KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Tun hamida batasan kanta ba Rayuwar ta ya kasance a karkashin inuwar yar uwata mufida kowa yakan nuna tasa fifikor a bayyane batare da sun lura da halin da zasu jefa ta aciki ba. ayanzu haka zuciyarta cike yake da kishi da kuma qaunar yar uwarta saidai abunda bata iya banbancewa ba shine wanne ne yafi yawa acikin ranta?

A kullum ta zauna cikin tunani takan raya aranta cewa
Tana matukar kaunar yar uwata mufida kuma tanajin tausayin ta aranta amma ayanzu hakan baida wani amfani awajen ta

A duk inda takai wajen kololuwar son ta nuna nata son da kulawar sai taga iyayen su da yan uwan su da dukkan kawayen su suna mata irin shi koma wanda ya fishi

Ta lura Babu abunda zatayi ta birge kuma ta sha kokarin kin son hakan ya zauna mata araina amma sai takasa.

Itama mutum ce me ra’ayin son jin dadin rayuwa,shakatawa da matukar son nuna wayewar ta a fili kamar yar uwanta Fifi sai dai babu wanda ya lura da hakan bare abata irin waccan kulawar

Kowa ya mance da cewa mintuna biyar ne mabanbanta a rayuwan mu,tunda ni da ita munyi zaman mahaifa guda kuma muka fito acikin uwa guda
Aka yanke mana cibiya rana guda aka saka mana suna a rana guda sannan aka shayar damu nonon uwa guda.

Yadda yar uwata mufida take tsananin son life haka nima nake matukar so araina

Na dade da burika irin na mufeeda musamman babban burin ta akan kalar mijin data ke so tayi rayuwarta dashi wato namiji kamar ameed dan gayu me karancn shekaru young,rich,kyakkwa me aji mai ginannen jiki wanda ya kwarance a iya rayuwa da soyayya.

Zai kasance kamar ita ko kuma wanda ya fita da karancin shekaru wanda baifi uku zuwa biyar ba

Cikin sakin dogon numfashi ta rage gudun motar ta data keja ta danna horn abakin katafaren gate din gidan su tayi parking ta tattari yar jakan ta ta shiga ciki

Asalin damuwarta baifi tsoron meyene zata samu anan gaba wanda yar uwarta ta baxata rabata da shi ba

Sallama tayi ranta cike da kuncin hakan aranta mahaifin su dake zaune batare da ya dago kai ba yace wa’aliksam,bata karasa ba ya katse ta da cewa mufida kece?murmushin karfin hali tayi tace a’a hamida ce nan ya dago idanun sa yana me mata kallo mai kama dana tuhuma da tambayar ina ta bar yar uwarta mufida?

Hamida tace suna tare da kawayen ta amma tare muka kamo hanyar gida,yace meyesa zaki barta ita kadai baki da hankali ne call her now,yanayin yadda ya bata rai yasa Da sauri ta shiga dialing number mufidan yay ringing har sau biyu amma ba a daga ba…kasa cewa komai tayi ta tsaya tana kallon dady

ita kanta bata ji dadin yadda dadyn ya nuna rashin gamsuwar sa ba
Iya bayani ta masa kuma tasan ya fita sanin kalula irin na fifi,ta rasa meyasa ake yawan son nuna mata abunda bata fiye gane yuwar adalcin sa ba

Kowa yasan fifi tana rayuwar ta ne akan dokokin ta,she does what she feel like a lokacin da taga ya mata.. kuma banga lefin ta ba tunda su suka dora mata dukkanin gata da sakalci,sam basa iya mata fada kosu ce mata bari duk dan gudun kar ranta ya baci.

To meye ne nawa aciki shine ban fahimta ba.

sallamar ta ne ya dakatar da su gaba daya atare suka juyo suka tsura mata idanu,wani rau fifi tayi da idanun ta tana me aje jakarta akan table da dan sauri ta taho jikin dadyn su ta fada tana me dora kanta akan cinyoyin sa cikin sakaltaccen shagwaba cikin sanyin murya
“agafarce ni nayi latti ko?Girgiza kai daddy yyi ya dan shafa kanta cikin tsananin nuna kulawar sa tamkar ba shine yake shirin nuna damuwar sa akan rashin dawowarta yanzu ba

