KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
“Ai dama ba zaki sani ba Mufida,in tambaye ki mana?ina sbd jin daɗin da kike yi har kasa tantance abin da ya dace ki mallaka da wanda bai dace ki mallaka ba kika kasa zama ki tantance?tukunna a lokacin da kike jin daɗin ai baki san akwai abinda ba naki bane da bai kamata ya zamo naki ba right?everything ke everything ke sbd ke ce fitilar kowa”!!
kuma datse ta Mufida tayi cikin tashin hankali Khalid kam na gefe yayi yayi tayi shiru amma ta ƙi sauraron sa instead ta taso mai da ɓacin rai akan ko ya bar ta tayi maganar ta ko a ji su a gidan yau ɗin nan..
“Hamee wai meke faruwa ne na kasa samo ma’ana a cikin kalaman ki”!!..dakatar da ita Hamida tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tana fashewa da kukan mai tsananin radadi tanafaɗin’
“Save that name for someone kar ki kuma kiran wannan sunar dan baki cancanci kiran sa ba,tsakanin ki da Allah kin taɓa zama kin lura da wasu abubuwan dake faruwa da ke a rayuwar ki?am sure baki taɓa ba dan baki da wannan lokacin you are so occupied da soyayyar family ɗin mu,duk wasu jin daɗi a kan ki ya ƙare ɗiyar so,i cried all years duk a dalilin ki ke kaɗai Mufida,you stole everything komai”!!a ruɗe Mufida ta ce
“Me na sace maki Hamida”!?a tsawace Hamida ta amsa mata rai ɓace
“Komai Mufida,kin sace min komai da nake mafarkin samu,komai da ya dace in mallaka Mufida you own it,can you believe that you have been leaving my dream?
Ni marainiyace gaba da bayana Banda kowa aduniya tunda na rasa mahaifiyata sbd nasan ita kadaice tasan ciwo da zafina bazata taba wareni kamar Mara galihuba,
Banda kowa Banda komai I have no other choice than to fight for myself Kota wace hanyace Koda kuwa ta hanyarda bai dace bane sbd kune kuka bani wannan choice din,
ohh Mufida kin gama sace min komai na duniyar nan kin ƙwace min komai na rasa me na tare maki kika zaɓi yi min haka”!!a ɗan tsawace Khalid ya kira sunan ta
“Hamidaa just shut up”!!itama a tsawace ta mayar mai da
“No ba zan yi shiru ba,gata nan Mufida ce silar faruwar komai da yake faruwa da ni a rayuwa ta,she stole everything for me and i don’t want to forgive her”!!hawaye ne cike taf a idanun Mufida jin zafaffan kalaman da Hamida ke faɗa mata..
Ƙarasowa kusa da su tayi ta tsaya suna fuskantar juna ita da Hamida sai da Mufida ta sauke wata nunfashin kukan zuciya mai nauyi sannan ta ce cikin tsananin rawar murya da rashin ƙarfin gwiwa ta ce
“Hamida ina son sanin asalin abinda na maki a iya rayuwar mu da zaman da muka yi ni da ke”!!wani irin kallo Hamida ta bi fifi da shi sannan ta hau yi mata magana cikin faɗa da haushi..
“Yanzu zan fayyace maki asalin abin da kika min a rayuwa wanda bai da bambanci da baƙin taɓo duk da na so Ƙaunarmu ta ɗore amma kika san yadda kika yi kika datse wannan ƙaunar tamu”!!kuma yi mata wata tambayar fifi tayi gaban ta na faɗi
“Hamee ta yaya na datse Ƙaunarmu“?..
