KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Sanyi gwiwar Ammy yayi zuciyar ta ya karye duk wannan maraicin ita da Hajja ce sanadin faruwar sa dan tun yarinta da suka taso tare da daddyn su basu damu da son jin ya lafiyar ta yake ba sai dai na Mufida..
Kasa cigaba da tsayuwa Ammy tayi haka ta fita ta koma sashen ta tana nadamar ƙiyayyar da suka dasa a zuciyar Hamida game da su sannan inda abin ya fi muni shine ƙiyayyar ƴar uwar ta da suka taimaka wurin haddasa sa a zuciyar ta..
Maimakon ta tsanesu suda sukai komai Amma yar uwarta ta tsana.
Kwanaki uku kenan a tsakani Hamida da Mufida babu fahimtar juna sai sabuwar ƙiyayyar juna tun abin na faruwa a tsakanin Hamida da mijin ta a sashen su har ya fito fili Mufida ta gane son ta ne ƴar uwar nata bata yi already ƙiyayyar da take mata ya rinjayi soyayyar da take mata dan haka ta sakawa zuciyar ta haƙurin dole akan bayan wasu lokuta zata kuma komawa ta roƙi yafiyar ƴar uwar nata maybe by then ta huce..
Ana jibi monday exams ɗin su Mufida Ammy ta rinƙa ƙarfafa mata gwiwa dan dai tayi ta kammala lafiya ta dawo gida ta natsu dalilin da ya sa bata sanar da ita dawowar mijin ta ba kenan kar fargaba ya hana ta concentrating a karatun ta,duk yadda zata yi kar su haɗu for now tana yi because bata san ya reaction ɗin Mufidar zai kasance ba in har things turn out to be in a negative way…
Da sanyin safiya ta fito zata tafi inda ya fiye mata daɗin karatu wato garden,tana tafe tana nazarin abinda ta karanta a daren jiya..
Tana tafe tana karatun tana ɗan rausayawa unknowingly kawai ta juyo tayi ido biyu da wani mutumin da bata taɓa ganin sa cikin gidan ba..
Cak ta tsaya a wurin hannun ta dogare da ƙirjin ta littafin ta riƙe a ɗaya hannun ta idanun ta akan wannan mutumi sbd sanin Babu wani Wanda ke rayuwa a gidan bayansu..
Shi wannan mutumi dama morning workout ya fito yi as usual kuma yanzu ya kammala zai koma cikin gida..
Gama juyowar sa ke da wuya fifi ta nemi natsuwar ta ta rasa hatta da handbook dake hannun ta saura ƙiris yayi slipping daga hannun ta ya faɗo ƙasa sbd tsananin faduwar da gabanta yayi lokacinda idanuwanta suka hadu da nasa wanda yasa jikinta Neman daukar rawa..
yana zuwa zai wuce ta kuwa ta ƙara girman idanun ta ganin kamar ta so sanin sa amma kamar ba shi bane..
Da zuwan sa zai wuce ya ga mace tsaye ta ƙame kamar soldier tana kallon sa sai ya buɗe baki ya furta
“Excuse me if you wouldn’t mind”!!ja da baya tayi ta matsa mai ya wuce ta da ɗan gudu gudu in form of jugging..
Sumewa ne kaɗai ya rage fifi bata yi ba da ba a germany ta taso ba inda nan ne ƙarshen masu workouts,
Maza masu abs sune best mazan datake tsananin so da birgewa tagansu kala kala Amma Bata taba ganin Wanda jikinsa yayi building kamar wannan ba,
Zufan dake gangara daga jikinsa kawai was very neat and shiny,
But waye wannan ɗin!?
Who is he????tambayar da tayi wa kan ta kenan amma babu amsa sai ta cigaba da bin sa da kallo..
Ko me ta tuno kuma oho sai ta taɓe baki ta ɗage kafaɗar ta ta ƙarasa zuwa garden ɗin tayi zaman ta da zumar yin karatu sai dai karatun nan bai yiwu ba because tana yi rabin hankalin ta na ga tunanin wanene wannan gentile good looking man ɗin..
Ƙarshe tashi tayi ta ƙarasa sashen su Ammy na mata tambayar ya karatu amma kasa amsa ta tayi sai shiru da ta mata..
