KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Kowa na cin abincin sa cikin kwamciyar hankali banda fifi da tsananin tsarguwa ya gama addabar ta kamar wacce tayi wani illegal act..
Sarai ya fuskanci halin da take ciki na rashin sakewar ta amma abin mamaki sai ya ɗaure fuska ya ƙi tashi ya ƙi yin hira da su Ammy ko dannita ta sami chance na cin abincin..
Sai da ta ga bai da niyar tashi a wurin kuma ba zai yi mgn da kowa ba bare ta sami damar cin abincin sai ta yi shahada ta sunkuyar da kan ta ƙasa tana cin abincin a hankali..
Ko sau ɗaya bata ɗago kan ba bare ya takura ta ta kasa samin natsuwar cin abincin..
Sai da ya ga ta ɗan sake tana cin abincin sannan ya matsar da nasa plate ɗin yana goge baki haɗe da faɗin
“Ammy zamu fita ni da Khalid zamu duba site ɗin nan na ga kamar basu saurin aikin ne”sai Ammy tayi murmushin manya tana faɗin
“Allah ya kiyaye min ku kai da shi ya sa ku je lafiya ku dawo lafiya,ka kula kar ka bari Khalid yayi tuƙin ganganci da kai dan ya saba ka ji”!?gyaɗa mata kai yayi yana tuno ranar da suka fita shi da Khalid ɗin irin tuƙin da ya rinƙa yi da shi…
Har ya juya zai tafi Hajja ta saka baki tana faɗin
“Ga takwara ta kawai ku tafi tare da ita ka rabu da Khalid itama tana buƙatar buɗe ido rabon ta da fita ya jima”!!bai juyo ba bare ya amsa shawarar Hajja,ita kuma fifi gaban ta ne ya faɗi ai da ta fita da shi gwara ta zauna a gidan,he is a matured man ba wani daɗin da zata ji ko ta fita da shi,ba sanin shi tayi ba kuma from all indications kamar moon face shi ya fi fitting nasa sama da murmushi toh ita ta yaya zata ji daɗin fita da shi?.tsintar kan ta tayi da faɗawa Hajja
“Ina da online review class by 10:30 da safen nan”!already 10:20am ne ssi ya dubi agogon sa ya ga lkc kawai girgiza kai yayi ya fice abin sa shi dama bai ɗau shawarar Hajjan da muhimmanci ba…
Kallon ta Ammy da Hajja suka yi,za su yi mgn ta tashi ta nufi hanyar sama,suka bi ta da kallo har ta shige,murmushin manya kawai suka yi suka ƙada kai musamman Hajja dake ankare da duk motsin su…
Juye juye kawai take ta yi a kan gadon tana jin yadda bugun zuciyar ta ke ƙaruwa sai dai bata san dalili ba..
Muryar Ammy ne ya saka ta tashi zaune ta dube ta,daga tsaye Ammy ta ce mata
“Baby mijin ki fita zai yi zuwa duba wani uncompleted building ɗin Abban su kuma ina tunanin sai dare zasu dawo dan ya matsu a kammala wurin kasancewar yanayin aikin sa ba sosai yake zama a nan ba kuma shi Khalid bai da wani isasshen lkcn zagawa zuwa wurin sai dai in shi mijin naki ya dawo sai ya tafi da kan sa,dan haks ina ga ki je ku gana kafin ya fita ba dawowa da wuri zai yi ba sai dare”!!abin mamaki abin dariya me ya sa Ammy ta sauya mata ne haka da yawa?kalmar “mijin ki mijin ki” duk ya addabe ta ta gaji da jin sa daga bakin Ammy sannan Ammyn ta daina bata kula ta musamman kamar yadda ta saba a baya yanzu sai dai sama sama in ta ɗan ɓata fuska sai ta rarrashe ta hakan bai hana anjima ta kuma janye jiki da ita ba…
Bata saba da yi ma Ammy musu ba sai kawai ta tashi ta nufi hanyar fita amma ta ji ƙarar abu kamar ana fetsa perf,juyawa tayi sai ta ga Ammy gab da ita tana fetsa mata turare tana murmushi,rasa ta cewa tayi sai itama ta maida mata murmushin daga haka ta fita abin ta…
A natse take takun ta har ta iso part ɗin nasa tayi sallama ta shiga,bata tsaya a waje ba ta ƙarasa ciki ta kuwa yi sa’ar samin sa a parlor yana zaune yana sipping wani abu a matsakaicin cup sai ta mai sallama ya amsa yana kallon ta..
Ganin yadda ya tsare ta da kallo sai ta gaida shi,abin sai ya ɗan bashi dariya but bai bayyana dariyar ba ya gyaɗa mata kai alamar ya ji kuma ya amsa..