“Ta ko ina Mufida,Mufida kin mamaye min komai,soyayya,kulawa,rarrashi d ƙauna duk kin mamaye komai kin riƙe,ni ba mutum ba ce?ban dace a so ni bane?ban da ƴancin samin gata ne?ke kaɗai ce mutum mai jini a jiki da kika cancanci gata?Mufida tun da muka taso da zuciya ɗaya na riƙe ki a matsayin ƴar uwa ta ta jini ba ƴar uwar dangantaka ba,tun yarintar mu Mufida kika fara ƙwace min abinda nake so,attention ɗin daddyn mu duk ke kika samu ni ban samu ba ban yi complaining ba,karatu ni ba a maida hankali akan nawa ba ke har special classes ake baki a gida ni kuma ko oho dan an fi ƙarfi na ni ban da gata,abincin ki sai an ɗanɗana kafin ki ci gudun kar ki ci ya maki illa ni kuma kai tsaye ake bari na na ci abincin haka,sutura sai wanda kike so kike sakawa kan ki tsaye ba a maki gyara bare a hana ki ni fah?idan zan saka wanda rai na ke so toh sai daddy ya maida ni in canza zuwa wanda ran sa ne ke so i never complained,soyayya da kafa kafa da ake yi da ke kar ran ki ya ɓaci Mufida ni bana samu ni ban taɓa ɗanɗanar sa ba,kaf su Ammy da Hajja da ke suke magana in suka kira a waya dan ke ce tasu ni ko daidai da rana ɗaya ban taɓa ganin kiran su ba ni ba mutum ba ce?ranar da muka iso ƙasar nan imagine wai hankalin kowa akan ki ya komo ni dake tsaye an manta da ni ba a san ni ba sai ke,wai fah har wucewa aka yi da ke aka shige mota za a tafi a bar ni ana ta maki wasa da dariya ana gwada maki soyayyar da family ke nunawa ƴaƴan su da ƴan uwan su,mun dawo gidan nan aka kai ni wani irin pit wai ɗaki aka ce shine nawa naki kuwa kamar ta princess Cinderella komai an tsara maki dan ke ce kaɗai aka sani ake considering a matsayin ɗiya,abinci sai an tabbatar wanda ran ki ne ke so sannan za a girka kuma ba a ci sai an tabbatar kina nan za a jira ki sai kin zo sannan a ci ni fah?wa ya damu da ni wa kuma ya san ina raye bare a ba ni abinci,dawowar mu ƙasar nan ke kaɗai ce kika rinƙa experiencing soyayya da ƙaunar family ɗin mu ni ban samu ba,masoyi na abin alfahari na da nake muradin aure kafin in aura shima aka nemi a baki shi dan ni ban dace da shi ba sai ke tunda ke ce kika nuna soyayyar ki gare sa a fili,auren namu ma a sace aka ɗaura sa dan kar soyayyar ki da kulawar ki ya sami tangarɗa we ran away,muka dawo muka yi bayani a tunanin mu za a yarda da auren amma sai aka juya mana baya aka ɗau fushi da mu dan mun yi tempering da tunanin ki,babu wanda ya damu da mu a gidan nan daddy,Ammy da Hajja duk babu wanda ke sauraron mu akan karon farko da na tashi nayi standing ma right ɗi na,ni ce wacce bata dace da jin daɗin rayuwa ba aka ɗau wani a matsayin wanda za a ba ni tsoho mai mata wanda ni da ke duk mun san irin mijin da nake so,a lokacin da aka ce za a haɗa ni aure da yaya Saheeb Mufida kika maida ni abin tsokanar ki safe rana dare baki tunanin negative impact ɗin da tsokanar ki ke min a ƙwaƙwalwa ta kawai ana nuna maki so and you think ke ɗin angel ce that deserves everything right?muna nan ni da ke Ammy ta aika aka kwashe duk kayan ki dake sashe na aka maida maki ni kuma aka kwaso nawa aka kawo min,ni da ke ɗin ba abu ɗaya bane?ba uterus ɗaya muka zauna ba?ba rana ɗaya aka haife mu ba?komai naki ba nawa bane?Ammy ta kawar da fuskar ta akan hakan ta min abinda ta min dan ni ba mutum ba ce i never complained,now miji na ya siyo abu na gani na ce ina so ya bani amma ya hau jayayya da ni akan abinda nake tunanin ina da iko da shi ashe still ban tsira ba Mufida kina nan kina bibiya ta da farinciki na kina yunƙurin ƙwace min,for goodness sake Mufida me zan maki ne a rayuwar nan dan ki rabu da ni hakan nan in ji daɗin sabuwar rayuwa ta??uhum?tell me please”!!hawaye ya gama ɓatawa Mufida fuska kaca kaca haka Hamidar mai magana itama fuskar ta jiƙe yake da hawaye sakamakon tuno da irin rayuwar ƙinci da tayi a baya all because of Mufida..
Numfasa fifi tayi tana kuma matsawo kusa da Hamida ta kawo hannu ta riƙo ta tana tambayar ta murya a karye.
“Hamida yaushe duk waɗannan abubuwan suka faru?ban sani ba baki sanar da ni ba ban taɓa gani ba,Hamida all these happened amma baki tsayar da ni kin sanar da ni ba?why”?fizge hannu Hamida tayi ta amsa mata.
“Yaushe na sami lokacin sanar da ke?kina da lokaci na ne?soyayyar family ɗin mu ya mamaye ki baki da lokaci na baki taɓa lura da yanayi na ba ta yaya kike tsammanin zan iya tsayar da ke in nuna maki wannan abin?already akwai third party a tsakanin mu Mufida tell me how did you think i have been feeling lately all those years”!!kuka sosai Mufida ke yi Khalid kan sa a ƙasa Hamida kam hawayen ne kaɗai ke fitowa amma babu kuka tsantsar ɗacin da ran ta ke mata…
Mufida bata haƙura ba ta kuma matsowa ta riƙo hannun Hamida tana kallon ta ta fara magana da sansayyar murya..