KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

” ya bita da hararar jan kunne yace sit down,tana xama kuwa ta fashe da dariya duk ajin suma suka dauka da dariyar.

Wani hakurin ta sake bayarwa wannan karon da kyar dai aka agama practical din nan tare da ita cikin lumana…

Khadijat mufida nuhu mande,itace dalibar data fi kowa kokari a set dinsu duk dama bata dauki duniyar nan abakin komai ba,rayuwar ta kawai takeyi bata taba tsaurara tsanani akan dukkan lamarin ta ba.

Duk abunda xai bata nishadi da jin dadin rayuwa bata wasa da shi,great sense of humourn ta wajen iya mu’amala da mutane ya sa kusan kowani dalibi a makarntar ya san da zaman ta.

“Fifi mande” shine nick name din da kowa yake kiranta da shi tun suna shekarar su na farko,sosai sunan ya zaga ko ina in baka san ta dan wani abu ba dole zaka san ta dan wani abun dan duk inda shakatawa dajin dadin rayuwa yake to ita ne akan gaba

Aguje take biyo maheeda abaya dake tafiyar ta cikin masifa tana kukkuni

Mahee..maheeda pls now,juyowa maheeda tayi a masife Tace da Allah malama dakata min
Sau nawa na kira wayar ki?

Tace sau takwas..

Wani angry face maheeda ta sa tace and?…
matsowa kusa da ita tayi ta kama cheeks din ta tana mata murmushi tace and dady ne ya jawo komai wallahy…kinsan wani abu mahee?

Maheeda dake mugun son jin gulma tace what?..yatsinawa fifi tayi cikin iya zolaya tace nothing..in kina son ji ki biyo ni cike da takun ta na rigima ta wice gaba maheeda taja tsuka ta shiga biyo bayan ta..

Hadadden student cofee stall ta nufa nan take tayi odering kofuna biyu na shayin dayafi kowanne jin kayan hadi da dadi da tsada..

suna sha suna yar hirar su ahaka basa yin minti 10 batare da wani ko wata ta katse su da gaisuwa ba

dake mufida kusan favourite din kowa ne a makarantar so duk inda ta xauna sekaga mutane suna son mata magana in one way or the other,wani ajiyayyan numfashi ta saki tace wa maheeda gurl friend saura kwana nawa mugama karatun nan ma?Mahee ta yatsina idanun ta ta zuki shayin ta da alaman rashin kulawa,can tace 1 month i ques,wai meye ne zaki fada min kinsan na matsu inji kike ja min rai?..,dariya fifi tayi tace calm down dama nasan matsalar ki ai sarauniyar son jin gulma ..mahee tace whateva nan mufida ta matso kusa kamar me neman mata yar tsegumi tace ke maheeda ki shirya wannan karon ina so muyi abun da babu wanda ya taba yi a ranar graduation dinsa

Maheeda Tace kamar yay fa?

Tace i mean party ina son in hada babban get togher da ni da dukan abokai na amma kafin nan ina son muje yawon
Shakatawa ina son sauran ragowar college time dina ya zamto wanda bazan taba mancewa da shi arayuwata ba

..Maheee ta ce ehem?karatun fa?tace ohhh mance da wannan zamuyi catch up,.mahee dagaske nake miki
I want to go wild maheeda tace ure alwys wild,tayi kwafa ta maida bayan ta kan kujeran cikin dauke numfashi tace wannan karon ina nufin”wildest”..

Mahee tace hmmm to me kike shirya mana ne haka? shiru tayi sanda ta karashe shanye shayin ta tas sannan tace alot. Starting from today?..maheeda ta dan dube ta tace and hamida?

Tace oho wallhy bansan ko zata amince ba amma zan tabo ta inji,tace i hope she did nan suka gama yar hirarrakin su suka watse kowa ta nufi gida

Kafin satin ya kare ita da kawarta maheeda da meena yar gidan dr fatima yonas datake daukar ta kamar yar uwan ta da duk sauran gang na friends din ta suka taru suka harhada
Nau’i nau’i na shirye shiryen yadda zasu more rayuwar su a cikin wayannan kwanaki.

