KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Ƙarar zubar ruwa ta ji sai tayi firgigit ta dawo daga tunanin da ta faɗa,kai duban ta tayi ga ruwan da yake tafarfasa tayi saurin kashe gas ɗin..
Da yake hankalin ta ya rarrabu kashi daban daban kawai sai ta kai hannu directly ta riƙo handle na pot ɗin da niyar juye ruwar Ai kuwa tana taɓawa ta ji wani irin zafi ya ratsa ta har kan ta da sauri ta cire hannun ta tana yarfewa,sai a sannan ta dawo hayyacin ta bayan wasu seconds ta nemo pot holder mai laushi ta riƙe hannun pot ɗin ta fara juye ruwan a wani ƙaramin cup ɗan daidai sannan ta juye sauran a wani bowl din cikin nitsuwa..
Mayar da pot ɗin ta yi saman gas plat ɗin ta juya ta fara nemo kayan tea wayanda bata gani ba,ta dai san ba yadda za’a ce bai da su amma rashin sanin inda zata gan su ya sa ta hau dube dube..
Da ta gaji sai tayi saurin ɗagowa da niyar fita zuwa sashen Ammy wai ta tmby ta ta bata kayan tea..
Tunowa da tayi da abinda Ammy ta mata na ƙin kula ta sai ta dawo da baya kuma ta riga ta yi ma kanta alƙawarin yau babu ruwan ta da wani duk abinda ta ga ya dace shi zata rinƙa yi tunda ba ƙaramar yarinya bace ita a hakan aka mata aure kuma kula da Marshall dake a matsayin miji ya zama nata
Haka nan ta ɗauko cup da bowl ɗin ta fito ta nufi cikin ɗakin ta same sa gwanin tausayi rawar sanyin bai daina ba lallai ba ƙaramin zazzaɓi ke damin sa ba in har tun ɗazu yake ta jin zazzaɓin amma ya daure ya raka ta sashen su Ammy suka rinƙa buga ƙofa tabbas ya kokarta..
Tana ajiye ruwan zafin ta dawo kan gadon tana kallon sa cikin tausayawa ta saka hannu a hankali ta ɗan yi ƙasa da blanket ɗin tana ce mai
“Tashi ka sha warm water it will help u”!!
kasa tashin yayi sai da ta taimaka masa ya tashi da ƙyar,ya jingina da gadon yana rawar sanyin da sauri ta ɗauko cup ɗin ta kawo kusa da bakin shi tana mai sannu tana saka mai ruwan..
Sipping kaɗan yayi ya ɗago kai sai tayi saurin mayar mai da kofin bakin sa tana girgiza mai kai tabbacin wannan da ya sha bai isa ba..
Haka yayi ta sipping warm water ɗin nan har ya ƙare,sai ta ajiye cup ɗin tana hango zufar dake ɗan keto mai.
Tmbyr sa tayi inda bathroom yake ya nuna mata da hannu ta tashi ta shiga,bata da natsuwar ta dan haka bata tsaya kallon toilet ɗin ba ta nemi towel kawai..
Wasu jerin towels ta hango kusan biyar a hangers sai ta kai hannu ta ɗau ƙaramin ciki da mai bi mai ta fito da ɗan saurin ta..
Hijabin jikin ta na damin ta sai tayi tunanin cire sa tunda aiki sosai zata yi yanzu.. .
Ba tare da wani tunani ba ta cire ta ajiye a gefe sannan ta dawo gare sa tana mai ɗaukar zuwan dake bowl ɗin ta zauna bisa gadon gefen sa ta tsoma towel ɗin cikin ruwan ta matse ta ɗora mai a saman goshin sa..
Take yayi responding dan sai da ya nuna sabida ƙame jikin sa yayi,hakan ya bata damar cigaba da maimaitawa ɗin har ruwan ya salamce sannan ta sauke ta ajiye a ƙasa ta dawo gare sa tana kallon sa yana bata tausayin da bata san na menene ba…
“Ina kayan tea ɗin ka in haɗa maka ka sha tunda dare yayi babu abinci a nan”!!
kallon ta yayi da idanun sa dake nuna zazzaɓin sa sai ya kasa ce mata komai illa ɗan kwantar da kan sa da yayi yana kallon ta..
Ganin kamar bacci yake ji sai ta ƙyale sa dan ɓarin jikin ya tsaya sai zufar da yake ɗan yi..
Can cikin damuwa tace”Ka kwanta kar wuyar ka yayi ciwo ba pillow kuma position ɗin nan bai yi ba”bai ce komai ba still tazo ta tallafo sa da taimakon ta ya kwanta tayi supporting nasa kan da two pillows on both sides ɗin sa..
