KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

MamuhMamuhgee

18

Zazzaune suke bisa dinning suna breakfast Ammy sai bin fifi da kallo take dan son gano wani abu amma haƙar ta bata cin ma ruwa ba dan ƙeƙashewa Mufida tayi bata yarda sun haɗa ido ba sai abincin ta da take ta ci tana hira da Hajja suna ɗan ɗariya ƙasa ƙasa.
Suna yunƙurin kammala cin abincin sai Mufida ta ji kamar an tsikare ta wuf ta tashi tana cewa Ammy tana zuwa sai suka bi ta a da kallo har ta haura saman abin na basu mamaki..
  Bayan tafiyar ta ne Ammy ta labartawa Hajja abin da ya faru a daren jiya tsakanin ta da fifi,abin gwanin ban dariya sbd wautar fifin..

Shigar fifi ɗakin Ammy dan ɗauko wani handbook ɗin ta sai kuma kamar ta hango wani dan haka ta dawo da baya ta ɗan yi facing window,nan ta hango clear view ɗin abin da idanun ta ke hango mata a nesa..
  Tsayawa tayi tana kallon sa almost months kenan rabon da ta gan shi,ta dai san last time da Ammy ta mata magana akan sa shi da matar sa shine wai sun tafi honeymoon apart from ranar wata magana mai ƙarfi da ta shafe su bata kuma ji ba..

Ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da kan ta ta ɗau handbook ɗin nata tayi zaman ta a ɗakin bisa kujerar karatun ta ta buɗe tana duba abin da ya faɗo mata ɗazu da take cin abinci har ta kasa haƙura ta tashi..

Kimanin mintuna talatin tana karatun ta bata tashi ba sai da ta kammala sannan ta mayar da littafin ta miƙe ta sauko zuwa ƙasan..

Da zuwan ta Ammy da fara’ar ta ta sanar da ita dawowar su Khalid har sun shigo sun gaida su amma lokacin tana sama so presently Ammy is directing to go and welcome them since da kan sa shi Khalid ɗin yayi requesting Ammy ta bar fifin ta zo dana akwai wani muhimmin abu da yake so ya mata,toh ita dama Ammy tun ranar da ya sanar da ita tafiyar su ta ɗau sassauto da zafin ba dan komai ba sai dan yanayin rayuwa da ganin shi ɗin jinin ta ne…

At first fifi was like scared ne ko fargaba ne na haɗuwa da su dukan ko ya nene bata sani ba,so tana ta son shashantar da zancen amma wani iri tsananin kewar ‘yar uwarta na damunta tundaga qasan ranta sbd tun haihuwansu Basu taba yin nesa da junaba ko banxatar da junaba sai yanzu Wanda tasani kowannensu abin na qwaqwalar zuciyarsa da radadi mai zafi.
tashi tayi ta fita cikin faɗuwar gaba ta nufi apartment ɗin su Hamida tana addu’ar samin sanyin zuciya dan kuwa har ciwo ciwon kai take ji..

Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga main entrance ɗin sashen amma shiru sai ta kuma kimtsa kan ta tayi sallama ta shiga asalin parlor ɗin,this is her first time na shiga sashen haka ta rinƙa bin sashen da kallo tana yaba kyawun wurin tana takawa zuwa ciki a natse..
  Bata san daga ina magana ke fitowa ba amma ta ɗan ji hayaniya da alama ƙaramin sa’insa ne ya kaure a inda hayaniyar ke fitowa..
 