Tana tsaye bata iya ce mai komai ba shi kuma bai yi offering nata kujerar zama ba,for a moment sai ya dube ta a fizge ya kawar da kai ya ce
“Lafiya”?sai ta dube sa cikin sanyin murya ta ce
“Eh”!!kallon ta yayi sai ya ƙyale ta tana tsayen shi kuma yana sipping abin kofin sai da ta gaji kuma ta zauna abin nata kamar har da yarinta a ciki ya faɗa a zuciyar sa,if not ta yaya mutum zai zo ya tsaya maka a tsaye ya ce ba komai ya kawo sa ba amma yana nan tsaye sannan yanzu ta zauna bai ce mata ya bata dama ba..
Muryar sa ne cikin sigar gar da gar babu wasa ya ce
“Ke,shekarun ki nawa”?sai tayi mamaki ta ɗago kai ta dube sa ta ga babu wasa a tare da shi kawai ta ce
“20”!!scoffing yayi na mamaki yayi tsammanin ta kai irin 25years ɗin nan ma dan mantawa yayi da lissafin sa yana ta ɗaukar ta to be a 25years old girl..
Ganin abinda yayi sai ta ayyana a zuciyar ta hala ta girma ne da yawa shi ya sa ya bata wannan look ɗin mamakin sai ta ji ina ma 19 ta ce mai dan ya san ba babba ba ce ita ɗin..
Bata san ya aka yi ba sai tsintar kan ta tayi da sha’awar tmbyr sa haka kawai bakin ta ya furta
“Kai fah”?sai ta ga ya kalle ta rai a haɗe yana ajiye kofin hannun sa,sai ta ji tsoro dan yanzu ta tuno abinda bakin ta ya furta..
Tashi zata yi sai ya umarce ta da ta zauna kar ta matsa,haka ta koma ta zauna sai ya kafe ta da ido har ta ji ta tsargu fiye da misali kamar ba zai ce komai ba sai ya ce
“Are u asking for my age”!?ya tmby yana ɗage gira ɗaya sama sai ta ji fargaba ya tsirga ta ta kasa amsa mata,yana kallon ta yana jiran amsar ta amma bata amsa ba sai ya murmusa ya ce
“Am 45”!wani irin firgita fifi tayi tayi saurin tashi tsaye tana rufe bakin ta idanu a waje ta dube sa shi kuma sai ya tsaya yi mata kallon mamaki menene na firgita?..
“What?me ya faru”?saurin girgiza mai kai tayi tana juyawa da zumar fita,ai ko ya taso ya juyo da ita da sauri suka fuskanci juna,hannun ta rufe da bakin ta har yanzu,hannun sa ya saka ya cire nata hannun daga bakin ta ya zama bata kare fuskar da komai ba..
Kallon juna suka tsaya suna yi sai da suka ɗau daƙiƙu sannan ya ce
“Me ya faru”!?cikin separate sentence ta ce
“Ba…ba..b..komai”sai ya kuma kallon ta sannan ya sake ta ta fita cikin sauri shi kuma ya tsaya hannun sa a ƙugun sa yana tunanin me ya sa ta firgita,bai sani ba amma yana mamaki..
Sallamar Khalid ne ya farkar da shi daga tunanin abinda fifi tayi sai ya juya ya ɗau wayar sa ya fito suka wuce..
A motar bai daina nemo dalilin da ya saka fifi yin abinda tayi ba haka Khalid ya rinƙa yi mai mgn amma bai bashi doguwar amsa hankalin sa na kan son samo dalilin reaction ɗin fifi..
Kawai sai hankalin sa yayi hitting nasa akan maybe shekarun sa da ya faɗa mata ne,yana wannan tunanin sai kawai ya hau yin murmushi shi kaɗai tun Khalid bai lura ba har ya fara ganewa ya rinƙa mamakin yayan nasa sai dai bai ce mai komai ba suka cigaba da tafiya..
Har suka kai inda zasu tafi suka yi abinda ya dace suka kamo hanyar dawowa around 6pm tunanin fifi da reaction ɗin ta bai daina bijiro mai ba kuma a duk sa’in da ya tuno ta toh fah dole sai ya murmusa shi dai Khalid yau ya ga ikon Allah..
Yanzu burin Marshall bai wuce su koma gidan lfy ba ya san yadda yayi Ammy ta sako ta zuwa dan ya turke ta a gaba ya tmby ta dalilin yi mai wannan abin ba alhalin ita ta mai tmbyr dan ya lura tana da tsoro sai dai kafiyar zuciya ya sa ba a cika gane tsoron nata ba,shi kuwa yau sai ya tsorata ta dan ya ga abin dariya indeed yarinyar na tattare da abubuwan ban dariya kuma yau yana son ganin iya inda nata kalar tsoron ya tsaya…