KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

A halin yanzu da abubuwa suka saka fifi a gaba sai tayi tunanin ɗaukar shawarar ƙawar ta Meena dan kar tayi asarar rayuwar ta duba da yadda family ɗin ta ke ɗawainiya da farincikin ta sai take ganin kamar in ta yarda munanan maganganun Hamida suka yi tasiri a jikin ta toh tabbas zata asararwa family ɗin ta da kan ta..
Bata da wani option sama da ta ɗau shawarar Meena dan haka ta shirya sanar da Ammy ƙudirin ta kuma ta san Ammy ba zata hana ta ba dan ita kaɗai ta san irin ciwon da take ji a zuciyar ta a duk lokacin da Hamida ta zo ta mata magana son ran ta ta tafi…
Mamuh17
Ammy na shigowa ta taso ta zo ta faɗa jikin ta tana murmushi,da murmushin itama Ammy ta tarbe ta tana mamakin farincikin ta na yau dan a kwanakin nan ba kasafai ta fiye sakin jiki tana dariya ko fara’a ba sai ya zama dole.
“Baby me ya faru na ga yau kamar annashuwa kike ji”!gyaɗawa Ammy kai tayi tana lumshe idanun ta har suka zauna kafin ta tafi straight to the point ta bayyana Ammy abinda take so..
“Ammy so nake in koma makaranta tunda zaman wurin ɗayan yakan ɗan ishe ni ba dan bana jin daɗin kasancewa tare da ku ba sai dan ina tunanin tunda ban da wani abin da nake yi a nan sai zaman gida kuma baki yarda in taya ki aiki,so please kar ki hana Ammy komawa ta makaranta zai kawo min cigaba a rayuwa ta fiye da da tunda kin ga bana komai kuma dama ina manta wasu abubuwan amma in na koma makaranta na maida hankali na sai in fito da sakamako mai kyau ko Ammy na”?tayi maganar tana daɗa kwantar da kan ta a jikin Ammyn..
Shiru Ammy tayi tana sauraron ta har ta gama,ba hana ta take son yi ba hasalima jin dadin shawarar nata tayi ko ba komai ba zata rinƙa ƙarar da lokutan ta cikin tunani ba,matsalar yanzu shine wa zai rinƙa kula da ita a makarantar kuma wani irin makaranta ya fi dacewa da ita inda ba za a rinƙa ɗaga mata hankali ba..
Shiru ta sai ya saka fifi jin wani iri a tunanin ta ko Ammy bata yi na’am da shawarar ta bane sai ta kuma lafewa jikin Ammyn tana shirin shagwaɓa..
Murmushi Ammy tayi ta shafo kan ta ta bayyana mata fargabar ta amma fifi na nuna mata ai ba komai ita ɗin ai ta girma ba zata yarda hankalin ta ya rinƙa tashi ba zata kula da kan ta..
Da ƙyar Ammy ta yarda da kalaman ta dan cewa tayi sai an samo mata masu kula da ita amma ta tuɓure akan ita kan ta tayi girman da zata iya kula da kan ta,sai Ammy ta ce mata ba komai dama lokacin siyar da form ne sai cewa fifi zata yi magana da daddyn su duk yadda ake ciki zuwa nan da 2 weeks ta san komai zai kammalu…
Runguma sosai fifi ta kaiwa Ammy tana ta yi mata godiya da fatar gamawa da duniya lafiya,sai da Ammy ta dara ganin yadda fifi ta karɓi ragamar Ammyn ita kuma ta zamo kamar ita ce fifin dan irin adduo’in da fifi ke mata bai da maraba da addu’ar da uwa ke wa ƴaƴan ta..
Throughout ranar fifi ta yi sa ne cikin annashuwa da jin daɗi bata yarda ta saka damuwar Hamida ko wani a ran ta ba,kiran Dr Fatima Yonas tayi ta faɗa mata ai zata koma makaranta kuma burin ta na son zama cikakkiyar ƙwararriyar mai kare rajin haƙƙin ɗan adam wato Human right archivist na gab da cika,murna sosai Dr Fatima ta mata haɗe da fatar alheri da samin nasara a ƙarshe ta tambaye ta ya Hamida take dan sun ɗan jima basu yi magana ba ko ta waya..
Wani abu ne ya ziyarci zuciyar fifi jin sunan Hamida da Dr Fatima ta kira amma sai ta danne zuciyar ta ta amsa mata da tana nan lafiya ƙalau a haka suka ƙarasa hirar tasu suka yi sallama..
Kiran Ameed tayi shima ta faɗa masa ya mata murna da barka tun kafin abin ya kasance,Meena ce mutum na ƙarshe da ta sanarwa shima sai bayan hirar su da suka yi suka gama..
A iya nazari da lissafi fifi ta lissafa kwanaki goma sha huɗu kenan rabon ta da Hamida abin da ko a mafarki aka faɗa mata zata ƙaryata wai ita da ƴar uwar ta ta jini sun zamo ko ga maciji basu yi kuma suna zaune gida ɗaya..
