KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Ko da aka sanar da Hajja bata wani yi freaking out ba sai addu’ar Allah ya kai su lafiya ya dawo da su lafiya that’s all so duk da bata sauya ba amma ya ji daɗin addu’ar ta gare su..
Next target ɗin sa shine ya gana da fifi ya roƙe ta dan gani yake ko Ammy ta yafe masa haƙƙin fifi dake kan sa kaɗai ya isa ya hana sa jin daɗin rayuwar sa da Hamida amma duk iya ƙoƙarin sa na son su haɗu haƙar sa bata cinma ruwa ba dan Mufida bata da lokacin su tana can tana murnar samin gurbin karatun ta a Abuja university da lectures date ɗin ta fixed sati ɗaya mai zuwa,jin daɗin wannan gurbi da ta samu bai bar ta ta saurari labarun su Ammy ba bare ta san me labarun nasu ya ƙunsa ba..
A washegari tun asubahi jirgin su Khalid ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki sun tafi cike taf da adduo’in Ammy da na daddyn su Hamida da Khalid ɗin ne dai ya kira ya sanar da shi dan jin ko zai sassauto shima duk da dai dama ba wani ɗaukar zafi yayi sosai ba irin na su Ammy ba…
Wuraren 8am fifi ta fito cikin shirin ta na tafiya makaranta inda ta sami su Ammy zazzaune ana cin breakfast ga nata nan rufe ana jiran zuwar ta..
Fuskar ta ɗauke da fara’a ta ƙaraso tana gaida su,suna amsawa tana zama cikin sauri ta tambaye su ya daren su suka amsa da lafiya..
Sauri sauri ta ci abincin ta tashi wai zata tafi sai Ammy ta aje spoon ɗin ta tana kallon ta da mamaki
“Baby ina zaki tafi ba ki kammala cin abincin ki ba fah”!dariya ta ɗan yi ta zo ta bayan Ammyn ta rungume ta tana mata kiss ta ce
“Ammy na duba lokaci ki gani tara saura kuma ina da first lectures ɗi na by 10am beside na ƙoshi sosai kuma in ma yunwar na ji ai zan nemi school cafeteria in ci abinci sannan in cigaba da attending lectures ɗi na”!!a dame Ammy ta miƙe tana faɗin
“Wait for me ina zuwa”!bin ta da kallo fifi tayi tana jinjina irin ƙaunar da take mata sai Hajja ta yafito ta da hannu,saurin ƙarasawa tayi sai tayi murya ƙasa ƙasa ta ce
“Kin san Ammyn ku,abinci ta je kawo maki,kar fah ki bari karatu ya sha maki hankali ki ƙi cin abincin dan tun jiya take ta haɗa maki ta ce ƴar ta zata fara zuwa school dole ranar farkon ta ya zama abin tarihi a rayuwar ta dan haka ta dage ta maki girki mai daɗi so ki tabbatar kin ci abincin kar ki dawo da shi ta gani kin ga ai ran ta ba zai yi daɗi ba ko”?gyaɗa kai fifi tayi tana murmushi haɗe da jin son Ammy na kuma shigar ta..
Suna haka sai Ammy ta fito da wata ƙaramar basket mai cover ɗauke da food warmer da wani watter bottle kamar na ƴan primary school..
Yau da Mufidar da ne da ta tsaya ta yi dariyar ta son ran ta dan wannan shirin Ammyn shirin ƴan primary ne amma kasancewar rayuwa ta sauya ta zuwa ɗaya fannin ta sai kawai ta murmusa ta ƙarasa ga Ammyn ta amshi basket ɗin tana mata godiya da alƙawarin zata cinye abincin duka..
Har bakin mota Ammy ta rako ta da Hajja suna mata addu’ar nasara a ranar farkon ta sai da Ammy ta gargaɗi drivern da yayi tuƙi a hankali daga nan gida zuwa cikin university ɗin ba doguwar tafiya bace dan haka kar yayi gudu da fifi su tafi a hankali…
Murmushi kawai Mufida ke ta yi masu dan suna bata dariya da over protectiveness ɗin su,waving nasu tayi suka maida mata motar ya tashi suka fita su kuma suka dawo gidan suna tattauna yanayin rayuwar gidan da ya sauya ba yadda suka so ya tafi ba kafin bikin..
A nan Ammy ke ɗago zancen Saheeb akan ya kamata ya zo su ga juna da fifi ko da sau ɗaya ne in komawar zai yi sai ya koma amma ya zo ya gan ta damuwar ta kenan,Hajja ma ta matsu ya dawo dan tayi kewar sa ba kaɗan ba..
