KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Mamuh22
Da sanyin safiya Ammy ta tada fifi akan ta tashi ta yi wanka,sai abin ya mata wani iri is somehow wired Ammy da ba cika son tashin ta a bacci take ba sai ta ji dan kan ta ta tashi amma yau ta tayar da ita..
Bata yi musu ba ta miƙe ta tafi toilet tayi wankan ta gyara kan ta a ciki ta fito ta nufi mirror dan gyara jikin ta,Ammy ta riga ta fita zuwa ɗakin Hajja dan yi mata gaisuwar safiya inda daga gaisuwa kuma suka zauna hira har ta manta da ta saka fifi yin wanka..
Da ta gama gyara jikin sai ta nufi wurin closet ta buɗe ta tsaya ƙare ma kayan cikin closet kallo tana nazarin wanda zata saka,amma haka ta gaji tsayuwa bata samo wanda ya mata ba duba da irin yanayin sanyi na garin sai tayi tunanin saka hoodies da summer outfit kawai since ba fita zuwa ko ina zata yi ba..
Ciro wata leather summer Cardigan tayi mai ɗan tsayi da wata blue women jeans ta zuba su kan gadon sai ta dawo ta saka inner wears sannan ta saka kayan a sama ta saka hular ta ɗau wayar ta tana selfie dan turawa ƙawayen ta na germany..
Tana kan ɗaukar na uku ta ji turo ƙofa sai bata juya ba tunanin ta Ammy ce sai ta cigaba da ɗaukar hotunan amma sai ta ji ba a kuma motsawa ba sai ta juyo tana faɗin
“Ammy tun ɗazu ina kika shiga almost an hour”!!mgnr nata ne ya sarƙe sakamakon haɗa ido da tayi da Marshall kawai sai ta ji kamar an saka mata battery ana controlling movement ɗin ta..
Kasa natsuwa tayi shin gaida shi zata yi ko dai ta juya baya ne?,tana tsaye ta kuma kallon sa sai ta kawar da kan ta tayi shiru shima yayi kamar bai san state ɗin da ta shiga ba ya waske kawai ya buɗe baki ya tambaye ta inda Ammy take sai ta amsa mai da
“Nima ban san ina ta tafi ba”!!sai ya ga kamar ta mai amshin rashin kunya duk da sigar da tayi amfani da shi wurin amsa mai ba sigar rashin kunyar ba ce..
Juyawa yayi ya fice abin sa bai sake ce mata komai ba as bata yi ilimin gaida mutum ba kamar yadda yayi tagging nata..
Bayan fitar sa sai ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya ta jingina da closet ɗin tana mai lumshe idanun ta sakamakon jin wani baƙon lamarin dake bijiro mata a fizge..
Tana nan tsaye idanun ta lumshe sai ga sallamar Ammy ta shigo ɗakin,a hankali ta buɗe idanun ta ta zubawa Ammy sai ta raba jikin ta da closet ɗin ta ƙaraso ga Ammy tana tambayar ta ina ta tafi tun ɗazu..
Bata amsa mata ba ta ja hannun ta tana ce mata
“Baby je ki gaida Hajja tana son ganin ki”!!kallon Ammy tayi kamar ta faɗa mata ai yaya Saheeb ya zo amma sai ta ƙyale kawai ta fita zuwa hanyar ɗakin Hajja hankalin ta na nan na tuno mata Marshall..
Sallama tayi a ɗakin aka amsa mata sai ta saka kai ta shige ba tare da ta tsaya duba wa ke gaban ta ba..
Tuntuɓe ta yi da mutum kawai sai kamar zata faɗi amma tayi saurin kama jikin ta cikin sauri ta ɗago ta kalli wa ta buge..
Ganin sa tayi zaune cikin mamakin ta itama da mamaki ta kalle sa yaushe kuma ya zo nan ɗakin?ohh ita Mufida yau ta ga abin al’ajabi yanzu yanzu ya bar ɗakin Ammy kuma har ya zo nan ita me ya sa suke haɗuwa ne da yawa haka…
“Ƙaraso mana takwara ta zo ki zauna”!!ƙarasawa ciki ta yi a natse ta sami wuri ta zauna nan kusa da Hajja sai kuwa ya miƙe dama ya gama gaisuwar tashi zai yi ya fita sai fifi ta shigo..
“Na tafi Hajja na”cewar Marshall ya saka kai ya fita sai Hajja ta juyo ta kalli fifi tana faɗin
“Kin ga ɗabi’un mijin ki ko takwara?haka yake ya cika son zaman kaɗaici kuma bai dace da lafiyar sa ba”!shiru ta yiwa Hajja kamar bata ji ta ba sai ta gaida ta itama ta tashi tayi fitar ta..