Tsayawa tayi a tsakiyar parlorn tana ƙare ma parlorn kallo a hankali,duban ta ta maida ga wall ɗin parlorn sai ta ga wani babban enlargement mai ɗauke da hotuna kala uku na Khalid da Hamida suna murmushi cikin yanayin jin daɗi..
  Rintse ido tayi cikin faduwar gaba kafin ta juya ta kalli ɗayan nan ma sun yi kyau,haka ɗayan da ta kalla nan ma sun kyau ba kaɗan ba,idanun ta na kan wannan last photo sai ta ji muryar Hamida na faɗin
“Mine ba fah zan yarda da wannan sigar ba fah,na ce wannan nake so amma baka ganewa,hankali na kuma ya biya me ya sa kake son haramta min”!!.daidai sun fito parlorn kenan ana jayayya Khalid na saka wani abu cikin aljihun sa yana ƙarasa fitowa cikin parlorn Hamida kuma na turo baki cikin shagwaɓa da ɗan ɓacin rai..

  Basu san fifi na parlorn ba sai da Khalid ɗin ya gama maganar sa da Hamida cikin ɗan ɗaure fuska.
“Luv amma kin san wancan bracelet mai haɗe da wrist watch ɗin nan na farko da na siyo kin ce kina so,na damƙa maki right?wannan bai maki ba yet this one da na faɗa maki mai shi shima kika ce kina so and you knew ba naki bane,wannan ma ba naki bane duk na mutum ɗaya ne amma na baki ɗayar so why still insisting on this one again?haba Luv be just akan wannan lamarin i just can’t give this one to you”!!rai ɓace Hamida ta ƙaraso cikin parlorn da nufin saka mai rikici da rigima duk dan ya bata dan bata ƙaunar ya mallakawa wacce yake da nufin mallakawa ɗin..

Har ta buɗe baki da zumar fara yi mai rikici sai kawai tayi tozali da fifi dake tsaye tana sauraron conversation ɗin su tana wondering rigimar nasu ko akan menene..
  Wani haɗe rai Hamida tayi ta aikawa fifi wani irin kallon da sai da ya ƙarawa fifi fargaban ta a zuciya amma ta ɗan kawar da fuskar ta ta buɗe baki ta gaida Khalid..
“Yaya Khalid ina kwana”!!nan take ya juyo ya gan ta tsaye sai ya ji nauyin ta hakan ya tabbatar mai da cewa lallai ta ji duk conversation ɗin su dan haka ya sake fuska ya tunkare ta yana amsawa..
  “Zo ki zauna mana kina tsaye yaushe kika shigo”!!wani takaici ne ya mamaye zuciyar Hamida kawai tayi folding hannuwar ta a ƙirjin ta tana bin su da kallo..
  Kasa zama fifi tayi ta tsaya a tsaye tana girgiza mai kai akan ba zata zauna ba idanuwanta nakan hameeda datakejin kaman taje ta rungumeta sbd take taji kamar zata fashe da kukan kewar hameeda din

Khalid ɗin ya rasa ya zai fara yi mata magana akan haƙurin da ya jima yana son bata but sai tayi cutting tunanin sa off ta hanyar ce mai
  “Yaya Khalid Ammy ce ta ce in zo wai kana nema na shine na zo”!!gyaɗa mata kai yayi yana saka hannun sa dan fiddo da agogon hannun da ya ɓoye ma Hamida.

Ai kuwa Khalid na fiddo wannan ƙaramin packed gift box ɗin nan ɗan madaidaici da zumar miƙawa Mufida a matsayin tsarabar da ya siyo mata Hamida ta waro idanun ta,rai ɓace ta ƙaraso gare su ta fauce abin kafin ya gama miƙowa Mufida..
  Rai ɓace tana kallon Mufida cikin tsananin baƙin ciki da kishin dake cin ranta na fifin tsawon shekaru tace’

  “Wallahi a’a,ba zan yarda ba akan wani dalili zaɓi na zaɓin rai na ka ɗauka ka yi ƙudirin damƙawa wata shi alhalin ka san ina so kuma yanzu na gama yi maka magiyar ka bani amma ka ƙi but ka ɗauka zaka damƙawa fifi akan me”!??tsayawa kallon ta Mufida tayi haka shima Khalid ɗin ya bi ta da kallo bai taɓa tsammamin Hamida zata iya bada wannan reaction ɗin ba akan mere wristwatch da bai kai nata da ta karɓa da fari tsada ba..

