KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Kusan mintuna biyar babu abinda ya faru sannan ita ta fara gajiya da tsayuwar sai kawai ta yi shahada ta buɗe baki cikin fargaba ta ce mai
“Abincin ka…ur food….i just serve it kalla gashi”!!kalaman nata are not coordinated wanda ya saka su Ammy kasa riƙe dariyar dake ta cin su suka sake ta.
Sai a sannan Saheeb ya farfaɗo daga kallon ƙurillar da yake yiwa fifi wanda a wurin sa kallon saurin girman ta yake yi yayin da su Hajja ke tunanin ko ya razana ne da kyawun fifi har ya kasa daina kallon ta shi yasa ran su yayi fari tas…
Gyara murya yayi yayi saurin kai idanun sa ga abincin sai kuwa fifi ta sulale ta baya ta gudu ta haura upstairs..
Ba wanda ya ankara sai da Ammy ta ɗago dan kallon ta sai ta ga wayam ba kowa a wurin,ƙara danne dariyar ta Ammy tayi ta dubi Saheeb da yake shirin fara cin abincin sai ta ɗan murmusa ta cigaba da cin abincin nata.
Hajja ce ta ƙura mai ido tana kallon sa sai ta ga yadda ya lumshe ido da ya kai spoon ɗaya,sai ta ji tausayin sa ya mamaye mata zuciya Allah kaɗai ya san rabon sa da cin girkin mahaifiyar sa,matar nasa bata da lokacin kan ta bare nasa ta yaya zai sami abinci irin wannan,cigaba da kallon sa tayi mutumin that is worth marrying his daughter out amma yana cin girkin mahaifiyar sa kamar wani ɗan shekaru goma sha wannan irin aure nasa na farko da shi da babu duk ɗaya ne a wurin ta shawarar auren sa da fifi yayi ma’ana kuma yayi amfani ko ba komai ta san fifi ba zata kunyata su ba in dai fannin kula da shi ne da cikin sa…
Sai da ya ci kusan rabin plate ɗin sannan ya kalli Ammy cikin jin daɗi a ran sa ya ce
“Ammy na it’s awesome i love d dish”!da fara’a Ammy ta kalle sa ta tambaye sa
“Da gaske yayi daɗi”?gyaɗa mata kai yayi yana kuma kai spoon ɗaya bakin sa sai kawai ta ce
“All thanks to Mufida ita ta girka i only gave her directions”!!ƙamewa spoon ɗin yayi a bakin sa bai ƙarasa saka sa ciki ba haka bai fitar da shi waje ba take ya ji kamar ba shi ba..
Kallon sa Ammy tayi tana murmushi tana ganin yadda ya sauya amma tayi kamar bata gan sa ba..
Ai kuwa ɗan halas sai ya fiddo spoon ɗin waje da abincin ciki ya mayar cikin plate ɗin ya ɗau tissue yana goge bakin sa haɗe da tashi yana faɗin
“Na ƙoshi Ammy tnx sai da safe”!bin shi da kallon mamaki suka yi sai Hajja ta juyo da sauri ta dubi Ammy tana bata kallon meye hikimar ta na yin haka sai Ammy ta ɗan murmusa ta ce
“Hajja rabu da shi na san ya ji daɗin abincin kuma da sani na na ce mai fifi ce ta girka ba dan komai ba sai dan in ƙara janyo su kusa da juna kin dai san auren nan nasu ba a natse aka yi sa cikin kwanciyar hankali ba dole akwai gaps da yawa a tsakanin su da sai dai mu da muka haɗa su zamu taimaka mu cike masu gaps ɗin wannan dalilin ya sa na bar shi ya ɗan nitsa cikin cin abincin sannan na ce mai Mufida ta girka duk da ba ita ɗin ba ce amma Hajja believe me wannan hikimar da na yi zata janyo su kusa ke dai ki tsaya ki ga me zai faru next”!faɗaɗa murmushin fuskar ta Hajja tayi tana gyaɗa kai alamar gamsuwa,da haka suka ƙarasa cin abincin nasu suna tattauna irin dramar da Saheeb da fifi suka yi…
Fifi na shiga ɗakin Ammy sai ta faɗa saman gado ta rinƙa sauke ajiyar zuciya tana jin fargaba na shigar ta ta yaya tsoron Saheeb yake mamaye ta ne haka a sannu?girgiza kai tayi kawai ta rufe idanun ta da tafin hannuwar ta ta rinƙa tunane tunane ta yaya Ammy ta ƙi taimaka mata wurin yiwa Saheeb mgn bayan ta gama zuba mai abinci alhalin ta san bata iya yi mai mgn..
Lkc ta ɓata tana tunanin abinda ya faru gashi ta gama kwaɗaituwa da girkin Ammyn amma bata ci ba duk sbd wannan yaya Saheeb ɗin..
