KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Ammy tace nadawo da kayan.

Shiru yayi kamar baiji ba kafin yace”

Ok ki dauka na gama.

Tashi tayi cikin mamakinsa da Dan Jin haushinsa na yanda yake wani basarwa ta dauki kayan ta fice batareda tace Masa komaiba.

Mamuh21

Dawowa sashen su tayi tana jin mamakin sa har ta shiga kitchen bata ankara ba sai da ta ji kamar ta buge abu sannan ta dawo hayyacin ta ta kalli abinda ta buge..
  Ɗan tsaki ta ja tana dire tray ɗin saman babbar fridge ɗin kitchen ɗin tana mai zama saman wani stool mai juyawa amma bata bari ya juya da ita ba sai ta zauna still ta dogara hannun ta da saman kitchen table dake nan kamar round dinning table,sannan ta tallafe kumatun ta da hannuwan ta biyu ta yi shiru tana kallon direction ɗaya..

“Ni kam wannan wani irin mutum ne shi?daga haɗuwa da shi har yana nuna min jin kai yana wani basarwa hala bai san Ammy ce ta tursasa ni kai mai abin shan ba ƙila shi ya sa ya min wannan jan ajin,toh amma ai nima kyau ne da ni ko?ina da kyau mana toh da me yake taƙama”?wata zuciyar ta amsa mata da ai shi soldier ne ko kin manta..

  Jan iska tayi sannan tayi breathing out tana girgiza kai sai ta kuma faɗawa wata duniyar tunanin daga bisani ta kalli agogon dake manne a kitchen ɗin ta ga 6:40pm magrib na gabatowa sai ta sauko daga kan kujerar ta nufi hanyar upstairs dan kaiwa Ammy sakamakon aiken ta da ta yi..

Wani abin al’ajabi da ya faru shine tana haurowa ta yi kicibis da fuskar sa sai ta ga kamar tsananin damuwar sa da ta saka a ran ta ne game da shi ya sa ya zo yake mata gizo.
  Har zata wuce sai ta kuma kallon sa ta ga yayi blinking idanun sa haka ya tabbatar mata da shine a zahiri ba mafarki ba..

Saurin wuce sa tayi tana jin faɗuwar gaba matsananci da bata san dalilin sa ba,bin ta da kallo yayi har ta gushewa ganin sa ya girgiza kai yana mamakin ɗabi’ar ta kamar ta ga dodo har da gudu,shi kam su Ammy sun haɗa shi da aiki wannan yarinya a matsayin matar sa abin na bashi mamaki har yau,dan shi har yanzu da ya kalle ta tunowa yake yi still da lokacin da aka haife ta ita da ƴar uwar ta Hamida aka bashi su ɗai ɗaya ya riƙe su,wai an wayi gari ɗaya cikin yaran ne kuma aka aura mai at his age ya san ko a haihuwar kaji ya haife ta ya kuma haifi wacce zata girme mata..

Ƙarasa saukowa yayi yana ta nazari a zuciyar sa game da irin rayuwar da zai yi tare da fifi a ƙarƙashin inuwa ɗaya a matsayin mata da miji..

Da gudu ta shigowa Ammy ɗaki har sai da Ammyn ta ji tsoro ta kalle ta da mamaki ta ce
“Me ye kuma haka baby,ko kin manta kina da aure ne yanzu da kike guje guje haka”?kallon Ammy tayi sai kuma ta ji bata jin sanar da ita abinda Saheeb ya mata kawai sai ta yi murmushi ta ce
  “Am sorry Ammy i was eager to see you”!!kallon zargi Ammy ta bi ta da shi har sai da ta ji ta tsargu sai ta shashantar da zancen ta hanyar jan hannun Ammy ta kai ta saman sallayar da take shirin hawa dan bada farali..

  Kallon ta kawai Ammy ke ta yi har ta je ta kwanta bisa gadon Ammy ta ba Ammy baya sai Ammy ta girgiza kai kawai bata mata magana ba ta tayar da iƙamar ta dama fifi na fashin sallah sai tayi kwanciyar ta kawai…

2 hours later

  A dinning table yau Ammy ta ji a yi dinner sai ta sa aka kawo duka abincin nan har wanda za a kaiwa Saheeb ta ce a bar shi a kawo nan shima zai yi joining ɗin su..
  Fifi dai na jin Ammy amma da so samu ne da ta roƙi alfarmar kar a bar ta a nan a bata dama ta wuce da nata sama ta ci a can dan ta san ko presence ɗin sa kaɗai ya isa ya hana ta sakewa bare ta ci abincin har ta ƙoshi..