Bakin sa cike da magana da niyar hana ta cigaba da fiddo maganganun dake zuciyar ta dan wannan maganganun ya san zai yi leading ma wani matsala ne babba dan yana gudun in bai dakatar da Hamida ba yadda ran ta ya fara ɓacin nan toh komai na iya faruwa..
  Bai gama nazarin sa ba ya jiyo muryar Hamida cikin tsantsar ɓacin rai daya fara karya muryanta tana cewa’

  “Ka daina yi min haka rai na na ɓaci a ce kana nawa ɗin ma amma ban da iko da kai ban isa in mallaki abin da nake so ba daga gare ka sai an raba min shi da wata,ta yaya kake tunanin ba zan yi fushi ba?meye hakan”?Mufida na tsaye na kallon yadda ta rufe ido tana faɗa kamar bata san gaban wa take ba..

Hamidar da ta fuskanci jimami fifi ke yi akan maganganun da ta gama faɗa yanzun nan sai ta ƙara fuskantar ta rai ɓace cikin haɗe fuska ta ce
  “And you,,na yi ƙarya ne?ba gaskiya na faɗi ba kike kallo na?komai ba so kike ki mallaka ba a duniyar nan?ko ina kowa kina so ya zama naki mijin nawa ma ban isa in mallake sa ba ni kaɗai sai na raba sa da ke,abin hannun sa da nake so nake kuma da iko akan sa shima ban isa in mallaka ba ni kaɗai sai an ƙidaye min wanda ya cancanci zama nawa all because of you”!!da zuwan Khalid gaban su da jawo Hamida jikin sa bai fi blink of an eye ba..
  Abinda yake gudu ne ke gab da faruwa dan babu irin kishin da Hamida ke yi akan Mufida da Khalid bai sani ba,komai akan irin kishi da haushin Mufida da matar sa ke ji dan haka yayi saurin janyo ta jikin sa sbd kar ta cigaba da maganar amma ina tayi nisa sai fizge jikin ta da tayi tana hana sa kuma riƙo ta dan ba ƙaramin ɓaci ran ta yayi akan wannan abin da,duk da ta mallaki Khalid ɗin amma bata da cikakkiyar iko akan sa akwai abinda ya fi wannan ciwo a ce mijin ka na ɓare ɓaren ba wata da ba matar sa ba kyautar abinda ita da take matar sa ke muradi,ai wannan masifa ce,kenan in ta cigaba da yin shiru shikenan tana zaune tana ji tana gani shi kan sa mijin zai zamo under control ɗin Mufidar kenan since she is the ƴar so…
  Mufida na ƙare mata kallon mamaki dan bata san musabbabin wannan maganganun ƴar uwar nata ba..
  “Ai sarai kin gane me nake nufi kuma me nake magana akai,komai ke jawo sa and you should be asked for that”!!cikin mamaki da fargabar kalaman Hamida Mufida ta ce
  “Me ya faru Hamida”??wani irin kallon banza ta aikawa Mufida da shi sannan tayi ƙwafa ta ce..
  “Tambaya ta kike ko?ok yanzu zan sanar da ke,Mufida you are a thief asalin ɓarauniya mai kwashewa mutum komai,you are a thief who steals what is rightfully hers and not hers,baki da wani abin da ya zama mallakin ki duk sacewa kika yi kika maida sa naki kuma baki da ranar daina satar,you are a thief Mufida”!!dum dum gaban Mufida ya bayar cikin ƙaraje da rashin natsuwa Mufida ta kasa haƙuri ta tari numfashin ta
  “Hamida me na maki da kike aibata ni haka kuma ki rasa irin kalmar da zaki yi amfani da shi wun aibata ni sai da ɓarauniya?me na maki da tsauri haka Hamida”??datse mata maganar Hamida tayi ta hanyar ɗan ɗaga muryarta dake rawar kukan takaici da bacin Rai tace’

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button