KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
“Amma Hamida for once kin taɓa tunanin kira na ki faɗa min ni da ke?Hamida all my life na yi sa ne ina so maki farincikin rayuwa kamar yadda kike so min Hamida ban taɓa kawowa a rai na wannan kulawar da ake ba ni yana taɓa maki zuciya ba,ban san ana treating ɗin ki a haka ba,zuciya ta da tunani na bata taɓa kawo min ana ɓata maki irin haka ba tun yarintar mu har girman mu,Hamida ban san irin rayuwar da nake yi kike so ba believe me i swear,Hamida kina ganin kamar da niya nake ɗauke kai na akan ki??no, Hamida ban san halin da kike ciki ba,har zuciya ta ban san kina jin zafin wannan abin ba,Hamida ban taɓa lura ba Allah ne shaida na ban taɓa lura da yanayin rayuwa ta mafarkin ki bane,Hamida komai nawa naki ne komai naki nawa ne,ki yafe min na maki katsalandar a rayuwar ki soyayya da kulawar daddyn mu Ammy da Hajja duk na tara a kai na ni kaɗai ban bari kin mora ba Hamida ki yafe min am so sorry and i promise to make it up to you Hamee tun yanzu zan sanar da su Ammy da Hajja su canza su daina saka ki jin irin wannan feelings ɗin am coming”!!?duk a ruɗe take maganar zata juya Hamida ta wani finciko ta a hasale ta ce
“Stop this i don’t like it,ki daina wannan pretence ɗin i hate liars and pretenders,Mufida duk wata so da zai fito daga wurin su Ammy,Hajja da daddyn mu a ƙarƙashin alfarmar ki bana so ki je ki cigaba da more goodies ɗin ki all i want is you to leave me and my husband alone na roƙe ki Mufida ba dan hali na ba na haƙura da jin daɗin family ɗi na dan na san ba zan samu ba sai a dalilin ki ni kuma bana so dan haka ki rabu da rayuwa ta da na miji na please Mufida”!!!a yanzu sosai kukan Mufida ya fito sarari ta kasa ɓoye sa,zafin da take ji a zuciyar ta ya sa ta kasa tsayawa ta juya da zumar kawa sashen Ammy amma sai me..
Ammy ce da Hajja ke share hawaye suna jan hanci abinda ya kuma girgiza Mufida kenan dan ta tabbatar suma sun saurari abinda ya faru sai kawai ta ƙarasa ta faɗa jikin Ammy tana matsanancin kuka tana kuma nanatawa Ammy abinda ya faru Ammy ba abinda take yi sama da kuka mai sauti,hankalin ta in yayi dubu ya tashi bata taɓa kawo maltreating Hamida suke yi ba da soyayyar da suke nunawa Mufida..
Hajja da tayi making attempt ɗin rungumo Hamida jikin ta bayan ta ƙarasa shigowa cikin parlor kawai Hamida ta ture hannun Ammy ta haura sama abin ta Khalid kam ya tsaya ya rinƙa ba su Ammy haƙuri tunanin sa basu ji daɗin maganganun Hamida bane sai da Ammy ta tura sa ya je ya lallaso Hamidar kafin ta kai fifi ɗaki dan kan ta har ya fara sara mata jikin ta na ɓari…
Jiki sanyaye Hajja da Ammy suka koma apartment ɗin su da nadama mai tsanani duk rayuwar da suka yi da su Hamida a gidan nan basu taɓa sanin suna zaluntar ta ba sai yau da ta furta da kan ta..
Abu kamar wasa fifi zazzaɓi ya rufe ta tun safiyar nan har dare haka Hamida sai da ta ji sauyi a jikin ta dan zazzaɓi ne mai tsanani ya rufe ta amma taurin zuciya ya sa ta ƙi yarda Khalid yayi nursing ɗin ta..
Kamar wasa kwana biyu kenan da faruwar wannan abin amma komai ya taɓarɓare Ammy da Hajja ba yadda basu yi ba akan Hamida ta sake jiki da su suna jawo ta jiki amma sam Hamida ko sauraron su bata yi dan ta san fake affection suke nuna mata ba dan son ran su ba..
Rannan Hajja ta ga abin ya fi ƙarfin ta ƙiyayyar kamar ta gama ginuwa a zuciyar Hamida game da ƴar uwar ta sai ta kira daddyn su Hamida tana sharɓe kuka tana mayar mai da abinda ya faru sannan tayi requesting ɗin sa da ya dawo Nigeria ya zo su haɗu su gyara wannan ɓarakar…
A rana na ukun ne da faruwar hakan Hamida ta fito farfajiyar gidan ta tana nemar wanda zata aika ya karɓo mata saƙon mijin ta a sashen su Ammy dan ko sashen ta daina zuwa sbd zafin da zuciyar ta ke mata game da su..
Rasa samin ɗan aika ya sa ta fito zuwa farfajiyar gidan dan nemo ko da driver ne ko mai gadi dan aiken sa..
Tana tsaka da dube duben ta idanun ta ya hasko mata wani mutum daga baya yana taaye hannun sa riƙe a ƙugun sa sanye da sport suit yana bada direction,tsayawa tayi tana kallon mutumin daga baya dan bata san waye shi ba a gidan bata taɓa ganin sa ba..