Juyawa tayi ta lumshe idanun ta tana tuno abinda ya faru a tsakanin su tun safen yau har ɗazu,juyi ta rinƙa yi har Ammy ta shigo ta rinƙa murmushi tana kallon ta daga bisani ta kira sunan ta a ɗan firgice ta juyo ta kalli Ammyn sai ta ce da ita
“Baby daga yi serving yayan ki abinci kuma shi kenan sai ki gudo nan ɗaki ba tare da kin ci ba”?shiru fifi tayi tana sauraron Ammy kamar ta ce mata a matse take tana son ɗanɗana abincin amma sai mgnr Ammy yayi intruding.
“Kin san me ma kuwa”?sai fifi ta girgiza kai Ammy na murmushi ta ce
“Yayan ki ya ce abincin ya mai daɗi sosai dan ce mai nayi ke kika yi so u have to improve in ur cooking skills dan yana son girkin gargajiya kawai dai bai cika samin irin na gargajiyar bane amma yana matuƙar so”!!
Huhh..is Ammy for real!?toh ita meye ruwan ta da Saheeb da Ammy ke ta nanata mata yanda yake son girkin gargajiya?ita fah har yanzu tana ganin abin a almara wai Saheeb ɗin nan ne mijin ta…
Share tunanin tayi kawai ta hau sauya kayan ta zuwa na bacci duk Ammy na lura da ita sai da ta zo zata kwanta Ammy ta ce ya haka sai tayi tsaye tana kallon ta nan Ammy ta ce mata ai Saheeb baya kwanciya sai ya sha warm nscafee if not ya rinƙa damuwa kenan dan haka ta je ta haɗa mai a kitchen ta kai mai and she should make sure ya sha kafin ta dawo..
Mamakin Ammy ta rinƙa ji sai ta ga kamar Ammyn ta daina son ta amma ba ɗabi’ar ta bane yin jayayya da Ammy ba sai kawai ta ɗau hijabin ta ta saka ta fito ta nufi parlor ta wuce kitchen tana haɗa nscafee ɗin tana tunanin ko ya zata kasance a tsakanin su in ta kai mai ɗin ita wlh cika idonta yakeyi yayi Mata kwarjini da yawa..
“Ko damuwa da rashin cin abinci na Ammy bata yi ba wai in zo in kai mai toh ni fah”?ta tambayi kan ta,kamar zata zauna ta ci abincin ta sai kuma ta fasa ta ɗau ƙaramin tray ta ɗora mug cup ɗin ɗin ta nufi hanyar sashen sa…
Tana tafe haske na haska mata sashe biyun da na ƴar uwar ta Hamida da na yaya Saheeb ko ta ce wai nata ita da wata..
Tuno da Muhibbah da ta yi sai ta ɗan ji wani iri haka dai ta ƙarasa ciki,bata tsaya ko ina ba sai inda ta gan sa ɗazu ko da ta isa wurin sai bata gan shi ba,bata tsaya wani tunani ba ta nufi hanyar wani ɗaki ta tura ƙofar ɗakin da sallamar ta..
Saheeb dake tsaye yana gyara carving ɗin sa na fuska ɗaure da towel gaban mirror da nufin in ya gama ya shiga wanka sai kawai ya ji sallamar mace bai bada izini ba ya ga shigowar ta..
Daga ita har shi sai da suka razana da gudu ta juya mai baya shi kuwa cikin ɓacin rai ya furta
“Goddamn it meye haka ke ba a koya maki in kika yi sallama ki tsaya a baki izinin ba tukun ki shigo”?ya mata tmbyr ba wasa a tare da shi.
Jikin ta na ɓari bakin ta na rawa ta ce da shi cikin tsoro
“Ka…k..ka yi haƙuri…coffee na kawo maka”!!kasa ƙarasawa tayi akan Ammy ce tayi assigning ɗin ta sai tayi saurin nemar inda zata aje trah ɗin kafin yayi slipping daga hannun ta dan hannun nata kyarma yake yi…
Tsaki ya ja yana wurgar da hand clip ɗin ita kuma ta fita cikin sauri ta koma sashen su gaban ta na faɗi tana ta numfarfashi kamar ta yi gudun tsere..
Ko da ta shigo sai ta ga har Ammy ta yi bacci dan haka ta hau gadon kamar matsoraciya ta kwanta ta ƙanƙame jikin ta cikin blanket haɗe da runtse idanun ta ko baccin dole zai ɗauke ta dan ta daina ganin gizon fuskar ta sai dai ta kasa baccin sai juyi dama da hagu daga baya da ƙyar baccin yayi nasarar fizgar ta bayan ciwon kai ya mamaye ta….