KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Batun zamantakewar ta da su Ammy kuwa babu abinda ya sauya dan nesanta kan ta da su take yi ba kaɗan ba har ta kai ta kawo in Hajja ta zo sashen ita Hamidar ta manta bata rufe ƙofa ba da ta ga Hajjan sai tayi saurin tashi ta wuce da zarar ta gaishe ta abin na damin Hajja har da Ammy ba kaɗan ba dan da zuciya ɗaya suke son jawo Hamida jikin su amma ita gani take kamar yi suke yi na ganin ido shi yasa ta ƙi sakin jikin ta da su..
Yau monday yau ne fifi ta yi nasarar kammala jarabawar ta na first semester kuma da farinciki ta dawo gidan dan papern ya mata daɗi bata yi zaton zai zo mata da sauƙi haka ba.
Ranar Hajja ta shawarce ta ko zata tafi ta kaiwa ƴar uwar ta ziyara ƙila ta yarda da ita su tsaya su yi magana tunda su dai bata tsayawa su yi wata doguwar magana bata zuwa sashen su su kuma in suka tafi sai ta tashi ta bar su..
Fifi dai bata gamsu da shawarar kakar nata ba dan ita kaɗai ta san irin zafin da ta ji a lokacin da Hamida ta ture ta daga jikin ta haɗe da bata wani dirty look ranar ta ji ba daɗi bata san ƙiyayyar da ƴar uwar nata ke mata ya kai haka ba sai ranar shi ya sa ta yanke hukuncin bata kuma zuwa wurin ta sai dai ta cigaba da yi mata addu’ar saukowa dan ba iya nan ta tsaya ba hatta da silent intimidations ɗin da ta ke yi mata a baya ta cigaba da yi har yanzu bata daina ba kawai dai bata sanar da su Hajja ne dan kar abin ya kuma taɓarɓarewa Hamida ta kuma tsanar ta…
A daren ranar ta fito parlor bayan kowa ya kwanta bacci ta zauna ta saka system ɗin ta a gaba tana duba wani abu gudun kar ta tayar da Ammy ya sa ta dawo parlor dan ta sake ta yi abin ta da kyau..
Kimanin mintuna talatin tana ta abinda take yi sai ta tashi tana rufe system ɗin alamar ta gama ta cire shi daga chargi tana naɗewa ta saka footwear ɗin ta tana miƙa tana salati..
Juyowar nan da zata yi sai ta ga mutum a hanyar water dispenser yana ɗiba ruwa dan sha..
Saurin gyara rigar baccin jikin ta tayi duk da riga da wando ne kuma bai bayyana tsiraicin ta ba amma sai ta ji faɗuwar gaba ya riske ta..
Wanene wannan ɗin da ya tsallake kitchen ya ratsa har main parlor ya zo shan ruwa,sai da ya juyo shima ya lura da ita dan akwai tazara tsakanin ta da shi kasancewar parlorn babba ne..
Shaƙewa ya so yi da ruwan dan yayi zaton ghost ne bai taɓa jin tsoro irin wannan ya riske shi farat ɗaya ba..
Sai da ya ƙare mata kallo ya tabbatar mutum ce kuma itama kamar a tsorace take sai shi ya riga ta magana.
“Am sorry”daga faɗin haka ya juya ya fice abin sa ita kuma ta haura a guje dan ganin fuskar mutumin ranar nan da ta yi wanda Ammy ta ce wai shine yaya Saheeb ɗin da suke jin labarin shi…
Da tunanin shi ta kwanta tana ƙoƙonta anya shine ko dai wani Saheeb ɗin ne dan wannan bai yi kamar shine Saheeb ɗin da suke tsammanin gani ba..
Gari na wayewa ta nufi sashen Hajja da yanzu ta idar da sallah tana azkar ta zauna jiran ta har ta ɗan taƙaita suka gaisa bata yi nauyin baki ba ta tambayi Hajja ko waye wannan da ya zo ɗin,Hajja ta tambaye ta dan neman ƙarin bayani nan ta mata kwatancen sa sai Hajja tayi murmushi ta bayyana mata ai shine yayan nasu almost same amsa da Ammy ta bata ne Hajja ta bata sai ta kuma tambayar Hajja wai shin shekarun sa nawa..
A nan sai da Hajja ta dara ta ce ba tsakanin ta da mijin ta bane wannan,haka fifi tayi tayi Hajja ta faɗa mata amma Hajja ta ƙi ƙarshe ma kora ta tayi dan kawo mata zancen wai ya ce matar sa zata dawo daga jibi zuwa juma’a sai fifin ta kama jiki dan Muhibbah ƴar gayu ce kuma ta girme mata ba kaɗan ba..
