KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

“Sai da safe” ta ce mai tana mai tashi da sauri bayan ta ajiye mai coffee ɗin sa,shi bai ce mata komai ba haka ta fita abin ta yana mamakin kasa tsorata ta da yayi niyar yi..

Yana nan zaune kamar mintuna biyar da fitar ta sai ya kuma jin sallamar ta abin ya ɗaure mai kai,izinin shigowa ya mata sai ta shigo hannun ta riƙe da tray tana ɗan haki..
Kallon ta kawai ysyi sai ta fara mgn on her own
“Su Ammy sun rufe sashen su ina ta sallama ba a amsa ba na yi ta buga ƙofar mai entrance ba a amsa ba,kuma dare bai yi ba fah,pls ka kirawo min Ammy da wayar ka ta sa a zo a buɗe min ban fito da waya ta ba”!!mamakin courage ɗin ta yayi sai ya tsaya kamar ba zai yi wani abu ba daga bisani ya ɗau waya yayi kiran Ammy amma bata ɗaga ba,yayi yayi har ya gaji bata ɗaga ba,sanar da ita yayi Ammy ta kwanta sai ta roƙi alfarmar ya kira mata Hajja nan ma yayi ta kiran ba a ɗaga ba..
Hamma yayi ya dube ta yana observing trembling da jikin ta ke yi kamar marar gaskiya sai ya ce mata
“Duk sun kwanta sai dai in zaki kuma komawa ki duba”!!da sauri ta kalle shi tana tsoron kuma fita it’s alread past 9 ta yaya zata kuma fita ita kaɗai bai raka ta ba kuma bai da niyar raka ta.
“Ok?sai da safe”!!ya faɗa mata yana mai yin hanyar bedroom ɗin sa da sauri ta sauke tray ɗin abincin ta biyo bayan sa tana mai magiyar ya tausaya mata ya raka ta su koma..
Kamar ba zai juya ba sai kuma ya juya haka suka fito tare bayan ta ɗauki tray ɗin suka koma sashen su Ammy aka yi ta bugawa amma ba a buɗe ba,wani fargaba ne ya shigi fifi ya zata yi in su Ammy da gaske sun rufe ƙofar?ta kwana a ina?sai tayi saurin tmbyr sa
“Da gaske su Ammy sun rufe ƙofa ne”?kallon ta yayi yana tunanin anya shagwaɓa bata yi mata yawa ba kuwa tana ganin yadda yake ta ƙoƙarin ganin an buɗe ƙofar amma tana tmbyr sa wai da gaske an rufe ne.

Fasa cigaba da bugun yayi dan ko ina shitu ne daga shi sai ita a waje hakan ya sa ya juya yana faɗin
“Ina jin bacci ki zo mu tafi”!da mamaki ta ce
“Mu je ina”?kallon ta yayi ya amsa mata kai tsaye
“Sashe na in kuma kina iya cigaba da tsayuwar jiran buɗe ƙofar toh shikenan am out of here”!!ganin fah da gaske tafiyar sa yake yi kuma ko ƙarar tsuntsu babu shi a wurin sai ta ajiye tray ɗin a nan ƙasa ta biyo sa da gudu..
Hango shadow ɗin ta a bayan shi sai ya saka shi yin taƙaitacciyar murmushi ya girgiza kan sa ya cigaba da tafiyar sa..
Saurin cin mai a tafiyar ta yi sai suka zama suna tafiyar a tare amma babu mai ce ma wani komai..
Daidai sun zo apartment ɗim su Hamida kenan zasu wuce ita kuma ta leƙo dan shan iska because kasa baccin tayi abubuwa da yawa a zuciyar ta na damin ta,tana saka kai a balcony ɗin ta sai ta hango su suna zuwa,wani ras gaban ta ya bayar sai ta kuma fitowa tana kallon su har suka shige suka rufe ƙofar..
Ba ƙaramin ɓaci ran ta yayi ba wato da gangar su Ammy suka haɗa auren nan dan a ci mata fuska ko?in ba haka ba ita nata mijin yana nan yana bacci su kuma suna yawon su a tsakar gida.
Buge ƙarfen tayi da ƙarfi ta ma rasa me ke damin ta a yanzu kan ta kasa kawo mata komai yayi..
Tsaki ta ja ta koma ciki tana kallon mijin nata dake baccin sa cikin kwanciyar hankali..
Ya ta iya dole ta kwanta beside him tana mai ɗora kan ta a ƙirjin sa itama baccin ya fara fizgar ta tana son mijin ta amma a zahirin gaskiya kishin ƴar uwar ta ya gama rufe mata ido da bata ganin komai sama da fuskar fifi da mijin ta in a negative way.