A gaban ta Ammy ta kira sa a waya ta ce mai ya zo su haɗu a dinning ta girka mai favourite ɗin sa,sai ko ba a jima ba yayi sallama ya shigo direct ya nufi sashen da dinning ɗin yake nan ma ya kuma doka sallamar sai da fifi ta ji sallamar a kan ta dan ba normal voice da mutani ke amfani da shi wurin yin magana shi yayi amfani da shi ba..
  A matsayin sa na babba kuma elder person yayi sallamar,yana ƙarasowa dan gaida su Ammy kafin ya zauna fifi ta rinƙa kallon sa ƙasa ƙasa..
  Har ya zauna bata sani ba sai muryar Ammy da ta ji tana umartar ta da ta yi serving yayan ta..
 
Duban ta ta maida ga Ammy sai Ammy ta kuma maimaita mata ta tashi tayi serving yayan ta shima Saheeb ɗin sai ya dubi Ammy ya kuma dubi fifi wacce a dai dai lokacin idanun ta ya kai gare sa dan ganin ya zai yi reacting da jin wai ita ce zata yi serving nasa abinci..
  Sai ta ga idanun sa akan ta yana kallom ta abin sa ya bata mamaki tayi tunanin attitude ɗin da ya bata ɗazu zai bata yanzu amma sai ta ga akasin hakan,a zuciyar ta sai ta rinƙa muhawwara da kan ta akan ai ƙila ko halin sa kenan abinda ya maki ɗazu nan gaban mahaifiyar sa ce ba zai yi hakan ba..

Taɓe baki tayi kawai ta tashi a natse dama atamfa ce a jikin ta ɗinkim doguwar riga A-shape dan har yau bata gama zama gwana a ɗaura zani ba dama dama skirt takan ɗan saka sa wasu lokutan but ta fi yin free da doguwar riga..
  Gyara ƙaramin gyalen kan ta tayi ta hau tafiya a hankalin dan table ɗin babba ne kuma yana da faɗi in har so kake kayi serving abinci comfortably toh sai dai ka zagaya dan in ka tsaya a inda kake ba zaka ji daɗi ba..

Takun da take yi shi ya saka sa kai idanun sa gare ta ya rinƙa kallon ta a hankali cikin hikima har ta zo gab da shi ta tsaya,sai kuma ƙamshin ta ya shige sa nan ma still ya kuma aika mata wani irin kallo ita kuwa matsanancin faɗuwar gaban da ta rinƙa samu ne ya sa ta kasa natsuwa ta tambaye sa me zai ci sai kawai ta fara bubbuɗe wadatattun food warmers ɗin ta ɗau babban serving spoon ta fara ɗibar mai abincin tana zubawa..
  Sai da ta zuba mai abinci kusa 4 dishes a plate ɗaya ko wanne da inda take zuba sa da ta gama ta rasa ya zata ce mai ta gama zuba mai sai ta dubi Ammy..
  Abin mamaki sai ta ga idanun Ammy da na Hajja a kan su da har su sun fara cin nasu abincin amma suka dakata suna kallon dramar ta su kamar ba komai suke yi ba..
  Ammy na ganin ta kalle ta sai ta kalli Hajja wacce itama da sauri ta kawar da kan ta daga kallon su ta maida ga abincin gaban ta..
“Hajja kin ƙoshi ko in ƙara maki”!?sai Hajja ta amsa mata da ya isa hakan daga nan suka cigaba da cin abincin su ba tare da sun kuma kallon sashen su fifi ba sai dai sun ƙunshe dariyar su a ciki kar ya fito but ba ƙaramin dariya fifi ta ba su ba duba da yadda ta tsaya kamar soldier a tsaye ta kyaɓe fuska kamar zata yi kuka shi kuma yana kallon ta kamar tana abinda ba daidai ba..

  Tayi tayi Ammy ta ɗago ta kalle ta dan ta taimake ta ta mai mgn amma ko a kuskure Ammy bata ɗago ta dube ta ba haka Hajja kuma ba wai basu san tana buƙatar taimakon bane,sune ankare sai dai suna ganin in suna shiga al’amarin ta har yanzu da mijin nata ke nan toh ba zasu saba ba kuma ba zasu san juna su fahimci juna ba…

  Fifi na nan tsaye kamar an dasa ta Saheeb na zaune yana kallon ta yana girgiza kai dan mamakin saurin girman da ta yi farat ɗaya shi sam bai ma san ana wata drama a wurin ba bare ya ɗauke kan sa daga kallon nata..
  Ita kuma bata yarda ta haɗa ido da shi ba bare ta ga reaction ɗin sa addu’ar ta Allah ya sa ya juyar da kan sa ko wani abu ya shige mai idon da zai ja hankalin sa ya ga abincin ita kuma ta gudu..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button