KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Tana gama tabbatar da cewa ya fita ta tashi da sauri ta je ta rufe ƙofar ɗakin da double lock ta dawo ta zauna..
Ji tayi kamar zafi na mata yawa alhalin akwai air split a bedroom ɗin but zafin da take ji ko mutumin dake cikin kango sai haka..
Cire kayan jikin ta tayi ta nufi toilet ta kunna shower ɗin wanka dan ba zata iya zama cikin bathtub ɗin ba tsabar rashin natsuwar zuciyar ta..

Wankan nan ana iya kiran sa da wanka baƙin ciki because the more the water is dropping on her skin the more her mind is leaving her soul..

Fuskar mijinta ya fado Mata tareda duk wani abinda ya shafesa ta lumshe idanuwanta cikeda so da qaunarsa saidai tsananin kishin yar uwarta da irin mijin data samu Wanda a gani na ido yafi nata Yana yaqi gurin danne son nata mijin,

Bayan ta gama wankar ne ta fito ta shirya cikin simple abaya ta wuce kitchen ta haɗa masu lunch..

Bata kira Khalid a waya ba bare ta sanar da shi abincin su is ready,rather tayi zaman ta ta ci nata ta bar mai nashi ta tashi tayi ficewar ta zuwa zuwa garden ɗin gidan tayi zaman ta a nan
Ita wato ko yanxuma Bata sauya Mata ba Fifi is always ahead of her,
Meyasa su hajja suka zabarwa Fifi Marshall???
Hawayen tsananin kishin fifin suka gangaro mata tanajin wani irin nauyi cikin ranta.


“Baby ki ci abincin nan mana kin taɓa ganin inda mutum ya warke garau kuma baya cin abinc?ana haka”?shiru fifi tayi,tun ranar da ƴar uwar ta ta mata confessing abinda ke ran ta ta kasa natsuwa haka ciwon da take ji a zuciyar ta har yanzu bai warke ba yana nan yana daɗa yaɗuwa,ita dai ta san har ga Allah zuciyar ta ɗaya take yiwa ƴar uwar nata so amma ta rasa yadda aka yi tana raye tayi witnessing irin wannan blast ɗin ta yaya ma aka yi duk waɗannan abubuwan suka faru amma basirar ta ya shafe bata lura ba..
Ko a mafarki bata taɓa kawo rana irin ta ranar nan zata zo ta riske su a rayuwar su ba mostly a labarai take jin ana irin hakan amma ashe it has been designed for her tuntuni ranar da abin ya faru ne dai Allah yayi zai zamo mata eye opener..

Hawaye ne ya fara bin fuskar ta sai hankalin Ammy ya kuma tashi dan a kullum sai dai in fifi bata farka daga bacci ba amma in har idanun ta biyu daga silent tears sai kuka mai sauti hatta da abinci in aka mata maganar sa sai ta saka kuka dan tunowa take da yanzu Hamida na nan na mata kallon selfish person…
Da ƙyar Ammy ta rarrashi fifi ta tashi ta ci abincin dan har an kawo mata ɗakin..
Zama tayi tana kallon abincin sai ta ji appetite ɗin ta yayi ceasing sai ta kalli Ammy ta girgiza mata kai alamar ba ci zata yi ba..
Girgiza mata kai Ammy itama tayi tana faɗin
“Baby not now again rabon ki da abinci tun daren jiya kuma shima liquid sips ne ta yaya zaki warke baki ci abinda zai saka maki ƙarfin jiki ba?uhum?amsa min?ki mana adalci Hajja na can na zaryar sashen Hamida tun ɗazu amma bata same ta ba duk dan mun gyara kuskuren mu amma ke baki son yarda ki taimaka mana why”?jan hanci fifi tayi sai ta kalli Ammy ta ce
“Ammy kina ganin Hamida zata yafe min laifin da na mata kuma yafiyar har abada”?tausayin ta ne ya mamaye Ammy sai ta rungume ta tana amsa mata da eh Hamida zata yafe mata mana ai ba da sanin ta hakan ya faru ba..

Sai da fifi ta ɗan natsa sai ta kuma kallon Ammy muryar ta na rawa ta ce
“Ammy exams ɗin mu saura kwanaki kaɗan,bana concentrating a karatu na ina so in ɗan zaga gidan maybe in sami ikon tuno wasu abubuwan”..
Ɗaga ta Ammy tayi bata ce ƙala ba ta rako ta har main parlor sai fifin ta ce mata ta huta ita kaɗai zata tafi..

Fita tayi ta fara tafiyar ta a hankali tana yi tana tuno irin rayuwar ƙuncin da ƴar uwar ta tayi duk a dalilin ta,a ko da yaushe in ta tuno wannan abin takan yi takaicin irin rayuwar da take yi ta yaya ƴar uwar ta jinin ta ta girma tun yarinta har auren ta a irin wannan baƙin ciki ba tare da sanin ta ba,abin na taɓa mata zuciya..

