KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

  Kamar kullum yau ma tana zaune tana duba pamphlet ɗin nata sai mijin ta ya zo dan dama yana ta nemar ta bai gan ta ba sai yayi tunanin zuwa nan dan tun rana da idanun ta ya mata tozali da Saheeb ta fara sauyawa Khalid abincin da suka saba ci tare ta yanke sai dai ta ci nata ta bar mai nashi,wankan da ake yi tare shima ta datse,hirar dare da ake yi kafin a yi bacci nan shima ta yanke sa dan bata da lokacin sauraron hirar lokacin ta na wani abu ne chan daban,toh shi kuma bai ɗau abin da muhimmanci ba ya fi alaƙanta sa da ƙila conflicts ɗin da ya faru ne tsakanin ta da ƴar uwar ta..

  Da zuwan sa ya zauna kusa da ita haɗe da ɗora kan sa a kafaɗar ta yana lumshe ido sai a sannan ta san ya zo dan idon ta na kan Saheeb a kaikaice..

Harga Allah cikin ranta batada wata soyayyar ‘da namiji bayanta mijinta khaleed Saidai Sam takasa dauke idanuwanta daga kan Marshall ne sbd son gano wani aibunsa dazai nuna mijinta yafi na Fifi Wanda shine yasa zuciyarta Sam kasa sukuni da walwala.

  Ko da ta juya ta ga shine sai tayi saurin ɗaga kan sa daga jikin ta tana ce mai
  “Miye kuma haka Kuma ka manta a waje muke?shagwaɓe fuska yayi ya kalle ta ya ce
  “Luv Ina ruwanmu da waje tunda Babu kowa a gurin?sai ta bi shi da wani look tana ja da baya kaɗan kafin ta tashi rai a ɗan jagule dan ya hana ta ƙarasa abinda ya kawo ta..
  Yana kallon ta ta tashi ta wuce dan bata yarda kowa ya san da wannan abinda take yi ba iyakat ita da mahaliccin ta..

Yana kallon ta tana wuce sa ya jiyo kiran yayan sa sai ya maida hankalin sa wurin itama ta tsaya a inda take dan jin muryar sa..
  Ƙarasawa Khalid yayi zuwa wurin da yayan sa ke tsaye,da zuwan sa ya gaida Saheeb cike da ladabi da biyayya dan akwai tazara sosai tsakanin su kuma baya da haka tarbiyar gidan dole na ƙasa ya ba na sama da shi mutuncin sa..
  Tana jin yadda Khalid ɗin ke gaida Saheeb tattare da mutuntaka sai kawai ta ja wani tsaki ta wuce ran ta na ɓaci idanun ta na kawo ruwan hawayenda ke sulala zuciyarta ganin mijinta shine yake qasqantarda Kai ga mijin Fifi.

Tare suka ƙaraso Saheeb ɗin na sanar da shi yana so yau su tafi site wato wani ginin da ake yiwa Saheeb a nan cikin Abuja..
  Da murna Khalid ya ce ya yarda zai bi shi har driver ɗin sa zai zama yau dan sun daɗe basu haɗu ba kasancewar ranar da ya kamata su haɗu aka sami akasin ɗaurin auren nan sai ta waya suka cigaba da magana dan ya koma toh yanzu da ya dawo ne Khalid ɗin ke son faranta mai dan ya san yayi laifi kuma shi yayan nasa ba mai damuwa bane yana iya yiwuwa yana da matsala  amma bai furta ba ya barwa kan sa..

Hamidar da yanzu ta ƙarasa cikin sashen su kunnuwan ta suka jiyo mata inda Khalid ke faɗin ai har driver ɗin Saheeb zai zamo a yau,wani baƙin cikin ne ya kuma turnuƙe mata a zuciya wannan karon kasa dannewa tayi tasaki wani irin kuka Mai qarfi tana zubewa kan kujera da qarfi

Ko da ya shigo ya sanar da ita abinda yayan sa ya ce sai ta mai banza kamar bata jin sa sai da ya kuma maimaitawa sannan ta kalle sa a karkace ta ce
  “Ai na ji kuma na fahimta ba kurma bace ni da zaka faɗi magana ka kuma nanatawa duk dan in ji ka ba”!!a yanzu wannan amsar da ta bashi sai ya ji abin wani iri bata taɓa responding mai magana a haka ba sai yau bai san dalilin ta ba amma ko menene dalilin ai bai cancanci irin wannan kalamai daga gare ta ba…

Miqar da ita tsaye yayi cikin yanayi na tsananin damuwa da kulawa yace”

Luv menene please tell me sbd Sam nakasa gane kanki
Please tell me meye matsalar?
Idan maganar Fifi ne inaga mun wuce gurin right?

Kallonsa tayi da sauri hawayenta na sake saukowa cikin rawar murya tace”

Fifi is always ahead of me,
Meyasa bazaa daina qina da wareni ba acikin family na sbd Fifi?
Meyasa mijina zai zai zama bawan mijin fifi sbd mijin Fifi yafi nawa..