Ameed dake shi doctor ne so bai ciika samun lokacin kansa ba amma da shike yana matukar kaunar fifi hakan ya kukkusa ya mata alkwarin samun kulawar sa a dukkan wayannan kwanakin

Fifi tana sane da cewa zasu bar germany zuwa nigeria maybe na har abada amma se ta barshi aranta batare da ta nuna ma kawayen ta ba

bayan tawainiyar ta hameeda da dad dinsu dr fatima ce da yayan ta Ameed da meena suke da masaniya akan tafiyar sun ahakan ma tanajin dan babu yadda ta iya ne,aranta ji take kamar in ta rabu da germany hala tayi tafiyar karshe kenan na har abada waya sani ko ma a nigeria zata mutu.

Tun daga lokacin takanyi abune ta inda kowa zaiji matukar nishadin wanda tasan hala bazasu taba mancewa da hakan aransu ba..

A karo na farko suka shirya fita su biyar yan mata maheeda meena harda hameeda da wasu kyafaffun yan mata guda biyu wato yesmin da arsala dukan su kowa tanajan sport car kaloli mabanbanta

Awani katafaren resort suka sauka ita da kawayen shakawatan nata All girls out so basu gayyaci wani namiji ba

ita yesmin yar gidan wani turkish tycoon ce arsala kuma brazillian ce gaba daya baya

Daga yanayin dressing dinsu zakasan suna matukar ji da wani abu waishi kyau kyaun jiki da asalin wayewa na iya kwalliya da daukar wanka uwa uba dukiya da wadata

Dukan su sanye suke da crazy jeans da brigt colour tops
Da manyan manyan sun glasses hannun su dauke da jakunan rataya na bvlgari wayayoin su masu tsadan gaske

saidai iya kokari sunyi wajen lullube kawunan su da muflers wasu da kananan veils wasu da hoodie ta inda da kaci karo da su dole zaka san cewa sudin musulmai ne

Kowaccen su ta sha kwalliyar ta na kece raini amma banda hameeda dake sanye da Egyptian jallabiya da pure red veil tayi roling kamar wacce ta fito masallaci

Tun suna gida da ta fito cikin nata haddenen shirin irin nasu fifi daddy ne ya umarceta data je ta sauya dresing dan dole.

Batayi musu ba tabi umarnin san amna Se ta ga mufida ta fito a kile amma bai ce mata uffan akan nata shigar ba and of course ta san bazai wuce dan yana gudun bata mata ranta ba ne

Hameeda ita ta fito odd a cikin su tayi daban sekace dukkan wajen ta girme su,shiru shiru zaka ganta kamar wacce bata da nacewa amma azahirin gaskiya zuciyarta ya fara hura wata wutar da takejin hala nan gaba bazata iya sassaita shi ba

wani irin surutayya suke yi a tsakanin su wanda ya nuna tsananin shakuwa jin dadi da hadin kai
Amma zuciyar hameeda cike yake da sake sake ganin dukan hankalin kowa akan mufida yake,ita kam ma har mancewa da zamanta awajen akeyi,a duk sanda akayi abun dariya ita murmushin karfin hali takeyi

Abu daya yake damun hameeda acan kasan ranta amma bata son bayyana ma kowa dan bata san tana ina zata fara ba.

Shin su dady basa kaunar nata farincikin ne ko ita ba yar su bace rayayya kamar yar uwanta fifi?
Cikin Wannan tunanin ta tsunduma sosai har aka kammala outing din kowacce ta shiga motar ta bata san anayi ba.

Tuki takeyi ita kadai tamkar wacce gangan jikin ta ne kawai ke motsi hankalin ta ya nitsa ne wajen tuno da asalin ciwon dake cin zuciyarta a kullum yana mata zugi.

mamuhZAFAFA BIYAR NA KUDINE KA NEMI WAINNAN NUMBERS DIN KABIYA KA KARANTA CIKIN AMINCI

07067124863
OR
09032345899

3

Wannan cuta da yar uwarta mufida ke dauke da ita shiya kara rage kaifin kauna tsakanin ta da dukkan wani abu me samar mata da kwanciyar hankli da salama a zuciyar ta

Ta zama tamkar batacciya marar amfani a duniyar mutanen da ta dauke su jigo kuma babban madogara a rayuwa kaunar da duniya take nunawa yar uwarta mufidan wani abu ne wanda za”ace har ta mutu batasa ran zata ci karo da shi ba

Son da mahaifin su yake nuna mata na musamman ne mufida Allah yayi mata baiwar da tasan ita batasaka ran samun irinsa.

Bayan kyau kyaun jiki ilimi wayewa Allah sai ya kara mata muhibba da tsananin farinjini

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button