KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Bai shigo ba sai misalin 8:30am sakamakon zama sashen Ammy da yayi suka gaisa ya kuma kai ziyara wa Hajja wacce ita ta ja sa da hira har ya daɗe..
Da shigar sa ta tare sa abin sai ya burge sa kenan kalaman sa gare ta na safiyar yau yayi tasiri a zuciyar ta lallai da haka zai rinƙa sanyaya mata zuciya har yayi nasarar yaƙice mata kishin ƴar uwar ta a zuciyar ta ya gyara alaƙar su..
Brush kaɗai ta bar sa yayi sai wanka sannan suka dawo suka fara cin abincin nasu cikin so da ƙaunar juna,yana iya faɗin rabon sa da fuskantar hakan daga gare ta wanda ba komai ya sa ta rikiɗe masa ba sai kishin fifi da ta sakawa ran ta..
Da suka kammala shi ya kwashe kayan tunda yana hutu baya on call sai ya shashance akan matar sa through out yau babu inda ya tafi yana tare da ita soyayya yake gwada mata na fitar hankali so yake ta gama yarda da shi har zuciyar ta dan hakan zai taimaka ta cire batun fifi daga ran ta dan suyi rayuwar su..
Yau Komai tare suka yi sa abin gwanin sha’awa,duk da wannan abin da Khalid ya rinƙa yiwa Hamida bai hana ta ware seconds 30 ƙwarara ba wurin son ganin baƙin Mufidah da kasawar ta,haka kawai ta rinƙa tursasa zuciyar ta da kan ta kan sai ta samo wani abu da Mufida ke lacking da zata rinƙa alaƙanta ta da shi,sai dai bata samu dama sosai dan da zarar zata fara tunanin abin sai mijin ta ya ɗau hankalin ta..
Ko da dare yayi bai bar ta tayi zaman tunanin ba ya rinƙa gaya mata sunayen wuraren da yake son su tafi a washegari sannan yana hiran yana showering nata da kisses da tickling dake saka ta dariya,da haka har tayi bacci a jikin sa shima yayi baccin cikin farincikin ganin first move ɗin sa an samu nasara.
A ɓangaren su fifi da Marshall kuwa da safe yayi kamar an tsungule sa ya farka ya buɗe idon sa sai ya ga haske daga curtains,juyowa yayi sai ya ga sleeping fifi,ƙura mata ido yayi yana ta kallon ta yana tunanin abinda ya faru a daren jiya,mamaki ya rinƙa yi yana ayyanawa hala Ammy ce ta saka ta yin aikin..
Ɗan taɓe baki yayi ya yunƙura ya tashi zaune yana hamma,ya ɗan sami ƙarfi kaɗan dan dole sai ya haɗa da pills but normal emergency care da ta bashi jiya ma ya taimaka masa.
Zaman kallon ta yayi yana ƙarawa sai da ta motsa a hankali sai yayi saurin kawar da kan sa yana tari..
Tarin nasa ne ya ƙarasa farkar da ita ta tashi tana kallon sa a firgice tana tmbyr me ya same sa sai ya nuna mata hanyar window..
Nan ta kai duban ta sai ta ga haske da sauri baki buɗe ta sauko daga kan drawer ɗin tana mai zuwa kusa da shi..
“Bamu yi sallah ba safe yayi”!!kallon ta yayi sai ta kawo hannu tana son taimaka masa ya tashi ba musu ya karɓi taimakon nata,suka shiga toilet da ƙyar yayi alwalar suka fito ta nemo darduma bayan ta tmby sa inda yake ya nuna mata. …
Ta shimfiɗa mai ta miƙo mai jallabiya ita kuma ta koma ciki tayi alwalar da sauri ta fito lkcn har ya fara sallah sai ta tada nata iƙamar a ɗan nesa da shi..
Da suka idar sai tsaya jiran sa har ya shafa addu’ar sa,kawai ta ji ya kamata ta gaida sa sai ta yi ƙasa da kai..
“Ina kwana”!mamakin ta duk ya gama cika sa amma ya amsa mata sai ta kuma faɗin.
“Ya jikin naka”!gyaɗa kai yayi yana faɗin
“Alhamdulillah”fatar samin lfy ta mai tayi shiru sai can shi ya ce
“How was ur night”?kallon shi tayi ta saukar da kan ta ƙasa sai yayi murmushi dan ya fi kowa sanin ya night ɗin nasa ya kasance..
Da taimakon ta ya koma ya kwanta ita kuma ta ce mai tana zuwa..
Fitar ta bata zarce ko ina ba sai sashen su Ammy..
Ko da ta shiga sai ta gan su zaune gaida su tayi kawai ta sanar da su Marshall ba lfy daga haka ta haura ta ɗau wayar ta ta fito bayan wasu minutes har ta sauya kayan jikin ta zuwa simple gown mai ɗan kauri sbd yanayin sanyi na garin..