Tana tafe tana tunanin ta bata san har ta zago zuwa hanyar garden ba sai ji tayi kamar ta jefa ƙafar ta a wani soft place,hakan ya sa ta dawo hayyacin ta ta kalli ƙasa sai ta ga grass carpet alamar garden ta zo..
Ɗan kalle kallen ta tayi ta hango wani kujera sai ta ƙarasa nan ta zauna tana mai haɗe hannun ta da goshin ta wuri ɗaya..

Bata ɗago ba sai da ta ji hawayen idanun ta na nemar tado mata da matsalar zuciyar ta mai wuyar sha’ani sannan ta ɗago ta kalli garden ɗin for a while..
Juya kan ta da zata yi ta hango ƴar uwar ta zaune tayi crossing ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallon anterior view ɗin ta..

Ai bata tsaya wani tunanin ba ta tashi da gudun ta dan dama ta jima tana son ta gana da Hamidar amma bai faru ba sakamakon rashin lafiyar da ya lulluɓe ta tun ranar da abin nan ya faru..
Hamida dake zaune a zahiri amma a baɗini duniyar tunani ta dulmiya,kawai sai ta ji an faɗo mata from no where..

Ɗago kai tayi sai ta ga Mufida a jikin ta tana kuka tsakanin ta da Allah

Wani irin tsananin so da kewar fifin ya taso Mata harta daga hannu zata rungumota sai kishinta ya motso Mata mai qarfi ai kam bata wani jira ba ta ture ta daga jikin ta tana kakkaɓe jikin ta haɗe da jefawa Mufida wani irin mugun kallo..
Ita dai bata damu da kallon ba ta kuma zuwa dan rungume ta amma nan ma ta ƙara datse nufin Mufidar tana gargaɗin ta akan kar ta kuskura ta matso ta..

Abin bai ɓatawa Mufida rai ba dan ta san zafin laifin ta ne ya sa Hamidar yi mata hakan.
“Hamee ki saurare ni,i am ready to receive your punishment ko ta ya nene na yarda zan karɓi hukuncin ki in dai zai goge baƙin tambarin da na dasa nawa a zuciyar ki kin ji”?wani dirty look Hamida ta aikawa Mufida da shi kafin ta ja tsaki ta wuce Mufidar tana tafe tana maganganu ciki ciki ita kaɗai ke jin sa..

Durƙusawa Mufida tayi a wurin tana kuka mai taɓa zuciya a duk lokacin da ta tuno irin raɗaɗin da ta sakawa ƴar uwar ta a zuciya sai ta ji kamar kukan nata kaɗai bai isa ba..
Sai da tayi kukan sosai sannan ta tashi tana tangaɗi ta koma sashen Ammy inda da zuwan ta ta sami wuri ta kwanta,forcing kan ta tayi dan bacci ya ɗauke ta kar damuwar ya mata yawa..

Ko da Ammy ta shigo ta gan ta a haka bata yi gigin tada ta daga baccin ba dan ta san labarin gizo baya wuce koƙi dole kukan baƙin cikin ƴar uwar ta ne ya saka ta baccin dole..
Fitowa Ammy tayi tana share hawayen ta dan abin na damin ta ganin da hanun ta ta taimaka wurin nesanta Hamida da Mufida wanda a matsayin ta na uwa a gare su bai kamata ta bayyana soyayyar ɗaya akan ɗaya a fili haka ba kamar yadda ta rinƙa nunawa a baya..
Ta kan zauna tayi kuka cikin dare idan fifi tayi bacci ba dan komai ba sai tuno irin wariya da bambancin da ta rinƙa nunawa Hamida kamar ba tare aka haife su da Mufidar ba..
Tabbas da ace Khadija na Raye da bazata bambamta yayanta ba sbd ita ta haifesu,
To su yanxu me kenan sukayi???.

Tun ranar ita da Hajja suka rinƙa zaryar zuwa duba ta dan nemar afuwar ta amma sai ta tsiro da hanyar guje masu kar na su haɗu bare su karanta mata fake love ɗin su gare ta…
Musamman yanxu dataga mijinda suka zabarwa Fifi tasake tabbatarda sun qara fifita fifin,

Sashen Hamida Ammy ta nufa bayan doguwar sallamar da ta tsaya tana yi a bakin ƙofa ba tare da an amsa mata ba sai ta yanke kawai bari ta shiga ciki..
Da shigar ta sai ta hango Hamida zaune a ɗan kishingiɗe kunnen ta sagale da earpiece bakin ta na nanata abinda take sauraro a earpiece ɗin wanda waƙar maher zain ne na number one for me cikin album ɗin sa,shigowar Ammy daidai inda yake baitin “my mamma is alright is a brand new day i will like to put a smile on your face every day”..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button