Suna nan zaune suna halin shiru ita da Ammy sai aka doko sallamar da sai da ya shiga ciko cikin kunnuwar Mufida ta ji nan take natsuwar ta ya fara yunƙurin barin jikin ta…
Bata gama alhinin wannan sallamar ba ta ji muryar Ammy na faɗin
“Yau da wuri ka shigo,na ga baka cika fitowa da wuri ba hope babu wata matsala”!?hankalin fifi sai ya dawo ga conversation ɗin su har suka gama magana tana kallon bakinsa a sace yanda yake magana cikin cool and matured tune dinda ya gama kashe jikinta musamman dataketa son tantace wane mizani zata kallesa sbd bata gama sanin wayeba.
yana fita fifin ta rufe idanuwanta ahankali ta bude ta yaqi da shaqar kamshin turarensa na Armani daya gama kame sanyin AC na dakin ta kalli Ammy a hankali ta ce
“Ammy waye shi wannan ɗin”?murmushi Ammy ta mata tana shafo fuskae ta a hankali sannan ta amsa mata
“Baby kin ga illar rashin sani shi ya sa na matsu ku dawo,yanzu jinin naki ma baki san shi ba sai an nuna maki,toh dama ban so ku haɗu tun a yanzu ba sbd jarabawar ki amma tunda Allah ya ƙaddari yau zaku haɗu ina ga sai ki kai mai gaisuwar barka da dawowa kusan 4 days kenan da dawowar sa”!!shiru fifi tayi tana jiran cigaban sharhin Ammy sai kuwa kamar Ammyn ta sani ta cigaba..
“Yayan ki ne baby SAHEEB ne”!!, gaban Mufida ne ya faɗi at once..
“What did Ammy just said?yaya na Saheeb ne?what”?tambayar da ta yiwa zuciyar ta kenan tana ƙara hasashen yanayin sa..
Tashi tayi ta sallami Ammy wanda sallamar ya ɗan tsorata ta tunanin ta ko Saheeb ɗin bai yi ma fifi bane…
Da shigar fifi ɗakin Ammy tayi wurgi da littafin hannun ta ta warware mayafin kan ta ta zo gaban mirror ta tsaya tana ƙarewa kan ta kallo daga sama har ƙasa,sai da ta share mintuna biyar tana kallon kan ta a mirror sannan ta jijjiga kai tana furta
“Ya salam,
“wani irin reaction ne ya riske ta ta kuma kallon kan ta sai ta rainawa kyawun ta da wayewar ta da zamanancin ta dan in aka tsaya aka yi comparing nata da wannan da Ammy ta kira sa da yayan ta Saheeb wanda kuma a addinance shine mijin ta for now toh ita ɗin mummuna ce abinda ya ɗaga mata hankali kenan ta rinƙa tunanin anya Ammy ba tsolanar ta take yi ba kuwa ta yaya mutumin da suka ji labarin sa suka kuma daɗe da tagging nasa old man zai yi turning out to be a gentile,handsome and well kept man like this har ma kyawun sa na nemar ɗare nata kyawun,anya ba tsokanar ta Ammy ke yi ba kuwa..
Kasa samin kan ta fifi tayi sai da ta ga in fah ta cigaba da wannan tunane tunanen da ba lallai bane gaskiya ne ba toh zata yi biyu babu because ba zat sami cikar burin ta ba sannan tayi causing mistrust a zuciyar family members ɗin ta akan ta..
So tun ranar wanda ya kasance saturday fifi bata kuma bi ta kan tunanin wanda aka ce mata yayan ta bane dan ta san hasashen Ammy ne ba asalin wanda take jin sunan sa bane is not even possible a ce shine wannan..
Ranarda taji hajja tayiwa ammy mgnar tarewar Fifi din gurin saheeb hankalinta ya tashi matuqa Amma taqi nunawa
Hankalinta bai sake tashiba Saida taji ammy na cewa abari aji ta bakinsa idan matarsa ba yanxu zata dawoba.
Concentrating tayi a karatun ta har ranar litinin da tayi shirin ta na musamman dan fara zana jarabawar ta,good wishes Ammy ta mata ta fito driver ya wuce da ita zuwa makaranta dan attending exams ɗin ta…
Mamuh20
Yau kimanin kwanaki takwas kenan da fara jarabawar fifi kuma ana saka ran gobe zata kammala da hukuncin ubangiji.
Yanayin jarabawar ya sa bata da isasshen lokacin zama tayi hira da su Ammy bare har ta sami lokacin tunanin wani abin..
A wannan tsawon kwanaki tara zuwa goman abubuwa da dama sun faru a gidan wanda fifi bata da masaniya akai..
Cikin wadannan abubuwa akwai wasu halayyar Hamida da ba a san ta da su ba amma ta rinka yin sa a boye,wannan abin ba komai bane sai salon da ta dauko wurin ganin ta sami wani abinda take so..
A natse cikin kamun kai da wayewa take haduwa da Saheeb a garden kullum safe in ya tafi morning workout ɗin sa ita kuma sai ta tafi ta zauna tayi concentrating akan wani pamphlet da take yawo da shi a hannun ta kullum da sunan dubawa take yi..
Haka kawai ta ji duniyar nan babu wanda take son gani kullum safiya zuwa yamma sama da fuskar Saheeb,abin mamaki kamar mantawa tayi ƴar uwar ta Mufida ke aure da shi kuma ita ke da wannan dama da ikon ba ita dake auren ƙanin sa ba..