..shiru hamida tayi tana kallon su cikin tuno da Allah me kyautar kunci,ya dada ma kuma dole kace ka gode…

shiru me cike da tarairaya shi ya ratsasu hamida kuwa na cigaba da kwantar da wuyarta sulalewa tayi ta barsu awajen har takai bedroom din ta baxata iya bada tabbacin sun san ma tayi hakan ba

Haka rayuwar take tafiya a dadi babu dadi lamarin fifi da kawayen ta da dr ameed kai da gaba daya duniyar ma bai sauya ba

Wani abun ma gaba gaba yake yi musamnan tsakanin ameed da fifi inda yake nuna mata kulawar sa cikin tsananin nuna soyayayar sa agareta ita kuma fifi tana daukar sa ne a matsayin dan uwa kuma babban aboki

Rayuwar su atare gwanin ban sha’awa ce,”duk sa’in da suke tare sukanyi wasu abubuwan da in ka gansu ido da ido zaka ji ina ma inama kaine…

Hamida ma hakan takeji aranta dan ameed irin kalar mazan datake buri arayuwarta ne wanda anan ma yar uwanta fifi tayi mata fintinkau a zuciyar sa

Bayan windown hamida ne kawai agidan yake da lovely moonlight reflection kuma balcony ne ata kasan shi me dan fadi yana da step step na takawa

dake ba a ma yawan biyewa ta wajen akan iya zama akai a huta in waje yay sanyi

Hamida takanji matukar son tana kasancewa anan musamman can cikin dare dan ta dinga samun nitsuwa da daidaituwar tunani

Amma da ta doshi hanyar wajen sai ta shiga tuno da lokacin da ta same fifi da ameed sun jeru kafada da kafada suna kallon hasken wata suna hirar su irin ta masoya..

This is also her dream,and mufida is living it right behind her window.

Yawu ta hade tare da cewa hmmmm ta wuce dakin ta ta rufe kanta da damuwa ita kadai take mirginawa akan gadon ta,can ta mike tsaye ta bude right hand drawa ta dau wani tsohon family album ta xauna tana kallo

Tasan kwata kwata Basu wani jima da mahaifiyar su araye ba amma haka kawai takanji kewar ta da azaban kaunarta aranta duk dama tana harsashen da itama tana raye hala mufida zata zaba ba ita ba.

Cigaba da kare ma hotunan kallo takeyi tana dan shafawa da yatsun ta cikin wani irin yanayi me tafe da ssanyar sanyin zuciya.

Tabbas Mahaifiyar su kyakyawiyar mace ce kyaun ta da kalar fatar ta duk suka debo amma da alama mufida ta hada kamannin fuskn ta har dana kakar su hajja dan tafi su doguwar karan hanci da cikar suman gaban goshi

Kamar yadda mahaifin su yake da lotsawar gefen kunci na dimples haka ma mahaifiyar su take da su saidai na daddy a gefe daya ne na maman su kuma a duka site biyu

Nan ma fifi ce ta dauko kamanni mai kyaun ciki wato na mamar mu,nikuma dimple dina a site daya yake nunawa irin na daddyn mu.

Ta dade a kwance da hotunan agaban ta tana kallo cike da admiring wani karamin abun hannun winston diamond bracelet dake makale a hannun mahaifiyar su wanda yayi matukar daukar hanklin ta ya kuma shige ranta

Tasan ba komai bane awajen mahaifin su dan ya siya mata irin sa amma aranta so take abata shi kamar kyauta irin wanda zata sa arai taji tana matukar daraja shi in ta tuno shi.

Kasa kasa take sauke nishin gajiya da jin bacci can ta rufe album din ta maidasa maxaunin sa nan ta koma kan katifar ta ta nitsu jim kadan bacci yayi awon gaba da ita

Washe gari Ayanayin da bata son ta farkawa ta tsinci kanta

zagaye da duk wani yanayi dake dasa mata damuwa da jin kishin yar uwan ta fifi.

Ita kuwa fifi bata damu da komai ba hasalima babu damuwar komai aranta ayanzu face tsananin son mahaifin ta da yar uwan ta da zuciyarta yake wuni aciki kullum

Kamar yadda take bukata so tuni ta bude Babban shagalin enjoyn life ita da kawayen ta su na more rayuwar su yadda ya kamata.

Anan germany fifi bata da wasu shakikan kawayen da suka fi mata meena da maheeda

In tana gida kullum Meena na makale da ita dake dama su makwafta ne kuma kamar yan uwan juna suke ayanzu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button