Dawowa ɗakin Ammy tayi ta sanar da ita sun gama gaisawar da Hajja sai Ammy ta ja hannun ta zuwa ƙasa,basu tsaya ko ina ba sai kitchen inda a nan Ammy ta rinƙa jan ta da labaru mostly akan mijin ta wato Marshall Saheeb ita dai fifi na jin Ammy a wasu labarun mata sai ta ga kamar da gangar Ammy ke faɗa mata su duk dan shi ɗin ɗan ta ne kuma tana nema masa shiga a wurin ta..
A kai a kai Ammy ke kuma tunatar da ita yadda mace ke karɓe mijin ta musamman ta fannin girki haka ta nuna mata nata mijin mai son abinci ne sai dai ij bai samu ba sai ya haƙura amma yana son abinci musanman na gargajiya..
Da hirarrakin Ammy wanda fifi ba amshin baki take bata ba sai uhum uhm suka kammala ayyukan suka fito da wasu yayin da ƴan aikin suka fito da sauran dan tun dawowar Marshall Ammy da kan ta take shiga ta rangaɗa mai girki da kan ta sanin duk duniya tun yarintar sa har yau da ya manyanta in har yana gidan baya yarda ya tsallake girkin ta dan yayi ranking ɗin ta a matsayin world most best a fannin girki haka ya sa even after his marriage ko da a ɗan suɓuce Muhibbah ta mai girki baya yarda ya tsallake na mahaifiyar sa bare ma ba lkcn sa Muhibbahn ke da ba…
Zazzaune suka yi a dinning table ana ɗan hira mai kama da muhawwara tsakanin Ammy da Hajja ita dai fifi nata ido,ana haka sai sallamar Saheeb ya tsaidar masu da hirar tasu..
Gaban Mufida ne ya faɗi amma bata bari ya bayyana ba,yawa yawan haɗuwar su a tsakanin jiya zuwa yau na bata mamaki da ɗaure mata kai dan tun jiyan nan har yau sam zuciyar ta ta kasa samin natsuwa bare ta tantance menene sahihin abinda ke damin ta..
Jin zaman shi kawai tayi sai ta ɗago kai a yayin da shi kuma nasa fuskar na fuskantar Ammy yana gaida ta da warhaka..
Ƙare mai kallo fifi ta tsaya yi tans kallon suturar jikin sa,ba wasu casual or native bane kawai khaki top ne sai wandon jeans deem blue fuskar sa ya ƙare haske sakamakon carving sajen sa da yayi compare to jiya da bai yi ba..
“Baby pls serve us muna jin yunwa”!ta tsinkari muryar Ammy na mgn sai ta juya ta kalli Ammyn sannan ta tashi ta fara daga plate ɗin Hajja ta gama ta dawo na Ammy daga nan ta juya ta kalli na Saheeb dake fuskantar su kamar jiya.
Rasa courage ɗin tmbyr sa ta yi sai ta ɗan tsaya sai kuma ta matsa daga inda ta ke ta miƙa hannu tana zuba mai chips ɗin,da ta gama ta ɗau bowl ɗin plantain chips nan ma ta miƙa hannu ta zuba mai,next scrambled egg ne ta fara zuba mai a hankali tana gab da gamawa sai bowl ɗin ya suɓce daga hannun ta ya faɗi bisa table ɗin wasu suka zuba wasu suka rage..
A hanzarce ya riga kowa fara tmbyr ta
“Are u alright”?ɗago ido tayi suka sarƙe cikin na juna sai kuma tayi ƙasa da kan ta tana gyaɗa mai kai,ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin
“Be careful next time,glass ne it might hurt u”!!shiru wurin yayi Ammy da Hajja na kallon juna ƙasa ƙasa suna murmushi sai da suka ga kamar fifi zata juyo sannan Hajja ta riga Ammy mgn
“Takwara ta me ya same ki?ina hankalin ki yake”?shiru dai tayi ta zauna a mazaunin ta sai Ammy ta tambaye ta ko me take tunani bowl ya faɗi da fatar dai bai ji mata ciwo ba ta faɗa tana riƙo hannun nata dan ganin ko ta yanke..
“Ammy ba komai am ok”?kallom ta Ammy tayi ta ce
“Are u sure”?gyaɗa mata kai tayi sai ta karɓe spoon ɗin da fifi ta riƙe da niyar serving kan ta abinci ita ta zuba mata tana ce mata
“Baby bismillah”kallon Ammy tayi sai ta gyaɗa kai..
Ikon Allah kamar wata kurma,Hajja ta faɗawa kan ta a zuciyar ta sai dai bata ce komai ba ta yi shiru abin ta..
Duk wannan abin Marshall na kallon su yana mamakin inda hankalin fifi ya tafi har bowl ya kusa yanke ta a hannu dan ma dai bowl ɗin mai kauri ne..
Ƙala bai ce da su ba da ya gama kallon su ya maida hankali ga abincin gaban sa ya san wannan mahaifiyar sa ta yi sa ba yarinyar da ta ce ita tayi na jiya ba..