan bai saba zama cikin fushin mahaifiyar sa ba sai dai matar sa na iya ƙoƙarin ta wurin ganin ta ɗauke mai hankalin sa ga duk waɗannan matsalolin dake fuskantar su..
Kimanin watanni uku da faruwar wannan lamari amma babu abin da ya sauya hasalima abubuwa sabbi ke faruwa akai akai dan irin secret silent intimidations da Hamida ke yiwa fifi ya wuce tunanin ɗan adam kwata kwata ta sauya kamar ba Hamida ta da ba bata ragawa fifi ko kaɗan amma duk wannan abin da ke gudana a iya tsakanin su hakan ke faruwa bata taɓa yarda Ammy ko Hajja ko mijin ta sun gane tana treating fifi very bad ba secretly bare daddyn su da ya ɗan jima da komawa germany sakamakon business ɗin sa..
Duk tsawon wannan lokaci da Hamida ta ɗauka tana threatening fifi dai dai da rana ɗaya fifi bata taɓa ɗaga kai ta kalle ta ba bare ta tankawa threats ɗin ita iyaka in ta zo ta mata wani lokacin sai ta rufe kan ta tayi kuka har sai ta ji sanyi a ran ta because mostly takan manta da tana da aure sai Hamida ta zo ta mata rashin kirkin ta ta tafi sannan take tunowa da auren nata,bata taɓa faɗawa Ammy ko Hajja ba duk da daddyn su kan kira ta akai akai dan jin ya lafiyar ta amma har su wayar su gama bata faɗa mai wani abin da Hamida ke mata dan ta ɗau hakan a matsayin nata ƙaddarar rayuwar ne..
Some times Khalid kan so ya tubkare ta amma sam bata basa chance kallon sa ma bata ɗaga kai tayi sai dai in ya laƙanci zata zo kusa da inda yake yayi targeting ɗin ta ita kuma ta lura sai ta sauya hanya,bata yarda wani abin ya shiga tsakanin su ba tun ranar da abin ya faru..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button