Kallonta yayi da wani irin zallar mamaki da tsoro yace”
Hameeda me kike fada?
Meye ruwanki da mijin Fifi ko Kuma wani Abu kaman hakan tunda dai mijinta baifi nakinba……

Cikin fita hayyaci tace”

Yafi nawa tunda yafisa komai
Dukiya,ilimi, wayewa hutu, kyau soyayyarsu ammy da hajjo da komai da komai ma…..meyasa mijinta yafi nawa zuciyata quna takeyi I can’t take ita Kun taru kun hainceni Kun boyemin Asalin wayene Marshall sbd tun farko baaso ya aureniba…..

Cikin kaduwa khaleed ya girgiza ta Yana cewa”

Hameeda ki daina wainnan zancen kishin Fifi ne ke cinki zai gurbata tarayyarki da yar uwarki please stop wannan kaman kina Mata hassadane…

Ture hannuwansa tayi tana kuka tace”

Kaima da kake nawa bayanta kakebi,
Harda Kai aka taru aka boyemin baa fada min gskiyar waye saheeb ba you lied to me khaleed….you hid this from me..

Daskarewa khalid yayi agurin cikin tsananin firgici da tashin hankali tareda tsananin tsoro idanuwansa suka ciko da wasu irin hawayen nauyinda zuciyarsa ta dauka ya kasa furta komai sbd nauyinda bakinsa yayi.

Atake tadawo mutsuwarta tareda Dana sanin maganarta cikin sauri ta riqo hannunsa tana hawaye tace”

Baby I’m
I’m sorry ba abinda nake nufiba kenan plea….

Bata qarasaba ya janye ya nufi daki da sauri haryana buge qafarsa da kujera ko gani bayayi sosai.

Jininsa daya buge qafarsa ta durqusa agurin tareda fashewa da sabon kuka tana cewa”

Da gaske hassadar Fifi nakeyi???

Ni meyasa ko yaushe Fifi ce abakin kowa?

Daqyar yayi wanka yafito ya wuceta a palon jikinsa duk a sanyaye Saidai zuciyarsa acike takeda damuwa da bacin Rai Saidai kamar yanda yayi alqawari hameeda itace farin cikinsa zai tsaya tsayin daka Dan ganin bai Bari wannan halinda aka jefata ya Bata rayuwartaba zai zame Mata bango Kuma abokin rayuwa na qarshe.

Basu dawo gidan ba sai dare lis dan yawo ya rinƙa jan yayan nasa yana gargaɗin sa shi kuma yana mai nuni da ai faranta mai yake son yi dan rabon su da juna shekaru da dama,toh sai Saheeb ɗin bai ja ba ya ƙyale Khalid ɗin har sai da dan kan shi ya bar su suka dawo gida…

  Har sashen yayan nasa ya raka sa ya kira sashen su Ammy da a kawo wa yayan nashi abinci,sai da aka kawo ya tabbatar yayan nashi baya buƙatar komai sannan ya mai sai da safe ya nufi sashen su..

Bai yi mamaki ba ganin an kashe light ɗin parlor dan ta saba sai ya ƙarasa ciki ua hango ta kwance tana danna waya..
  Da sigar zolaya ya ce da ita
“Luv ba sai kin kira ni ba na san kewa ta kika ji kuma kin ga ban dawo da wuri ba shi ya sa kike son kira na right”!?ya ɗage gira ɗaya sama sai ta taso da sauri tafada jikinsa tareda qanqamesa tana fashewa da qaramin kuka batareda ta iya furta komaiba.

Sake shigarda ita jikinsa yayi Yana sauke numfashi ahankali.
 

Haka suka cigaba da yin rayuwar zaman shiru a gidan nan sam Hamida bata da lokacin Khalid kullum safe tana garden tana kallon Saheeb kuma da zarar lokacin tashin sa yayi sai ta bar wurin dan kar ya gane ta kuma daidai da rana ɗaya bai taɓa sanin da zuwan ta ba sai dai yayi abinda ya kai sa ya gama ya wuce..
  In ma fannin abinci ne in ta gama bata saka mai a food warmer sai dai ta bar mai haka nan duk inda ya kai ya kawo da yunwar sa in ya dawo daga aiki haka zai yi reheating abincin ya ci kamar bai da mata,sam sam zaman su ba wani daɗi,kyautatawa sai wanda ta ga damar yi take mai,lokacin sa ma bata da shi sai ta ji dan kan ta ta saurare sa,haƙƙin sa kam ya manta rabon ta da ta ba shi sai dai da ya matso ta ta ɓata fuska ta ce she is not in the mood..
Duk wannan abinda ke gudana babu wanda ya san da shi daga ita sai shi ba ƙaramin gasa mai aya a hannu Hamida ke yi ba kuma bai da ikon yin magana dan yana tunanin wa zai tunkara da wannan batu a wurin sa kamar abin kunya ne a ce shi da matar sa amma bai isa ya ji daɗi ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button