Ko da suka shiga daga ciki duk tsoro ya gama dabaibaye fifi sai ya shiga ciki ya kawo mata blanket da pillow,bai tsaya jin komai daga gare ta ba yayi wucewar sa dan a gajiye yake bacci ke damin sa.
Haka ta kwanta bisa kujerar ta lulluɓe jiki tun tana shakka shakkar yin baccin har dai baccin ya sace ta ta bar kan ta tayi sa dan dama tana ji tsoro ke damin ta amma tunda ya tafi ta san ai ba zai fito ba..
Da wannan tunanin baccin ya ɗauke ta bayan tayi addu’ar yin bacci ta lulluɓe daga sama har ƙasa dan gudun wani abin ƙi…

Mamuh24

Cikin baccin ta ta rinƙa jin numfarfashin mutum a halin wahala da azaba,kamar a mafarki sai ta juya da nufin cigaba da baccin ta amma jin numfarfashin ya ƙi ƙarewa sai kawai ta miƙe da sauri tana mai yaye blanket ɗin..

Tashi tsaye ta yi ta fara bin kusurwa kusurwar parlorn tana bin inda numfashin ke fitowa,haka ta zaga kaf dama da hagu bata ji komai ba ga parlorn ba laifi yana da ɗan girma.

Dawowa da baya tayi zuwa bayan ta ta natsu nan ta fara jin asalin numfashin..

Da hanzari ta yaye curtain ɗin wurin sai ta ga door ne da sauri ta tura ta shiga tana ɗan kalle kalle Daga can cikin lulluɓe ta hango kan sa gabaɗaya karkarwa yake yi tsabar zazzaɓin da ya addabe sa..

Bazata iya ta tancewa ba amma haka kawau ta gan ta kusa da shi cikin halin damuwa da sanyin murya ta rinƙa tmbyr sa lafiya me ke damin sa..

Nishi yake saukarwa baice uffan ba

Sam baya jin ta ko kaɗan haka ta gaji ta rasa abin yi ga ɓarin jikin nasa bai daina ba sai ma lura da tayi da kamar convulsion ke son zuwar mai..

Ganin haka ya sa cikin sauri ta sauke hannun ta daga kan blanket ɗin da ya lulluɓe jikin sa ta nufi hanyar waje a ruɗe dan tsakanin ta da Allah bata san me zata mai ba kan ta kasa kawo mata komai yayi..

A firgice ta bar sashen tana tfy tana sauri kamar zata tashi sama da hanzarin ta ta ƙarasa sashen su Ammy.

Bugun duniyar nan ta yi amma babu amsa haka har ta gama bugunta gaji bata da yadda zata yi amma abin takaici babu wanda ya motsa bare a zo a buɗe mata ta shiga ta sanar da su abinda ke faruwa da Marshall..

Da ta gaji da bugun sai ta ji wani ɓacin rai ya ziyarce ta a zuciye ta bar wurin tana tafe idanun ta na kawo ruwa tana ayyana cewa yanzu da mutuwa ce ta zo haka nan za a bar ta ta mutu kenan..

Sosai hankalin ta ya tashi,bacin su ammy duk suna sane kuma sunji bugun amma dan su cusa mata dawainiyar aurenta yasa suka ki amsa ta..

Tana dawowa sashen Marshall bata tsaya ko ina ba sai cikin bedroom ɗin sa da yake kwance,yanzu ma ɓari ya ninka na ɗazu da ta fita ta bar sa yana yi..

Wani abu ne ya faɗo mata a rai sai ta tashi kai tsaye ta nufi hanyar parlor,da kan ta ta binciko inda kitchen yake ta samo shi tayi tafiyar ta ciki Gas ce mai kai takwas sai ta nemo portable pot wanda yake sabo fil cikin kwala alamar kayan nata ne da Ammy ta siyo mata..

Wanke pot ɗin ta yi ta zuba ruwa ɗan daidai misali ta ɗora bisa gas ɗin ta zauna zaman jiran yayi zafi dan ta san ruwan in ta saka a electric kettle ba zai yi sauri ba ita kuma yanzu a uzurce take..

Tagumi tayi Tana jiran ruwan yayi zafi tana kuma nazarin kalaman Marshall ɗin na ɗazu da yake mata gorin babu abin da ta sani ta yi dan kan ta sai wanda Ammy ta ce ta yi..Abin na ta taɓa mata zuciya sai kawai hawaye ya zubo mata ta saka hannu ta goge,lallai kalaman sa sun farkar da ita daga bacci da take yi na komai bata iyayi dan kan ta sai wanda aka saka ta yi ko bari..

Aranta tace Ga tabbaci nan an kuntata ma yar uwantan akanta bata gane ba gashi a gaban ta mutum na rawar sanyi amma ta kasa aiwatar da komai ta fita nemar taimakon wasu

tuno kalaman sa ya sa ta ƙarfafawa kan ta dajin dan dolen ta wasu lokutan kai da kan ka zaka rinƙa aiwatar da abubuwa ba sai an saka ka ba..

Lallai a rayuwa kana buƙatar aboki na gari wanda zai rinƙa ɗora ka ko ya nuna maka asalin gaskiyar rayuwar ka,rashin mutumin da zai rinƙa tantance maka zaƙi da ɗacin rayuwar ka asara ce babba kuma tangarɗa ne a gare ka na mutum mai hankali da nazari…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button