Tun ranar da Ammy ta sa aka yi musayar kayan ɗakin su akan ai kayan fifin aka kai ɗakin da Hamida ke ciki presently ita kuma na Hamida na sashen fifi sai ta sa aka je aka kwashe kaf hatta da akwatinan fifi sai da ta sa aka musanya akwatinan da yake sashen Hamida da ta ƙi aka kwasa aka kai mata wanda su Ammyn ne suka yi na fifi kuma aka dawo mata da su amma waɗanda angwayen suka yi sai ba’a canza ba dan dama an sami sauyin angwayen,toh ranar da Ammy ta saka aka yi wannan kwashen ba ƙaramin ƙiyayyar fifi ta jefa a zuciyar Hamida ba wato ita bata yi deserving abu mai kyau ba kenan,tun ranar da fifi da ta fito ta leƙa ta ga abinda ke faruwa ta ce da Ammy ai ba wani amfani sauya kaya amma Ammy ta ce no sai an sauya ai ita Hamidar rufe ido tayi ta aure Khalid so dan me tunda yanzu itama da nata mijin ba za a saka mata kayan da yake mallakin ta bane,tun ranar da ta hangi Hamida bata kuma ganin ta ba har rana mai kamar ta yau..
Da maganar su da Ammy yanzu ya kai kwanaki tara bata dai san ya ake ciki ba but tana ankare da kwanakin kuma takan yiwa Ammy godiyar ƙoƙarin da take yi akan ta time to time ita kam Ammy bata cika son jin hakan ba dan gani take kamar fifi bata gama sakin jiki da ita ba..
Fannin rayuwar su Hamida ita da mijin ta soyayya ake yi ba ji ba gani kamar akan su aka fara soyayya,duk damuwar family ɗin nasu baya hana su nunawa junan su kulawa da soyayya dan shirin tafiya zuwa wani wurin shaƙatawa ma suke tunda plan ɗin su yayi failing ba yadda suka tsara sa ba akan bayan bikin zasu tafi honeymoon toh yanayin bikin ya sa suka ɗan dakata har sai yanzu da abubuwa suka ɗan yi masu sauƙi..
A kullum dai kafin Khalid ya tafi aikin sa zai shiga ya gaida Ammyn sa da Hajja but iyakar amshin su bai wuce lafiya ba bayan haka babu canji tun faruwar lamarin har kawo yanzu,haka zai tafi aikin sa ya dawo ya kuma shiga gaida su da gida babu bambanci abin na damin sa ba kaɗan ba.
Ko ga kan matar sa Hamida duk haka ne basu sauraron ta ita dai abin bai wani ɗaɗa ta da ƙasa dan mijin ta ya gama yi mata komai tunda ya ɗaukaka soyayya da ƙaunar ta a zuciyar sa da ruhin sa,she doesn’t care about irin attitude da suke bata a gidan..
Tana ƙoƙarin yiwa mijin nata hidima da sauke haƙƙoƙin da ya rataya akan ta na aure,a wannan fannin kam Khalid bai da matsala dan bayan matsalar family ɗin sa da irin ƙibar da zai yi sai ya fi wanda yayi a yanzu.
Bai cire rai ba ya san watan wataran iyayen nasu zasu yi accepting relationship ɗib su da auren su kuma su yafe masu,yana buri da addu’ar zuwar wannan ranar…
Sun shirya tafiyar su dai dai ƙarshen wata wanda yake daidai da lokacin da fifi zata fara zuwa makarantar ta,burin Hamida bai wuce su kai ziyara ɗakin Allah ba a matsayin umara after that sai su zarce zuwa ƙasar Oman dan jin daɗin honeymoon ɗin su.
Zaɓin ta ya zamo na Khalid dan haka ya amince aka yi processing masu visa suka haɗa kayayyakin su ɗan kaɗan a cewar Khalid ta bari in suka tafi can zasu sayi wasu kayayyakin…
Ana washegari zasu tafi Khalid ɗin da kan sa ya shiga sashen Ammyn sa ya gaida ta ta amsa mai kamar kullum sai ya fara nemar yafiya da afuwar ta akan tafiya zasu yi shi da matar sa ya san tana fushi da shi amma ta yafe mai dan ya ga haske a wannan tafiyar tasu duka su biyu tunda tafiyar hanya ce ba lallai bane su dawo a raye in kuma ta Allah ta kasance akan su yayin da take fushi da su ba zai ga rahamar ubangiji ba..
Ba ƙaramin shigar ta kalaman sa yayi ba sai ta ji zuciyar ta na gaza cigaba da fushin da shi abu ne da bata saba yi masa ba,bata da wani zaɓin da ya wuce sassauta fushin nata ta mai addu’a shi da matar nasa ta masu fatar alkhairi da farinciki mai ɗorewa a rayuwar su..
Kasa natsuwa yayi sai ya je ya rungume ta yana murna kimanin watanni uku kusan na huɗu kenan Ammyn sa bata sauraron sa yau ta saurare sa sai ya ji kamar an sauke mai nauyi a zuciyar sa..