A fannin fifi kuwa tana iya cewa ranar ta na farko a makaranta rana ce da ba zata taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwar ta dan abubuwan al’ajabi,ban mamaki da ban dariya ta rinƙa gani wanda a germany bata taɓa experiencing irin wannan school life ɗin ba kasancewar can kowa minding business ɗin sa yake yi amma nab ko baka da niyar magana wani sai ya saka ka yi..
Ƙalau ta ida lectures ɗin ta aka dawo da ita gida,tun daga farfajiyar gidan Ammy ta san an sami nasara a makaranta..
Biyewa fifi tayi ta fito tana amsa kiran ta,rungume Ammy tayi ta hau labarta mata abubuwan ban mamakin da suka faru a idon ta yau,ita da Ammy suka rinƙa dariya sai farincikin Ammy ya ninku ya ɗare na fifi duba da yadda yau kaɗai ta sake tana dariya abin da ta jima rabon ta da yin sa..
Har dare in fifi ta tuno wani abin sai ta rinƙa dariya ita kaɗai kusan kaso saba’in cikin ɗari na damuwar ta ya tafi kuma tayi farinciki da faruwar hakan..
Bayan sun gama dinner ta je ta kwanta har ta riga Ammyn bacci a cewar ta ta zamo ƴar makaranta dole ta rinƙa minimizing time ɗin ta kar ya rinƙa tafiya ba tare da ta aiwatar da abu mai muhimmamci ba..
A kwana a tashi ga mai rai ba wuya,fifi ta cinye semester ɗaya har tana gab da zana jarabawar ta saura sati ɗaya hankalin ta duk ya karkata ne ga karatun ta bata son disappointing Ammy da Hajja duba da irin so da ƙaunar da suke mata she want to make them proud…
Ko da Ammy ta sanar da ita tafiyar su Hamida sai ta share zancen ta masu fatar more tafiyar tasu lafiya ita kuma tayi facing damuwar ta dan bata so ta fara jarabawa da layin baya duk da ma bata san nature ɗin jarabawar nan ba amma ta dage sosai sai shirya mai take da makaman karatu..
Rannan da dare tana karatun ta misalin ƙarfe ɗaya na dare sai Ammy ta farka ta gan ta gaban littafi saman table abin sai ya dami Ammy ta taso ta zo ta rufe littafin,ɗago kai fifi tayi sai ta ga Ammy ta ɗan ɗaure fuska sigar kar ma fifin tayi tambayar dalili ko magiyar a bari ta ƙarasa..
Bata jira ta cewar ta ba ta ja hannun ta ita kuma tana murmushi ta bi Ammyn,Ammy bata dakata ba sai kan gadon ta inda ta saka fifi kwanciyar dole ta rufe ta ta je ta kashe wutar ɗakin ta bar na gefen gadon ta ce da fifi
“Go to sleep dare yayi”gyaɗa mata kai tayi tana murmushi mai sauti sai kuma ko me Ammyn ta tuno bayan ta juya baya ta kuma Juyowa ta kalli fifi da idanun ta biyu ta ce
“Baby yayan ku zai dawo nan da kwanaki uku kuma sashen sa na buƙatar gyara ina tunanin assigning wasu su mai gyaran amma babu yarjewar ki shi ya sa nayi delaying dan na ga hankalin ki na kan karatu kar in takura ki ya kika gani kin yarda su shiga su yi gyaran”?kasa fahimtar Ammy fifi tayi ita meye haɗin ta da Khalid da ake nemar permission ɗin ta wurin gyara masa sashe sai ta dubi ta ce
“Ammy ai matar sa zaki tambaya ni ina ruwa na da sashen su”!kallon ta Ammy ta yi sai ta ce
“Da zan so hakan amma matar nasa ba sanin wurin baccin sa tayi ba bare lafiyar sa tana can wani ƙasar daban but ke da kike nan nake nemar yarjewar ki”gaban Mufida ne ya faɗi jin zancen Ammy..
Wai ashe da ita ake yi da aka ce yayan su zai dawo,kaf tunanin ta ya ta’alaƙa akan Khalid ne,ashe wai nata mijin ake nufi.
Dafe goshi tayi ta kalli Ammy sai ta juya mata baya kuma gaban ta na cigaba da faɗi,Ammy sai tayi tunanin hala kunya ce ta kama fifi sai ta ƙyale ta ta kashe hasken dake gefen ta ba jimawa bacci ya ɗauke ta,ita kam ko gyangyaɗin kasa zuwar mata yayi fargaba ne tattare da it da alhinin irin yanayin mijin nata da zata gani in ya zo ohh ita Mufida auren tsoho bata taɓa mafarki ba da ƙyar dai baccin ya ɗauke ta bayan doguwar tunane tunane…