Mamakin ta suka ji ganin bata yi shagwaɓa ko ta tsaya tmbyr su dalilin ƙin buɗe mata ƙofa ba jiya wanda intentionally suka yi hakan duk wai dan ƙaunar ta da Marshall ya girmama..
Dawowa sashen Marshall tayi ta same sa kwance sai ta buƙaci ya bata numbern family doctor ɗin su tana so ta kira sa ya zo ya duba sa..
Miƙo mata wayar yayi bayan ya fiddo da numbern sai ta kwasa a wayar ta tayi dialing,bayan an ɗaga ne suka gaisa ta mai bayanin abinda ke damin Marshall but kasa kiran sunan sa tayi sai cewa take “yaya soldier wai dan doctorn ya gane da wanda take referring..
Shi dariya ta bashi har ta sauke wayar ta miƙo mai yana kallon ta sannan daga bisani ya ce da ita
“Ammy told u to do this right”!?shiru ta mai tana kallon sa,sai ya girgiza kai yayi shirun shi ma..
Ba jimawa Ammy da Hajja suka zo duba sa sai a nan yake jin wai rashin lafiyar nasa yanzu suke ji daga bakin fifi abin ya bashi mamaki wato ita ce dan kan ta ta ji tayi hakan kenan?lallai ashe tana da tunani mai zurfi ba yadda yayi tsammanin ta ba..
Suna zazzaune doctor ya zo ya duba sa ya mai abinda ya dace Ammy ta koma ta kawo masu abinci dan ta lura kamar fushi fifi ke yi da su ganin yadda duk ta maida hankalin ta ga mijin ta sai suka yi ta mamaki haka shima Marshall ɗin sai da suka jima sannan suka tafi ita kuma ta maida hankalin ta gare sa ta bashi magani yana karɓa yana tunanin ɗabi’un ta..
Ita kam ko a jikin ta kula da shi ta saka a gaba a matsayin abunda ya dace ba tunanin abinda Ammy take mata ba..
Ranar dai ta ƙauracewa su Ammy a nan part ɗin ta kwana dan bashi kula ta musamman kamar yadda doctor yayi ta nanatawa wanda tun su Ammy na damuwa har suka daina suka haƙura suka zuba mata ido.
Chan cikin dare tana kwance a parlor kamar jiya sai ta rinƙa tunanin rayuwar ta da na ƴar uwar ta Hamida numfasawa tayi ta juya tana mai cigaba da tunanin ta,rasa yadda aka yi ta kasa fahimtar halin kuci da zafi da Hamida ta shiga ciki tun yarintar su tayi har kawo girman su..
Ji tayi kwata kwata bata kyautawa kan ta ba ita tana ta kwace soyayya Hamida na can cikin damuwa da rashin kulawa wai amma bata taba sani ba,a duk lkcn da ta tuno wannan abin ran ta kan sosu ba kaɗan ba..
Daga wannan ranan Ta ma kan ta alƙawarin safiyar gobe a sashen Hamida zai mata tunani tayi da hala halin da take ciki rashin sauraron ta da Hamida bata yi ne ya sa take fuskantar wannan abin hakan ya sa ta yanke zuwa duba ta gobe ita ko zagin ta Hamidar zata yi ta yi in dai zata furta mata kalmar yafiya toh ita tayi alƙawarin cike mata gurbobin da ta rasa na soyayya a rayuwar ta..
Da safe bayan ta gama abinda zata yiwa Marshall ta ce mai tana zuwa sai bai ce mata komai ba dan sabbin ɗabi’un nata na mai shammaki..
Gaban ta na faɗuwa ta iso part ɗin su Hamida ta tsaya ta rasa ya zata yi sai dai ta ɗan natsu ta yi sallama a hankali,sau uku tana yin sallama sannan aka zo aka buɗe ƙofar wanda fuskar Khalid ne ya bayyana..
Da mamaki ya gaida ta sai itama ta gaida sa tana tmbyr sa ko Hamida na ciki,cikin tausayin ta ya amsa mata da eh..
Hamida dake tsaye bakin kitchen tana rige rigen ɗora breakfast ita da Khalid da kamar competition ne sai kawai ta gan sa tare da fifi..
Take ta ɗaure fuska ta haɗe rai,yana kallon sauyin yanayin ta fifi kuwa da zuwa tayi saurin ƙarasawa gare ta murya na rawa ta buɗe baki zata yi mgn sai Hamida ta kawar da kan ta gefe..
Kallon ta fifi tayi
sai ta haɗiye wani abu mai ɗaci ta kuma yunƙura ta ce
“Ina kwana Hamee”!wani kallon ƙiyayya Hamida ta watso mata ta ja tsaki ta juya zata tafi sai muryar fifi ya mata amo a kunne da ɗan ƙarfi