A sannu mutumin ya juyo a natse cikin kamewa ya fuskanci hanyar ɗaya apartment ɗin dake kusa da nasu
Atake kwarjininsa da haibarsa tareda wani kamewarsa da tsantsar kyawun fuskarsa da fatarsa dake bayyana tsantsar hutu da dukiya data gama kamesa ya cika gurin hartana Dan sauke kanta qasa sbd cika idanuwansa
yana tafe yana amsa waya kan sa direct yana kallon hanyar da zai shiga..
Sbd cikin Daren Koda ya iso baa shiga da kayansaba sai yanxu da safen
Wani irin suman tsaye Hamida tayi ta ƙame tana bin wannan mutumi da kallo da bata san ko wa nene shi ɗin ba,gaban ta ne ke faɗi da ta rasa dalili,ai kuwa tana tsayen sai ga Khalid ya fito da ɗan sauri yana dube dube sam bata san da zuwan sa ba sai ji tayi yana
“Luv kin ga min Marshall ba a ta nan wurin”?
dum ta ji gaban ta ya faɗi jin sunan da ya kira kasa kallon sa tayi sai sashen da take kallon an wuce ɗazu..
Tunowa Khalid yayi akan Hamidar fah bata san Marshall ɗin ba sai yayiwa kan sa murmushi ya ce
“Na manta Luv baki san shi ba am sure ya shige part ɗin sa dan yanzu na hango sa yana wucewa ina kiran sa amma yana waya bai ji ni ba am coming bari in duba shi”!!
tsinkewa zuciyar Hamida yayi jin an kira wannan mutumi da Marshall kenan yaya Saheeb..
“Inalillahi wa’inailaihir raji’un”!!shine kalmar da Hamida ta rinƙa nanatawa a zuciyar ta tana tsaye Khalid ya wuce ta zuwa apartment ɗin dake next to them batareda ta iya motsawa ba..
MamuhMamuhgee
19
Jiki sanyaye Hamida ta nemi hanyar komawar ta sashen ta gaban ta na cigaba da faɗi tana cigaba da nanata innalilahi wa’inailaihir raji’un idanun ta na mata mugun hasashen..
Da shigar ta parlorn ta zauna daɓas akan kujera tayi shiru tana kallon gefe ɗaya tana tunanin yadda tayiwa kan ta tuwon tulu gashi a yanzu ta rasa marar kwashe ta..
Me idanuwanta keson nuna Mata???
Mijin Fifi yafi nata??
Ko yanxuma kenan Fifi ce ke gabanta??
Hawaye ne ya hau zarya a fuskarta fuskarsa da haibarsa na sake cika idanuwanta..
Share hawayen tayi ta hau jujjuya kai tana girgiza ƙafa rasa madogara tayi kawai ta tashi ta shige ɗakin ta bata jira komai ba ta saka lock ta rufe ɗakin ta faɗa kan gado ta saki kukan raɗaɗin zuciya da zafin rai..
Kimanin mintuna arba’in da wani abu Hamida na rufe a ɗaki tana sharɓe kuka tsakanin ta da Allah wanda ita ta san dalilin yin sa,tana nan tana kukan har bacci yayi nasarar cin ƙarfin ta bata ankara ba sai ji tayi ana tapping bayan ta ana kiran sunan ta..
Ɗan buɗe idanun ta tayi ta sauke akan fuskar Khalid dake kan ta fuskar sa cike da damuwa ƙarara..
Tashi tayi ta zauna ta zuba mai idanun ta da ya sauya daga farare tas zuwa rage red..
Shima ita ɗin yake kallo yana tunanin me ya ɗaga mata hankali har haka da idanun ta suka sauya suka kumbura sannan jikin ta yayi zafi kamar wacce fever ya ma kamun sauri..
Kawo hannu yayi ya taɓa jikin ta ya ji zafi rau sai yayi saurin kai hannun sa goshin ta nan ma zafi rau,hankali a tashe ya hau tambayar ta me ke faruwa amma kasa amsa mai tayi sai bin shi da wani irin kallon tsarguwa take yi wanda ya fara bashi tsoro shima..
“Luv me ke damin ki ne i hope ba zazzaɓin ne ya kuma dawowa ba”?ya tambaye ta a ruɗe sai ta kawar da fuskar ta daga kallon sa ta ɗau wasu seconds sannan ta girgiza mai kai sai ya kuma yunƙurowa zai tambaye ta amma ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga mai hannu sannan ta ce
“Bacci nake son yi”!!gyaɗa mata kai yayi sai ya kwantar da ita a kan gadon ya jawo duvet ya lulluɓe ta yana manna mata kiss a goshin ta ya tsaya yana kallon ta..
Ganin bai da niyar fita ita kuma a matse take tayi nazarin ta sai ta lumshe idanun ta dan dai ya ga tayi bacci ya fita..
Shi kuma ganin ta fara bacci ya matso ta ya zauna kusa da ita duk tana jin shi ya hau kwararo mata addu’ar samin lafiya har da na fatar Allah ya sa albarkar sa ne a tare da su..