Bata tashi daga kan gadon nan ba sai da ta ga ya fara bacci sannan ta tashi ta zauna bisa side drawer ɗin gadon cikin rasa me zatayi tunani akai..
A yanzu ne take ƙare ma ɗakinsa kallo take yaba kyawun sa da tsarin sa kuma sai a yanzu ta gane bata da hijabi ajikinta sannan hankalin ta ya kai ga hala ganin bata da hijabin ne ya sa yake ta kallon ta dazu..
Saurin ɗauko hijabin ta yi ta maida tana mai komawa inda take zaune lokaci zuwa lokaci takan kalle sa har ta leƙe sa ta ji tausayin sa ya kuma kama ta..
Tana ta wannan abin ne bacci ya ɗauke ta ta jingina tana yi haɗe da ƙanƙame jikin ta sosai kamar mareniya.
Asubahin farko Khalid ya farka daga bacci sai ya ga Hamida kwance jikin sa tana bacci but daga ganin ta ya san baccin ɓacin rai take yi,daga lokacin da suka yi aure zuwa yanzu da suka shafe watanni sama da huɗu tare ya gama karantar matar nasa,ya san komai da ya shafi halayyar ta ko da kallo ta mai ya san fassarar kallon nata haka a gefe ɗaya in aka dawo ga rayuwar ta da mu’ammalar ta da ƴar uwar ta,babu abinda bai sani ba,irin tsatssaurar kishin ƴar uwar ta da ta sakawa zuciyar ta ba ƙaramin damin sa yake yi ba,babu wani abu sabo ba dangane da Hamida da bai sani ba akan alaƙar ta da fifi..
Ajiyar zuciya ya sauke tuno da yadda yake son fara aiwatar da nufin sa ga matar nasa dan ya wanke mata zuciyar ta akan halayyar da ta ɗorawa kan ta na kishin yar uwar tawainiyar ta..
Kissing forehead ɗin ta yayi yana shafa fuskar ta sai ta buɗe ido a hankali tana kallon sa..
Bata ce komai ba haka bata motsa ba sai shi ne ya soma tada mgnr..
Yace “Goodmorning wify hw was ur night”?kallon sa tayi tana murmushi sannan ta amsa gaisuwar nasa sai ya kuma rungume ta yana kallon ta kamar zai hadiyeta har sanda ta ce mai
“Wat”?murmushi yayi yana kallon ƙwayar idanun ta daga bisani ya amsa mata da cewa
“I just naturally luv my wife kuma ina son tasan zan iyayin komai akanta and i promise to protect her to my last breath,hamida kiban dama,inshaAllah zan cike miku wani gurbin da ba kowa zai iya ba i wll replace back ur lost love for many years,wannan alkwari ne from me to u”!!
wani sanyi hamida ta ji a ran ta da saukar waɗannan kalamai nasa sai ta kuma rungume sa tana faɗaɗa fara’ar ta bata dai ce komai ba amma ya san kalaman nasa ya ratsa ta sai ya cigaba..
“Na san kin rasa soyayyar iyayen mu daddy,Ammy,Hajja and…ur sister’s care but ina so ki sani ni mijin ki Khalid na maki alƙawarin cike maki gurbin waɗannan so ƙauna da kulawar gata da duk wani abu da kika rasa da zuciya ɗaya,dan a kan ki na yarda in zama wawa in hakan zai faranta miki,i love u hamida..ina so ki yarda da ni ki bar min amanar yardar ki ni kuma zan baki mamaki da irin sigar ƙauna da soyayyar da zan nuna kuma in gwada miki”!!
sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tana jin sabon son mijin ta fiye da kowa haka nan wani bangaren tana jin tsananin kishin Mufida mai zafi a ran ta dan idanun ta rufewa yake da kishin ƴar uwar tan da ya riga ya mata mugun shiga..
Kamar zata sauke hawaye tace””kamun alkawrin zaka kasance dani khalid bazaka ci amana ta ba !gyaɗa mata kai yayi yana mats murmushi mai ƙayatarwa haɗe da kai mata direct french kiss as good morning kiss..
Hakan ya tabbatar mata da cewa mijin nata a shirye yake, ever ready to protect and cherish her..
Sai da aka kira sallah sannan suka tashi shi da ita,tare suka yi alwalar suka fito shi ya sauya kayan sa zuwa jallabiya ya fita zuwa masallaci ita kuma tayi nata sallar a ɗaki…
Ko kafin ya dawo har ta yi yan kimtse kimtsen ta ɗin ta ta masu breakfast tayi wanka ta fito cikin ƙananan kaya da maroon kimono kan ta ta yafawa ƙaramin mayafi ta ɗan yi kwalliya ta hakimce saman dinning ɗin su tana latsa wayar ta..