Wannan zancen Hajjan ne ya kori fifi ta miqe ta nufi qofar fita da sauri ta bude tareda ficewa gaba daya daidai shikuma ya budo qofar zai shigo qirjinta ya sauka a kirjinsa sosai Wanda ya haddasa musu Shirin faduwa sbd baisan da itama hakama itama
Sukayi baya ya dafe bango da hannunsa daya yayinda dayar hannun ya riqeta sbd yanda tsoro da firgici yasa ta qanqamesa tana rufe idanuwanta.
Ahankali ya dago ya kalli fuskarta akaro na farko dayaji razanar zuciya Bayan kallon wata ‘ya mace,
Itama ahankali ta bude idanuwanta ta sauke Masa zuciyarta na tsananta harba Wanda haryanaji a qirjinsa datake Kai.
Hajja ce ta Dan daga murya tace”
Meyake faruwane agurin wai naji shiru???
Saurin sakinsa tayi shikuma ya fuske tareda dauke Kai ya fada dakin da sallamarsa data sake fadar da gaban fifin ta waiwayo ta kalli bayansa tana Jin wani zazzabi nason kamata
ta koma ta kwanta a gadon Ammy tana ta tunani da ƙiyasta ya matar nasa zata kasance dan in har shi yayi appearing a haka ba a tsohon da tayi tsammani ba ya matar nasa zata kasance ga shi Hajja ta ce ƴar gayu ce…
Ba ƙaramin halin tunani da jimami fifi ta shiga ba sakamakon waɗannan abubuwan al’ajabi da take gani a gidan right now tunanin Hamida da yanda komwi ke Naman lalacewa a tsakaninsu Yana damunta saikuma na wannan ɗin da wai shine mijin ta da na matar sa da wai zata zo abin na ta mata yawo har bacci dai ya ɗauke ta,tsabar ta saka abin a ran ta sai ta rinƙa ƙananan mafarke mafarke kala kala a baccin nata game da matar yaya Saheeb ɗin ƙarshe da ciwon kai ta tashi ta rinƙa tsaki tana jin haushin ɗorawa kan ta damuwar wasu,da haka ta bar gadon babu Ammy a ɗakin ta wuce dan yin wanka a lokacin har 11am yayi…
Kamar ko yaushe tayi wankanta na yamma tana Shirin zuwa gurin hameda ammy takirawota kicin fuskarta Babu alamar Wasa ta nuna Mata qaramin tray da aka jera combo juice nasu fruits marasa zaqi tace’
Dauka kikai sashen mijinki Yana jira Kuma idan kinkai ki jira yagama ki kawomin kayan.
Kallon ammyn tayi tasake kallon kayan kafin takuma kallon ammyn taga Babu Wasa ko sauqi a fuskanta saitaji jikinta yayi sanyi har zata dauka saita fasa tace”
Bari nadauko mayafina….
Kije ahaka jira yakeyi and karnaga qafarki anan sai ya gama infact ki zauna acan zakuyi mgnar inda kikeson zama.
Rau Rau tayi da ido zatai mgn ammyn ta wuceta tana sake tsuke fuska sbd taga idan Bata tashi tsayeba akan Fifi idan muhibba tazo da matsala.
Part din ta nufa tayi knocking ahankali Kai tsaye yace”
Com in Yana amsa waya.
Murda qofar tayi ta tura ta shigo wani sanyin AC da qamshi suka daketa ta qarasa shigowa tareda tura qofar tana kallon qasa sbd bazata iya kallonsa ba.
Shima dagowa yayi yayi Mata kallo daya ya maida kansa kan kallon laptop Yana cigaba da wayarsa.
Ajiye Masa tray din tayi hannuwanta na Dan rawa ahankali ta furta”
Ina wuni cikin siriryar muryanta data Kuma sashi dagowa ya kalleta da idanuwansa dasuke wasu blue blue.
Kamar bazai amsaba yace”
Lfy klau sit.
Zama tayi adarere tana kallon yanayin tsarin palon a takure ga zuciyarta dake wani irin tsallen rashin sukuni.
Yana gama wayar ya ajiye ya rufe laptop dinsa bai dagoba ya zuba combo din a cup ya dago ya Dan kalli gefenta ya hango zallar yarintarta da kuruciyarta sai kawai ya dauke Kai Babu abinda ya fado Masa sai ranarda aka haifesu Amma shine su ammy basuyi wani dogon tunanin nisan shekarunsu ba aka ɗaura Masa aure da ita alhalin zai Isa haihuwarta insha Allah.
Kamar bazaiyi mgn ba cikin wani irin class yace”
Kije.
Ahankali ta dago ta Dan kalli gefen fuskarsa dake kwance fresh da qananun gashinda suka mugun kwanta cikin siriryar muryar basarwa tace’